Ayar Isra'i

Daga wikishia
Ayar Isra'i

Ayar Isra'i (Larabci: آية الإسراء) aya ce ta farkon suratul Isra'i aya ce da ta sauka game da Mi'iraji, bisa wannan aya,cikin dare an ɗauki Annabi (S.A.W) daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Al-Aƙsa, hadafi daga wannan mi'iraji shi ne Allah ya nunawa Annabi (S.A.W) girmansa, daga wannan aya an ciro kasancewar jikkantuwar mi'iraji da mujizar da take cikinsa.

Gabatarwa

Aya ta farkon suratul Isra’i aya ce wacce cikinta aka yi ishara kan tafiyar da Manzon Allah (S.A.W) ya yi daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Al’Aƙsa.[1]

سُبْحَانَ الَّذِی أَسْرَی بِعَبْدِهِ لَیْلًا مِّنَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ إِلَی الْمَسْجِدِ الأَقْصَی الَّذِی بَارَکْنَا حَوْلَهُ لِنُرِیَهُ مِنْ آیَاتِنَا إِنَّهُ هُوَ السَّمِیعُ البَصِیرُ
Tsarki ya tabbata ga wanda ya ɗauki bawansa cikin dare daga Masallacin harami zuwa Masallacin Al-Aƙsa wanda muka albarkaci geffansa domin mu nuna masa daga ayoyinmu, lallai shi Allah mai ji ne mai gani ne.



(Kur'ani: Isra'i: 1)


________________________________________

Sha'anin Sauka

Asalin Maƙala: Mi'iraji

Wannan aya ta sauka game da tafiyar da Annabi (S.A.W) ya yi daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Al-aƙsa, Baitul Muƙaddas,[2] a cewar Shaik Ɗabarsi daga Malaman tafsiri na Shi'a a ƙarni na shida h ƙamari, bayan Annabi (S.A.W) ya idar da sallolin Magariba da Isha a Masallacin Harami, aka ɗauke shi daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Baitul Muƙaddas, kuma cikin wannan dare ya dawo ya yi sallar Asubahi a Masallacin Harami, wannan maudu'i ne da dukkanin musulmi sun yi ittifaƙi a kansa, wasu ba'arin Sahabbai misalin Ibn Abbas, Ibn Mas'ud, Jabir Bin Abdullahi da Huzaifatu sun naƙalto wannan batu.[3] Malaman tafsiri a ƙarshen wannan aya sun kawo bayanin Mi'iraji filla-filla, daga lokacin da ya faru, wurin da ya faru da ƙaƙa ya faru.[4]

Shiryarwa Ayar Kan Kasancewa Mi'iraji Mu'ujiza

Ba'arin Malaman tafsiri sun bayyana ayar Isra'i matsayin ɗaya daga cikin mu'ujizozin Annabi (S.A.W),[5] Jafar Subhani cikin Tafsir Manshur Jawid, ya kawo cewa wannan tafiyar dare da aka yi da Annabi (S.AW) daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Baitul Muƙaddas ta kasance ɗaya daga cikin mu'ujizozin Annabi (S.A.W) tafiya ce da ta kasance ba tare da tsanantuwa da kayayyakin sufuri na zamani ba wanda hakan ya ketare ƙudura da ƙarfin ɗan Adam,[6] a cewar Murtada Muɗahhari wanda ya rasu shekarar 1358 h shamsi, Mufakkirin Shi'a, cikin wannan aya an naƙalto rahotan wata tafiya da ta saɓawa al'ada, tafiya da aka yita da gangar jikin Annabi (S.A.W), saboda haka misalin irin wannan tafiya a cikin dare ɗaya a zamanin da ake amfani da raƙuma domin sufuri, ba zai taɓa yiwuwa ta kasance wani abu saɓanin mu'ujiza ba,[7] na'am Ayatullahi Makarim Shirazi ya tafi kan cewa, wannan aya ita kaɗai ƙarara a zahiri ba ta bayyana mu'ujiza, sai tare da jingina mata wasu riwayoyi da kuma sha'anin saukarta wanda aka yi bayaninsa cikinsa tafsiri da cewa tana daga mu'ujizozin Annabi (S.A.W).[8]

Shiryarwar Ayar Dangane Da Jikkantuwa Mi'iraji

Malaman tafsiri cikin ƙarshen wannan ayar sun yi magana game da kasancewar yin wannan tafiya da gangar jiki ko da ruhi, Allama ɗabaɗaba'i wanda ya rasu shekara 1360 h shamsi, ya ce aksarin Malamai sun tafi kan cewa an yi Mi'iraji tare da gangar jiki ne,[9] na'am hatta shi kansa Allama yana kan wannan fahimta tare da dogara da wannan aya da kuma ayoyin suratul Najamu, amma tafiyarsa da tashinsa daga Masallacin Al-Aƙsa zuwa sama ya kasance Ruhu,[10] ba gangar jiki ba, a cewar Ayatullahi Makarim Shirazi bisa dogara da kalmar (Bi'abdihi) za a fahimci cewa wannan tafiya anyi ta ne da gangar jiki, saboda ita kalmar tana nuna Annabi (S.A.W) ya yi tafiyar tare da gangar jikinsa.[11] haka kuma jafar Subhani yana cewa da ace wannan tafiya ta kasance da ruhu to ya kamata ne a yi amfani da kalmar (Bi'ruhihi) Maimakon (Bi'abdihi).[12]

Bayanin Hadafin Mi'iraji A cewar malaman tafsiri, kalmar "Luniriyahu min ayatina" tana nufin manufar mi'iraji ne[13] Manufar yin mi'iraji kuwa ita ce nuna girman ayoyin Allah ga Annabi (S.A.W) domin ruhinsa ya girmama ya ƙuma kara girma. wanda aka shirya domin shiryar da mutane[14] Tabrasi a Majma'ul al-Bayan ya yi la'akari da tafiyar dare da Annabi ya yi daga Makka zuwa Baitul Muƙaddas, ƙudus, da hawan sama da ganin annabawa daga cikin wadannan alamomi. "A cikin ayar sun fahimci cewa Annabi ya ga wasu alamomin girman Allah a cikin wannan tafiya,[15] amma ba dukkaninsu ba.[16]

Bayanin kula

  1. Mu'assaseh Almarif Fikihi Islami, Farhang Fiƙh Farsi, 1385, juzu'i na 1, shafi na 179.
  2. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 6, shafi na 215.
  3. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 6, shafi na 215.
  4. Misali, duba Tabatabai, Al-Mizan, Ismailian, juzu'i na 13, shafi 7-35.
  5. Sobhani, Manshur Javid, 1390, juzu'i na 7, shafi na 217-216.
  6. Sobhani, Manshur Javid, 1390, juzu'i na 7, shafi na -216.
  7. Motahari, amjmu'eh Asar Ustad Shahid Motahari, 2004, juzu'i na 26, shafi na 200.
  8. Makarem Shirazi, Payam ƙur'an, 2006, juzu'i na 8, shafi na 343-344.
  9. Tabatabai, Al-Mizan, Ismailian. Juzu'i na 13, shafi na 32.
  10. Tabatabai, Al-Mizan, Ismailian. Juzu'i na 13, shafi na 32.
  11. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 12, shafi na 9.
  12. Sobhani, Forough Ebediyat, 2005, shafi na 370.
  13. Tabatabai, Al-Mizan, Ismailian, juzu'i na 13, shafi na 7.
  14. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 12, shafi na 11-9.
  15. Tabarsi, Majma al-Bayan, 1415 AH, juzu'i na 6, shafi na 218.
  16. Tabatabai, Al-Mizan, Ismailian, juzu'i na 13, shafi na 7; Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 12, shafi na 11-9.

Nassoshi

  • Sobhani, Jafar, Forough Abdiyat, ƙom, Bostan Kitab, 2005.
  • Sobhani, Jafar, Manshur Javid, ƙum, Cibiyar Imam Sadiƙ (AS), 1390.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur'an, Ismailian, B.T.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Majma al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, Beirut, Al-Alami Foundation, 1415 AH.
  • Mu'assaseh Almarif fikh Islami, Farhang Fikih Farsi, ƙum, Cibiyar ilimin fikihu, bugu na biyu, 1385.
  • Motahari, Morteza, Majmu'eh Asar Ustad Shahid Motahari, Tehran, Sadra Publishing House, bugu na 7, 2004.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Payam ƙur'an, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, bugu na 9, 1386.
  • Makarem Shirazi, Nasser,Tajumeh Kur'an Kareem, ƙum, Darul Kur'an al-Karim Publications, bugu na biyu, 1373.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsif Namuneh, Darul Kitab al-Islamiya, Tehran, bugun: 32, 1374.