Labarin Karya Gumaka

Daga wikishia
wannan kasida ce game da labarin Karya gumaka domin neman nazarin littafi mai suna da yake da wannan suna ku duba: Karya Gumakan Jahiliyya
Haramin Imam Ali (A.S)

Waki’ar Karya Gumaka (Larabci: واقعة كسر الأصنام) batu ne dangane kakkarya Gumakan da suka kasance a Saman Rufin dakin Ka’aba hakan ya faru ne ta hannun Imam Ali (A.S) ya dora kafafun sa kan kafadun Annabi (S.A.W) ya yunkura ya hau saman dakin Ka’aba ya wuwwurgo Gumaka Misalin Hubal da sauransu, dukkanin litattafan bangarori biyu Shi'a da Ahlus-sunna sun nakalto wannan tarihi, sannan na bayyana cewa wannan abu ya faru ne a Lailatul Mabit daren da Imam Ali (A.S) Ya kwanta a kan gadon Annabi (S.A.W) domin dauke hankalin Makiya, ko kuma dai Fatahu Makka. Labarin Karya Gumaka ya kasance dalilin saukar ayoyin

«وَ قُلْ جَاءَ الْحَقُّ وَ زَهَقَ الْبَاطِلُ...» و «وَ رَفَعْناهُ مَكاناً عَلِيًّا»

Hazrat Muhammad bayan faruwa wannan lamari ya bayyana cewa Annabi Ibrahim (A.S) shi ne farkon wanda ya fara karya Gumaka sannan kuma Imam Ali (A.S) shi ne Karshen wanda ya krya Gumaka, a wata riwaya an ambaci Imam (A.S) matsayin Kasirul Asnam (Mai Karya Gumaka)

Waki’ar karyar Gumaka tana daga cikin falalolin Imam Ali (A.S) Imam Ali (A.S) cikin kwamitin shura wanda ya tattaro mutane shida domin zabar wanda zai gaji Umar Bn Khattab hakika ya jingina da wancan falala ta karya Gumaka, wasu ba’arin Masadir na Ahlus-sunna sun dogara da wannan Kissa kan wajabcin rusa duk wani abu da zai taiamaka kan aiakata saɓo.

Sharhin Waki'a

Labarin Karya gumaka, Kasr Asnam, wanda aka shirya a karni na 11 bisa umarnin Sultan Murad III, Sarkin Daular Usmaniyya, da Seyed Suleiman Kasim Pasha.

Labarin Karya Gumaka ko kuma (Hadisul Kasri Asnam)1 wata Kissa ce da Annabi (S.A.W)[1] ya dauki Imam (a.s) a Kafadar sa domin ya hau kan saman rufin dakin Ka’aba ya rusa dukkanin Gumakan da suke kan rufinta [2] cikin wannan waki’a tana hikaya ne game da rusa wasu ba’arin Gumaka misalin Hubal [3] na’am game da juz’iyyat wannan waki’a akwai sabani ra’ayi , a wani yanki na wani nakali ya zo cewa da farko Imam (A.S) ne ya nemi Annabi (S.A.W) ya hau kan kafadar sa amma sai ya zamana bai samu iya yin hakan ba sai Ali (A.S) ya hau kan kafadar Annabi (S.A.W) ya tsallaka rufin Ka’aba [4] ya wurga Gumaka daga rufin ta zuwa kasa, a wani rahotan ya zo cewa shawara ta farko daga Imam Ali (A.S) shi ne ya nemi Annabi (S.A.W) ya hau kan kafadar sa, sai Annabi (S.A.W) ya tunatar da shi cewa babu wanda zai iya zartar da wannan aiki[5] an fadin Jabir Bn Abdullahi wannan mas’ala ta kasance sakamakon nauyin sako [6] an kawo wasu dalilan na daban [7] kan asasin wani nakali ya zo cewa tun farko Annabi (S.A.W) ne ya fara yin umarni ga Imam Ali (A.S) ya hau kan kafadar sa.[8] [Yadasht 1]

Dangane da yaya Imam Ali (A.S) ya sauko daga saman Ka’aba an nakalto daga wasu ba’arin riwayoyi cewa Imam (A.S) yayi tsalle ya sauko kasa da kansa daga saman rufin dakin Ka’aba wanda nisansa [9] ya kai ziara’i 40 kuma tare da haka bai ji ko da kwarzane daga ciwo ba [10] a wani hadisi ya zo cewa bayan Imam ya diro kasa Annabi (S.A.W) ya ce: Jibrilu ya dauko ka daga saman Ka’aba zuwa kasa[11] kan asasin wani hadisi an samu rahoto daga Umar Bn Kattab cewa bayan Imam Ali (A.S) ya wurgo Gumaka kasa Umar ya yi buri da fatan samun wannan daraja da matsayi yana cewa Ubangijin da Ali yake bautawa bai bari Ali ya fado kasa ba [12]

A wasu riwayoyin ya zo cewa Annabi (S.A.W) cikin wannan waki’a [13] ya dinga karanta ayar [14]

«وَ قُلْ جَاءَ الْحَقُّ وَ زَهَقَ الْبَاطِلُ...» و «وَ رَفَعْناهُ مَكاناً عَلِيًّا»

Gaskiya ta zo Karya ta gushe lallai ita Karya ta kasance Mai gushewa Da wannan ne abin d aya faru na karya Gumaka ya zama sababin saukar wannan aya [15] haka kuma a wata riwaya da Ibn Shahre ashub ya nakalto ayar

«وَ رَفَعْناهُ مَكاناً عَلِيًّا»

Mu daga shi zuwa wani matsayi madaukaki [16] Ta sauka ne kan wannan waki’a [17] labarin karya Gumaka an nakalto daga dukkanin bangarori biyu na musulmi `Yan shi’a [18] da Ahlus-sunna [19] Abdullahi Bn Abbas [20] Jabir Bn Abdullahi Ansari [21] Abu Maryam [22] sun rawaito wannan waki’a. Allama Amini cikin littafin Alghadir ya ware Fihrisa guda da ya tattaro Malaman Ahlus-sunna da suka bada rahoton wannan waki’a [23]

Ƙididdigar kyawawan halaye

Daukar Imam (A.S) a kafada da Annabi (S.A.W) ya yi yana cikin Falaloli da ya kebantu da su [24] wannan waki’a an kawo ta cikin litattafan Falala [25]da Wakokin Mawaka [26] Hazrat Muhammad (S.A.W) bayan wannan waki’a ya bayyana Annabi Ibrahim (A.S) a matsayin farkon wanda ya fara karya Gumaka Imam Ali (A.S) kuma matsayin na karshen wand aya karya Gumaka [27] a wasu riwayoyin an ambaci Imam Ali (A.S) da taken Kasirul Asnam (Mai karya Gumaka) [28] haka kuma Ibn Jauzi Malamin Ahlus-sunna wand aya bar duniya 655 h cikin littafin Tazkiratul Khawas cikin nakalin zantuka mabambanta yayi nakali kan asasin sunan da Mahaifiyar Imam Ali (A.S) ta sanya masa wato Haidar, sannan kuma ta fuskanin hawa kan kafadar Annabi (S.A.W) domin karya Gumaka saman rufin Ka’aba ya samu sunan Aliyu (Madaukakin daraja) da wannan hali Ibn Jauzi ya tafi kan cewa sunan Aliyu Mahaifiyar sa ce ta zaba masa shi a lokacin haihuwar sa [29]

Jingina da Waki’ar Karya Gumaka a Kwamitin Shura na Mutane Shida

Imam Aliyu (A.S) ya kasance yana alfahari da karya Gumaka da ya yi [30] yana cewa: ni ne wanda na dora kafafuna kan Hatamin Annabta (alamar da take tsakankanin kafadun Annabi) [31] a lokacin zaman kwamitin shura da Umar ya samar domin fitar da wanda zai gaje shi wadannan mutane na cikin Kwamiti sun tabbatar masa da faruwar waki’ar karya Gumaka da cewa babu wanda ya samu wannan Falala banda shi [32] haka kuma Umar Bn Kattab ya kasance yana buri da fatan samun wanda daraja inama ni ne na samu wannan abin alfahari [33]

Lokaci

A galibin Masadir an ambaci cewa wannan waki’a ta faru ne da daddare [34] a boye [35] tare da haka a wasu Masadir din kuma an bayyana cewa ta faru a daren (Lailatul Mabit) [36] daren da Imam Ali (A.S) ya kwanta kan shimfidar Annabi (S.A.W) domin kawar da hankalin Makiya a daren da Annabi (S.A.W) ya fita daga garin Makka ko kuma lokacin Fatahu Makka [37] Allam Majlisi cikin littafin Biharul-Al-Anwar ya kawo wata riwaya daga Imam Sadik (A.S) cewa wannan waki’a ta faru ne a Noruz (sabuwar shekarar Farisawa) [38]

Cikin littafin Daneshnameh Amirul Muminin bayan binciken riwayoyin masu yawa, ya bayyana cewa yiwuwar faruwar wannan waki’ar a daren (Lailatul Mabit) yana da karfi sosai [39] haka kuma Allama Majlisi ya kawo tsammani kan cewa karya Gumaka ya faru a lokuta da dama [40]

Natijoji

Kan asasin ba’arin wasu riwayoyi karya Gumaka ta hannun Imam Ali (A.S) shi ne dalili da ya hana Mushrikai kara ajiye Gumaka cikin Dakin Allah [41] a wasu Masadir din Ahlus-sunna wannan waki’a dalili kan wajabcin rushe duk wani abu da ake aikata sabo da shi [42]

Bayanin kula

  1. Allameh Hali, Nahj al-Haq, 1982, shafi na 223.
  2. Shushtri, Ihqaq al-Haq, 1409 AH, juzu'i na 18, shafi na 162.
  3. Haskani, shawaheed al-Tanzil, 1411 AH, juzu'i na 1, shafi na 453-454; Ibn Shahar Ashub,
  4. Nasa’i, Al-Sunan al-Kubra, 1421 AH, juzu’i na 7, shafi:451; Abi Ya’ali, Musnad, 1410H, juzu’i na 1, shafi na 251-252.
  5. Bahrani, al-Burhan, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi na 579-580.
  6. Ibn Shahrashob, Manaqib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 135.
  7. Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, 1403 AH, shafi na 350-352; Bahrani, al-Burhan, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi na 576-578.
  8. Ibn Shahr Ashub, Manaqib, 1379 Hijira, Juzu'i na 2, shafi na 136, 141.
  9. Ibn Shahrashob, Manaqib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 141.
  10. Hakim Neishaburi, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, 1422 AH, juzu'i na 2, shafi na 398.
  11. Bahrani, Al-Burhan, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi na 580.
  12. Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 38, shafi na 77, ya nakalto daga majiyoyin Sunna.
  13. suratu Isra, aya ta 81
  14. Hakim Neishaburi, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, 1422 AH, juzu'i na 2, shafi na 398; Juzu'i na 3, shafi na 6.
  15. Haskani, shawaheed al-Tanzil, 1411 AH, juzu'i na 1, shafi na 453-454; Ibn Shahrashob, Manaqib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 135.
  16. suratu Maryam, aya ta 57
  17. Ibn Shahr Ashub, Manaqib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 135.
  18. Misali, Ibn Shahrashob, Manaqib, 1379 AH, juzu'i na 2, shafi na 135-142; Shushtri, Ihqaq al-Haq, 1409 AH, juzu'i na 18, shafi na 162-168.
  19. Ibn Abi Shaiba, al-Musannaf, 1429 AH, juzu'i na 13, shafi na 146-147;Ahmad Ibn Hanbal, Musnad, 1416 AH, juzu'i na 2, shafi na 73-74; Bezar, Musnad Bezar, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi na 21-22; Nasa’i, Al-Sunan al-Kubari, 1421 AH, juzu’i na 7, shafi:451; Abi Ya’ali, Musnad, 1410 AH, Juzu’i na 1, shafi na 251-252; Al-Tabari, Tahdhib Al-Akhtar, Masnad Ali bin Abi Talib (AS), Beta, shafi na 236-240; Hakim Neishaburi, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, 1422 AH, juzu'i na 2, shafi na 398, juzu'i na 3, shafi na 6.
  20. Ibn Shahrashob, Manaqib, 1379 AH, Juzu'i na 2, shafi na 136, 141.
  21. Haskani, shawaheed Al-Tanzil, 1411 AH, juzu'i na 1, shafi na 453; Ibn Shahrashob, Manaqib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 135.
  22. Misali: Ibn Abi Shaiba, al-Musannaf, 1429 AH, juzu'i na 13, shafi na 146-147; Ibn Hanbal, Musnad, 1416 AH, juzu'i na 2, shafi na 73-74; Bezar, Musnad Bezar, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi na 21-22; Nasa’i, Al-Sunan al-Kubari, 1421 AH, juzu’i na 7, shafi:451; Abi Ya’ali, Musnad, 1410H, juzu’i na 1, shafi na 251-252.
  23. Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, Mujalladi na 7, shafi na 18-24.
  24. Nasa’i, Al-Sunan al-Kubra, 1421 AH, juzu’i na 7, shafi:451; Nasa’i, Kasa'is Amirul-Mu’uminina, 1424H, shafi na 96; Basti, Kitab al-Maratb, 1421H, shafi na 124.
  25. Ibn Shahrashob, Manaqib, 1379 AH, juzu'i na 2, shafi na 135-142; Shushtri, Ihqaq al-Haq, 1409 AH, juzu'i na 18, shafi na 162-168.
  26. Bekri, Anwar, 1411 AH, shafi na 148; Har Aamili, Isbatul al-Huda, 1425 AH, juzu'i na 3, shafi na 424.
  27. Ibn Shazan, Al-Fadael, 1363, shafi na 97.
  28. Ibn Shazan, al-Rawda, 1423 AH, shafi na 31.
  29. Ibn Juzi, Tazkira al-Khawas, 1418H, shafi na 15.
  30. Ibn Shahrashob, Manaqib, 1379 AH, juzu'i na 2, shafi na 136; Ibn Shazan, Al-Fadael, 1363, shafi na 85.
  31. Ibn Shahrashob, Manaqib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 136.
  32. Tabarsi, al-Ihtijaj, 1403 AH, juzu'i na 1, shafi na 138; Bahrani, Hilyatul Abrar, 1411 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 329.
  33. Ibn Shahrashob, Manaqib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 136.
  34. Hakim Neishaburi, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, 1422 AH, juzu'i na 2, shafi na 398; Ibn Shahrashob, Manaqib, 1379 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 141.
  35. Ibn Hanbal, Musnad, 1416 AH, juzu'i na 2, shafi na 73-74; Bezar, Musnad Bezar, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi na 21-22; Abu Yali, Musnad, 1410 AH, Juzu’i na 1, shafi na 251.
  36. Hakim Neishaburi, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, 1422 AH, juzu'i na 3, shafi na 6.
  37. Ibn Shahr Ashub, Manaqib, 1379 Hijira, Juzu'i na 2, shafi na 135, 140.
  38. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 56, shafi na 138.
  39. Mohammadi Rishahri, Daneshnameh Amirul Mominin, 1389, juzu'i na 1, shafi na 223.
  40. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 56, shafi na 138.
  41. Ibn Shazan, Al-Fadael, 1363, shafi na 97.
  42. Al-Tabari, Tahdhib Al-Asar, Masnad Ali bin Abi Talib (A.S), Beta, shafi na 240-238.

Nassoshi

  • Ibn Abi shaibah, Abdullah bin Muhammad, al-Musannaf Laban Abishaibah, bincike na Osama bin Ibrahim bin Muhammad, Alkahira, Farooq al-Hadithah na bugawa da bugawa, 1429 Hijira.
  • Ibn Jauzi, Yusuf bin Hussam, Tazkira Al-Khawas, Qum, Al-Sharif Al-Radhi's Manifesto, 1418H.
  • Ibn Hanbal, Ahmad bin Muhammad, Masnad al-Imam Ahmad bin Hanbal, Shoaib al-Arnawut da Adel Murshid suka yi bincike a Beirut, Cibiyar Al-Rasalah, 1416H.
  • Ibn Shazan, Shazan bin Jibreel, al-Rawda fi Fada’il Amir al-Mu’minin Ali bin Abi Talib (a.s.), Bincike na Ali Shekarchi, Kum, Makarantar Al-Amin, 1423 Hijira.
  • Ibn Shazan, Shazan bin Jibreel, al-Fadael, Kum, Razi, bugu na biyu, 1363.
  • Ibn Shahrashob Mazandarani, Muhammad Bin Ali, Menaqib Al Abi Talib (AS), Qom, Allameh, 1379H.
  • Abi Ya'ali, Ahmad bin Ali, Musnad na Abi Ya'ali al-Mosali, Huseen Salim Asad bincike, Damascus, Darul Ma'amun na gado, bugu na biyu, 1410H.
  • Amini, Abdul Hossein, Al-Ghadir a cikin Al-Kitab da Sunnah da Al-Adab, Qum, Al-Ghadir Center for Islamic Studies, 1416H.
  • Bahrani, Hashim bin Suleiman, Al-Burhan fi Tafsirin Al-Qur'an, bincike na Islamic Research Unit of Ba'ath Foundation, Qom, Ba'ath Institute, 1415 AH.
  • Bahrani, Hashim bin Suleiman, Hilyatul Al-Abrar fi Ahwaal Muhammad wa Alah al-Athar (AS), Qum, Islamic Encyclopaedia Foundation, 1411 AH.
  • Bazzar, Ahmad bin Amr bin Abdul Khaliq, Bahr al-Zakhar (Musnad Bazzar), bincike na Mahfuz al-Rahman Zainullah, Beirut, Al-Qur'an Institute, 1409 AH.
  • Basti, Ismail bin Ahmed, Kitab Al-Muratab Fi Fada'el Amir al-Mu'minin da Sayyid Al-Wasiyin (AS), Bincike na Mohammad Reza Ansari Qomi, Qom, Dilil Ma, 1421H.
  • Bakri, Ahmad bin Abdullah, Al-Anwar da Miftah al-Sarur da al-Afkar fi Mauld al-Nabi al-Mukhtar, Qom, Razi, 1411H.
  • Hakeem Neishaburi, Muhammad bin Abdullah, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, bincike na Mustafa Abd al-Qadir Atta, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, bugu na biyu, 1422H.
  • Hurrul Amili, Muhammad bin Hassan, Isbataul Huda bin Nususi wal-Mujizat, Beirut, Alami, 1425H.
  • Haskani, Obaidullah bin Abdullah, Shawaheed Al-Tanzil na Qabam al-Tfadil, Bincike na Mohammad Bagher Mahmoudi, Tehran, Ma'aikatar Al'adu da Jagorar Musulunci, 1411H.
  • Ragheb Esfahani, Hossein bin Mohammad, Kalmomin Al-Qur'ani, wanda Safwan Adnan Dawudi ya yi bincike a Beirut, Darul-Qalam, 1412H.
  • Shafi'i, Muhammad bin Idris, Diwan, Beirut, Darul Katb al-Arabi, 1414H.
  • Shushtri, Nurullah, Ihqaq al-Haq wa Izhaq al-Batil, Kum, Laburaren Ayatullah Murashi Najafi, 1409H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ma'ani Al-Akhbar, bincike na Ali Akbar Ghafari, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, 1403H.
  • Tabarsi, Ahmad bin Ali, Al-Ihtijaj Ali Ahl al-Jajj, Mohammad Baqer Khorsan, Mashhad, Mawallafin Morteza, 1403H ya yi bincike.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tahdib Al-Asar da cikakken bayanin manzon Allah (SAW) Man al-Akhbar, Musnad Ali bin Abi Talib, Mahmoud Muhammad Shakir, Alkahira, Al-Madani Press, Beta ya yi bincike.
  • Ameli Bayazi, Ibrahim bin Suleiman, Al-Ozan da Al-Maqadir, Beirut, Bina, 1381
  • Allameh Hilli, Hassan bin Yusuf, Nahjul al-Haq da Kashf al-Saddeq, dakatarwar Ainullah Hosni Ermoi, Beirut, Dar al-Kitab al-Lebanani, 1982.
  • Majlisi, Mohammad Baqir, Bihar al-Anwar al-Jamaa Lederer Akhbar al-Imam al-Athar, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • Mohammadi Rayshahri, Muhammad da sauransu, Daneshnameh Amir al-Mu'minin, Qum, Dar al-Hadith Scientific and Cultural Institute, 2009.
  • Nasa'i, Ahmad bin Shoaib, Al-Sunan Al-Kubara, Beirut, Al-Risalah Foundation, 1421H.
  • Nasa'i, Ahmad bin Ali, Kasa'is Amirul Muminina Ali bin Abi Talib, bincike: Dani bin Munir al-Zahwi, Beirut, al-Maktaba al-Asriyah, 1424H.