Jump to content

Tabarri

Daga wikishia
(an turo daga Bara'a)

Tabarri, (Larabci: التبرّي) yana nufin barranta da nesanta daga maƙiya Allah da waliyyan Allah. A wurin Shi'a tabarri yana daga furu'ud-dini (Rassan addini) kuma yana da matsayi na musamman a koyarwar aƙida da mu'amalolin na su. Malaman Shi'a tare da jingina da ba'arin ayoyi da riwayoyi, sun tafi kan cewa wajibi ne a barranta daga mushrikai da kafirai da maƙiya Ahlul-Baiti (A.S) da jagororin ɓata da kuma azzulumai.

Aksarin ƴanshi'a game da salo tsari da uslubin bayyana barranta daga maƙiya Ahlul-Baiti (A.S) da waɗanda suka kwace musu haƙƙinsu na halifanci, suna ganin cewa bayyana barranta daga gare su ya saɓawa asalin haɗin kai da ƙarfafuwar alaƙoƙi tsakanin musulmi da kiyaye kusanto da mazhabobin Muslunci.

Nazarin Ma'ana

"Tabarri", a isɗilahi yana nufin barranta da kuma nesanta kai daga maƙiya Allah da waliyyansa.[1] Kalmar tabarri an ciro ta ne daga asalin "Bur'u" asali ɗaya suke da kalmomi misalin bara'a waɗanda a lugga suna da ma'anar nesanta daga wani abu wanda zama da shi abu ne mara kyawu.[2]

Matsayi Da Muhimmanci

Tabarri ɗaya ne daga koyarwa da kuma aƙidun Shi'a[3] a mazhabar Shi'a kusa da tawalli ana lissafa shi daga cikin furu'ud-dini.[4] A cikin riwayoyin Shi'a, an ƙarfafa muhimmancin tabarri.[5] Kulaini a cikin Al-Kafi ya keɓance sashe guda ɗauke da taken "Babin soyayya cikin Allah da ƙiyayya cikin Allah) ya kawo hadisai da suke magana kan haka waɗanda adadinsu ya kai hadisai 16.[6]

A cikin wani hadisi da aka naƙalto daga Annabi (S.A.W), tabarri ko ƙiyayya saboda Allah, yana cikin mafi ƙarfafa mafi amintar igiyoyin imani[7] A cikin wani hadisi da aka naƙalto daga Imam Rida (A.S), an ambaci cewa barranta daga maƙiya Allah da Annabi (S.A.W) da Ahlul-Baiti (A.S) tare da yarda da wilayarsu shi ne kammaluwar addini.[8]

Wajabcin Tabarri

A mazhabar Shi'a, tabarri wajibi ne na addini.[9] A cewar Shaik Saduƙ, malamin fiƙihu da aƙida ta Shi'a, imanin Shi'a shi ne cewa tabarri da barranta daga azzalumai wajibi ne.[10] Hurrul Amili, a cikin Wasa'ilush Shi'a, wutsiyar wani babi mai ɗauke da taken "Wajabcin son mumini da ƙin kafiri" ya tattaro wasu riwayoyi da ya fitar da wajabcin tabarri daga cikin riwayoyin.[11]

Domin halasci da kuma wajabcin tabarri, an jingina da ayar farkon suratul mumtahana.[12] Allama Ɗabaɗaba'i yana cewa wannan aya ta tsananta hanawa muminai son maƙiya Allah.[13] Sayyid Abdul-Husaini Lari a cikin sharhin littafin Al-makasib na Shaik Ansari, ya ce wannan aya da kuma riwayoyi a sarari suna nuni zuwa ga wajabcin tabarri.[14]

Mutanen Da Ya Wajaba Ka Barranta Da Su

Malaman Shi'a, bisa la'akari da ayoyi da riwayoyi, su na ganin wajabcin barranta daga adadin wasu mutane:

  • Mushrikai: A cewar Allama Ɗabaɗaba'i, a cikin aya ta 3 suratul tauba da aya ta 114 suratul tauba da aya ta 19 suratul an'am, ƙarara an yi bayani game da bayyana barranta da annabawa suka yi daga mushrikai da shirkar da suke aikatawa. Haka nan a cikin ayoyin farkon suratul tauba, ma'ana aya ta 1-3, wanda ayoyi ne da aka fi sani da ayoyin bara'a, [15]barranta daga mushrikai ƙarara ta zo.[16]
  • Maƙiya Ahlul-baiti: Malaman Shi'a tare da jingina da wasu riwayoyi da suke wajabta bayyana barranta daga maƙiya Ahlul-Baiti (A.S) da waɗanda suke kwace haƙƙinsu na halifanci, sun bayyana ra'ayinsu.[17]
  • Makasan Ahlul-Baiti: A cikin hadisi da Shaik Saduƙ ya naƙalto a littafin Al-Khisal daga Imam Sadiƙ (A.S), yana ganin wajibi ne a bayyana barranta daga makasan Ahlul-Baiti (A.S) da mutanen da suka kwace musu haƙƙi.[18]
  • Barranta daga zalunci da daulolin zalunci: Wajibi ne a barranta daga zalunci da azzaluman hukumomi da suke aikata danniya da zalunci kan musulmai da raunanan mutane a duniya.[19] Ana cewa a yau (Ƙarni na 21 miladiyya) gwamnatin Sahayoniyya ita ce mafi bayyana a mastayin hukumar zalunci da kwace wadda zalunci da baƙin zalunci na ta kai tsaye yake kasancewa kan musulmi da mutanen ƙasar Falasɗinu.[20]

Alaƙa Mai ƙarfi Tsakanin Tabarri Da Tawalli

A cikin ba'arin riwayoyi a litattafan hadisi ya zo cewa tawalli, shi ne son Ahlul-Baiti (A.S) da yarda da wilayarsu,[21] ana karɓa daga mutum idan ya kasance ya yi imani da tabarri. Alal misali a cikin wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) an naƙalto cewa mutumin da ya ke da'awar soyayyar mu, amma ba ya barranta daga maƙiyan mu, to wannan mutumi maƙaryaci ne.[22] An rawaito daga Imam Rida (A.S) faɗinsa, wilayar Ahlul-Baiti (A.S) ba ta kammaluwa haka soyayya da ƙaunar su ba ta tabbatuwa sai da tsanantuwa da barranta daga maƙiyansu.[23]

Murtada Muɗahhari ya rubuta cewa tabarri shi ne duk wanda yake da wilayar Imam Ali (A.S) to wajibi a samu hali na korewa daga gare shi, ma'ana duk wani abu da yake kishiyar Ali da hanyarsa dole ne ya yi inkarinsa ya ƙaryata shi, ma'ana dai anan wurin imani da Allah kaɗai ba ya iya wadatarwa, dole ne a kore ɗagutu tare da wancan imani.[24] Abul Fatuh Razi, malamin tafsiri na Shi'a a ƙarni na shida hijira, shi ma yana ganin tabarri matsayin sharaɗi kuma muƙadddimar imani da wilaya, yana cewa ma'abota tauhidi da farko, tare da furta kalmar tauhidi, to wajibi ne su barranta daga duk abubuwan da suke bayyana kafirci da shirka domin su shiga kwazazzabon imani.[25]

Tabarra'iyyun

A zamanin mulkin daular Safawiyya, an samu wata ƙungiya da ake kira da "Bara'atiyan" sun yi imani cewa tabarri da barranta daga maƙiya Ahlul-Baiti (A.S) da waɗanda suka kwace halifanci wajibi a dinga tsine musu a bayyane.[26] Lungu da Saƙo kasuwa da kan hanya sun kasance suna ɗaga murya suna iƙrari da wilayar Imam Ali (A.S) da kuma tsinewa masu saɓa masa da maƙiyansa tare kuma da tsinewa halifofin Bani Umayya da Bani Abbas.[27] Kishiyar wannan ƙungiya, da yawa-yawan ƴanshi'a su na ganin wannan salon bayyana barranta da zagi da tsinewa ababen girmamawar sauran ƙungiyoyin musulmi ya saɓa da asalin ƙarfafa haɗin kai da ƙarfafa igiyoyin alaƙoƙi tsakanin musulmi da kuma kiyaye kusanto da mazhabobin Muslunci.[28]

Ku Duba

Bayanin kula

  1. Motahari, Majmu'e Asar, 1391, juzu'i. 26, shafi. 133; Alavi, Aqaid al-Mu’minin, 1437 AH, shafi na 214.
  2. Raghib Isfahani, Al-Mufradat, karkashin kalmar "bara'a".
  3. Motahari, Majmu'e Asar, 2011, Juzu'i. 26, shafi. 133.
  4. Motahari, Majmu'e Asar, 1391, juzu'i. 26, shafi. 133; Alavi, Aqaid al-Mu’minin, 1437 AH, shafi na 214.
  5. Jam'i Az Nawisandigan, Farhange Fiqh Farsi, 2008, juzu'i. 2, shafi. 337.
  6. Kulayni, Al-kafi, 1407 AH, juzu'i. 2, shafi na 124-127.
  7. Kulayni, Al-kafi, 1407 AH, juzu'i. 2, shafi. 125; Allama Majlisi, Mir'at al-Uqul, 1404 AH, juzu'i. 8, shafi. 260.
  8. Allama Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 27, shafi. 58.
  9. Lari, Al-Ta'liqa 'ali al-Mukasib, 1418 AH, juzu'i. 1, shafi. 232; 'Alawi, 'Aqa'eed al-Mu'minin, 1437 AH, shafi. 217.
  10. Sheikh Sadouq, Al-Ithiqadat, 1414H, shafi. 102.
  11. Hurr Amili, Wasa’il al-Shi’ah, 1416 AH, juzu’i. 16, shafi. 176.
  12. Lari, Al-Ta'liqa 'ala al-Mukasib, 1418 AH, juzu'i. 1, shafi na. 232.
  13. Tabataba'i, Al-Mizan, 1393 AH, juzu'i. 19, shafi. 226.
  14. Lari, Al-Ta'liqa 'ala al-Mukasib, 1418 AH, juzu'i. 1, shafi. 232.
  15. Tabatabaei, Al-Mizan, 1393 AH, juzu'i. 9, shafi. 146.
  16. Tabataba'i, Al-Mizan, 1393 AH, juzu'i. 9, shafi na 146-147 da 149.
  17. Misali, duba Sheikh Saduq, Al-I'tiqadat, 1414H, shafi na 102-103; Mohaqiq Lahiji, Sarmaye Iman, 1372 AH, shafi na 154-155; Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1405 AH, juzu'i. 6, shafi na 64-67.
  18. Sheikh Saduq, Al-Khisal, 1362, shafi. 153.
  19. Ismaili, Tawalli Wa Tebarri Az Negahi DIgar, 2005, shafi. 75.
  20. Ismaili, Tawalli Wa Tebarri Az Negahi DIgar, 2005, shafi. 75.
  21. Misali, duba Tabrizi, Sirat al-Najāt, 1416 AH, juzu'i. 3, shafi. 452; kungiyar marubuta, Farhang al-Fiqh al-Farsi, 1387 AH, juzu'i. 2, 667.
  22. Allama Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 27,shafi. 58.
  23. Allama Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 27,shafi. 58.
  24. Motahari, Majmu'e Asar, 2011, juzu'i. 26, shafi. 133.
  25. Abu Aftouh Razi, Rouz al-Janan, 1376, juzu'i na 2, shafi na 283.
  26. Khani Arani, "Shakeshhaye Fikri Wa Ruyekerdihaye Amali Juryane shi'ej Wahdat Satizi," shafi na 14-15.
  27. Rawandi, Tarikh Ijtima'i Iran, 2003, juzu'i. 8, shafi. 136.
  28. Salmani, "Tabari", shafi. 378.

Nassoshi

  • Abu Iftouh Razi, Hussein bin Ali, Rawd al-jinan wa Ruh al-jinan Fi Tafsiril Alqur'an, editan Muhammad Jafar Yahaqi, Mashhad, Astan Quds Razavi, 1376.
  • Ismaili,Mahdi,Tawalli Wa Tabarri Az Negahi Digar, Qom,Cibiyar Nazarin Musulunci,1384.
  • Tabrizi, Mirza Jawad, Sirat al-Najat, Qom, Salman Farsi Publications, 1416 AH.
  • Rukunin marubuta, Farhange Fiqh Farsi, Qum, Cibiyar Encyclopedia Fiqhu, 1387.
  • Hurrul Ameli, Muhammad bin Hassan, Wasa’il al-Shi’ah, bugun Sayyid Muhammad Reza Hosseini Jalali, Qum, Cibiyar Aal-Bait (AS), 1416 Hijira.
  • Khani Arani, Elah, Shakes'haye Fikiri Wa Ruyekerdehaye Amali Juryane Shi'eh Wahdat Satizi, Jaridar Quarterly na Tunanin Siyasa a Musulunci, No. 31, Spring 1401 AH.
  • Ragheb Isfahani, Hussein bin Muhammad, Al-Mufradat fi Gharib al-Quran, Beirut, Dar al-Qalam, 1412 AH.
  • Ravandi, Morteza, Tarikh Ijtima'i Iran, Tehran, Negah Publications, bugu na biyu, 1382H.
  • Salmani, "Tabari", shafi. 376.
  • Sheikh Saduq, Muhammad bn Husayn, Al-I'tiqadat, Qum, Sheikh Mufid Congress, 1414H.
  • Sheikh Saduq, Muhammad bn Husayn, Al-Khisal, Ali Akbar Ghaffari, Qum, Jamia Madrassin Publications ya gyara, bugun farko, 1362H.
  • Tabatabai, Sayyid Muhammad Husayn, Al-Mizan fi Tafsir al-Quran, Beirut, Al-Alamy Publications Foundation, 1393H.
  • Allamah Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Al-Wafah Foundation, 1403 AH.
  • Allamah Majlisi, Muhammad Baqir, Mirat al-Uqol fi Sharh Akhbar Aal al-Rasul, Tehran, Darul Kutb al-Islamiyya, 1404H.
  • Alavi, Sayyid Adel, Aqeed al-Mu'minin, Qum, Cibiyar Yada Da Shiriya ta Musulunci, 1437H.
  • Qasimi, Saleh, Marja'eyat Maurusi Ya Tashayyu Ingilisi, Tehran, Salman Pak Publications, bugu na biyu, 1394H.
  • Kulaini, Muhammad bn Yaqub, Al-Kafi, Ali Akbar Ghaffari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kutab al-Islamiyya suka gyara, 1407H.
  • Lari, Sayyid Abdul Hussein, Al-Ta'liqat 'alal al-Makasib, Qom, Maarif Islamic Foundation, 1418H.
  • Mazandarani, Muhammad Saleh, Sharhu Usulil Al-Kafi, Beirut, Dar Ihya' Al-Kutab al-Arabi, 1429H.
  • Mohaqq Lahiji, Abdul Razzaq, Sarmeye iman, Tehran, Al-Zahraa Publications, 1372H.
  • Motahhari, Morteza, Majmu'eh Asar, Qum, Sadra Publications, 1391H.
  • Najafi, Muhammad Hassan, Jawaher al-Kalam, Beirut, Dar Ihya' Al-Turath al-Arabi, 1405H.