Ayar Amanar Rasul

Daga wikishia

Ayar Amanar Rasul (Larabci: آية آمن الرسول أو آيتا آمن الرسول) ko kuma ayoyi biyu na amanar rasul, ayoyi ne waɗanda suke cikin suratul baƙara, su waɗannan ayoyi guda biyu suna nuni kan imani da Allah da gasgata Annabawa da imani da ranar lahira da kiyaye haƙƙi na bayin Allah, da kuma imani na cikin zuciya da biyaya a aikace ga muminai da kuma gafara da kuma ɗorawa baye abin da yafi ƙarfin su. Kuma littatafai na ahlus-sunna da shi'a suna ƙarfafa karanta su kamar yadda ake karanta su a masallatai bayan sallar Magariba da Isha'i.

Nassin Aya

آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنزِلَ إِلَيْهِ مِن رَّبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ ۚ كُلٌّ آمَنَ بِاللَّـهِ وَمَلَائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّن رُّسُلِهِ ۚ وَقَالُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا ۖ غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ ﴿٢٨٥﴾ لَا يُكَلِّفُ اللَّـهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا ۚ لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ ۗ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْرًا كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِنَا ۚ رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلْنَا مَا لَا طَاقَةَ لَنَا بِهِ ۖ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا ۚ أَنتَ مَوْلَانَا فَانصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ



286


Falala da kuma abin data ƙunsa

Aya ta 285 da 286 a cikin suratul baƙara ana kiransu da ayar amanar rasul, sabo da sun fara da kalmar amanar rasulu.[1] an rawaito ruwayoyi da yawa a kan falalar wannan ayoyi guda biyu a litattafai na shi'a,[2] da ahlus-sunna,[3] misali kamar yadda aka rawaito daga Annabi (s.a.w), cewa wannan ayoyi guda biyu suan daga taskokin Allah a ƙarƙashin al'arshi, Allah ya bawa annabi Muhammad (s.a.w).[4] Sannan Mustahabi ne mai ƙarfi a karanta su a cikin sallah ta nafila.[5] da ƙarshan dare kafin bacci.[6]

An rawaito ruwaya a litatafan ahlus-sunna. daga abdullahi bin umar daga annabi (s.a.w) cewa karanta waxannan ayoyin guda biyu bayan sallar Magariba da Issha yana wadatarwa akan sallolin nafilar dare.[7] Saboda haka ne ake karanta su a wasu masallatai bayan sallar Isha'i.[8]

sayyid kutub malamin tafsiri ɗan ƙasar Masar ya yi imani cewa an taƙaice suratul baƙara da hadafinta abin nufi saƙon da ake so a isar a cikinta a cikin waɗanna ayoyi guda biyu na Amanar rasul, kamar imani da Allah da Mala'iku da Annabawa da litattafai da ranar alƙiyama da neman gafara daga Allah maɗaukaki.[9] wannan al'amari yana tabbatar da cewa waɗannan ayoyi guda biyu ana la'akari da cewa suna ɗauke da ilimi na muslinci da aƙida kuma sune ayoyin da Baƙara ta fara da su.[10]

Sha'anin Sauka

Amma dangane da sha'ani saukar wannan aya, lokacin da wannan ayar ta sauka, (وَإِنْ تُبْدُوا ما فِي أَنْفُسِكُمْ أَوْ تُخْفُوهُ يُحاسِبْكُمْ بِهِ اللهُ) Ma'ana idan kuka bayyana abun da yake cikin rayukan ku ko kuka ɓoye shi to fa Allah ya na sane da shi kuma zai yi muku hisabi da shi ranar gobe ƙiyama.

Sai wasu daga cikin Sahabbai suka tsorata da maganar hisabi, sai suka cewa Annabi: babu wani mutum a cikin mu face yana da wasiwasi shaiɗan a cikin zuciyar shi, sai wannan aya ta amnar rasul ta sauka tana bayyana hanyar gaskiya ta imani, da yadda ake ƙasƙantar da kai da neman gafara da ganawa da Allah da kuma miƙawuya ga al'amarin Allah maɗaukaki.[11]

Tsokaci A Kan Tafsirinta

Akwai tsokacin da malaman tafsiri suka yi akan ayar Amanar rasul kamar haka:

  • Haƙiƙa muminai sun yi imani da abin da manzanni suka zo da shi, kuma basa banbanta wani akan wani wato sun yi imani da su dukkansu.[12]
  • Kuma su Annabawa sun yi imani da abin da aka saukar musu daga ubangijinsu, basa shakka akan abin da suka yi imani akan shi, kamar yadda suka yi imani da shi, wato abin da aka saukar musu da shi kafin kowa, kuma sun nemi tsayawa akan shi.[13]
  • Allah ba ya ɗorawa da ɗanfarawa mutane abin da ya fi ƙarfinsu, sabo da haka hukunce-hukuncen addini za a iya fassarasu ko dabaibaye su da irin wannan ayar.[14]
  • Za a iya kafa hujja da kalmar Sami'ina da Aɗa'ana kan cewa muminai suna aiki da abin da ya haukansu daga zuciyarsu da kuma a aikace, abin nufi sun yi imani har cikin zuciyarsu da biyayya a aikace.[15]
  • Waɗannan ayoyi guda biyu suna magana a kan haƙƙin Allah kan mutane da kuma haƙƙin mutane kan Allah, Ibada haƙƙin Allah ne kan mutane, yafiya da gafara haƙƙin mutane ne Allah ya wajabta shi akan shi.[16]
  1. Dayrat Al-Ma’arif Qur’an, juzu’i na 1, shafi na 418.
  2. Allama Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 18, shafi na 239; Al-Qummi, Tafsirin Qummi, 1404H, juzu'i na 1, shafi na 95.
  3. Ibn Kathir, tafsirin Alqur’ani al-azeem, juzu’i na 1, shafi na 569-573.
  4. Abu Ubaid Al-Harawi, Falalar Alqur’ani, Damascus, shafi na 233.
  5. Ibn Tawus, Iqbal al-A’mal, juzu’i na 2, shafi na 667, 668, 691, 722.
  6. Ibn Kathir, tafsiri Alqur’ani al-azeem , juzu’i na 1, shafi na 569.
  7. Al-Qurtubi, Al-Jami` fi Ahkam al-Qur’an, juzu’i na 3, shafi na 433.
  8. «اشتباه‌نويسی واشتباه‌خوانی قرآن در مساجد؛ چه كسی مسئول است؟»
  9. Sayyid Qutb, fi zilalil Alqur’ani, juzu’i na 1, shafi na 344.
  10. Makarem Al-Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 2, shafi na 363.
  11. Makarim Al-Shirazi, Al-Amsal fi Tafsir ktabullahi al-munazzal juzu'i na 2, shafi na 363.
  12. Al-Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 2, shafi na 440.
  13. Makarem Al-Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 2, shafi na 364
  14. Makarem Al-Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 2, shafi na 367
  15. Al-Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 2, shafi na 443.
  16. Al-Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 2, shafi na 443.

Bayanin kula

Nassoshi

  • Ibn Tawus, Ali bin Musa, Iqbal al-A’amal, Tehran, Darul Kutub al-Islamiyyah, 1409H.
  • Ibn Kathir, Ismail bin Omar, Tafsir Alqur'anil ak-azeem, wanda: Muhammad Husaini Shams al-Din, Beirut, Darul Kutub al-Ilmiyyah, 1419 H.
  • Abu Ubaid Al-Harawi, Al-Qasim bin Salam, Fada'ilul Qur'an, Damascus, Dar Ibn Kathir, ed.
  • «اشتباه‌نويسي و اشتباه‌خواني قرآن در مساجد؛ چه كسي مسئول است؟» خبرگزاري بين‌المللي قرآن، انتشار: 3 شهريور 1387ش، مشاهده: 8 بهمن 1398 ش.
  • Sayyid Qutub, Fi Zilalil Alqur'an, Beirut, Dar Al-Shorouk, 1425H.
  • Tabatabaei, Muhammad Hussein, Al-Mizan fi Tafsiri Alqur'ani, Beirut, Al-Alami Publications Foundation, 1390 AH.
  • Kira'ati, Mohsen, Tafsir Nour, Tehran, Farhangi Darshayi Az Quran Center, 1388 AH.
  • Qurtubi, Muhammad bin Ahmad, Al-Jami’ li Ahkam Al-Qur’an, Tehran, Nasir Khusraw, 1364H.
  • Al-Qummi, Ali bin Ibrahim, Tafsirul Qummi, bugun: Tayyib Al-Musawi Al-Jaza’iri, Qom, Darul Kitab, 1404H.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar, Beirut, Larabawa Heritage Revival House, 1403H.
  • Markaz Farhang wa ma'arif Kur'ani, dayiratul marif Kur'ani kareem, Qum, Bustan Kuttab, 1382 A.M.
  • Makarim Al-Shirazi, Al-Amsal fi Tafsiril Al-Qur’an Al-Manzil, Kum, Mazhabar Imam Ali bin Abi Talib (a.s), 1379H.