Ayar Wasila
| bayanan aya | |
|---|---|
| sunan aya | Ayar Wasila |
| akwai shi cikin sura | Ma'ida |
| lambar aya | 35 |
| juzu’i | 6 |
| bayanan abin da yake ciki | |
| wurin sauka | Madina |
| maudu’i | Aƙida |
| game da | Tsani da madafa zuwa ga Allah |
| saura | Kira zuwa taƙawa da jihadi |
Ayar wasila, (Larabci: الآية الخامسة والثلاثون من سورة المائدة) suratul ma'ida aya ta 35, aya ce da take bayyana samun rabauta ya dogara da sharuɗɗa uku: Taƙawa, neman wasila (Tsani) zuwa ga Allah da jihadi cikin tafarkin Allah.
Abin da ake nufi da wasila shi ne duk wani aiki da yake zama sababi da sanadin samun kusancin bawa zuwa ga Allah. Malaman tafsiri tare da jingina da riwayoyi, sun lissafa adadin abubuwa da suke amsa sunan wasila, daga jumlarsu akwai aiki nagari, tawassuli da Annabi da Ahlul-baiti da kuma rantsuwa da Allah da muƙaminsu da matsayinsu.
Nassi Da Tarjamar Ayar
Aya ta 35 suratul ma'ida wace aka fi sani da ayar wasila.[1] cikin wannan aya an yi amfani da kalmar wasila, kuma domin tabbatar da halascin tawassuli an jigina da wannan aya.[2]
A cikin wannan aya taƙawa, wasila da jihadi cikin tafarkin Allah an bayyana su matsayin hanyoyi uku na samun ceto da rabauta.[3] A ra'ayin ba'arin malaman tafsiri, jihadi a cikin wannan aya ya haɗo da jihadi tare da kafirai da kuma jihadin yaƙar biyewar son zuciya duka suna daga abubuwa da ake kira wasila.[4] Samfuri:Pull ƙuote
Abin da Ake Nufi Da Wasila
Ana kiran duk wani aiki da yake zama sababi da sanadin samun kusanci zuwa ga Allah[5] Allama Ɗabaɗaba'i daga malaman tafisiri na Shi'a, ya fassara wasila da duk wani nau'in alaƙa ta ruhaniyya tsakanin mutum da ubangiji wace take samuwa ta hanyar ibada kuma ilimi da aiki ana lissafa su abubuwan da suke lazimtar wannan alaƙa.[6]
Abubuwa Da Suke Kasancewa Wasila
A cikin riwayoyin Shi'a, Annabi,[7] Imam Ali (A.S),[8] da Ahlul-Baiti[9] an ambace su a matsayin wasila da tsani zuwa ga Allah, a cikin Tafsirin Al-Amsal tare da jingina da wata riwaya daga Imam Ali (A.S),[10] ayyuka misalin sallah, azumi, ciyarwa, sadaka, ambaton Allah, hajji, umara, imani da Allah da Annabi, jihadi da sadar da zumunci ana lissafa su daga wasila.[11] Haka nan ceton Annabawa, Imamai da salihai, biyayya gare su da rantsuwa da Allah albarkacin muƙamansu da matsayinsu (Musamman ma Annabi da Ahlul-Baiti) suma suna daga cikin wasila zuwa ga Allah.[12]
A cewar marubucin Tafsir Aɗyabul Bayan, wasila tana haɗowa da dukkanin aƙidu, kyawawan halaye da ayyuka nagari da Kur'ani, Annabi (S.A.W), Ahlul-Baiti ko muƙamansu da matsayinsu, kuma suna kasancewa mafi cikar abin da yake amsa sunan wasila tsani zuwa ga Allah.[13]
Bayanin kula
- ↑ Dubi Arefi da Najibi,Barrasi Taɗbiƙi Aye Wasila Az Nazre Manabi Tafsiri Fariƙaini, shafi. 59, taken labarin.
- ↑ Misali, duba Subhani, Ayineh Wahabiyyat, Ofishin Daba’ar Musulunci, shafi na. 168.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsire Namune, 1371SH, juzu'i. 4, shafi. 364.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1390ƙ, juzu'i. 5, shafi. 328.
- ↑ Tabarsi, Majma' al-Bayan, 1372SH, juzu'i. 3, shafi. 293; Fakhr al-Razi, Al-Tafsir al-Kabir, 1420ƙ, juzu'i. 11, shafi. 349.
- ↑ Tabataba'i, Al-Mizan, 1390ƙ, juzu'i. 5, shafi. 328.
- ↑ Dubi Arefi da Najibi, Barrasi Taɗbiƙi Aye Wasile Az Nazre Manabi Tafsiri Fariƙaini, shafi. 66.
- ↑ Bahrani, Al-Burhan, 1415ƙ, juzu'i. 2, shafi. 292.
- ↑ Kashani, Tafsir al-Mu'in, Ayatullah Mar'ashi Library, juzu'i. 1, shafi. 290.
- ↑ Ibn Shu'bah Harrani, Tuhf al-Uƙol, 1404ƙ, shafi na 149.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsire-Namune, 1371SH, juzu'i. 4, shafi. 364.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsire-Namune, 1371SH, juzu'i. 4, shafi. 366.
- ↑ Tayeb, Atyabul Al Bayan, 1378SH, juzu'i na 4, shafi na 375.
Nassoshi
- Ibn Shu'bah Harrani, Hassan bn Ali, Tuhaf al-Uƙol, Ali Akbar Ghaffari, ƙum, Mawallafar gidna Musulunci, 1404ƙ.
- Bahrani, Sayyid Hashim bn Sulayman, Al-Burhan fi Tafsir Al-ƙuran, ƙum, Gidauniyar Bissat, 1415ƙ.
- Subhani, Ja'afar, A'yineh al-Wahhabiyyah, ƙum, Mawallafar gidan Musulunci, babu kwanan wata.
- Tabataba'i, Muhammad Hussein, Al-Mizan fi Tafsir ƙur'an, Beirut, Wallafar Gidauniyar Al'alami, 1390ƙ.
- Tabarsi, Fadl ibn Hassan, Majma' al-Bayan, Tehran, Mawallafar Nasser Khosrow, 1372SH.
- Tayyib, Abdul Hussein, Atyib al-Bayan fi Tafsir al-ƙuran, Tehran, Mawallafar Islam, 1378SH.
- Arefi, Mohammad Yunus da Mohammad Ali Najibi، «بررسی تطبیقی «آیه وسیله» از نظر منابع تفسیری فریقین», (Bincike na kwatantawa "Ayar wasila" daga mahngar ɓangarori biyu) Karatun kwatankwacin Alƙur'ani da Hadisi na 23, A lokacin sanyi 2022M.
- Fakhr Razi, Muhammad bn Omar, Al-Tafsir al-Kabir, Beirut, Mawallafar Dar Ihya al-Turat al-Arab, 1420ƙ.
- Kashani, Muhammad ibn Murtaza, Tafsir al-Mu'in, wanda Hossein Dargahi da Mahmoud Mar'ashi suka yi bincike, ƙum, Laburare Ayatullah Mar'ashi Najafi, babu kwanan wata.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namune, Tehran, Mawallafar Darul Kutb al-Islamiya, 1371SH.