Ku tambaye ni kafin ku rasa ni

Daga wikishia
Gutsiren kyakkyawan zanen rubutun Hadis Saluni. na Muhammad Al-Masharafawi

Ku tambayeni Kafin ku rasa ni, (Larabci: سلوني قبل أن تفقدوني) wannan wata sananniyar jumla ce da take ishara zuwa ga fadaduwar iliminsa , bisa dogaro da nakalin Masadir din Shi'a da Ahlus-sunna, hakika Imam Ali (A.S) ya fadi wannan kalma a lokuta masu yawan gaske, cikin su a lokacin huduba yayin da Sa'adu Ibn Abi Wakas ya tambaye shi adadin gashin Kansa da fuskar sa , cikin bashi amsa Imam yace babu gashi a Kanka saboda cikin kanka akwai Shaidan zaune, haka zalika ya bada labarin Shahadar dansa Imam Husaini (A.S) da zata kasance a hannun Umar Ibn Sa'ad. Ku tambaye ni kafin ku rasa ni wannan jumla ce daga falaloli da suka kebanci Imam Ali (A.S) kuma dalili ce kam fifikonsa kan sauran Sahabban Annabi (S.A.W)

Takaitaccen bayani

Ku tambaye ni kafin ku rasani, wata jumla ce daga bakin Imam Ali (A.S),[1] bisa dogara da riwayar da ta zo daga littafin Yanabi'ul Muwadda hakika Imam ya fadi wannan jumla a lokuta masu tarin yawa,[2] daga ciki bayan mutane sun karbi Halifancinsa sun masa Mubaya'a, a cikin wata huduba da ya yi ta a garin Kufa,[3] a cikin wasu jama'a daga Sahabbansa bayan Yakin Siffin da Naharawan,[4] Wannan jumla (ku tambayeni kafin ku rasa ni)[5] ta tattaro (ku tambaye ni duk abin da kuke so)[6] ko kuma (ku tambaye ni gabanin da ba zaku iya tambaya ta ba).[7] haka zalika ta zo a nakali (ku tambaye ni)[8]

Abin da hadisin yake shiryarwa shi ne bunkasar ilimin Imam Ali (A.S)

Daga cikin ba'arin sharhohin da aka yi kan Littafin Nahjul Balaga ya zo cewa wannan jumla tana shiryarwa ne kan cewa Imam Ali (A.S) yana da ilimin komai da komai,[9] kamar yanda Mulla Salihu Mazandarani daya daga Malaman Shi'a wanda ya mutu hijira na shekara 1081 yana cewa ba'arin Malaman Sunna suna cewa wannan jumla shaida ce kan bunkasa da fadadar iliminsa.[10] Ya zo daga Imam Bakir (A.S) ya zo cewa ma'anar wannan jumla ta (ku tambaye ni gabanin ku rasa ni) shi ne cewa babu wani da ya samu ilimi sai ta hanyar Imam Ali (A.S) mutane su je duk inda suke son zuwa na rantse da Allah babu komai anan sai ilimi da gaskiya da,[11] cikin cigaban riwayar da aka nakalto daga Imam Bakir (A.S) Imam Baki yayi nuni da hannunsa zuwa gidansa, Allama Majlisi yana cewa: manufar Imam Bakir (A.S) kan ishara gidansa shi ne gidan wahayi da Annabta.[12] Cikin cigaba kan (ku tambaye ni kafin ku rasa ni) mabanbantan bayanai sun zo duka da suke ishara kan fadin Ilimin Imam Ali (A.S) daga cikinsu: lallai ilimin mutanen farko da na karshe yana wurina, ni zan yiwa Yahudawa fatawa kan asasin Attaura, zan yiwa Kiristoci,[13] kan asasin Linjila, zan yiwa musulmi kan asasin Kur'ani. Me yasa ba zaku tambayi mutumin da yake da ilimin musibu da bala'I da ilimin nasaba ba.[14] Hakika ni nafi sanin hanyoyin sama da ilimin sanin Allah fiye da hanyoyin kan doran Kasa.[15] Na rantse da Allah zan baku amsar duk abin da kuka tambaye ni, ku tambaye ni littafin Allah na rantse da Allah na san ayoyin da suka sauka da daddare ko wanda suka sauka da rana, a doren Kasa suka sauka ko a kan dutse.[16] Na rantse da Allah zan baku amsar dukkanin tambayar da kuka yi kan zamanin da ya shude da wanda zai zo.[17]

Kebantacciyar falalar Imam Ali (A.S)

A fadin Ibn Mardawaihi Isfahani Babban Malamin Hadisi na Ahlus-sunna a Karni na hudu zuwa na biyar, jumlar (ku tambaye ni kafin ku rasa ni) dalili ne kan fifikon ilimin Imam Ali (A.S) kan sauran Sahabbai,[18] haka kuma Ibrahim Ibn Muhammad Jawini Shafi'i Malamin Ahlus-sunna wanda ya mutu a shekara 730 hijira kamariya, cikin littafin Fara'idul Samdaini ya kirga wannan jumla daga cikin falalar da kebanci Imam Ali (A.S) wacce Makiyansa ba yanda za su iya da ita sai dai karbarta a haka,[19] a mahangar Sayyid Ibn Tawus lokacin da Imam Ali (A.S) ya bijirar da wannan jumla a taron Makiyansa da masu sabani da shi ya kasance wani nau'in kalubale na ilimi,[20] a cikin wannan hali Malam Shamsu dini Azzahabi da Ibn Taimiya[21] daga bangaren Salafiya cikin raddi kan wannan falala suna cewa: Imam Ali (A.S) ya fadi wannan jumla ne cikin taron Jahilan mutanen Kufa.[22] Kan asasin ba'arin wasu riwayoyi,[23] ya zo daga Imam Bakir (A.S) da Imam Sadik (A.S)[24] kan wannan jumla ta (ku tambaye ni kafin ku rasa ni) haka jumlar (ku tambaye ni abin da kuke so) an nakalto su daga Annabi((A.S)[25] wasu ba'arin Malaman Ahlus-Sunna sun nakalto cewa babu wani da ya taba fadar wannan jumla in banda Imam Ali ((A.S)[26] haka ma wanan magana ta zo cikin littafin Yanabi'ul Muwadda.[27]

Wadanda Suka yi Da'awar Jumlar Bisa karya

Malaman muslunci sun bada labarin cewa wasu adadin mutane sun yi da'awar wannan jumla, sai dai cewa sun gaza bada amsar tambayoyin da akayi musu, daga cikin wadannan Makaryata akwai Katada Ibn Da'amatu,[28] daga Tabi'ai kuma Fakihan Basara, kuma Ibn Jauzi Fakihin Hanbaliya da ya rayu a karni na shida.[29] Haka kuma Allama Amini cikin littafin sa Algadir ya kawo sunayen mutane biyar daga wadannan Makaryata da suka kunyata yayin da suka gaza bada amsoshin tambayar da aka yi musu bayan da'awar da suka yi, Allama Majlisi da Mulla Salihu Mazandarani suna cewa: duk wani wanda ba Imam Ali (A.S) ba da yayi da'awar wannan jumla bai gushe ba sai da ya kunya ta,[30] asirin sa ya tonu.[31]

Marawaitan Hadisin da kuma Ingancin sa

Ku tambayeni kafin ku rasa ni an rawaito wannan magana da wasu adadin Marawaita kamar haka: Amiru Bn Wasila[32] Abdullahi Bn Abbas[33] Sulaimu Bn Kaisu Alhilali [34] Asbagu Bn Nabata A[35]bayatu Bn Rab'i [36] Hakim Nishaburi [37] sannan kuma riwyar da ta gangaro daga Abu Dufailu Amiru Bn Wasila sun kidaya matsayin mai ingancin isnadi.

Martanin Sa'adu Bn Abi Wakas

bisa bayanan da suka zo a ba'arin wasu Masadir bayan Imam Ali (A.S) ya furta wannan jumla cikin wata huduba sa Sa'adu Bn Abi Wakas ya tambaye shi na wane adadin gashin da yake kaina da gemuna? sai Imam Ali (A.S) cikin bashi amsa ya rantse cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya bashi labari da cewa wata rana kai din za kai min wannan tambayar, hakika babu gashi a kanka da gemunka sai dai a asalinsu akwai Shaidan zaune. haka kuma cikin gidanka akwai Bunsuru (yana masa ishara ne da dansa Umar Bn Sa'ad) wanda ya kashe Imam Husaini [38] wasu ba'ari sun nakalto wannan kissa kan Sinanu Bn Anas daga cikin Makasan Imam Husaini (A.S)[39]

Bayanin kula

  1. duba: Safar, Basair al-Darraj, 1404H, shafi na 266-268, 296-296; Ibn Qolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1356, shafi na 74; Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 133 da 341-344; Nahj al-Balagha, Sahih Sobhi Saleh, hadisi na 189, shafi na 280; Hakim Neishaburi, al-Mustadrak, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi.383; Khwarazmi, Al-Manaqib, Gidan Bugawa na Musulunci, shafi na 91; Joyni, Faraid Al-Samatin, 1400 AH, Juzu'i na 1, shafi na 340 da 341; Ibn Abi al-Hadid, Sharhin Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 286, juzu'i na 6, shafi.136, juzu'i na 7, shafi.57, juzu'i na 10, shafi na 14, juzu'i. 13, shafi na 101.
  2. Kunduzi, Yanabi al-Moudah, Dar al-Soh, Mujalladi na 1, shafi na 222.
  3. Mofid, Al-Arshad, 1413 AH, Juzu'i na 1, shafi na 34, 35 da 330.
  4. Duba: Hilali, Kitab Salim bin Qays al-Hilali, 1405 Hijira, Juzu'i na 2, shafi na 802 da 941.
  5. Nahj al-Balagha, editan Sobhi Saleh, hadisi na 93, shafi na 137.
  6. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi 399, h2; Safar, Basair al-Darraj, 1404H, shafi na 12.
  7. Hakim Neishaburi, al-Mustadrak, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 506.
  8. Duba Ibn Abd al-Barr, al-Istiyab, 1412 AH, juzu'i na 3, shafi na 1107; Tabari, al-Aqabi reserves, 1428 AH, juzu'i na 1, shafi na 399 da 400; Ibn Asaker, Tarihin Damascus, 1415 AH, juzu'i na 27, shafi 100 da juzu'i na 42, shafi 398 da juzu'i na 44, shafi 335 da 397; Khwarazmi, Al-Manaqib, Gidan Bugawa na Musulunci, shafi na 94; Haskani, Havadad al-Tanzil, 1411 AH, Juzu'i na 1, shafi na 40-42 da 45.
  9. Mazandarani, Sharh al-Kafi, 1382 AH, juzu'i na 5, shafi 192; Hashemi Khoi, Minhaj al-Baraa', 1400 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 402 da juzu'i na 11, shafi na 172.
  10. Mazandarani, Sharh al-Kafi, 1382 AH, juzu'i na 5, shafi na 192.
  11. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi 399, h2; Safar, Basair al-Deraj, 1404 AH, shafi na 12, h1.
  12. Majlis, Mer'atul Ukuli, 1404 s, juzu'i na 4, shafi na 308.
  13. Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 341.
  14. Saffar, Baseer Al Darajat, 1404 s, shafi na 266-268.
  15. Nahj al-Balagha, Tashihi Sobhi Saleh, hadisi na 189, shafi na 280.
  16. Ibn Abd al-Barr, al-Istiyab, 1412 AH, juzu'i na 3, shafi na 1107; Haskani, shawaheed al-Tanzil, 1411 AH, juzu'i na 1, shafi na 42; Tabari, al-Aqabi reserves, 1428 AH, juzu'i na 1, shafi na 399 da 400; Ibn Asaker, Tariku Damascus, 1415 Hijira, juzu'i na 27, shafi na 100 da juzu'i na 42, shafi na 398.
  17. Ibn Qolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1356, shafi na 74; Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 133 da 134; Mofid, Al-Arshad, 1413 AH, Juzu'i na 1, shafi na 330 da 331.
  18. Ibn Marduyeh Isfahani, Manaqib Ali Ibn Abi Talib, 1424H, shafi na 86 da 87.
  19. Jowini, Faraid al-Sumatin, 1400 A.H., juzu'i na 1, shafi na 340.
  20. Sayyid bin Tawoos, Al-Taraif, 1400 BC, Part 2, shafi na 510.
  21. Dhahabi, Al-Muntaqi Man Minhaj al-Etdal, shafi na 342.
  22. Ibn Taimiyyah, Minhaj al-Sunnah al-Nabawiyyah, 1406 BC, Part 8, shafi na 56 da 57.
  23. Ibn Hayyun, Sharh al-Akhbar, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 292.
  24. Ibn Abi-Zaynab, Al-Ghaiba Lal-Nu’mani, 1397 AH, shafi 87; Dhahabi, Tarikh al-Islam, 2003, juzu'i na 3, shafi na 828; Kundozi, Yanabi Al-Moudeh, Dar al-Soweh, juzu'i na 1, shafi na 222.
  25. Misali, duba Nishaburi, Sahih Muslim, Dar Ihya al-Tarath al-Arabi, juzu'i na 4, shafi na 1834.
  26. Ibn Athir, usud al-Ghaba, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 597; Ibn Abd al-Barr, al-Istiyab, 1412 AH, juzu'i na 3, shafi na 1103; Ibn Asaker, Tarihin Damascus, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 399; Haskani, shaida al-Tanzil, 1411 AH, juzu'i na 1, shafi na 50; Ibn Abi al-Hadid, Sharhin Nahj al-Balagha, 1404 AH, juzu'i na 7, shafi na 46.
  27. Ibn Hanbal, Fadael al-Sahaba, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 646; Dhahabi, Tarikh al-Islam, 2003, juzu'i na 2, shafi na 361; Ibn Asaker, Tariku Damascus, 1415 AH, juzu'i na 42, shafi na 399; Khwarazmi, Al-Manaqib, Islamic Publishing House, shafi na 90 da 91.
  28. Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, Juzu'i na 3, shafi na 355 da 356; Mazandarani, Sharh al-Kafi, 1382 AH, juzu'i na 5, shafi na 192.
  29. Nabati Ameli, Al-Sarat Al-Mustaqim, 2004, juzu'i na 1, shafi na 218.
  30. Duba: Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, Juzu'i na 6, shafi na 275 da 276.
  31. Majlesi, Mir'atu al-Aqool, 1404 AH, juzu'i na 4, shafi na 308; Mazandarani, Sharh al-Kafi, 1382 AH, juzu'i na 5, shafi na 192 da juzu'i na 6, shafi na 400.
  32. Hakim Neishaburi, al-Mustadrak, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi.383; Ibn Asaker, Tariku Damascus, 1415 AH, juzu'i na 17, shafi na 335; Ibn Abd al-Barr, al-Istiyab, 1412 AH, juzu'i na 3, shafi na 1107; Tabari, Zaka'ir Al-uqba, 1428 Hijira, Juzu'i na 1, shafi na 399 da na 400.
  33. Kunduzi, Yanabi al-Moudah, Dar al-Soh, Mujalladi na 1, shafi na 224.
  34. Hilali,Kitab Salim bin Qays al-Hilali, 1405 Hijira, Juzu'i na 2, shafi na 802 da 941.
  35. Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 133 da 341.
  36. Safar, Basair al-Deraj, 1404 AH, shafi na 266; Kunduzi, Yanabi al-Moudah, Dar al-Soh, Mujalladi na 1, shafi na 222.
  37. Hakim Neishaburi, al-Mustadrak, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 383 da 506.
  38. Bin Qolwieh, Kamel al-Ziyarat, 1356, shafi na 74; Sadouq, Al-Amali, 1376, shafi na 133 da 134; Mofid, Al-Arshad, 1413 AH, Juzu'i na 1, shafi na 330 da 331.
  39. Ibn Abi al-Hadid, Sharhin Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 286; Mazandarani, Sharh al-Kafi, 1382 AH, juzu'i na 6, shafi na 400.

Nassoshi

  • Ibn Abi al-Hadid, Abdul Hamid bin Hibatullah, Sharhin Nahj al-Balagheh, Bincike na Muhammad Abulfazl Ibrahim, Qum, Maktabatu Ayatullahi Murashi Najafi, bugu na farko, 1404H.
  • Ibn Abi-Zainab, Muhammad Ibn Ibrahim, Al-Ghabiyah Lal-Nu'mani, bincike da gyara na Ali Akbar Ghafari, Tehran, Madba'a Sadouq, bugun farko, 1397H.
  • Ibn Athir, Muhammad bin Muhammad, usud al-Ghaba, Beirut, Darul Fikr, 1409 AH-1989 Miladiyya.
  • Ibn Taimiyyah, Minhaj Sunnah al-Nabwiyyah fi nakadi Kalam Shi'a al-Qadriyah, Bincike na Muhammad Rashad Salem, Jami'atul Imam Muhammad bin Saud al-Islamiyya, bugu na farko, 1406H.
  • Ibn Hanbal, Ahmad Ibn Hanbal, Fadael Sahaba, bincike na Wasillah Muhammad Abbas, Beirut, Cibiyar Risala, bugun farko, 1403H.
  • Ibn Hayyun, Nu'man bin Muhammad al-Maghrebi, Sharh al-Akhbar fi Fada'il al-Ima'ah al-Atahar (a.s.), bincike da gyara na Muhammad Hossein Hosseini Jalali, Qum, Jamia Madrasin, bugu na farko, 1409 AH.
  • Ibn Abd al-Barr, Yusuf bin Abd Allah, Al-Istiyab fi Marafah al-Asahaba, bincike na Ali Muhammad al-Bajawi, Beirut, Dar al-Jeel, bugun farko, 1412 Hijira.
  • Ibn Asaker, Ali Ibn Hasan, Tarihin Damascus, Binciken Amr Ibn Gharamah Amrowi, Beirut, Darul Fikr, 1415 AH-1995 Miladiyya.
  • Ibn Qolwieh, Jafar bin Muhammad, Kamel al-Ziyarat, Abdul Hossein Amini, Najaf, Dar al-Mortazwieh, bugun farko, 1356 ya yi bincike kuma ya gyara shi.
  • Ibn Mardowieh Isfahani, Ahmed Ibn Musa, Manaqib Ali Ibn Abi Talib da Manzil Man Al-Qur'an Fi Ali, bincike na Abdul Razzaq Muhammad Harzuddin, Qum, Dar al-Hadith, bugu na biyu, 1424H.
  • Amini, Abdul Hossein, Al-Ghadir, Qum, Cibiyar Al-Ghadir, bugu na farko, 1416H.
  • Joyni, Ebrahim bin Mohammad, Faraed al-Samatin, bincike na Mohammad Baqer Mahmoudi, Beirut, Mahmoudi Institute, 1400 AH.
  • Hakim Neishaburi, Muhammad bin Abdullah, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, bincike na Mustafa Abd al-Qadir Atta, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1411 AH-1990 AD.
  • Haskani, Obaidullah bin Abdullah, Shawaheed al-Tanzil na al-Qawam al-Tafazil, bincike da gyara na Mohammad Bagher Mahmoudi, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Jagorar Musulunci, bugu na farko, 1411H.
  • Khwarazmi, Muwafaq bin Ahmad, Manaqib, Kum, Cibiyar Buga Harshen Musulunci, B.T.
  • Dhahabi, Shams al-Din, Al-Muntaqi Man Minhaj al-Aitdal a cikin cin zarafin Kalam Ahl al-Rafaz al-Itzal, bincike na Mohib al-Din Khatib, Bina, Bita.
  • Dhahabi, Shams al-Din, Tarikh al-Islam da Wafiyat al-Mashahir al-Alam, bincike na Bashar Awad Maruf, Dar al-Gharb al-Islami, bugu na farko, 2003.
  • Zamakhshari, Mahmoud bin Umar, Al-Kashaf kan haqiqanin Ghawamaz Al-Tanzil da Ayun Al-Aghawil a fuskar Ta’awil, bugun Mustafa Hossein Ahmad, Beirut, Darul Kitab al-Arabi, bugu na uku, 1407 AH.
  • "Saloni", mawallafin mawallafin Mohammed Al-Mushrafavi akan Pintres, ranar ziyarar: Maris 12, 1400.
  • Sharif Razi, Muhammad bin Hossein, Nahj al-Balagheh, Sobhi Saleh, Kum, Hijira ya gyara, bugun farko, 1404H.
  • Sadouq, Mohammad Bin Ali Bin Baboyeh, Al-Amali, Tehran, Kitabchi, bugu na 6, 1376.
  • Safar, Muhammad bin Hasan, Basa'ir al-Darraj fi Fadael al-Muhammad (a.s), Kum, Mazhabar Ayatullahi Murashi Najafi, bugu na biyu, 1404H.
  • Tabari, Mohib al-Din, Al-Aqabi reserves in Manaqib Dhu al-Qurabi, Qom, Dar al-Kitab al-Islami, bugu na farko, 1428H.
  • Tousi, Muhammad bin Hassan, Rizal Al-Tousi, bincike na Javad Qayoumi Isfahani, Qum, Cibiyar Buga Musulunci, bugu na uku, 1373.
  • Kundozi, Suleiman bin Ibrahim, Yanabi Al-Mouda Lzavi al-Qorabi, Qom, Dar al-Soweh, Bita.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-Kafi, bincike da gyara na Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, bugu na 4, 1407H.
  • Mazandarani, Mohammad Saleh bin Ahmad, Sharh al-Kafi (ka'idoji da ka'idoji), bincike da gyara na Abul Hasan Shearani, Tehran, Islamic School, bugun farko, 1382H.
  • Majlesi, Mohammad Baqir, Mir'atu al-Aqool fi Sharh Akhbar Al-Ar-Rasoul, bincike da gyara na Seyyed Hashem Rasouli Mahalati, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, bugu na biyu, 1404H.
  • Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Arshad Fi Mafarah Hajjullah Ali Al-Abad, Qum, Congress of Sheikh Mofid, bugun farko, 1413 AH.
  • Nabati Ameli, Ali bin Mohammad, Al-Sarat al-Mustaqim al-Maghtibri al-Taqadim, editan Mohammad Baqer Behboodi, Tehran, Al-Muktaba al-Mortazawieh, 2004.
  • Neishabouri, Muslim bin Hajjaj, Sahih Muslim, Binciken Muhammad Fouad Abd al-Baghi, Beirut, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, Bita.
  • Helali, Salim bin Qays, Kitabu Salim bin Qays al-Hilali, Muhammad Ansari Zanjani Khoini ya yi bincike kuma ya gyara shi, Qum, Al-Hadi, bugun farko, 1405H.