Ƙissar Taya Murna
ƙissar taya murna, (Larabci: قضية التهنئة) labari ne da ya ƙunshi ƙissar taya Imam Ali murna da Abubakwar da Umar suka yi bayan Manzon Allah (S.A.W) ya shelanta cewa shi ne Halifansa a filin Ghadir Khum wannan labari ya kasance dalilli kan cancantuwar Imam (A.S) da halifanci
Kalmomin Taya Murna
ƙissar taya murna, labarin kan taya murnar da Sahhaban Hazrat Muhammad (S.A.W) suka yi bayan shelanta Imam Ali (A.S) matsayin Halifan Manzon Allah (S.A.W) wanda ya kasance a ranar 18 ga watan Zil-Hijja shekara ta goma bayan hijira, [1] Umar Bn Khaɗɗab ya taya Imam Ali (A.S) murna da amfani da kalmar
»
Lale maraba gareka ya Ali ka zama shugabana kuma shugaban dukkanin wani Mumini da Mumina. [2] cikin ba’arin naƙali maimakon Ali kalmar Ibn Abi ɗalib ce ta zo cikin naƙalin [3] ko kuma kalmar Amirul-Muminin, haka kuma cikin ba’arin matanai maimakon Mumin da Mumina kalmar Muslim ce ta zo, [4] Ahmad Bn Hanbal shima ya ce Umar ya yi amfani da kalmar
Madalla ya ɗan Abi ɗalib, ka wayi gari ka wuni kana halin kasancewa shugaban dukkanin wani Mumini da Mumina. [5] cikin littafin Tarikh Bagdad talifin Khaɗib Bagdadi an yi ishara cewa bayan Umar ya taya Imam Ali (A.S) murna, sai ayar Ikmal ta sauko. [6]
Su Wanene Suka Taya Imam Ali (A.S) Murna?
Abubakar, Umar Bn Khaɗɗab, ɗalha da Zubairu suna cikin Sahabbai da suka taya Imam Ali (A.S) [7] wasu ba’arin marubuta sun kawo cewa Abubakar da Umar a farko ba su yarda sun taya shi murna ba, sai dai cewa bayan Annabi (S.A.W) ya gamsar da su cewa shelanta halifancin ya kasance da umarnin Allah [8] tare da kasancewar saɓawa wannan umarni zai iya zama sababin kafirta, sai suka haƙura suka yi masa barka da taya shi murna, [9] amma cikin wasu matanan daban ya nuna cewa Umar ya yi farin ciki, [10] [yadash 1] an kuma bada labarin kan yadda ya taya Imam Ali (A.S) murna cikin ƙwarin gwiwa fiye da sauran mutanen waɗannan suka taya shi murna [11] ko kuma cewa Umar ne mutum na farko [12] da ya fara taya shi murna. [13] Duk da cewa masadir masu yawa sun naƙalto taya murnar Umar, [14] amma tare da haka cikin wasu litattafan ya zo cewa Abubakar da Umar cikin bai ɗaya suka taya Imam Ali (A.S) Murnar Halifancinsa. [15] Cikin ba’arin wasu litattafai ya zo cewa ƙissar taya murnar da Umar ya yi an naƙaltota ta hannun Sayyid Alu Addi [16] ko Sayyid Bani Addi [17] an ce nasabar Halifa na biyu tana danganewa ga Addi bn Bn Ka’ab, [18] ko kuma wani Mutum da ba a ambaci sunasa ba. [19] Kan asasin Naƙalin Halifa na biyu bayan shelanta wilayar Imam Ali (A.S) Umar ya gayawa Manzon Allah (S.A.W) ya ga wani Matashi yana shelanta cewa babu wanda zai yi watsi da wannan umarni sai wanda ya kasance Munafuki Annabi (S.A.W) ya gaya Umar cewa wannan Matashi ba kowa bane illa Mala’ika Jibrilu. [20]
Shiryarwa Kan Imamancin Imam Ali (A.S)
Taya murnar Umar ga Imam Ali (A.S) dalili ne cewa abin da Annabi (S.A.W) yake nufi daga gabatar da Imam Ali (A.S) a filin Ghadir Khum [21] ya kasance a matsayin Halifansa kuma yana daga shaida kan fifitarsa [22] da fifikon Iliminsa [23] kan sauran Mutane [24] a cikin ba’arin litattafai ya zo cewa Imam Ali (A.S) bayan wannan waƙi’a cikin ganawar da ya yi da Halifa na farko ya bayyana masa wannan ƙissa matsayin dalili kan cancantuwarsa da halifanci. [25] a cewar Faizul Kashani Halifa na biyu bayan taya Imam Ali (A.S) murna ya yi masa sallama a matsayin Sarkin Muminai. [26]
Lokacin Da Waƙi’ar Ta Faru
Cikin Aksarin Masadir an kawo rahotan ƙissar taya murna da Sahabbai suka yiwa Imam Ali (A.S) ne bayan Annabi (S.A.W) ya ayyana shi halifansa a bayansa a waƙi’ar Ghadir Khum [27] kan asasin wasu riwayoyi bayan ayyana Imam Ali (A.S) da Annabi (S.A.W) ya yi matsayin Magajinsa ya bada umarni kafa Tanti ga Imam Ali (A.S) domin Sahabbai su je wurin su taya shi murna ɗaya bayan ɗaya. [28] Cikin ba’arin Masadir an danganta wannan waƙi’a da ranar Mubahala da rana ƙulla ƴan’uwantaka wacce bayan Annabi (S.A.W) ya shelanta Wilayar Imam Ali (A.S) Umar ya taya shi murna. [29]
Bayanin kula
- ↑ Amini, Al-Ghadir, 1416 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 508.
- ↑ Helali, littafin Salim bin Qays, 1405 AH, juzu'i na 2, shafi na 829; Firat Kufi, Tafsirin Firat al-Kufi, 1410 AH, shafi na 516; Mofid, Al-Irshad, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 177. al-Tafsir Mnsub Imam Al-Askari, 1409 AH, shafi na 112; Khatib Baghdadi, Tarikh Baghdad, 1417 AH, juzu'i na 8, shafi.284; Ibn Asaker, Tarikh Damashk, 1415 Hijira, juzu'i na 42, shafi na 233.
- ↑ Khasibi, Al-Hidaya Al-Kubra, 1419 AH, shafi na 104.
- ↑ Sadouq, Amali, 1376, shafi na 2; Khatib Baghdadi, Tarikh Baghdad, 1417 AH, juzu'i na 8, shafi.284; Ibn Kathir, Al-Bidaya wa Al-Nihaya, 1407 AH, juzu'i na 7, shafi na 349.
- ↑ Ibn Hanbal, Musnad Ahmad Ibn Hanbal, 1416 Hijira, juzu'i na 30, shafi na 430.
- ↑ Khatib Baghdadi, Tarihin Bagdad, 1417 AH, juzu'i na 8, shafi na 284.
- ↑ Hali, Al-Adad Al-Qawiyya, 1408H, shafi na 183.
- ↑ Al-Tafsir Al-mansub ila Imam al-Askari, 1409 AH, shafi na 112; Faiz Kashani, Nawader Al-Akhbar, fima yata'allak bi'Usulil Al-dini, shafi na 166.
- ↑ Helali, Kitab Salim bin Qays, 1405 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 829.
- ↑ Erbali, Kashf al-Ghumma, 1381 AH, juzu'i na 1, shafi na 237.
- ↑ Mofid, Al-Irshad, 1413 AH, Mujalladi na 1, shafi na 177; Ɗabarasi, Elamul Alwara, 1390 AH, shafi na 133.
- ↑ Mufid, Masar Al-Shia, 1422 AH, shafi na 44; Bahrani, Madinatul Ma'ajiz, 1413 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 269.
- ↑ Ibn Tawus, Taraf Min Al-Anba wa Al-Manaqib, 1420 AH, shafi na 362.
- ↑ Helali, Kitabe Salim bin Qays, 1405 AH, juzu'i na 2, shafi na 829; Al-Tafsir Almansub ila Imam Al-Askari, 1409 AH, shafi na 112; Khasibi, Al-Hidaya Al-Kubra, 1419 AH, shafi na 104; Sadouq, Amali, 1376, shafi na 2; Mofid, Al-Irshad, 1413 AH, juzu'i na 1, shafi na 177.
- ↑ Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, Mujalladi na 1, shafi na 512.
- ↑ Shami,Al-Durarul Al-Nazim, 1420H, shafi na 444.
- ↑ Dilmi, Ghurar Al-Akhbar, 1427 AH, shafi na 356.
- ↑ Ibn Abd Al-Barr, al-Istiy'ab, 1412 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 1144.
- ↑ Firat Kufi, Tafsir Furat Al-Kufi, 1410H, shafi na 516.
- ↑ Shami, Al-Durarul Al-Nazim, 1420H, shafi na 253.
- ↑ Karajki, Kanzul Al-Fawa'id, 1410 AH, juzu'i na 2, shafi na 96
- ↑ Shami, Al-durarul Al-Nazim, 1420 AH, shafi na 268-269.
- ↑ Dilmi, Ghurarul Al-Akhbar, 1427 AH, shafi na 349.
- ↑ Daylami, Irshad Al-Qulob, 1412 AH, juzu'i na 2, shafi na 264; Khasibi, Al-Hidaya Al-Kubra, 1419 Hijira, shafi na 103-104.
- ↑ Faiz Kashani, Nawadir Al-Akhbar, 1371, shafi na 166.
- ↑ Helali, Kitabe Salim bin Qays, 1405 AH, juzu'i na 2, shafi na 828-829; al-Tafsir Almansub ila Imam al-Askari, 1409 AH, shafi na 112; Furat Kufi, Tafsir Furat Al-Kufi, 1410 AH, shafi na 516; Sadouq, Amali, 1376, shafi na 2; Mofid, Al-Irshad, 1413 AH, Juzu’i na 1, shafi na 175; Ibn Asaker, Tarikh Damshk, 1415 Hijira, juzu'i na 42, shafi na 234.
- ↑ Helali, Kitabe Salim bin Qays, 1405 AH, juzu'i na 2, shafi na 829; Mofid, Al-Irshad, 1413 AH, Juzu’i na 1, shafi na 176; Tabarsi, Elamul Alwara, 1390 AH, shafi na 132.
- ↑ Ibn Batliq, Umdatul Ayoun, 1407 AH, shafi na 169; Ibn Shazan, Al-Rawda, 1423 AH, shafi na 76-77; Erbali, Kashf al-Ghumma, 1381 AH, juzu'i na 1, shafi na 328
- ↑ Ibn Batliq, Umdatul Ayoun, 1407 AH, shafi na 169; Ibn Shazan, Al-Rawda, 1423 AH, shafi na 76-77; Erbali, Kashf al-Ghumma, 1381 AH, juzu'i na 1, shafi na 328
Nassoshi
- Ibn Batliq, Yahya Ibn Hasan,Umdatul Ayoun Sahaah al-Akhbar fi Manaqib Imam Abrar, Qum, Madrasin Community, 1407H.
- Ibn Hanbal, Ahmad bin Muhammad, Masnad al-Imam Ahmad bin Hanbal, bincike na Abdullah bin Abdul Mohsen Turki da sauransu, Beirut, Al-Risalah Foundation, 1416H.
- Ibn Shazan Qomi, Shazan Ibn Jibreel, Al-Rawda fi Fda’il Amir al-Mu’minin Ali Ibn Abi Talib (AS), Research by Ali Shekarchi, Qum, School of Al-amin, 1423 AH.
- Ibn Tawus, Ali Ibn Musa, Tarf Al-Anbaa wa Al-Munaqib, bincike na Qais Attar, Mashhad, Tasu'a, 1420H.
- Ibn Abd al-Barr, Yusuf bin Abd Allah, Al-Istiy'ab fi Marifah Al-Ashab, bincike na Ali Muhammad al-Bajawi, Beirut, Dar al-Jeel, 1412 AH.
- Ibn Asaker, Ali Ibn Hasan, Tarikh Madinatu Damashk wa zikri Fadliha wa tasmiiyati man hallaha minal Amsal ai ijtaza bi nahaihia min waridiha wa Ahlaha, bincike na Ali Shiri, Beirut. Darul Fikr, 1415H.
- Ibn Kathir, Ismail Ibn Umar, Al-Bidaya wa Al-Nihaya, Beirut, Darul Fikr, 1407H.
- Erbali, Ali Ibn Isa, Kashf Al-Ghumma fi Marifah Al-Imam, Hashim Rasouli Mahalati ya yi bincike, Tabriz, Bani Hashemi, 1381H.
- Amini, Abd al-Hussein, Al-Ghadir a cikin Al-Kitab da Sunnah da kuma Al-Adab, Qum, Al-Ghadir Center for Islamic Studies, 1416H.
- Bahrani, Sayyid Hashim bin Suleiman, Madinatu Ma'ajiz A'immati Isna Ashar, Qum, Islamic Encyclopedia Foundation, 1413H.
- Al-Tafsir Almansub ila Imam Abi Muhammad Al-Hasan bin Ali Al-Askari (AS), binciken Imam Mahdi (AS), Qum, 1409H.
- Haskani, Obaidullah bin Abdallah, shawahidul Al-Tanzil lil Qawa'id Al-tafdil, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Jagorar Musulunci, 1411H.
- Hilli, Ali bin Yusuf bin Al-Muthahar, Al-Adad Al-Qawiyya Li daf'i Al-makawif Al-yaumiyya, Qum, Laburaren Ayatullahi Murashi Najafi, 1408H.
- Khasibi, Hossein bin Hamdan, Al-Hidaya Al-Kubra, Beirut, al-Balagh, 1419 AH.
- Khatib al-Baghdadi, Ahmed bin Ali, Tarikh Bagadad, Mustafa Abd Al-Qadir Atta, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, ya yi bincike, 1417 bayan hijira.
- Daylami, Hasan bin Muhammad, Irshad Al-Qulub ila Al-Sawab, Kum, al-Sharif al-Radhi, 1412 AH.
- Daylami, Hasan bin Muhammad, Ghurarul Al-Akhbar wa Durar Al-Akhtar fi Manaqib Abi Al-A'imma Al-Athar, bincike na Ismail Dighm, Qom, Dilil Ma, 1427H.
- Shami, Youssef bin Hatem, Al-Durarul Al-Nazim fi Manaqib Al-A'Imma Al-Hamim, Qum, Jamia Madrasin, 1420 AH.
- Sadouq, Mohammad Bin Ali, Amali, Tehran, Kitabchi, bugu na 6, 1376.
- Tabarsi, Fazl bin Hasan, Al-Wari Media na Alam Al-Hadi, Tehran, Islamia, bugu na uku, 1390H.
- Faiz Kashani, Mohammad Mohsen, Nawader Al-Akhbar Fima Yatalaq Bi Usul Al-Din, Tehran, Cibiyar Nazarin Al'adu da Bincike, 1371.
- Karajki, Muhammad bin Ali, Kanz al-Fawa'id, bincike na Abdullah Neema, Qum, Dar al-Zhakhar, 1410 AH.
- Kufi, Furat bin Ibrahim, Tafsirin Furat Al-Kufi, Bincike na Mohammad Kazem, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Jagorar Musulunci, Est.
- Majlisi, Mohammad Baqir, Bihar Al-Anwar Akhbar Al-A'Immathul Al-Athar, Beirut, Dar Ehiya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403 AH.
- Mofid, Muhammad bin Muhammad bin Nu'man, Al-Irshad fi Marafah Hajjullah Ali al-Abad, Qum, Sheikh Mofid Congress, 1413 AH.
- Mofid, Muhammad bin Muhammad bin Nu'man, Masar Al-Shi'a fi Mukhtasar Tarikh shari'a, wanda aka buga a "kungiyar Nafisa a tarihin Imamai (a.s.)", Beirut, Darul-Qari, 1422 AH.
- Helali, Salim bin Qais, Kitabe Salim bin Qais al-Hilali, Muhammad Ansari Zanjani Khoini ya yi bincike, Qum, Al-Hadi, 1405H.