Ayar Inzar

Daga wikishia

Ayar Inzar, Suratul Shu’ara aya ta 214 an umarci Annabi (S.A.W) da gargaɗin Danginsa da Makusantansa a bayyane tare da kiransu zuwa ga Muslunci, bayan saukar wannan aya Manzon Allah (S.A.W) ya ta shi ya kirayi Mutane Arba’in daga Makusantansa, bayan kiransu zuwa ga Muslunci sai ya gabatar musu da Ali Bn Abi ɗalib (A.S) matsayin Halifansa a bayansa, Malaman Kalam na Shi’a tare da jingina da riwayoyin sha’anin saukar wannan aya suna amfani da ita kan tabbatar da Halifancin Imam (A.S). Malaman tafsirin Shi'a sun yi la'akari da nisantar nuna wariya ga 'yan uwa wajen faɗakarwa da gargadin cewa kada a yi sakaci da wasu a cikin addini, da kuma faɗakar Danginsa kan tsafta da tsarkakar Annabi (S.A.W) matsayin dalilansa na farawa da kiransu zuwa ga Muslunci.

Sanadi da Madogara Ta Farko Kan Imamanci Imam Ali (A.S)

Aya ta 214 daga suratul Shu’ara ta kasance mafi shaharar aya da ake kiranta da ayar Inzar (ayar gargaɗi) an ce Ayar Nafar aya ta bakwai cikin Suratul Shura da ayoyi na 1-2 daga suratul Mudassir suma ana kiransu da wannan suna na inzar. [1] cikin wannan aya Ubangiji ya umarci Hazrat Muhammad (S.A.W) da ya kira Makusantansa zuwa ga Muslunci, haka kuma cikin Tafsir Namune ya zo cewa an umarce shi da ya gargaɗesu daga shirka da saɓawa Ubangiji. [2] Ana la’akari da wannan aya matsayi aya ta farko da ta sauko wurin Annabi (S.A.W) kan isar da saƙon muslunci a bayyane a fili [3] wasu ba’ari tare da jingina da riwayoyin da suka zo kan sha’anin saukar ayar inzar (Ayar gargaɗi) suna ganin wannan aya ita ce ƙarfafaffar Madogara da sanadi kan Imamancin Imam Ali (A.S) [4] Marubutan Tarihi sun bayyana cewa wannan aya ta sauka a shekara ta uku bayan aiko da Annabta. [5]

  1. Bashoy, “Ayeh Inzar”, shafi na 149.
  2. مکارم، تفسیر نمونه، ۱۳۷۴ش، ج۱۵، ص۳۶۶.
  3. Moulainia wa Momeni, “Tafsir Tadbiki aye Inzar Az didgahe Farikaini” shafi na 144.
  4. Moulainia wa Momeni, “Tafsir Tadbiki aye Inzar Az didgahe Farikaini” shafi na 164
  5. Misali, duba: Ibn Athir, Al-Kamal fi al-Tarikh, 2005, juzu'i na 2, shafi:60; Balazari, Ansab Al-Ashraf,