Ayar Naba'i

Daga wikishia
Ayar Naba'i

Ayar Naba'i, (Larabci: آية النبأ) Suratul Hujurat: 6 a ilimin Usulul Fikhi ana bahasi cikin wannan aya kan dalili da hujjar Khabarul Wahid, aksarin Malaman tafsiri suna ganin sha'anin saukar wannan ayar ya kasance dangane da labarin Walidu Bn Uƙba ya kawo na cewa ƙabilar Bani Musɗalaƙ sun ƙi bada zakka, bayan yaɗuwar wannan labari sai ayar ta sauka tare da umartar musulmai da su yi bincike kan labarin da Walidu Bin Uƙba ya zo da shi da gano rashin ingancin labarin. Cikin Usulul Fiƙhi cikin bahasin kan Khabarul Wahid ana bahasi daga wannan Ayar.

Matani da Tarjama

یا أَیهَا الَّذِینَ آمَنُوا إِن جَاءَكُمْ فَاسِقٌ بِنَبَإٍ فَتَبَیَّنُوا أَن تُصِیبُوا قَوْمًا بِجَهَالَةٍ فَتُصْبِحُوا عَلَیٰ مَا فَعَلْتُمْ نَادِمِینَ
Ya ku waɗanda suka yi Imani idan Fasiƙi ya zo muku da labari to ku nemi bayani don gudun kada ku cutar da wasu Mutane cikin jahilci saboda hakan ku wayi gari kuna nadama kan abin da kuka aikata.[1]



(Kur'ani: Hujurat: 6)


Sha'anin Sauka

Malaman tafsiri sun ambaci sha'anin sauka biyu dangane da wannan aya: aksarin Malamai sun tafi kan cewa wannan aya ta sauka a iya kan Waludi Bn Uƙba, bayan Annabi (S.A.W) ya aike shi wurin ƙabilar Bani Musɗalaƙ domin karɓo zakka daga hannunsu. [2] a cewar Fadlu Bin Hassan Tabarsi cikin Majma'ul Al-Bayan, yayin da suka samu labarin isowar Wakilin Annabi (S.A.W) wanda zai karɓi zakkarsu sai suka fito domin tarbarsa, sakamakon rigima da take tsakaninsu a Jahiliya sai Walidu ya yi tunanin sun fito domin kashe shi, da wannan dalili ne ya koma wurin Annabi (S.A.W) ya ce masa sun ƙi bada zakka. Annabi ya yi niyyar ɗaukar Matakin yaƙarsu kan ƙin ba da zakka da suka yi sai wannan aya ta sauka ta umarci musulmai duk lokacin da Fasiƙi ya zo musu da labari su nemi bayani su yi bincike kan labarin da ya kawo. [3] Wasu ba'ari sun ce wannan aya ta sauka ne kan Kaziyyar Tuhumar Mariya matar Annabi (S.A.W) cikin wannan ƙissa Imam Ali (A.S) wanda Annabi (S.A.W) ya umarce shi da yin bincike da hukunta wanda ya yi lefi, ya tambayi Annabi (S.A.W) shin zai iya watsi da jita-jitan da ya yaɗu idan ya zamana abin da ya gani ya saɓa da abin da sauran mutane suka faɗi, sai Annabi (S.A.W) ya bashi izini kan haka. Daga ƙarshe dai ta bayyana kaɗai ƙazafi ne aka yiwa Mariya sannan kuma jita-jitan da aka yaɗa duk ƙarya ce. [4]

Amfani Da Ayar Naba'I Kan Tabbatar Da Hujjar Khabarul Wahid

Cikn ilimin Usulul Fiƙhi ana amfani da wannan aya domin tabbatar da hujjar Khabarul Wahid, na'am Malaman Usul cikin tabbatar da Hujjar Khabarul Wahid ta hanyar wannan aya basu samu ittifaƙin ra'ayoyi ba. Daga Jumlarsu akwai Muhammad Husaini Na'ini yana ganin ingancin dogara da wannan aya kan tabbatar da hujjar Khabarul Wahid, [5] Amma Shaik Ansari ya tafi kan cewa ayar bata shiryarwa kan hujjar Khabarul Wahid.[6]

Bayanin kula

  1. Hujurat: 6)
  2. Makarem Shirazi, Tafsir namuneh, 1374, juzu'i na 22, shafi na 153.
  3. Tabarsi, Majmaal Bayan, 1372, juzu'i na 9, shafi na 198.
  4. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 9, shafi na 198 da 199
  5. Naini, Fawad al-Asul, 1376, juzu'i na 3, shafi na 187.
  6. Sheikh Ansari, Faraid al-Asoul, 1416 AH, shafi na 116-136.

Nassoshi

  • Sheikh Ansari, Morteza, Faraid al-Assul, ƙum, Al-Nashar al-Islami Foundation, bugu na biyar, 1416H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, Tehran, Nasser Khosro, 1372.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir namuneh, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 1374.
  • Naini, Mohammad Hossein, Fawad al-Asul, Kum, ƙom seminary community, bugun farko, 1376.