Ajiyoyin Imamai
Ajiyoyin Imamanci,(Larabci ودائع الإمامة) wasu keɓantattun kayayyaki ne na Annabawa da Imam Ali (A.S) Hazrat Zahra (S) waɗanda suke tare da Imaman Shi'a kuma ana ɗaukarsu a matsayin ma'auni na gane Imam. daga cikinsu akwai Takobi da zoben Annabi (S.A.W), Sandar Musa, zoben Sulaiman, da littafin Mus'hafu Fatima (A.S) da Mus'haf Jafru da Jamia. Imaman Shi'a idan suka fuskanci akwai masu da'awar Imamanci bisa ƙarya suna amfani da waɗannan abubuwan wajan kauda shakkun `yan Shi'arsu.
Mafhumi Da Matsayi
Abin da ake nufi daga Ajiyoyin A'imma shi ne abubuwa na musamman, kamar Takobi, littafi, zobe, waɗanda aka damƙa wa Imami daga wancen zuwa wancan, kuma alama ce ta Imamancinsu. tare da wasiyyar Imamin daya gabata , wannan na daga cikin muhimman ma'aunai na tantance Imami na gaba,[1] musamman da yake ba a iya tabbatar da Imamanci da wasiyya, a zamanin taƙiyya, waɗannan abubuwan suna tabbatar da kasancewar mutumin da yake ɗauke da su matsayin Imami na gaba,[2] da kuma kawar da duk wata shakka wajen gane shi.[3]
Misdakai
Ajiyar Imamai | Karin bayani |
---|---|
Takobin Annabi (s.a.w).[4] | A cikin riwayar Imam Sadik (a.s) bayan kamanta takobin Annabi da akwatin Bani Isra'ila, an ce: Idan takobin Annabi (s.a.w) yana tare da kowannenmu, an ba shi Imamanci kenan.[5]
A bisa hadisai wannan takobi daya ce da Zulfiqar[6] |
Jafru.[7] | Littafi ne da ake ambaton abubuwan da zasu faru a cikinsa har zuwa tashin kiyama.[8] |
Jami'atu | Littafi ne da Manzon Allah (s.a.w) ya shifta kuma a rubutun hannun Imam Ali (a.s) kuma dukkan hukunce-hukuncen halal da haram suna cikinsa.[9] |
Kitabu Ali (A.S).[10] | Wasu sun dauki Kitabu Ali da Jami'atu a matsayin littafi daya mai suna biyu.[11] Amma Agha Bozur Tehrani ya ambaci wannan littafi mai suna Amali Rasoolullah kuma yana ganin ya bambanta da Jafar da Jamia.[12] |
Mus'hafu Fatima (S). | Littafin da mala'ikan Ubangiji ya saukar wa Sayyida Fatima (AS) da Imam Ali (a.s) ya rubuta shi.[13] Game da gado a rubutun hannun Imam Ali (a.s).[14] |
Zoben Annabi (S.A.W).[15] | |
Sulken Annabi (S.A.W).[16] | Ya zo a cikin hadisai cewa daya daga cikin alamomin Imam shi ne, sulke na Manzon Allah (SAW) ya dace da girmansa.[17] |
Jafru Surki | Ma'ajiyar da makamin Manzon Allah (s.a.w) yake.[18] |
Jafru Safid | Wurin ajiya inda Attaura, Littafi Mai Tsarki, Zabura da sauran littattafan sama suke.[19] |
Diwani Shi'ayan | wanda ya hada da sunayen ‘yan Shi'a. A wasu ruwayoyin, ana kiranta da "girmama".[20] |
Gadon Sauran Annabawa | Kamar alluna, kwanoni, akwatuna, sandar Annabi Musa (a.s) da zoben Sulaimanu (a.s).[21] |
Kafa Hujja da Ajiyoyin Imamai Kan Ingancin Imamancinsu
Imaman Shi'a suna amfani da waɗannan abubuwan wajen magance shubuhohin Shi'a. Misali Imam Ali (A.S) ya ce a majalisar Shura mai mutane shida: "Shin a tare daku akwai wanda yake da maƙami da tuta da zoben Manzon Allah".[22] Imam Sadik (A.S) a gefe guda yana fuskantar yunƙurin Hasaniyyawa da ke yaɗa ƙaryar bayyanar Imam Mahadi ga Muhammad Bin Abdullah Mahaz,[23] a ɗaya ɓangaren kuma yana fuskantar mas'aloli biyu na Kisaniyya da Zaidiyya, Anan ne ya yi amfani da makamin Annabi wajan tabbatar da ƙaryar su da cewa iƙirarin su bai da tushe balle makama.[24] An ruwaito cewa an ce wa Imam Sadiƙ (A.S) Wasu suna ganin cewa takobin manzon Allah yana wurin Abdullahi bin Hassan. Sai ya amsa da cewa: "Na rantse da Allah, Abdullahi bin Hassan bai taɓa ganinta ba. Takobi da tutar Manzon Allah (S.A.W) suna tare dan. Makamin Manzon Allah kamar tabut ne a tsakanin Bani Isra'ila. Duk inda aka sami tabut Annabci yana nan. Duk wanda yake da makamin Manzon Allah shi ne Imami".[25]
Ajiyoyin Imamai Daga Imami Zuwa Imami
Kan asasin hadisan Shi'a, shi Imamanci ana miƙa shi ne daga wancem lmamin zuwa wani lmanin, ko dai kai tsaye ko a kaikaice ta hanyoyi, An karbo daga Imam Sadik (A.S): akwai Littattafai da suka kasance tare da Ali (A.S). Lokacin da zai tafi Iraƙi, ya ba wa Ummu Salama ajiyar waɗannan littattafan. Bayansa waɗannan littattafani suna tare da Hasan (A.S), bayansa kuma suna tare da Husaini (A.S), sannan kuma tare da Ali Bin Husain (A.S), bayansa kuma tare da mahaifina.[26] Haka nan kuma an ruwaito cewa lokacin da Imam Husaini (A.S) ya ɗau hanyar tafiya ƙasar Iraƙi, ya damƙa littattafan da wasiyya ga Ummu Salama, matar Manzon Allah (S.A.W). Lokacin da Ali Bin Husaini (A.S) ya dawo sai Ummu Salama ta ba shi.[27] Haka nan an karbo daga Imam Baƙir (A.S) yana cewa: "Lokacin wafatin Ali Bn Husaini (A.S) ya ɗakko akwatin ya ce da ni: "Ya Muhammad ka ɗauki wannan akwati". A cikin wannan akwatin akwai Takobin manzon Allah (S.A.W) da littafansa.[28]
Ma'ajiyar Waɗannan Abubuwa A Lokacin Gaiba
Kan asasin Rahoton Allama Majlisi ya bayyana cewa, a zamanin gaiba sugra waɗannan abubuwan sun kasance a hannun wakilan Imam Zaman (A.S) na musamman, ya zo a cikin rahotonsa cewa, a lokacin da mataimakin Imam na biyu Muhammad bin Usman ya rasu, bawansa ya miƙa wani akwati da yake ɗauke da waɗannan abubuwan ga mataimakin Imam na uku, Husaini Bin Ruhu Naubekti.[29] A cewar Agha Bozurg Tehrani, bisa hadisai na Shi'a, a halin yanzu an damƙa waɗannan abubuwan ga Imami na goma sha biyu wato Imam Mahadi (A.F).[30]
Bayanin kula
- ↑ Sheikh Tusi, Al-Ektisad, 1430H, shafi na 375
- ↑ Tabatabaei, "Jastari dar Asib shinasi Caleshahaye Agaze Imamat Imam Kazim", shafi na 104.
- ↑ Tabatabaei, "Jastari dar Asib shinasi Caleshahaye Agaze Imamat Imam Kazem", shafi na 79.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, juzu'i na 1, 1362, shafi na 305.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1362, juzu'i na 1, shafi na 238.
- ↑ Ibn Shahr Ashub, al-Manaqib, 1379 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 135 da 253.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1362, juzu'i na 1, shafi na 239; Safar, Basaer al-Darajat, 1404H, shafi na 152.
- ↑ Sheikh Sadouq, Kamaluddin, 1395 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 353.
- ↑ Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 186.
- ↑ Saffar, Basa'ir al-Darajat, 1404H, shafi na 147.
- ↑ Askari, Ma’alim Al-Madrasataini, 1410H, juzu’i na 2, shafi na 335-338.
- ↑ Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1408H, Juzu'i na 2, shafi na 306-307.
- ↑ Saffar, Basa'ir al-Derajat, 1404 AH, shafi na 152-153.
- ↑ Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1408H, juzu'i na 2, shafi na 162.
- ↑ Safar, Basa'ir al-Derajat, 1404H, shafi na 156
- ↑ Saffar, Basa'ir al-Darajat, 1404H, shafi na 156.
- ↑ Ibn Shahr Ashub, al-Manaqib, 1379 AH, juzu'i na 1, shafi na 253; Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 217.
- ↑ Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 186.
- ↑ Sheikh Mofid, Al-Irshad, 1413 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 186.
- ↑ Saffar, Basaer al-Derajat, 1404H, shafi na 173.
- ↑ Safar, Basa'ir al-Deraj, 1404H, shafi na 175.
- ↑ Safar, Basa'ir al-Derajat, 1404H, shafi na 182
- ↑ Najafian Razavi, "Barasi cegi9nagi Munasabat Husainiyan wa Imaman Shi'a, Mutala'at Tarikh Islami", 1392.
- ↑ Sheikh Mufid, Al-Irshad, 1413H, juzu'i na 2, shafi na 187-188.
- ↑ Saffar, Basa'ir al-Derajat, 1404H, shafi na 175.
- ↑ Saffar, Basa'ir al-Derajat, 1404H, shafi na 164.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1362, juzu'i na 1, shafi.304; Ibnshahrashob, al-Manaqib, 1379H, juzu'i na 4, shafi na 172.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1362, juzu'i na 1, shafi na 305.
- ↑ Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 85, shafi na 211.
- ↑ Agha Bozur Tehrani, al-Dhari'a, 1408H, juzu'i na 21, shafi na 126.
Nassoshi
- Aghabuzur Tehrani, Mohammad Mohsen, Al-Dhari'a zuwa Saneef al-Shi'a, Qum, Ismailian, 1408H.
- Allameh Majlisi, Mohammad Baqer, Bihar al-Anwar al-Jamaa shugaban Akhbar Al-Aima al-Athar, Beirut, Wafa Institute, 1403 AH.
- Askari, Seyd Morteza, Ma'alem Al Madrastin, Beirut, Cibiyar Noman, 1410H.
- Ibnshahrashoob, Muhammad bin Ali, al-Manaqib, Qum, Allamah, 1379H.
- Kilini, Mohammad bin Yaqub, Al-Kafi, Tehran, Islamia, bugu na biyu, 1362.
- Najafian Razavi, Leila, "Binciken alakar Hasaniyawa da limaman Shi'a har zuwa shekara ta 145 Hijira", Nazarin Tarihin Musulunci, lamba biyar, 1392.
- Safar, Muhammad bin Hassan, Basa'er al-Deraj fi Fadael al-Muhammad, Qom, Ayatullah Murashi Najafi Library, bugu na biyu, 1404H.
- Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Arshad fi Mafarah Hajjullah Ali al-Abad, Qum, Congress of Sheikh Mofid, 1413 AH.
- Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din da Tammam al-Naimah, Ali Akbar Ghafari, Tehran, Islamia, bugu na biyu, 1395H.
- Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Ektidis Fima Yajab Ali Al-Abad, wanda Seyyed Kazem Mousavi ya yi bincike, Qom, Dilil Ma, bugu na farko, 1430H.
- Tabatabaei, Mohammad Kazem, "Bincike Akan Dabarar Mafarkin Mafarkin Imamancin Imam Kazem", Jaridar Nazarin Imamanci, lamba 8, Shekara ta 2, Winter 2013.