Ayar Tahaddi

Daga wikishia
Domin sanin ma'anar tahaddi ku duba ƙasidar Tahaddi

Ayar tahaddi (Larabci: آيات التحدي), Ayoyin tahaddi ayoyi ne guda shida a cikin Al-ƙur'ani, Al-ƙur'ani yana ƙalubalantar waɗanda suke inkarin annabtar annabi Muhammad, abin nufi waɗanda basu yarda da ita ba, cewa su zo da kwatankwacin al-ƙur'ani koma su kawo sura goma irin na shi kai koda sura ɗaya ce.

Wasu malaman tafsiri sun tafi akan cewa wannan ayoyi an saukar da su ne a jere, abin nufi daga aya mai wahala zuwa mai sauƙi, misali daga farko an ƙalubalance su da dukkan ƙur'ani da sukaƙarsa sai aka ce to su kawo aya goma ita ma da suƙaƙasa, sannan aka ce su kawo aya ɗaya. Yayin da wasu suka tafi kan cewa ba a jere aka saukar da suba, kaɗai an saukar da su ne a loƙuta daban-daban.

Abin da Ake Nufi Da Tahadi Da Al-ƙur'ani

Tushen ƙasida: Tahaddi

ƙalubale shi ne neman fito na fito tsakanin mutane domin sanin gazawar wanda aka ƙalubalanta.[1] kamar yadda aka anbace shi a cikin Ulumul kur'an wato ilimin da ya shafi sanin al-ƙur'ani[2], kazalika ya zo a ilimin sanin aƙidun musulunci,[3] kuma shi ƙalubale yana cikin shariɗɗa na Mu'ujiza,[4] lalle annabawa suna ƙalubalantar duk wanda ya yi inkarin annabta, su na buƙatar mutum ya kawo irin abin da suka zo da shi.[5]

Amma shi ƙalubale da ƙur'ani yana nufi ƙalubalantar mutum da ya kawo irin ƙur'ani ga waɗanda suke su ma'abuta balaga da fasahane su,[6]to idan sukakasa zai zamo dalili kan cewa ƙur'ani mu'ajiza ne,kuma yana tabbatar da annabtar annabi Muhammad a musulinci.[7]

Nau'o'in Tahaddi A Cikin Al-ƙur'ani

Al-ƙur'ani ya yi ƙalubale da ayoyi guda shida,[8] sun kasu gida uku.

Ƙalubalan Dukkan Kur'ani

Allah ya ƙalubalanci mutane da su kawo cikakken ƙur'ani a cikin ayoyi guda uku.

  • Aya ta 34 suratul ɗur فَلْيَأْتُوا بِحَدِيثٍ مِثْلِهِ إِنْ كَانُوا صَادِقِينَ[9]
  • Aya ta 49 suratul ƙasas قُلْ فَأْتُوا بِكِتَابٍ مِّنْ عِندِ اللهِ هُوَ أَهْدَىٰ مِنْهُمَا أَتَّبِعْهُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ[10]
  • Aya ta 88 suratul isra'i قُلْ لَئِنِ اجْتَمَعَتِ الْإِنْسُ وَالْجِنُّ عَلی أَنْ یأْتُوا بِمِثْلِ هذَا الْقُرْآنِ لا یأْتُونَ بِمِثْلِهِ وَلَوْ کانَ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ ظَهیر[11]

Tahaddi Da Kawo Surori Gud Goma

A cikin aya ta 13 a cikin suratu Hud, Alkur'ani mai girma ya bukaci kafirai su zo da surori goma kwatankwacinsa idan za su iya.

أَمْ یقُولُونَ افْتَراهُ قُلْ فَأْتُوا بِعَشْرِ سُوَرٍ مِثْلِهِ مُفْتَرَیاتٍ وَادْعُوا مَنِ اسْتَطَعْتُمْ مِنْ دُونِ اللهِ إِنْ کُنْتُمْ صادِقینَ

Ko suna cewa Shi ne ya ƙirƙire shi? Ka ce: to ku zo da surori guda goma kwatankwacinsa ƙirƙirru, kuma ku kirayi wanda kuke iyawa, banda Allah, idan kun kasance masu gaskiya.[12]

Tahaddi Da Kawo Sura Guda ɗaya

Alƙur'ani yana ƙalubalanta a cikin wannan ayoyin guda biyu da su zo da sura guda ɗaya irinta ƙur'ani.

أَمْ یقُولُونَ افْتَراهُ قُلْ فَأْتُوا بِسُورَةٍ مِثْلِهِ وَادْعُوا مَنِ اسْتَطَعْتُمْ مِنْ دُونِ اللهِ إِنْ کُنْتُمْ صادِقینَ

Ko kuma suna cewa, “Shi ne ya ƙirƙire shi? Ka ce: To, ku zo da sura kwatankwacinsa, kuma ku kirayi wanda kuke iyawa, banda Allah, idan kun kasance masu gaskiya.[13]

  • Aya ta 23 a cikin suratul Baƙara:
وَإِن كُنتُمْ فِي رَيْبٍ مِّمَّا نَزَّلْنَا عَلَىٰ عَبْدِنَا فَأْتُوا بِسُورَةٍ مِّن مِّثْلِهِ وَادْعُوا شُهَدَاءَكُم مِّن دُونِ اللهِ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ

Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka saukar zuwa ga BawanMu, to, ku zo da sura guda kwatankwacinsa, kuma ku kira shaidunku, banda Allah, idan kun kasance masu gaskiya.[14]

Jerin Saukar Ayoyin Tahaddi

Wasu daga cikin malaman tafsiri sun tafi kan cewa ayoyi tahaddi wato ƙalubale sun sauka a jere daga mai wahala zuwa mai sauƙi.[15] ƙalubale ya fara da kur'ani duka sai masu inkari suka kasa,sai ya ƙalubalance su da aya guda goma ita ma suka kasa sai ya ce to yanzu su kawo sura guda ɗaya itama sukakarsa.[16]

Wasu masu bincike sun tafi akan cewa saukar kur'ani na nuni da cewa babu wani tsari a saukar da ayoyin kalubale, sai dai an saukar da su a lokuta daban-daban.[17]

Bayanin kula

  1. ƙasmul al-Kalam Majma al-buhusil al-islamiyya, sharhu al-mustalahat al-kalamiyya, shafi na 64.
  2. Marafah, Tamhid fi Ulum al-ƙur'an, juzu'i na 4, shafi na 16-27; Abiyari, Al-Masu’a Al-ƙur’ani, juzu’i na 2, shafi na 362; Al-Zarkashi, Al-Barhan a cikin ilimomin Kur’ani, juzu’i na 2, shafi na 226.
  3. ƙasmul al-Kalam Majma al-buhusil al-islamiyya, sharhu al-mustalahat al-kalamiyya, shafi na 64
  4. Al-Baƙalani, Ijaz al-ƙur’an, shafi na 161
  5. Moadeb, Ijaz Kur’ani dar nazare Ahlul Baiti, shafi na 17.
  6. Al-Sabzwari, Asrar al-Hikam, juzu'i na 1, shafi na 472.
  7. Al-Sabzwari, Asrar al-Hikam, juzu'i na 1, shafi na 473; Al-Baƙalani, Ijaz al-ƙur'an, shafi na 161 da 162; Al-Khoramshahi,daneshnameh ƙur'an wa ƙur'an pajuhi, juzu'i na 1, shafi na 481.
  8. Al-Khoramshahi,Daneshnameh ƙur'an wa ƙur'an pajuhi, juzu'i na 1, shafi na 481.
  9. الطور: 34.
  10. القصص: 49.
  11. الإسراء: 88.
  12. Hudu: 13.
  13. Yunusa: 38.
  14. Suratul Baƙarah: 23.
  15. Al-Zamakhshari, Al-Kashf, juzu'i na 2, shafi na 383.
  16. Al-Jisas, Al-Ahkam al-ƙur'an, juzu'i na 1, shafi na 34.
  17. Behjat Bor, "Barasi sairi tanzili ayat Tahaddi", shafi na 77.

Nassoshi

  • "Al-ƙur'an Al=kareem".
  • Al-Abiyari, Ibrahim, 'Masu'atu Al-ƙur'an, Alkahira - Egypt, Publisher: Arab Record Foundation, bugu na daya, 1405 AH.
  • Al-Baƙillani, Abu Bakr, 'Ijazul Al-ƙur'an, muallaƙ: Abu Abdul Rahman Awaida, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Al-Kutub Al-Ilmiyya, 1421H.
  • بهجت بور، عبد الكريم، وزهرا بهجت بور،"بررسي سير تنزيلي آيات تحدي"، نشرية قبسات، رقم 77، خريف 1394.
  • Al-Jassas, Ahmed bin Ali, Ahkam al-ƙur'an, editan: Muhammad Sadiƙ ƙamhawi, Beirut - Lebanon, mawallafi: Gidan Farfaɗo na Larabawa, 1405 Hijira.
  • Al-Khorshahi, Bahauddin, Danshnameh ƙur'an wa ƙur'an pajuhii, Tehran - Iran, publisher: Nahid - Dostan Publishing, 1377 AH.
  • Al-Zarkashi, Muhammad, Alburhan fi ulumil Kur'ani, editoci: Abdul Rahman Al-Maraashli, Ibrahim Abdullah Al-Kurdi, and Jamal Hamdi Al-Dhahabi, Beirut - Lebanon, publisher : Darul Ma’rifa, bugun farko, 1410H.
  • Al-Zamakhshari, Mahmoud, 'al-kashaf an haƙa'iƙ gawamiz tanzil, Beirut - Lebanon, bugun: Dar Al-Kitab Al-Arabi, 1407 Hijira.
  • Al-Sabzwari, Muhammad Baƙir, asrar al-hikam, mai bincike: Karim Al-Faydi, ƙum - Iran, mawallafi: Religious Publications, 1383 AH.
  • Kismul kalam fi majma al-buhus islamiyya, sharhu mustalahat kalam, Mashhad - Iran, Razavi Holy Shrine, 1415 AH.
  • Maddeb, Reda, Ijazi Kur'ani dar nazare Ahlul Baiti ismat, ƙom - Iran, mawallafi: Ahsan Al- Hadisi, 1379 H.
  • Maarifa, Muhammad Hadi, 'At-tamhid fi ulumi Kur'ani, ƙom - Iran, mawallafi: Mu'assasar Buga Musulunci mai alaka da kungiyar malamai a makarantar hauza ta Kum, bugu na 3, 1410H.