Ayar Maharim

Daga wikishia
(an turo daga Ayar Muharramai)
Ayar Maharim

Ayar maharim (Larabci: آية المحارم) aya ce ta 23 da uku a cikin suratul Nisa'i, a cikinta an anbaci wasu adadin matan da suka haramta mutum ya aura, a cikinta an anbaci kaso bakwai na mata waɗanda suka haramta mutum ya aura, ta sakamakon jini da nasaba, guda biyu ta sakamakon shayarwa da mata huɗu ta sakamakon sababi watau aure.

Sannan aya ta 31 da ɗaya a cikin sauratul nur wada aka fi sani da ayar hijabi ta anbaci wasu matan da suka haramta mutum ya aura.

Nassin Aya

ita ce aya ta 23 suratul nisa'i cikin wannann aya bayanin adadin matan da aurensu ya haramta ya zo

﴿حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ مِنَ الرَّضَاعَةِ وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ وَرَبَائِبُكُمُ اللَّاتِي فِي ﴾﴾حُجُورِكُمْ مِنْ نِسَائِكُمُ اللَّاتِي دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَإِنْ لَمْ تَكُونُوا دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ وَحَلَائِلُ أَبْنَائِكُمُ الَّذِينَ مِنْ أَصْلَابِكُمْ وَأَنْ تَجْمَعُوا بَيْنَ الْأُخْتَيْنِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَحِيمًا



([1])


Dalilin Saukar Ayar

Shaik Ɗusi (Rasuwa: 460 hijira) ya faɗa a cikin tafsirin shi mai suna At-tibyan a loƙaci da yake magana akan wani sashi na ayar 23 ta cikin suratut Nisa akan maganar Allah, "وَحَلَائِلُ أَبْنَائِكُمُ الَّذِينَ مِنْ أَصْلَابِكُمْ"Cewa ta sauka ne a lokacin da Annabi (S.A.W) ya auri Zainab Bint Jahash matar Zaidu ɗan Harisa bayan kashe shi d aaka a yaƙin mu'uta wanda ya kasance ɗa na riƙo a gun Annabi (S.A.W), sai Mushrikan Makka suka fara magana kan wannann aure tsakanin Annabi da matar ɗan riƙon shi.[2]

Hakanan ya zo a cikin tafsirul Amsal cewa annabi ya yi wannan auran ne domin dakatar da wata al'ada ta jahiliyya a tsakanin mutane,ita wannan al'ada ita ce duk wanda ya riƙi ɗa, to zai ɗabbaƙa hukunci a kanshi kamar ɗan da ya haifa, saboda haka ya zamo ba sa auran matan ƴayan su na riƙo. da matan da suka saka ko wadanda suka mutu suka bar su.[3]

Maharramai

Asalin Kasida: Muharramai Da Maharramai Na Shayarwa

Matan da suka haramta mutum ya aura sune mata da suke da alaƙa ta jini da mutum, kuma ya halitta ga kowannann su ya kalli kwalliyar kowa, aure ya haramta a tsakanin su.[4] kuma ita wannan aya tana haramata aure a tsakanin mutu da matar da suke da alaƙa ta jini da kuma alaƙa ta aure da kuma alaƙa ta shayarwa.[5]

  • Alaƙa ta jini: ita ce alaƙar da take faruwa sabo da haihuwa, sabo da haka ya haramta auran mata bakwai ga maza bakwai, kamar haka:[6]

• Uwa, wannan haramcin ya kunshi kaka ta ɓangaran mahaifi da kaka ta ɓangaran mahaifiya da kaka daga ɓangaran mahaifiya da ɓangaran mahaifiyarta.[7]

• ƴa da ƴayanta, wannan ya kunshi ƴarta da ƴar ƴa mace zuwa ƙasa wato ƴar ƴar da ka haifa da abin da ya yi ƙasa.[8]

• ƴar uwa wadda mutum yake uba ɗaya da ita ko kuma uwa ɗaya koma uwa ɗaya uba ɗaya.[9]

• ƴar ƴar uwa da abin da ya yi zuwa ƙasa.[10]

• ƴar ɗan uwa abin da yayi zuwa ƙasa.[11]

• Yar uwar mahaifi, wannan haramcin ya ƙunshi yar uwar mahaifi ta bangaran uwa da uba, vda yar uwar kaka namiji da kaka mace.[12]

• ƴar uwar uwa, wannan ma ya ƙunshi yar uwar uwa wadda suke uba ɗaya ko uwa ɗaya da kuma yar uwar kaka namiji da yar uwar kaka mace abin da ya yi sama.[13]


Shayarwa: tana faruwa ne ta hanyar mace ta shayar da yaro mamanta kai tsaye, amma matar ta zamo ba ita ta haifeshi ba.[14] cikin wannan ayar babu abuni da aka kawo sai haramcin auren iyaye mata da kuma ƴan uwan mutum waɗanda suka sha mama tare.[15] malaman fiƙihu sun yi hukunci cewa, duk matar da ta haramta kan wani mutum ta hanyar alaƙa ta jini, to kazalika wannan matar ta haramta gare shi ta hanyar shayarwa, bisa dogaro da maganar annabi (S.A.W), duk mace data haramta ta hanyar shayarwa, to tana haramata ta hanyar alaƙa ta jini.[16]


  • Alaƙa ta hanyar auratayya: Matan da suka haramta ta hanyar aure, haramcin yana faruwa ne daga an ɗaura aure tsakanin mace da namiji, ta hakan ne zai zama aure ya haramta tsakanin mijin da wasu ƴan uwan matar shi, itama aure ya haramta da wasu daga cikin ƴan uwan mijinta.[17] Ayar haramacin auran wasu mata tana nuni kan haramcin mata guda huɗu waɗanda suka haramta kan mutum ta hanyar auratayya,kamar haka:
  • Mahaifiyar matar mutum ta haramta gare shi har zuwa uwar uwa abin da yayi sama.

ƴar matar mutum, amma ya zamo ta zama matar shi ta hanyar ɗaurin aure, kuma ya zamo ya kusance matarsa bayan aurenta. Matar ɗan mutum ta haramta ga mahaifinshi. Kuma ya haramta mutum ya aure mata biyu ƴan uwan juna a lokaci guda.[18]

Nuƙuɗoɗi Game da Tafsirin Wannan Ayar

Wasu daga cikin malaman tafsiri sun tafi kan cewa wannan jumlar; وَأَنْ تَجْمَعُوا بَيْنَ الْأُخْتَيْنِ إِلَّا ما قَدْ سَلَفَ Tana nuni ne ga wata al'ada da take faruwa a tsakanin Larabawa a lokacin jahiliyya ta haɗa mata biyu ƴan uwan juna, wato mutum ɗaya ya aure su. Shi wannan hukuncin bai shafi duk wanda ya auri mata biyu ƴan uwan juna kafin zuwa hukuncin ba, Allah ba zai kama shi ba da wani laifi ba, amma daga yanzu kada ya kuma. Kuma ya wajaba kan shi ya zaɓi ɗaya daga cikin su, sai ya saki ɗayar, bayan saukar wannan hukuncin.[19] Allama Ɗabaɗaba'i ya ce: shi wannan sharaɗin ko kuma hukunci na haramcin haɗa ƴan uwa guda biyu, yana iya komawa zuwa ga sauran hukunce-hukunce da suka gabata a wannan ayar kafin shi kanshi wannan hukuncin, ba wai kawai haramcin yan uwa guda biyu ba, sabo da akwai wasu al'ummu da ba larabawa ba a duniya da suke auran matan da aka haramta a wannan ayar. Amma shi musulunci lokacin da ya hana auran mata guda biyu ƴan uwan juna, yana tabbar da cewa yin hakan ga irin waɗancan mutanan ya inganta a gunsu, kuma ya yi hukunci da tsarkin ƴayan su cewa su ƴa ƴa ne na halas.[20] Amma ƙarshe Allama Ɗabaɗaba'i ya rinjayar da maganar farko, cewa shi wannan hukunci ya taƙaita ne kan auran mata guda biyu ƴan uwan juna, kuma ita ce maganar da tafi bayyana.[21]

Amma Shaik Makarim Shirazi ya ce: jumalar ƙarshe a wannan ayar tafi dacewa da ma'ana ta biyu wacce Allama ɗabaɗaba'i ya kawo.[22] ya zo a cikin tafsirul Amsal daga cikin abin da ake tinanin ya sa Allah ya haramta auran mata biyu ƴan uwa juna a cikin wannan ayar akwai karo da zai faro a zuciyar su a rayuwarsu ta yau da kullin, ta yadda ko wace ɗaya daga cikin su za ta sami kanta a fagen soyayya da gasa a tsakanin su akan mijinsu.[23]

Wasu Ayoyin Da Suke Da Alaƙa Da Wannan Maudu'i

Tusheh Kaida: Ayar Hijabi

aya ce mashahuriya ta 31 da ɗaya a cikin suratut nur, wadda aka fi sani da ayar hijabi, tana daga cikin ayoyin da ta yi magana kan mazan da suka haramta wasu mata su aura.

Allah maɗaukaki yana cewa:

وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ... وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ آبَائِهِنَّ أَوْ آبَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ أَبْنَائِهِنَّ أَوْ أَبْنَاءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوْ إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي إِخْوَانِهِنَّ أَوْ بَنِي أَخَوَاتِهِنَّ..
Ya kai Annabi ka faɗawa muminai mata cewa: kada su nuna kwalliyar su ga kowa sai ga mazajansu ko kuma iyayansu ko kuma ga iyayan mazajansu ko ƴayansu ko `ƴa`yan mazajansu ko ƴa uwansu maza ko ƴaya maza na ƴan uwansu maza ko ƴaya maza na ƴan uwansu mata.....[24]



(Quran: Nur: 31)


Bayanin kula

  1. سورة النساء، الآية 23.
  2. Al-Tusi, al-Tabayan, juzu'i na 3, shafi na 159.
  3. Makarem Al-Shirazi, Al-amsal, juzu'i na 3, shafi na 173.
  4. Al-Mishkini, Mustalahat Al-Fikihi, shafi na 272.
  5. Al-Maqdis al-Ardabili, Zubadah al-Bayan, al-Muqabah al-Mortazawiyya, shafi na 523-524.
  6. Al-Muhaqq al-Hilli, Sharia'e al-Islam, juzu'i na 2, shafi na 225; Al-Maqdis al-Ardabili, Zubadah al-Bayan, al-Maqboeh al-Mortazawiyya, shafi na 523-524; Al-Najafi, Javaher Kalam, juzu'i na 29, shafi na 238.
  7. Al-Najafi, Jawaher Al-Kalam, juzu'i na 29, shafi na 238.
  8. Al-Imam Al-Khamini, Tahrir al-wsilah, juzu'i na 2, shafi na 282.
  9. Al-Imam Al-Khamini, Tahrir al-wsilah, juzu'i na 2, shafi na 282.
  10. Al-Imam Al-Khamini, Tahrir al-wsilah, juzu'i na 2, shafi na 283.
  11. Al-Imam Al-Khamini, Tahrir al-wsilah, juzu'i na 2, shafi na 283.
  12. Al-Imam Al-Khamini, Tahrir al-wsilah, juzu'i na 2, shafi na 283.
  13. Al-Imam Al-Khamini, Tahrir al-wsilah, juzu'i na 2, shafi na 283.
  14. Al-Najafi, Jawaher Kalam, juzu'i na 29, shafi na 264.
  15. Al-Fazel al-Miqdad, Kenz al-Irfan, juzu'i na 2, shafi na 182.
  16. Al-Qadi Al-Numani, Da'a'imul Al-Islam, juzu'i na 2, shafi na 240; Fadel Al-Miqdad, Kanz Al-Irfan, juzu'i na 2, shafi na 182.
  17. Al-Shaheed al-Thani, Masalak al-Afham, juzu'i na 7, shafi na 281.
  18. Al-Fazel al-Miqdad, Kenz al-Irfan, juzu'i na 2, shafi na 184.
  19. Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 4, shafi na 265; Makarem Al-Shirazi, Al-amsal, juzu'i na 3, shafi na 173.
  20. Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 4, shafi na 266.
  21. Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 4, shafi na 266.
  22. Makarem Al-Shirazi, Al-amsal, juzu'i na 3, shafi na 174.
  23. Makarem Al-Shirazi, Al-amsal, juzu'i na 3, shafi na 174.
  24. النور: 31.

Nassoshi

[Koran]]'

  • Makarem Al-Shirazi, Nasser, Al-Amsal fi Tafsirin Qum, Mazhabar Imam Ali Template:A.s, bugu na daya, 1379 Hijira.
  • Al-Fadil Al-Miqdad, Miqdad bin Abdullah, Kanzul Irfan fi Fikihi Alqur'an, Tehran, Mortazavi Publications, 1369H.
  • Al-Mishkini, Ali, Mustalahat Al-Fikihu, Qum, Al-Hadi Press, bugun farko, 1419H.
  • Al-Muhaqqiq Al-Hilli, Jaafar bn Al-Hasan, Shara'i Al-islami Qum, Mu'assasatan Isma'iliyya, bugu na 2, 1308H.
  • Al-Muqaddas Al-Ardebili, Ahmad bin Muhammad, Zuddat al-Bayan fi Ahkam al-Qur'an, Tehran, Al-Murtazawi Library for the Revival of Jaafari Antiquities, 1st edition, D.T.
  • Al-Najafi, Muhammad Hassan, Jawahir Al-Kalam fi Sharh Al-Islam', Beirut, Larabawa Heritage Revival House, 1404H.
  • Al-Qadi Al-Numani, Al-Numan bin Muhammad bin Mansour, Da'aimul Al-islam Qum, Mu'assasar Al-Baiti Template:A.s, bugu na biyu, 1385H.
  • Al-Tabatabai, Muhammad Hussein, Al-Mizan fi Tafsir Al-Qur'ani, Qum, Mu'assasar Daba'ar Musulunci, bugun 5, 1417 Hijira.
  • Al-Tusi, Muhammad bin Al-Hasan, 'Al-Tibyan fi Tafsir Alqur'ani, Beirut, Dar Revival of Arab Heritage, d.
  • Imam Khomeini, Ruhollah, Tahrir al-Wasilah, Qum, Mu'assasa Tsara da Buga Ayyukan Imam Khumaini, bugu na 1, 1434H.
  • Shahidi thani, Zainul-Din bin Ali al-Amili, Masalik al-Afham, Qum, Mu'assasa ilimin Musulunci, 1414H.