Jump to content

La Fata Illa Ali

Daga wikishia


La Fata Illa Ali(Larabci:لا فَتَی اِلَّا عَلِی) wani kirane da yazo daga sama daga ɗaya daga cikin mala’iku dan bayyana darajar Imam Ali (a.s.) [1] Dogaro da ruwayar da tazo daga shi'a da sunna cewa , a yaƙin uhudu, lokacin da imam Ali yazo yake kare annabi daga harin da ake kai masa , sai aka ji wata murya daga sama tana cewa “Babu takobi sai Zulfiƙar, kuma babu Saurayi mai jini a jiki sai Ali ”[2] A wasu hadisai ance wanda yayi wannan kiran daga sama shi ne Jibrilu [3] a wasu hadisai kuma yazo cewa wani Mala’ika ne mai suna Ridwan[4], wasu kuma sunce ba'a bayyana sunan mala'ikan da yayi kiranba [5]] A wasu rahotannin, an kawo cewa wannan lamari ya farune a yaƙin Badar [6] ko Khaibar [7] Allama Amini (ya rasu: 1390 AH), marubucin littafin Al. -Ghadir, ya kawo hadisai masu yawa a cikin wannan mahallin, ya yi imani da cewa wannan lamari ya faru sau da dama [8].Kamar yadda wasu ruwayoyi suka zo, Sayyidina Ali (AS) ya kawo wannan jumla wajen bayyana falalarsa[9].

Kamar yadda Allama Amini ya ce, malaman ilimin hadisi sun yi ittifaƙi a kan wannan hadisi [10] A cikin littafin Kefayatuɗɗalib fi Manaƙib, na bayanin falalolin Ali Ibn Abi ɗalib, ɗaya daga cikin littattafan Ahlul-Sunna (Rubutashi: ƙarni na 7 bayan hijira ) An samar da babi mai zaman kansa a cikin ruwayoyi daban-daban na wannan hadisi kuma an ce Ahlul hadis sunyi ittifaƙin ingancinsa [11] Amma a cewar wasu marubuta Ahlus Sunna, wannan lamari na ɗaya daga cikin hadisai da aka ƙirƙira[12] kuma sun ce Ibn Taimiyyah. ya ɗauki wannan rahoto a matsayin ƙarya.[13]

An wannan jimla a kan takubba masu yawa [14] Mawaƙa irin su Sa'adi, [15] Khajawi Kermani [16] da Aɗɗar Naishaburi, [17] sun rubuta ƙasidu daban-daban tare da wannan ibarar ta la fata illa Ali, Kamar yadda Allama Amini ya ce, Hassan bin sabit ma ya rubuta waƙaa kan haka da izinin Annabi (SAWW)[18].

Bayanin kula

Nassoshi