Bismillahi Ar-Rahmanir Ar-Rahim

Daga wikishia
Bismillah rubutun hannun Gulam Husaini Amir Khani

Bismillahi Ar-Rahmanir Ar-Rahim(Larabci:بسم الله الرحمنّ الرحيم) ko kuma basmala aya ce daga ayoyin Kur'ani wacce ita ce farkon dukkanin surori in banda suratul tauba, kamar yadda ya zo a riwaya an yi bayanin falaloli game da wannan aya, daga jumlarsu ita ce aya mafi karamci kuma mafi girman ayoyin kur'ani. Malamai suna ganin ayar bismilla daga mafi muhimmancin taken muslunci tare da yin nasiha kan fara yin bismillah gabanin kowanne aiki.

Kan asasin fatawowin malamai, haƙiƙa baya halasta a taɓa rubutun bismilla ba tare da alwala ba, haka nan yayin farauta ko yanka na shari'a wajibi ne karanta bismilla. Imamiyya da ba'arin malaman ahlus-sunna sun tafi kan cewa bismilla aya ce mai zaman kanta a cikin kowacce sura kuma wani yank ice ta wannan sura, sai dai kuma wasu ba'arin ahlus-sunna suna ganin cewa kaɗai cikin suratul fatiha ce basmala ta kasance aya mai cin gashin kanta kuma wani yanki na wannan sura, wasu kuma suka ce hatta a cikin suratul fatiha bata kasance aya mai cin gashin kanta ba, bari dai kadai ana karanta ta a farkon kowacce sura in banda suratul tauba domin neman tabarruki. A rahotan malaman tarihi, wannan aya tare da sauran ayoyin fatiha ita ce aya ta farko wacce aka tarjama zuwa harshen farisanci ta hannun salmanul farisi.

Muhummancin Bismilla Cikin Saƙafar Muslunci

Muhammad Jawad Mugniyya cikin tafsirul Al-Kashif ya ce “Bismillahir Ar-Rahmanir Ar-Rahim” bayan kalmar shahada guda biyu ta kasance taken musulmai, musulmai suna fara dukkanin ayyukansa da karatunsu bayan karanta bismilla[1] a cewar Murtada Muɗahhari wannan jumla tana daga mafi muhimmancin taken muslunci, sannan don gudun mantuwa ya dace musulmai sun zana rubutunta kan allon zayyana kyawawan rubutu, su kafa a kan bangon gidajensu, sannan gabannin dukkanin ayyukansu su fara da karantata.[2]

An ce daga abubuwan da suka bazu da yaɗuwa tsakanin musulman Iran shin c cewa domin neman albarka da neman tsari daga sharri da bala'o'I haƙiƙa suna rubuta wannan aya kan dutse ko tiles sannan su kafeta kan baƙin kofar gida[3] sakamakon yawan amfani da bismilla a farkon kowanne aiki wannan jumla wani lokaci a harshen farisanci maimakon amfani da fi'ilai misalin (Befarmayi) ko (Beshatabi) sai ayi amfani da ita.[4] haka nan a farkon risala ko littafai kalmar (bismillahir rahmanir Rahim) ana rubuta da tarjamar farisanci (Bename khodawande bakhshande mehraban) ko kuma wata jumla kwatankwacin haka..[5] An ce a farkon annabta Annabi (S.A.W) ya kasance yana amfani da jumlar “Bismikallahumma” a farkon wasisƙunsa da makamantansu[6]] har zuwa lokacin da ayar

وَ قَالَ ارْكَبُوا فِيهَا بِسْمِ اللَّهِ مَجْرَاهَا وَ مُرْسَاهَا»[7]

Ta sauka ya kasance yana amfani da bismillahi, bayan saukar aya ta 110 suratul isra'i yana karanta bismillahi Ar-Rahman, amma daga ƙarshe bayan saukar ayar

إِنَّهُ مِنْ سُلَيْمَانَ وَإِنَّهُ بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ»،[8] Misali, duba Tabari, Jame al-Bayan, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 38.

bayan Saukarta sai ya koma karanta bismillah a kammalenta.[9] wasu ba'ari sun tafi kan cewa “bismillahir Ar-rahmanir Rahim” cewa itace aya ta farko da ta sauka tare da suratul alaƙ wurin Annabi (S.A.W).[10] haka kuma ana kiranta da sunaye misalin basmala[11] da tasmiya[12]

Falaloli

A farkon kowane ƙaramin aiki ko babba, ka ce:

«بسم اللّه الرحمن الرحيم».

Sheikh Sadouq, Kitabul Tauhid, shafi na 232.

Akwai riwayoyi da suka daga tafsiran shi'a da ahlus-sunna da suke bayani kan darajoji da falalolinta, ƙurɗubi cikin tafsirinsa ya naƙalto daga Imam Ali (A.S) cewa ita bismilla magani daga dukkanin cuta kuma mai taimako ce ga duk wani magani.[13] kan asasin wani yankin riwaya cikin tafsirul Ayyashi naƙali daga Imam Rida (A.S). wannan aya ta kasance mafi karamci mafi girman ayoyin kur'ani.[14] haka nan cikin ba'arin riwayoyi ya zo cewa kyawunta rubutata domin girmama ubangiji yana sanya samun gafarar ubangiji,[15] karantata hanya ce ta kuɓuta daga wutar jahannama,[16] cikin ba'arin riwayoyian naƙalto cewa an tattaro sirrikan bakiɗayan litattafan sama a cikin kur'an, sannan dukkanin abin da yake cikin kur'ani yana cikin fatiha, kuma dukkanin abin da yake fatiha yana ƙunshe cikin bismilla.[17]

Farawa da Sunan Allah

Annabi (S.A.W):

كلُّ أمر ذي بالٍ لمْ يُذكَر فيه بسم الله فهو أبتر؛

Duk wani aiki mai daraja da ba a fara da Bismillah ba yankakke ne

Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 76, shafi na 305.

Malaman tafsiri suna cewa ana karanta bismilla gabanin kowanne aiki domin ya zama an fara da sunan Allah[18] a cewar Muhammad Husaini ɗabaɗaba'i cikin tafsirul Al-mizan, Allah ya buɗe kur'ani da sunansa mafi darajar suna domin zancensa ya kasance alama da tunawa da shi, haka nan ta haka ya koyar da bayinsa da su dinga buɗe ayyukansu da zantukansu da farawa da sunansa don zama na Allah kuma abin da yake nuna shi.[19]

Ma'anar Bismilla

Wasu ba'ari malaman tafsiri suna da ra'ayin cewa harafin ba'un a cikin bismilla yana bada ma'anar faraway, ma'ana lokacin da wani mutum yake faɗin “Bismilla” ma'anarta shi ne cewa yana fara aikinsa da sunan Allah.[20] wasu jama'a daban suna cewa harafin ba'un bai da wata keɓantacciyar ma'ana, kaɗai furta bismilla ana yinsa ne da niyya ambaton sunan Allah da kuma neman albarkarsa cikin yin aiki.[21] Wasu jama'ar daban daga malaman tafsiri suna ganin harafin ba'un ya zo ne da ma'ana isti'ana (neman taimako)[22] saboda haka bismilla zata zama da ma'anar ina neman taimakon Allah[23] wasu ba'arin malaman tafsiri na shi'a[24] sun karɓi wannan ma'ana tare da jingina da riwaya daga A'imma (A.S).[25]

Wasu ba'ari daban kuma suna cewa sakamakon babu mamaici a kur'ani, bismilla a kowacce suta tana da keɓantacciyar ma'ana da take da alaƙa da saƙon ayoyin wannan sura,[26]] cikin tafsirin Ayyashi, an naƙalto riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) cikin tafsirin bismilla cikinsa harafin ba'aun ya zo da ma'anar “Baha'u” hasken Allah, harafin sinun “Sana'ullahi” ɗaukakar Allah, harafin mimun “Majdullahi” girmamarsa.[27]

Hukunce-hukuncen Fiƙihu Game da Bismilla

Malaman fiƙihu cikin babuka misalin ɗahara sallah, aure, farauta, Yankan Shari'a da abin ci da abin sha sun yi bayani game da bismilla, ba'arinsu sun kasance kamar haka:

  • Taɓa basmala: bisa mahangar mashhur malaman fiƙihu na shi'a, taɓa rubutacciyar bismilla ba tare da alwala kasancewarta aya ta kur'ani[28] kuma siffa da daga siffofin Allah, yin hakan haramun ne.[29]

Haka nan sun ce bai halasta mai janaba ya shafa rubutun bismilla.[30]

  • Bismilla cikin karatun sallah: malaman fiƙihu na shi'a sun yi ijma'i cewa bismilla wani ɓangare daga bakiɗayan surorin kur'ani in banda suratul tauba, saboda haka wajibi ne karantata cikin sallolin farilla.[31]
  • Farauta da yankan shari'a: a fatawar malamai faɗin bismilla yana cikin sharuɗɗan ingancin yanka na shari'a.[32]

Haka nan cikin farauta, yayin da ake aika kare zuwa ga abin farauta ko kuma yayin da ake harba baka wajibi a karanta bismilla, idan ya zamana an ƙi karantawa da ganganci, naman da aka farauto baya halasta aci shi.[33]

  • Karanta bismilla yayin ɗaura alwala,[34] yayin kusantar iyali,[35] haka kuma mustahabbi ne lokacin cin abin ci ko shan abin shaa karanta bismilla.[36]

Shin Bismilla Aya ce Main Cin gashin kanta?

A cewar Rashid Rida wanda ya rayu tsakanin shekaru 1282-1354 bayan hijira, daga malaman tafsiri na ahlus-sunna a ƙasar Lubnan, kasancewar bismilla wani ɓangare daga aya ta 30 daga suratul namlim bakiɗayan musulmi sun ittifaƙi cewa ayar kur'ani ce,[37]] amma game da kasancewarta a farkon kowacce sura shin aya ce mai cin gashin kanta to lallai cikin hakan akwai saɓani tsakanin musulmai,[38] Alusi ɗaya daga cikin fitattun malaman tafsirin ahlus-sunna, cikin tafsirinsa Ruhul Ma'ani, ya ambaci mahanga guda goma[39] ba'arinsu sune kamar haka:

Ba'arin dalilansu sun kasance kama haka: 1-Ijma'in sahabbai kan cewa cikin mus'haf na farko, a farkon kowacce sura idan ka cire tauba akwai bismilla.[41] 2-an naƙalto riwayoyi daga madogaran shi'a da ahlus-sunna daga Annabi (S.A>W) da Imaman shi'a kan cewa bismilla aya ce mai cin gashin kanta kuma wani ɓangare ce ta bakiɗayan surori in banda suratul tauba.[42] 3-Sirar musulmai tun lokacin da Annabi (S.A.W) yake raye ta kasance a farkon kowacce sura in banda tauba ana farawa da karanta bismilla, idan bismilla ba ɓangare bace daga kur'ani, wajibi ne kan Annabi (S.A.W) ya yi wa musulmai bayani don gudun zama sababin ɓacewar musulmai.[43]

  • Malik ɗan Anas, Abu Hanifa da mabiyansa, Abu Umar da Yaƙub ɗan Is'haƙ daga ma'abota ƙira'a na garin basara da wasu ba'arin malamai suna ganin bismilla matsayin aya mai cin gashintakuma ana karantata domin nemn tabarruki kuma ta kasance bayanin farko surori, haka nan kuma rarrabewa tsakanin surori,[44] kuma bata kasance ɓangaren wata sura in banda abin da ya zo cikin aya ta 30 a suratul namli.[45]
  • Ahmad ɗan Hanbal, Hamza ɗaya daga ma'abota ƙira'a guda bakwai da wasu ba'ari sun yi amanna da cewa bismilla tana kasancewa aya mai cin gashin kanta kuma kaɗai ɓangare ce na cikin suratul hamdi.[46]

Tarjamar Bismillahir Ar-Rahmanir Ar-Rahim

An ce farkon tarjamar bismilla tare da sauran ayoyin fatiha zuwa harshen Farisanci ya kasance ta hannun Samanul Farisi bayan Farisawa sun nemi yin hakan,[47] ya tarjama wannan aya cikin wannan shakali (da sunan Allah mai rahama)[48] wasu ba'arin tarjamar farisanci sun kasance kamar haka:

  • Asfirayini, malamin tafsiri na ahlus-sunna a ƙarni na biyar bayan hijira: (Na fara da sunan Allah, mai ikon halicci mutane, mai son azurta mutane, mai son gafarta wa masu biyayya).[49]
  • Rashid-dini Abu Fazal Mubidi, malamin tafsiri a ƙarni na shida bayan hijira: (Da sunan Allah mamallakin duniya mai gafara da kyauta).[50]
  • Abul Al-Fatuhu Razi, malamin tafsiri na shi'a a ƙarni biyar: (da sunan Allah mai rahama mai yawan afuwa)[51]
  • Mulla Husaini Wa'iz Kashifi, malamin tafsiri na shi\a a ƙarni na tara bayain hijira: (Da sunan Allah wanda ya cancanci a bauta masa kuma ya ba da halitta kuma ya rayar da su kuma ya raya su ya raya da karfi da hikima ya kare su daga aibobi).[52]
  • Tarjamar tafsirin ɗabari wacce ta kasance daga mafi daɗewar tarjamar kur'ani zuwa harshen farisanci: (Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai).[53]
  • A cikin tarjamomin wannan zamani ma'ana ƙarni na goma sha huɗu da sha biyar bayan hijira, akwai tarjamomi daban-daban da aka yi wa bismilla, mafi yaɗuwa da bazuwarsu itace (Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai).[54]

Bambanci Tsakanin Rahman da Rahim

Basmaleh tile da aka rubuta a gaban wani tsohon gida

Rahman da Rahim siffofi ne biyu daga siffofin Allah a mahangar mafi yawan malaman tafsiri[55] an ciro ne daga tushen kalmar “rahamat”[56] galibin malaman tafsiri[57] sun ce “Rahman” keɓantacciyar siffa ce ta ubangiji.[58] da ma'ana gamammiyar rahama daga Allaha da taje haɗowa da dukkanin bayinsa muminai da kafirai, amma siffar “Rahim” tana shiryarwa ne kan dawwamammiyar rahamarsa da ta keɓanci muminai su kaɗai.[59] A ra'ayin ba'arin malaman tafsiri fuskar gamewar siffar rahamaniyyar Allah ga dukkanin bayinsa, tun da shi ne ya halicce su, shi ne zai ɗauki nauyin azurtar su.[60] sannan fuskar keɓantuwar rahimiyya ga bayinsa masu Imani shi ne cewa a rayuwarsu ta duniya zai basu taufiƙi a lahira kuma zai basu rahama zai gafarta musu zunubansu.[61]

Tafsirin Irfani

Cikin matanai da tafsiri na irfani, an yi bayanin tafsiri na baɗini game da bismilla,[62] wasu ba'ari suna cewa ubangiji ta hanyar harafin ba'un ya samar da dukkanin halittu,[63] Ibn Arabi ya ɗabbaka shakalin harafin ba'un da ɗigonsa kan duniyoyi guda ukum da wannan ne shakalin ba'un ya kasance duniyar malakut sannan ɗigonta duniyar jabruti wasalinta kuma duniyar shahada,[64] Abdur-Razaƙ Kashani shima cikin tafsirinsa yana ganin harafin ba'un ishara ce zuwa ga Aƙlul awwal ko sadirul awwal.[65]

Bisa ra'ayin Mulla Husaini Wa'iz Kashifi cikin Jawahirul tafsir, harafin alifun ishara ce zuwa ga tsarkakakken zati, sakamakon harafin farko ya kasance harafin alphabet, ga Allah Allaha ya zamana taken zati da ya kasance farko komai, daga kasancewarsa ba shi da ɗigo, yafi dacewa da tsantsar samuwa da ya koru daga dukkanin dabaibayi.[66]

Cikin ba'arin matanai da tafsiran irfani, “Rahman” ta zo da ma'anar mai rahama da failar samuwa da kamala ga dukkanin masu ababen samuwa, kan asasin hikima da tanadinsu ne ta zo,[67] sannan kalmar “Rahim” tana ma'anar mai kwarara kalamar ma'anawiyya kebantacciya ga mutum.[68]

Ayyukan Fasaha Cikin Rubutun Bismilla

Bismillah, wanda Mohammad Ozchai, masani na Turkiyya ya rubuta.

Basmalataba cikin jumlar ayoyi da rubutunta ya jawo hankalin ma;abita fasahar kyawunta rubutu, a tsawon tarihi na samar nau'i daban-daban na rubutun basmala.[69] zanen rubutun basmala cikin fasaha tayel ana ƙirga cikin ɗaya daga fasahohin ƙayata zanen gine-gine a ƙasar Iran, akwia kufaifayin daban-daban daga hakan da ya haɗa da masallaci, bakin ƙofar gida da wuraren ibada da ma wurare masu tsarki da ake kafe zanenta.[70] Har ila yau, masu zane-zane na musulmi sun kirkiro ayyuka daban-daban na zane-zane. Basmala cikin waƙa da adabi wani lokaci za ka samu ta zo a farko baitin waƙa.[71] wani lokacin kuma saƙon baitukan waƙar ya ƙunshi basmala daga nasiha fara kowanne aiki da sunan Allah cikin rera waƙen.[72] Basmala cikin adabin farisanci, cikin isɗilahi misalin”Murƙu bismil” da ma'anar kazar da aka yanke wuyanta da kuma “Murƙu basmal” kazar da bat agama mutuwa ba, haka nan “Basmal gahe” da ma'ana mahauta ko mayanka.[73]

Bayanin kula

  1. Mughniyeh, al-Tafsir al-Kashif, Dar al-Anwar, juzu'i na 1, shafi na 24.
  2. Motahari, Panzdeh Guftar, 1389, shafi na 162-163.
  3. موسوی آملی، «سر در نوشته‌های قرآن»، سایت پرتال علوم اسلامی.
  4. Moini, Amsal wa ta'abiri Kur'ani, 1394, shafi na 153-155.
  5. «ترتیب پایان نامه نویسی»، سایت کلام سبز.
  6. Qalqshandi, Sobh al-Ashi fi Sanaa al-Ansha, Dar al-Katb al-Alamiya, juzu'i na 1, shafi na 480.
  7. سوره هود، آیه ۴۱.
  8. سوره نمل، آیه ۳۰.
  9. Jisas, Ahkam al-Qur'an, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 7.
  10. Misali, duba Tabari, Jame al-Bayan, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 38.
  11. Misali, duba Hoshangi, “Basmeleh”, shafi na 426.
  12. Misali, duba Abolfatuh Razi, Rouz al-Janan, 1376, juzu'i na 1.
  13. Qortubi, Al-Jamael ahkam Al-Qur'an, 1364, juzu'i na 1, shafi na 107.
  14. Ayashi, Tafsir al-Ayyashi, 2013, juzu'i na 1, shafi na 21.
  15. Siyuti, Durrul al-Manthor, Dar al-Fakr, juzu'i na 1, shafi na 27.
  16. Bahrani, al-Burhan fi Tafsir Kur'ani, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 99.
  17. Kundozi, Yanabi Al Mowadda, 1422 AH, Juzu'i na 1, 213.
  18. Misali, duba Tabarsi, Majmael al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 54; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 1, shafi na 103; Tabatabaei, Al-Mizan, 1363, juzu'i na 1, shafi na 15-17; Tayeb, Ateeb Al Bayan, 1378, juzu'i na 1, shafi na 93.
  19. Tabatabaei, Al-Mizan, 1363, juzu'i na 1, shafi na 15.
  20. Misali, duba Ibn Qutaiba, Tafsir Gharib al-Qur'an, 1411H, shafi na 39; Tabarsi, Majma al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 54; Tabatabaei, Al-Mizan, 1363, juzu'i na 1, shafi 17; Hakim, Tafsirin Suratul Hamd, 1420H, shafi na 152-153.
  21. Khumaini, Tafsirul Al-Kur'anul Karim, 1418H, juzu'i na 1, shafi na 95.
  22. Misali, duba Arus Hawizi, Tafsirin Nur al-Saghalin, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 12-13; Tayeb, Ateeb Al Bayan, 1378, juzu'i na 1, shafi na 93.
  23. Aroos Hawizi, Tafsirin Nur al-Saqlain, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 12-13; Tayeb, Ateeb Al Bayan, 1378, juzu'i na 1, shafi na 93; Hakim, Tafsirin Suratul Hamd, 1420H, shafi na 152.
  24. Misali, duba Aroos Hawizi, Tafsirin Nur al-Saghalin, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 12-13; Tayeb, Ateeb Al Bayan, 1378, juzu'i na 1, shafi na 93. ^ Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1983, juzu'i na 3, shafi na 41.
  25. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1983, juzu'i na 3, shafi na 41.
  26. Qashiri, Lataef al-isharat, 2000 AD, juzu'i na 1, shafi.44; Khumaini, Tafsirin Al-Kur'anul Karim, 1418 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 96.
  27. Ayayyshi, Tafsir al-Ayyashi, 2013, juzu'i na 1, shafi na 22.
  28. Hakim, Mustamsak al-urwa, 1391 AH, juzu'i na 2, shafi na 272.
  29. Tabatabaei Yazdi, al-Auwa al-Wuthghati, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 352.
  30. Tabatabaei Yazdi, al-Auwa al-Wuthghati, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 509
  31. Hakim, Mustamsak al-urwa, 1391 AH, juzu'i na 6, shafi na 174-175.
  32. Najafi, Jawaharl al-Kalam, 1362, juzu'i na 36, ​​shafi na 113.
  33. Najafi, Jawaharil al-Kalam, 1362, juzu'i na 36, ​​shafi na 30.
  34. Shahid Sani, Al-Rawda Al-Bahiya, juzu'i na 1, shafi na 79.
  35. Tabatabaei Yazdi, al-urwa al-Wuthghati, 1417 AH, juzu'i na 5, shafi.482; Hakim, Mustamsk al-Arwa, 1391 AH, juzu'i na 14, shafi na 10.
  36. Najafi, Jawaharl al -Kalam, 1362, juzu'i na 36, ​​shafi.451.
  37. Rashidreza, Tafsir al-Manar, 1990, juzu'i na 1, shafi na 33.
  38. Rashidreza, Tafsir al-Manar, 1990, juzu'i na 1, shafi na 33.
  39. Alousi, Ruh al-Ma'ani, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 41.
  40. Rashidreza, Tafsir al-Manar, 1990, juzu'i na 1, shafi.33; Alousi, Ruh al-Ma'ani, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 41.
  41. Rashidreza, Tafsir al-Manar, 1990, juzu'i na 1, shafi na 33.
  42. Misali, duba Hakim Nishaburi, al-Mustadrak Ali al-Sahihin, 1411 AH, juzu'i na 1, 356-357; Kilini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 3, 312-313; Baihaqi, Al-Sunan al-Kubari, 1424 AH, juzu'i na 2, shafi:67; Boroujerdi, Jame al-Ahadith al-Shia, 1415 AH, juzu'i na 5, shafi na 128-130.
  43. Khoi, Al-Bayan, Mu'assasa Ihya'i Asare Khoyi
  44. Rashid Reza, Tafsir al-Manar, 1990, juzu'i na 1, shafi.34; Alousi, Ruh al-Ma'ani, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 41.
  45. Fakhr Razi, al-Tafseer al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 1, shafi na 172.
  46. Rashidreza, Tafsir al-Manar, 1990, juzu'i na 1, shafi.34; Alousi, Ruh al-Ma'ani, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 41.
  47. Sarkhsi, Al-Mabssut, 1414 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 37.
  48. Shoaibi, Mujam Musannafat Al-Qur'an, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 12
  49. Esfraini, Taj al-Tarajm, 1375, shafi na 39.
  50. Meibodi, Kashf al-Asrar, 1371, juzu'i na 1, shafi na 2.
  51. Razi, Rouz al-Janan, 1376, juzu'i na 15, shafi na 182.
  52. Kashfi, Jawaher al-Tafseer, 1379, shafi na 330.
  53. Tabari, Tarjameh TafsirTabari, 1356, juzu'i na 1, shafi na 10.
  54. Alal misali, duba Sajdi, “Muadil farsiri “Bism Allah al-Rahman al-Raheem” dar tarjamehhaye qadim wa jadid kur'an, shafi na 26-30.
  55. Qortubi, Al-Jamae ahkam Al-Qur'an, 1364, juzu'i na 1, shafi na 104.
  56. Ibn Qutaiba, Tafsir Gharib al-Qur'an, 1411 AH, shafi na 12; Tabatabaei, Al-Mizan, 1363, juzu'i na 1, shafi 18; Qurtubi, Al-Jamae ahkam Al-Qur'an, 1364, juzu'i na 1.
  57. Qortubi, Al-Jamae ahkam Al-Qur'an, 1364, juzu'i na 1, shafi na 105.
  58. Misali, duba Sheikh Tusi, al-Tabayan, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, juzu'i na 1, shafi na 29.
  59. Sheikh Tusi, Al-Tabayan, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, juzu'i na 1, shafi na 29; Tabatabai, Al-Mizan, 1363, juzu'i na 1, shafi na 18-19; Aroos Hawizi, Tafsir Noor al-Saqlain, 1415 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 12.
  60. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 54; Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 AH, juzu'i na 1, shafi na 166.
  61. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 1, shafi na 54.
  62. Misali, duba Qashiri, Lataef al-isharat, 2000 AD, juzu'i na 1, shafi 44; Ibn Arabi, Fatuhat al-Makiyya, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, juzu'i na 1, shafi na 102; Kashani, Tafsir Ibn Arabi (Tawilat Abd al-Razzaq), 1422 AH, juzu'i na 1, shafi na 7.
  63. Misali, duba Qashiri, Lataef al-Isharat, 2000 AD, juzu'i na 1, shafi 44; Ibn Arabi, Fatuhat Al Makkiyya, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, Mujalladi na 1, shafi na 102.
  64. Ibn Arabi, Fatuhat Al Makkiyya, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, Mujalladi na 1, shafi na 102.
  65. Kashani, Tafsir Ibn Arabi (Tawilat Abd al-Razzaq), 1422 AH, juzu'i na 1, shafi na 7.
  66. Kashfi, Javaher al-Tafsir, 1379, shafi na 334-335.
  67. Kashani, Tafsir Ibn Arabi (Tawilat Abd al-Razzaq), 1422 AH, juzu'i na 1, shafi na 7; Qonavi, Ejaz Al Bayan, 1381, shafi na 173; Sultan Alisha, Bayan al-Saada, 1408 AH, juzu'i na 1, shafi na 28.
  68. Kashani, Tafsir Ibn Arabi (Tawilat Abd al-Razzaq), 1422 AH, juzu'i na 1, shafi na 7
  69. Mati, "Tasmieh", shafi na 326.
  70. Mati, "Tasmieh", shafi na 326.
  71. Misali, duba Nizami, Kullliat Divan Hakim Nizami Ganjaei, 1335, shafi na 9.
  72. Mati, "Tasmieh", shafi na 326.
  73. Moini, Amsal wa ta'abir Kur'ani, 1394, shafi na 159; Mati, "Tasmieh", shafi na 326.

Nassoshi

  • Allameh Majlesi, Mohammad Baqer, Bihar Al-Anwar, Beirut, Al-Wafa Foundation, 1983.
  • Ayyashi, Muhammad bin Mas'ud, Tafsirin Ayyashi, Tehran, Al-Mattabah Al-Alamiya, bugun farko, 1380H.
  • Bahrani, Hashim bin Suleiman, al-Barhan fi Tafsirin Qur'an, Qum, Al-Ba'ath Foundation, 1415H.
  • Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, al-Tafsir al-Kabir, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1420H.
  • Ibn Arabi, Muhammad bin Ali, al-Futuhat al-Makkayya, Beirut, Dar Ihya al-Tarat al-Arabi, Bita.
  • Ibn Qutaiba, Abdullahi bin Muslim, Tafsir Gharib al-Qur'an, Beirut, Dar da Maktaba al-Hilal, 1411H.
  • Moini, Mohsen, Amsal wa ta'abir Kur'ani, Tehran, Gidan Buga Al'adun Zamani, bugu na uku, 1394.
  • Motahari, Morteza, Panzdeh Giftar, Qom, Sadra Publications, 2009.
  • Qalqshandi, Ahmed bin Ali, Sobh al-Ashi fi Sanaa al-Ansha, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, Bita.
  • Qonavi, Muhammad bin Ishaq, Ejaz al-Bayan fi Tafsir Umm al-Qur'an, Kum, Bostan Kitab, 2001.
  • Sarkhsi, Muhammad bin Ahmad, Al-Mabusut, Beirut, Dar Al-Marafah, 1414H.
  • Shaheed Thani, Ali bin Zain al-Din, al-Ruda al-Bahiya, Qum, wallafe-wallafen ofishin yada farfagandar Musulunci na makarantar hauza ta Kum, bugu na farko, 1412H.
  • Shoaibi, Ali Shawak Ishaq, Mujam Musannafat Al-Qur'an. Riyadh, Dar al-Rifai, 1403 AH.
  • Siyuti, Jalaluddin, Alder al-Manthor, Beirut, Dar al-Fakr, Bita.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Al-Bayan Majma, Beirut, Al-Alami Foundation for Press, 1415 AH.
  • Abul Fattouh Razi, Hossein bin Ali, Ruz al-Jinan da Ruh al-Jinnan fi Tafsir al-Qur'an, Mashhad, Islamic Research Foundation, 1376.
  • Alousi, Mahmoud bin Abdullah, Ruh al-Ma'ani fi Tafsirin Qur'an al-Azeem wa Al-Saba al-Mathani, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1415H.
  • Bayhaqi, Ahmad bin Hossein, Al-Sunan al-Kubari, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1424H.
  • Boroujerdi, Sayyid Hasan, Jame Al-Ahadith al-Shia, Kum, Mehr Publications, 1415 AH.
  • Esfraini, Shahfur bin Taher, Taj al-Tarajm, Ali Akbar Elahi Khorasani, Tehran, Kamfanin Buga Littattafan Kimiyya da Al'adu, 1375 ya gyara.
  • Hakim Neishaburi, Muhammad bin Abdullah, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, Beirut, al-Maktab al-Asriyah, 1420H.
  • Hakim, Sayyid Muhammad Baqir, Tafsirin Suratul Hamd, Qum, Majma al-Fikr al-Islami, 1420H.
  • Hakim, Seyyed Mohsen, Mastamsk al-Arwa, Beirut, Dar Ihya Al-Trath al-Arabi, 1391H.
  • Jisas, Ahmad bin Ali, Haqmat al-Qur'an, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1415H.
  • Kashani, Abd al-Razzaq, Tafsir Ibn al-Arabi (Tawilat Abd al-Razzaq), Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1422H.
  • Kashfi, Hossein bin Ali, Javaher al-Tafseer, Tehran, Written Heritage Research Center, 1379.
  • Khoei, Sayyid Abulqasem, Al-Bayan, Kum, Imam Al-Khoei Revival Foundation, Bita.
  • Khomeini, Sayyid Mustafa, Tafsirin Kur'ani Karim, Qum, Cibiyar Edita da Bugawa ta Imam Khumaini, 1418H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-Kafi, Ali Akbar Ghafari ya gyara, Darul Kitab al-Islamiyyah, 1407H.
  • Mati, Mehdi, "Tasmieh", in Islamic Encyclopedia, Tehran, Center of Islamic Encyclopedia, 1387.
  • Mughniyeh, Mohammad Javad, Al-Tafsir Al-Kashif, Beirut, Dar Al-Anwar, Beta.
  • Qanduzi, Suleiman bin Ibrahim, Yanabi Al-Muda, Kum, Darul Aswa, 1422H.
  • Qashiri, Abdul Karim Beh Hawazen, Lataif al-Isharat, Alkahira, Al-Masriyyah al-Katab, 2000 AD.
  • Qurtubi, Muhammad bin Ahmad, Al-Jamee Lahkam Al-Qur'an, Tehran, Nasser Khosro Publications, 1364.
  • Rashidreza, Muhammad, Tafsir al-Manar, Misr, Al-Masriyyah Al-Al-Katab, 1990.
  • Sajdi, Akbar, "Muadil farsi "Bismillah al-Rahman al-Raheem" ​​a cikin tsofaffi da sabbin tafsirin Alqur'ani", Hasna, No. 34, Spring and Summer 2017.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, al-Tabyan fi Tafsirin Qur'an, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, Bita.
  • Sultan Alisha, Sultan Muhammad bin Haider, Bayan al-Saada fi Maqamat al-Abada, Beirut, Al-Alami Foundation for Publications, 1408 AH.
  • Tabari, Ibn Jarir, Jami al-Bayan fi Tafsirin Qur'an, Beirut, Darul Marafa, 1412H.
  • Tabari, Mohammad Bin Jarir, Tafsirin Tabari, Tehran, Tos Publications, 1356.
  • Tabatabaei Yazdi, Seyyed Mohammad Kazem, Al-urwa Al-Wuthghati, Qum, Al-Nashar al-Islami Publishing House, 1417H.
  • Tabatabaei, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi al-Tafsir al-Qur'an, Qom, Ismailian Publications, 1363.
  • Tayeb, Abdul Hossein, Ateeb Al Bayan, Tehran, Islam Publications, 1378.
  • Urusi Hawizi, Abd Ali bin Juma, Tafsir Noor al-Saqlain, Qum, Ismaili, bugu na 4, 1415H.
  • Zamakhshari, Mahmoud bin Umar, Al-Kashaf an haqsiq Ghwamaz al-Tanzil, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1407H.
  • «ترتیب پایان نامه نویسی»، سایت کلام سبز، تاریخ درج مطلب: ۱۸ فروردین ۱۴۰۲ش، تاریخ بازدید: ۱۰ دی ۱۴۰۲ش.
  • موسوی آملی، سیدمحسن، «سر در نوشته‌های قرآن»، سایت پرتال علوم اسلامی، تاریخ بازدید: ۱۷ دی ۱۴۰۲ش.