Ayar Mubahala

Daga wikishia
Wannan wata ƙasida ce game da ayar mubahala. Domin sanin labarin mubahala ku duba: Mubahalar Annabi (S.A.W) Tare da Kiristcoin Najran.

Ayar mubahala (Larabci:آيَة المُباهلة) (suratul alu imran aya ta 61) aya ce da take magana game da mubahalar da annabi (s.a.w) ya yi tare da kiristocin najran, wacce ta faru sakamakon saɓani da yake da shi tare da su dangane da matsayin annabi isa (a.s). malaman tafsiri na shi'a da mafi yawan ahlus-sunna sun tafi kan cewa ana ƙidaya wannan aya matsayin shaida da alama kan gaskiyar da'awar annabin muslunci (s.a.w) da kuma falalar ahlul-baiti (a.s) suna cewa abin nufi daga «اَبْناءَنا» (ƴaƴanmu) a wannan aya su ne hassan da husaini (a.s) sannan abin nufi daga «نِساءَنا» shi ne faɗima (s) sannan kuma abin nufi daga «اَنْفُسَنا» shi ne imam ali (a.s).

Imaman shi'a da ba'arin sahabbai sun yi amfani da ayar mubahala cikin tabbatar da fifiko da falalolin imam ali (a.s), haka nan sun yi amfani da ita cikin tabbatar da halascin asalin mubahala da halascin tarayyar da kutsawar mata a fagen ayyukan siyasa da zamantakewa.

Matani Da Tarjama

فَمَنْ حَاجَّک فِیهِ مِن بَعْدِ مَا جَاءَک مِنَ الْعِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَأَبْنَاءَکمْ وَنِسَاءَنَا وَنِسَاءَکمْ وَأَنفُسَنَا وَأَنفُسَکمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَل لَّعْنَتَ الله عَلَی الْکاذِبِینَ
Duk wanda ya yi jayayya da kai bayan abin da ya zo maka daga ilimi. Kace ku zo mu kira ƴaƴanmu da ƴaƴanku da matanmu da matanku da kawukanmu da kawukanku. Sannan mu yi mubahala mu ƙanƙantar da kai, mu sanya tsinuwar Allah kan maƙaryata.



(Alu Imran: Aya 61)


Matsayi

Ayar mubahala tana daga cikin ayoyi da ake dogara da su kan tabbatar da falalolin as'habul kisa'i (Ali, faɗima, hassan da husaini)[1] abdullahi baizawi ɗaya daga cikin malaman tafsiri na ahlus-sunna, yana ganin wannan aya ɗaya daga cikin dalilai kan gaskiyar annabi cikin da'awar annabta da kuma falalar waɗanda suka kasance tare da shi a mubahala.[2] haka nan jarullahi zamakshari (Wafati:538.h.ƙ) malamin tafsirin ahlus-sunna shima yana ganin wannan aya matsayi ƙarfafaffen dalili kan falalar as'habul kisa'i.[3] fadlu ɗan hassan ɗabarsi (Wafati:469.h.ƙ) malamin tafsiri na shi'a shi ma ya ce wannan aya tana nuni kan fifitar sayyida zahara kan bakiɗayan mata.[4]

Sha'anin Sauka

Tushen ƙasida: Mubahalar Annabi (S.A.W) Tare da Kiristocin Najran

Ayar mubahala ta sauka matsayin amsa ga kiristocin najran.[5] wasu jama'a daga kiristocin najran sun je madina domin tattaunawa tare da annabin muslunci (s.a.w) dangane da da'awar aiko da Allah ya yi, annabi bayan ya gabatar musu da kansa, ya bayyana musu cewa annabi isa (a.s) bawan Allah ne, sai dai cewa kiristocin najran sun bayyana masa cewa haihuwar annabi isa ba tare da uba ba, hakan dalili ne da yake tabbatar da allantakarsa.[6] kiristocin najran sun kafe kan aƙidarsu da abin da suke imani kansa, sai annabi ya gayyace su zuwa yin mubahala, suka karɓi goran gayyatarsa. A ranar da aka sanya za a yi wannan mubahala sai annabi (s.a.w) ya halarci wannan mubahala tare da ali, faɗima, hassanaini (Hassan da Husaini); sai dai kuma Baya da waɗannan kiristoci na najran suka fahimci yadda annabi tare da ƴan rakiyarsa suka himmatu da gaske kan wannan batu, waɗannan kiristoci na najran sai suka janye daga wannan mubahala bisa shawarar manyan cikinsu, suka yi sulhu da annabi (s.a.w) suka roƙe shi ya bari su cigaba da yin addininsu da sharaɗin za su dinga biyan jiziya, sai annabi (s.a.w) ya yarda da buƙatarsu.[7]

Tafsiri

A cewar khadi nurullahi shushtari malamin kalam a shi'a, haƙiƙa malaman tafsiri sun yi ittifaƙi cewa «ابناءَنا» (ƴaƴanmu) a ayar mubahala ishara ce zuwa ga hassan da husaini, «نساءَنا» (Matanmu) faɗima (s), «اَنفُسَنا» imam ali (a.s).[8] allama majlisi yana ganin cewa hadisan da suke shiryarwa kan cewa wannan aya ta sauka ne kan as'habul kisa'i, hadisai ne mutawatirai[9] cikin littafin ihƙaƙul al-haƙƙi wanda aka rubuta a shekara ta 1014 an kawo litattafan ahlus-sunna ɗaiɗai har guda 60 da suka yi bayani ƙarara game da mutanen da wannan aya ta sauka kan sha'aninsu.[10] daga jumlarsu akwai jarullahi zamakshari cikin littafin kashshaf.[11] altafsirul al-kabir na fakhrur razi.[12] da anwarul tanzil wa asrarul ta'awil na abdullahi ɗan umar baizawi.[13]

Malaman tafsiri na shi'a dangane da kasancewar kalmomin «اَبْناءَنا»، «نِساءَنا» و «اَنْفُسَنا» sun zo ne da sigar jam'i daidai lokacin mutanen da suka sauka kansu ɗaiɗaiku ne da biyu ba jam'i ba, sun ce: 1.Sha'anin saukar ayar, shaida kan ingancin wannan fassara; saboda bisa ittifaƙin malaman tafsiri, haƙiƙa manzon Allah (s.a.w) babu waɗanda ya kirawo suka halarci wannan mubahala sai ali da fatima hassan da husaini.[14]

2.Cikin kwangila da yarjejeniya a wani lokacin ana amfani da lafuzzan jam'i domin su samu ɗabbaƙuwa kan dukkanin misdaƙai, amma a marhalar zartarwa ta yiwu su kaɗaitu kan iya mutum guda, wannan kadaicewa cikin misdaƙai baya cin karo da kasancewar gamewar mas'alar, alal misali cikin kwangila ana rubuta cewa waɗanda suke da alhaki cikin wannan kwangila sune mutanen da suka sanya hannu kan takardar kwangila da kuma ƴaƴansu; daidai lokacin ta yiwu ma shi wanda zai yi kwangilar ɗa guda ɗaya gareshi ko dai guda biyu.[15]

3.Cikin kur'ani akwai wurare da aka yi da sigar jam'i cikin saki kan misdaƙi guda ɗaya, misalin ayar zihari,[16] ayar zihari ta zo ne da lafazin jam'i «الَّذِينَ يُظَاهِرُونَ مِنكُم مِّن نِّسَائِهِم» daidai lokacin da ta sauka ne kan mutum guda ɗaya.[17]

Hujjoji Na Tarihi

Kan asasin riwayoyi, haƙiƙa imaman shi'a da ba'arin sahabbai sun jingina da ayar mubahala domin tabbatar da falalar imam ali (a.s):

Kafa Hujjar Sa'ad Bin Abi Waƙas

Amir ɗan sa'ad ɗan abi waƙas ya naƙalto daga babansa sa'ad ɗan abi waƙas cewa mu'awiya ya cewa sa'ad: me ya hanaka zagin ali? Sai sa'ad ya ce: matuƙar ina tunawa da abubuwa guda uku ba zan taɓa zaginsa ba, da ace ɗaya daga waɗannan abubuwa za su kasance kaina, zan kaunace su fiye da ace na samu jajayen raƙuma, daga jumlar waɗannan abubuwa akwai batun lokacin da ayar mubahala ta sauka, manzon Allah (s.a.w) ya kira ali da faɗima da hassan da husaini, sannan ya ce:

«اَللهُمَّ هؤلاءِ اَهلُ بَیتی»

Ya Allah waɗannan sune iyalan gidana.[18]

Kafa Hujjar Imam Kazim (A.S)

Haruna abbasi ya cewa imam kazim (a.s): ya zaka dinga cewa ku ne tsatson annabi, daidai lokacin da annabi bai da tsatso, saboda zuriya da tsatson mutum suna fitowa ne ta hanyar ƴaƴansa maza, ba mata ba, kai kuma kasancewa cewa kan ɗa ne na ƴar manzon Allah (s.a.w)? cikin wani ɓangare daga amsar da imam kazim ya bashi ya karanta ayar mubahala sannan ya ce: lokacin mubahala babu wanda yace annabi ya zo da wasu mutane komabayan ali da faɗima hassan da husaini, saboda haka abin nufi daga “ƴaƴanmu” su ne hassan da husaini, kuma abin nufi daga “Matanmu” ita ce faɗima, abin nufi daga “kawukanmu” shi ne ali ɗan abi ɗalibi.[19]

Kafa Hujjar Imam Rida (A.S)

Bisa rahotannida shaik mufid ya naƙalto, haƙiƙa mamun abbasi ya buƙaci imam rida (a.s) da ya kawo mafi girman falalar imam ali (a.s) daga cikin kur'ani. Imam rida (a.s) cikin bashi amsaya karanta ayar mubahala.[20] sai mamun yace: cikin wannan aya Allah ya kawo lafazin jam'i ne kan mata da ƴaƴa, daidai lokacin da annabi (s.a.w) kaɗai ya zo tare da rakiyar ƴaƴansa guda biyu da ɗiyarsa guda ɗaya, saboda haka amfani da lafazin (kawukanmu) yana nufi shi kansa shi kaɗai, saboda haka babu wata falala ga imam ali (a.s) cikin wannan aya, cikin bashi amsa imam rida (a.s) yace: abin da ka faɗa ba daidai bane saboda mai kira ba kowa bane face kansa yake kira kenan, kamar yanda shi mai umarni yana umarni ne ga waninsa, kuma bai kira wani mutum ba komabayan imam ali (a.s) saboda ta tabbata shi imam shi ne wannan nafsu da Allah yake nufi cikin littafinsawanda ya sanya hukuncinsa cikin kur'ani.[21]

Ijtihadodin Fiƙihu

Ba'arin masu bincike da malaman tafsiri a wannan zamani na ƙarni na sha biyar sun yi ijtihadi hukunce-hukunce daga wannan aya; daga jumlarsu:

  • Halascin mata suna iya shiga fagen gwagwarmayar siyasa zamantakewa: an ciro wannan hukunci ne daga kalmar «نساءَنا» tare da halartar da sayyada faɗima (s) ta yi cikin mubahala,[22] a cewar sayyid abdul a'ala sabzawari malamin tafsiri na shi'a (Wafati:1414.h.ƙ) duk da cewa maginar kur'ani ta kasance kan asasin kinaya da kare mutuncin mata, amma tare da haka amfani da kalmar «نساءَنا» cikin ayar mubahala tana shiryarwa kan shigar mata cikin fagen al'amuran da suka shafi addini.[23] a cewar rashid rida, cikin ayar mubahala na yi hukuncin tarayyar mata tare da maza cikin gwagwarmayar ƙabilanci da addini, kuma wannan hukunci ya ginu ne a kan daidaiton mata da maza a cikin ayyukan jama'a da na yau da kullum, sai dai cikin lamuran yaƙi da aka yi togaciya.[24]
  • Halascin yin mubahala: marubucin ƙasidar khoneshe fiƙhi jadid az aye mubahala (Sabuwar fahimar fiƙihu daga ayar mubahala) tare da amfani da da ayar mubahala, ya ciro halascin yin mubahala a cikin addinin muslunci.[25] domin tabbatar da abin da yake da'awa ya kafa hujja da samfuran wasiyoyi kan mubahala da yadda imamai ma'asumai suka koyar da yadda ake mubahala; misalin yadda buraira ɗan khudairu hamdani ɗaya daga cikin sahabban imam husaini (a.s) ya gayyaci yazidu ɗan ma'aƙil daga sojojin umar ɗan sa'ad a ranar ashura zuwa ga yin mubahala.[26] a gaban imam husaini (a.s) tare da haka imam bai kwaɓe shi kan mubahala ba.[27]
  • Cikin tafsirul amsal wanda aka rubuta shi a ƙarni na sha biyar bayan hijira. Ya zo cewa duk da cewa umarnin yin mubahala ya keɓantu da annabi (s.a.w) shi kaɗai, amma tare da haka gayyata zuwa ga mubahala wani abu ne da ya halasta kuma na kowa da kowa.[28]
  • Halascin kare muslunci tare da sadaukar da rai da dukiya,[29] a cewar sayyid abdul a'ala sabzawari cikin tafsiru mawahibul ar-rahman, ɗaya daga cikin nuƙɗoɗi daga ayar mubahala ana amfani da su da cewa hadafin kowanne mutum shi ne tabbatar da gaskiya tare da kareta, ya kasance yana da wannan tanadi na cewa shirye yake a kowanne lokaci ya sadaukar da rayuwarsa, danginsa da dukiyarsa kan kare gaskiya.[30]

Bayanin kula

  1. Misali, duba Tabarsi, Majmaal Bayan, 1372, juzu’i na 2, shafi na 764; Muzaffar, Dalai al-Sidegh, 1422 AH, juzu'i na 4, shafi na 403-404.
  2. Baidawi, Anwar al-Tanzil wa Asrar al-Tawil, 1418 AH, juzu'i na 2, shafi na 21.
  3. Zamakhshari, Al-Kashaf, 1415 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 370.
  4. Tabarsi, Majmaul al-Bayan, 1372, juzu'i na 2, shafi.746.
  5. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 2, shafi.762
  6. Makarem Shirazi, Tafsir namuneh , 1374, juzu'i na 2, shafi na 575.
  7. Makarem Shirazi, Tafsir namuneh, 1374, juzu'i na 2, shafi na 575.
  8. Marashi, Ahqaq al-Haq, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 46.
  9. Majlesi, Haq al-Iqin, Islamic Publications, juzu'i na 1, shafi na 67.
  10. Duba: Marashi, Ahqaq al-Haq, 1409 AH, Juzu'i na 3, shafi na 72-46.
  11. Zamakhshari, Al-Kashaf, 1415 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 370
  12. Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH. Juzu'i na 8, shafi na 247.
  13. Baidawi, Anwar al-Tanzil wa Asrar al-Tawil, 1418 AH, juzu'i na 2, shafi na 21.
  14. Duba Tabarsi, Majma al-Bayan, 1372, juzu'i na 2, shafi na 763; Tabatabai, Al-Mizan, 1351-1352, juzu'i na 3, shafi.223; Makarem Shirazi, Tafsir namuneh, 1374, juzu'i na 2, shafi na 586.
  15. Makarem Shirazi, Tafsir namuneh, 1374, juzu'i na 2, shafi na 586-587.
  16. Duba Tabatabaei, Al-Mizan, 1351-1352, juzu'i na 3, shafi na 223.
  17. Duba Tabatabaei, Al-Mizan, 1351-1352, juzu'i na 3, shafi na 223-224.
  18. Misali, duba Tabatabai, Al-Mizan, 1351/1352, juzu’i na 3, shafi na 232.
  19. Tabatabai, Al-Mizan, 1351/1352, juzu'i na 3, shafi na 229-230.
  20. Mufid, Al-Fusul al-Mukhtarah, 1414H, shafi na 38.
  21. Mufid, Al-Fusul al-Mukhtarah, 1414H, shafi na 38.
  22. Al-Ghafouri, " Khoneshe fikhi Jadid az ayeh Mubahlah (2)", shafi na 48-49.
  23. Sabzevari, Mohabeul Rahman, 1409-1410 A.H., juzu'i na 6, shafi na 18-19.
  24. Rashid Reza, Tafsir al-Manar, 1990, juzu'i na 3, shafi na 266.
  25. Al-Ghafouri, " Khoneshe fikhi Jadid az ayeh Mubahlah (1)", shafi na 73.
  26. Tabari, Tarikh al-Umam wa al-Muluk, 1387H, juzu'i na 5, shafi 432.
  27. Al-Ghafouri, " Khoneshe fikhi Jadid az ayeh Mubahlah (1)", shafi na 76-79.
  28. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh. 1374, juzu'i na 2, shafi na 589.
  29. Al-Ghafouri, " Khoneshe fikhi Jadid az ayeh Mubahlah (2)", shafi na 52
  30. Sabzevari, Mohabeur Rahman, 1409-1410 A.H., juzu'i na 6, shafi na 8.

Nassoshi

  • Beidawi, Abdullah bin Umar, Anwar al-Tanzil wa Asrar al-Tawil (Tafsir al-Baidawi), Beirut, Al-Ahya al-Tratah al-Arabi, 1418 AH/1998 miladiyya.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, al-Tafsir al-Kabir, Beirut, Dar Ihya al-Tarat al-Arabi, 1420H/1999 Miladiyya.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiyya, bugun farko, 1374
  • Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Fusul al-Mukhtara, bincike na Seyyed Mir Ali Sharifi, Beirut, Dar Al-Mofid, Al-Taaba al-Thaniyyah, 1414H.
  • Rashid Reza, Mohammad Rashid bin Alireza, Tafsir al-Qur'an al-Karim (Tafsir al-Manar), Al-Masriyyah Al-Al-Katab, 1990.
  • Sabzevari, Sayyid Abd al-Ali, Muhabbe al-Rahman fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Ahl al-Bait Institute (A.H.), 1409-1410 AH.
  • Shushtri, Qazi Nurullah, Ihqaq al-Haq wa Izhaq al-Batil, Kum, Laburaren Ayatullahi Murashi Najafi, bugu na farko, 1409H.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Al-umam wa Al-Muluk, wanda Muhammad Abulfazl Ibrahim ya yi bincike a Dar al-Trath, Beirut, bugu na biyu, 1387/1967 miladiyya.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosrow, bugu na uku, 1372.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, 1351/1352.
  • Zamakhshari, Mahmoud, Al-Kashshaf an haqa'iq Ghwamaz al-Tanzil, Qum, bugun Al-Balagheh, bugu na biyu, 1415 AH.
  • الغفوری، خالد، «خوانش فقهی جدید از آیه مباهله(۲)»، ترجمه محمودرضا توکلی محمدی، کوثر معارف، ش۲۲، تابستان ۱۳۹۱ش.
  • الغفوری، خالد، «خوانش فقهی جدید از آیه مباهله(۱)»، ترجمه محمودرضا توکلی محمدی، کوثر معارف، ش۲۱، بهار ۱۳۹۱ش.