Jump to content

Wanda aka haifa a ɗakin Ka’aba

Daga wikishia
(an turo daga Mauludul Ka'aba)
Allo dauje da zanen hoto wanda Farshiciyan ya yi

Wanda Aka Haifa A Dakin Ka'aba (Larabci: وليد الكعبة) ƙissar haihuwar Imam Ali (A.S) a ɗakin ka'aba, wanda ake daukar sa daya daga cikin kyawawan falalolinsa. A wasu madogaran ahlus-Sunna sun ƙirƙiri riwayoyi da manufar inkarin falalolin Imam Ali (A.S) tare da jingina wannan falalar ga wasu mutane daban.

Aƙalla majiyoyin ahlus-sunna goma sha shida da majiyoyin shi'a guda hamsin sun ce an haifi Imam Ali (A.S) a ɗakin ka'aba. (Littattafan hadisi da tarihi). Kuma an sami ruwayoyi da yawa wanda suka kai ga matsayin tawatiri a ilimin hadisi. Tabbas akwai bambance-bambance game da cikakkun bayanai da aka rubuta littafai da dama game da haihuwar Imam Ali (A.S) a ka'aba, daga cikinsu akwai littafin "Ali Walidul Al-Ka'aba" wanda Mirza Muhammad Ali Urdubadi ya rubuta (1380-1312), wanda aka fassara shi zuwa harshen Farisanci kuma ake kira da "Yegane Maulud Ka'abe".

Rahoto daga litatafai

An haifi Imam Ali (A.S) Imamin ‘yan Shi'a na farko a ɗakin Ka'aba[1] Allama Amini ya kawo daga majiyoyin ahlus-sunna goma sha shida da majiyoyin Shi'a hamsin cewa an haifi Imam Ali a cikin ka'aba.[2] Ya kuma ambaci mawaka 41 daga karni na 2 zuwa na 14 inda suka ambaci haihuwar Imam Ali a cikin Ka'aba a cikin waƙoƙinsu[3]

A cikin bayani da sharhin da akai wa littafin Ihƙaƙul-haƙ, an ruwaito haihuwar Imam Ali a ɗakin Ka'aba daga majiyoyi goma sha bakwai na ahlus-sunna,[4] cikin sayit din yanar gizo na mu'assase tahkikat waliyu asar (a.f) akwai fima-fimai har guda 30 na manyan malaman ahlus-sunna, daga misalin Shahabud-dini alusi, Mas'udi Shafi'i, Muhammad Bin Is'hak Fakihi, Safuri Shafi'i, Muhammad Amir San'ani Salafi da sauransu, duka sun bada rahoto cewa an haifi Imam Ali (A.S) a ka'aba[5] Sibɗu bin jauzi[6] Ibn Sabbag Al-Maliki[7] da Ali bin Burhanud-dini Halabi[8] gaba ɗayansu malaman ahlus-sunna ne su ma sun kawo haihuwar Imam Ali (A.S) cikin ɗakin ka'aba. A cikin Littafan Al-Mustadarak Alal Al-Sahihaini[9] da Kifayat Talib,[10] akwai riwayoyi game da wannan batu wanda ruwayoyin sun kai haddin Tawaturi.

Labarin Yanda Abin Ya Faru

Aikin Maragh, wanda aka yi shi bisa zanen Mawludul Kaaba, na Farshaciyan

Labarin haihuwar Imam Ali (A.S) a ka'aba ya zo a wurare guda uku: A cikin littafin Manaƙib Ibn Maghazili (Rasuwa: 483 bayan hijira) an ruwaito daga Imam Sajjad (A.S) Annabi ya ga Abu Talib yana baƙin ciki sai ya tambayi dalilinsa. Sai Abu Talib ya ce matarsa Fatima Bint Asad tana naƙuda. dukkansu sai suka tafi ɗakin ka'aba tare da Annabi, Abu Talib ya zaunar da Fatima Bintu Asad a gefan ɗakin ka'abar, bayan ta haifi Ali sai da Annabi ya raka su har gidansu.[11] Shaikh Saduk a cikin littattafansa na hadisai kamar Ilalu Sharayi[12] da Ma'anil Akhbar[13] da Amali[14] da kuma bayansa wasu masu Malaman hadisi[15] sun ruwaito daga Yazid Bin Ka'anab cewa Fatima bintu Asad ta ce. tana kusa da Ka'aba tana jin zafin naƙuda. Nan ta roƙi Allah ya sauƙaƙa mata haihuwa. A wannan lokacin ne bangon ka'aba na gefe ya tsage, Fatima ta shiga Sai wurin daya tsage ya koma ya haɗe da kansa, an kuma karɓowa daga Yazid bin Ka'anab cewa: duk yanda mukai mun kasa iya bude kofar ɗakin ka'abar a lokacin. . Don haka sai muka gane cewa Allah ne ya yi wannan aikin, Bayan kwana hudu Fatima bintu Asad ta fito daga ɗakin Ka'abar da Ali a hannunta. Na uku: Kamar yadda Hasan bin Ali ɗabari (wanda ya rayu a shekara ta 701 bayan hijira) a cikin littafin Tuhfa al-Abrar, Fatima bint Asad mahaifiyar Sayyidina Ali (A.S) ta kasance tana ɗawafi a ɗakin ka'aba a lokacin da take naƙuda, kuma ta kasa jurewa dawowa. gida. Don haka sai ta juya zuwa ɗakin ka'aba, kofar ɗakin ka'aba ta bude, ta shiga ɗakin ka'abar aka rufe ƙofar, nan ta haifi ɗanta a ɗakin Ka'aba. Ta kasance a cikin ka'aba kwana uku.[16] Bisa dogara da riwayar da ta zo a Biharul Al-Anwar hakika mahaifiyarsa Fatima Bint Asad kan kissar shigarta Dakin Ka'aba domin haifar Imam Ali (A.S) ta fifi ta kan Asiya da Maryam[17]

Labarin Hakim Bin Hizam

Shaik Mufid ya tafi kan cewa haihuwar Imam Ali (A.S) a dakin ka'aba wata kebantacciyar falala ce a gare shi da kafinsa ba ta faru kan wani mutum ba, kuma bayansa ba ta sake faruwa ba.[18] Sai dai kuma a wasu majiyoyin Ahlus-Sunna an bayyana cewa, an haifi daya daga cikin Sahabban Manzon Allah (S.A.W) mai suna Hakim bin Hizam a Ka’aba.[19] Tabbas wasu suna ganin cewa iyalan Zubairu daya daga cikin sahabban Annabi ne suka kirkiri wannan riwaya, saboda kaunar dan uwansu, da kuma manufar inkarin falalar Imam Ali (A.S); Domin kuwa nasabar Hakim bn Hizam bin Khuwayld bn Asad bn abdul uzi da iyalan Zubair sun kasance ga Asad bin Abdul Uzi.[20]

An yi suka kan wannan magana ta Hakim Bin Hizam kamar haka:

  1. Mus'ab Bin Usman daya daga cikin isnadin wannan magana mutum majhuli da ba a san shi ba, babu littafin sanin mazaje da ya ambaci sunansa.
  2. Riwaya ce Mursala (Rarrauna) saboda Mus'ab Bin Usman da ya rawaito wannan labari an haife shi ne bayan shekaru da faruwar labarin, saboda haka ba zai yi wu ya rawaito wannan labari ba kai tsaye ba tare da tsanantuwa da wani mutum ba.[21]

Labarin Haihuwar Imam Ali (A.S) Cikin Adabi da Wakoki

Labarin Haihuwar Imam Ali (A.S) a Ka'aba ya zo a cikin adabi da wakokin mawakan Shi’a da ahlus-sunna. Sayyid Himyari (Rasuwa: 179 bayan hijira) a cikin wannan baiti na wakarsa mai suna "Mahiafiyarsa ta haife ni a cikin haramin Allah da gidan Aminci* kuma gida ne a farfajiyarsa wurin ibada; yana mai ishara da haihuwar Imam. [22] Ibn Abil Al-Hadid Mu'utazili, (Rasuwa: 656 bayan hijira) ya kawo labarin da kalmar “«هوالذی بیت الله مولده/ فطهر البیت من ارجاس و اوثان; Shi ne babban mutum wanda dakin Allah ya kasance mahaifarsa, kuma daga wannan gida ya tsarkake Allah daga kazantar gumaka.[23] Mirza Isma'il Shirazi (Rayuwa: 1258-1305 bayan hijira) ya rera baitukan yabo game da haihuwar Imam Ali (A.S):

إِنْ یکُنْ یفرَضُ لِلهِ البَنُونَ
زفَتَعَالَی اللهُ عَمَّا یصِفُونَ
[24]فَوَلیدُ الْبَیتِ أَحْرَی أَنْ یکُونَ
لِوَلی الْبَیتِ حَقّاً وَلَداً

Tarjama: Da ace Allah yana da ɗa. Na'am sai dai kuma cewa shi Allah ya nesanta ya daukaka ya tsarkaka daga abin da suke siffantawa, hakika Allah bai da wani ɗa, to da haka ne to lallai wanda aka haifa cikin gida shi ne ya fi dacewa da kasancewa ɗan mai gida.[Tsokaci 1]

Har Ila yau Shamsu Istihabati shi ma ya rera baituka cikin harshen Farisanci:

این خانه را باید خدا در عرش معماری کند
آدم بنایش بر نهد جبریل هم یاری کند
آید خلیل الله در او یک چند حجاری کند
او را اولوالعزمی دگر منقوش و گچکاری کند
اینسان خدا از خانه‌اش چندی پرستاری کند
تا ساعتی از دوستی یک میهمانداری کند
وز میهمانداری دگر امر قوی جاری کند
پس نقش‌های ماسَلَف بُد بهر این زیبا خَلَف

Tarjama: Wannan gida Allah ne a kan karagar mulki ya gina shi, sannan Adam ya taimakawa Jibril aza harsashin gina shi Da Hannun da Khalil ya sassaka wasu adadin duwatsu shi da ya kasance daga ulul azmi ya yi zane-zane da kwalliya a jiki.. Bawan Allah ya kula da gidansa na dan wani lokaci, don ya ba wa wani abokinsa bakunta na tsawon wani lokaci, kuma karbar wani abu ne mai karfi, don haka matsayin magabata ya yi kyau ga wannan kyawun.


Mahanagar Allama Taharani dangane Asrar din Haihuwar Imam a Dakin Ka'aba

Sayyid Muhammad Husaini Husaini Tahrani Babban Malami ne na Shi'a a karni na 14 h ya ce: daya daga cikin Asraru na haihuwar Imam Ali (A.S) Dakin Ka'aba na iya kasancewa Allah ne ya ce: ya ke Ka'aba hakika albarkacin haihuwar wannan yaro zan tsarkake ki daga datti da kazantar Gumakan da suke cikinki. zan kuma ajiye wani sirri da za iya zama mafi zurfafa da nutso, shi ne cewa: Gaskiyar kula da Ka'aba ita ce kula da wannan haske da aka haifa a cikinsa; Domin idan aniyar kula da dakin Ka'aba ne kawai a kula da wannan gini da kuma wadannan duwatsu, to wannan ma wani nau'i ne na bautar gumaka, kuma rabon ya nuna cewa jikin dan Adam wanda datti ne ya kula. zuwa ga Ka'aba, kuma ruhin mutum, wanda yake a zahiri, ya mayar da hankali ga wannan haske guda; Kuma ko wane nau'i yana haɗuwa da irinsa: haske don haske, ƙasa don ƙasa..[25]

Nazari

An rubuta ayyuka dangane da Haihuwar Imam Ali (A.S) a Ka’aba, daga cikinsu akwai:

  • "Ali Waliduyl Ka'aba" na Muhammad Ali Urdubadi: An buga wannan littafi da kuma a cikin Mausu'atu Allama Al Ardubadi. Fassarar Farisanci ana kiranta da "Yegane Maulud Ka'aba".
  • "Walidul Ka'aba" na Sayyid Muhammad Rida Husaini Jalali: Wannan littafi ya kunshi hikayoyi da kasidu da dama game da haihuwar Imam Ali (AS) a dakin Ka'aba kuma an buga shi a shekara ta 2003.
  • "Almualud Fi Baitullahi Haram Aliyu Bin Abi Talib Am Hakim Bin Hizam" na Sayyid Nabil Hasani: A cikin wannan littafi, marubucin ya yi kokarin tabbatar da cewa haihuwa a Ka’aba na daga cikin Falalolin Imam Ali (A.S). Kuma Zubairu bin Bakir da baffansa Mus’ab bin Abdullahi sakamakon kiyayyarsu da Imam Ali (A.S) suka danganawa Hakim bin Hizam wannan labari.[26]

Bayanin kula

  1. Masoudi, Moruj al-Dahahab, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi.349; Mofid, Al-Arshad, 1414 AH, juzu'i na 1, shafi na 5.
  2. Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, Mujalladi na 6, shafi na 43-37.
  3. Amini, Al-Ghadir, 1416 AH, Mujalladi na 6, shafi na 44-51.
  4. Marashi Najafi, Sharhin Ihkakul Hakki, Maktabatu Ayatullahi Mar-ashi, juzu'i na 7, shafi na 486-491.
  5. Teburin amsa shubuhohi، «آیا بر اساس منابع شیعه و اهل سنت امیرمؤمنان علیه السلام در کعبه به دنیا آمده اند؟»، Yanar Gizo na Cibiyar Nazarin Hazrat Wali Asr.
  6. Sibt Bn Jawzi, Tadhkirat al-Khawas, 1401 BC, shafi na 20.
  7. Ibn Sabbagh, Alfusulu Muhimma, 1422 BC, sashi na 1, shafi na 171
  8. Halabi, Al-Sira Al-Halbiyyah, 1400 H., juzu'i na 1, shafi na 226.
  9. Hakim Nishaburi, al-Mustadrik Ali al-Sahiheen, 1422 H., juzu'i na 3, shafi na 483.
  10. Ganji Shafi'i, Kefaiya Talib, 1404H, shafi na 707
  11. Ibn Maghazali, Manaqib al-Imam Ali bin Abi Talib, 1424 AH, shafi na 58-59; Ibn Hatim Shami, Al-Dur al-Nazim, 1420H, shafi na 225.
  12. Sheikh Sadouq, Ilalusharayi, 1385, juzu'i na 1, shafi na 135.
  13. Sheikh Sadouq, Ma'ani Al-Akhbar, 1403H, shafi na 62.
  14. Sheikh Sadouq, Amali, 1376, shafi na 132.
  15. Mohammadi Rayshahri, Daneshnameh Amirul Momineen (AS) barfaye Alqur'ani wa Hadisi wa Tarik, 2018, Mujalladi na 1, shafi na 78.
  16. Tabari, Tuhfa Al-Abrar, 1376, shafi na 165-164.
  17. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 35, shafi na 9. Mofid, Al-Arshad, 1414 AH, juzu'i na 1, shafi na 5.
  18. Mofid, Al-Irshad, 1414 AH, juzu'i na 1, shafi na 5.
  19. Qureshi Asadi, Jamraha Nasab Quraysh wa Akhbaraha, 1381 AH, shafi na 353.
  20. Shushtari, Kamus Al-Rijal, 1410 AH, juzu'i na 3, shafi.387; Morteza Ameli, Sahih Man Sirah al-Nabi, 1426 AH, juzu'i na 2, shafi na 160
  21. Shushtri, Kamus Al-Rijal, 1410 AH, juzu'i na 3, shafi.387; Morteza Ameli, Sahih Man Sirah al-Nabi, 1426 AH, juzu'i na 2, shafi na 160
  22. Ibn Shahrashob, Manaqib Ale Abi Talib - Tabab al-Maktaba al-Haydariyyah, juzu'i na 2, shafi na 24
  23. Ibn Abi al-Hadid, Sharhu Nahj al-Balaghah.
  24. Amini, Al-Ghadir, juzu'i na 6, shafi na 29.
  25. حسینی طهرانی، امام شناسی، ۱۴۲۵ق، ج۱، ص۱۱۷؛ مقام امیرالمؤمنین و کیفیت ولادت آن حضرت در خانه، وبگاه مکتب وحی.
  26. Hosni, Al-Moloud Fi Baytullah Al-Haram, 1433 AH, shafi na 104-99.

Tsokaci

  1. Kamar yadda ayoyin Alkur'ani suka bayyana, Allah ya fi daukaka ya tsarkaka daga sifofin halittunsa kuma ba ya kamanta da wani abu. (Suratul Shura, aya ta 11 da suratul Tauhidi, aya ta 3) kuma idan aka yi amfani da irin wadannan tawili ta hanyar waka da makamantansu, ba yana nufin sanyawa Allah kwatankwacin halittun duniya ba.

Nassoshi

  • مقام امیرالمؤمنین و کیفیت ولادت آن حضرت در خانه، Adireshin ofishin wahayi.
  • Ibn Sabbagh Maliki, Ali Ibn Muhammad, Al-Fusul al-Muthama fi Marafah al-Imam, Qum, Dar al-Hadith, 1422H.
  • Ibn Maghazali, Ali Ibn Muhammad, Manaqib al-Imam Ali Ibn Abi Talib, Beirut, Darul Awtah, 1424H.
  • Amini, Abdul Hossein, Al-Ghadir fi Al-Kitab wa Sunnah wa Al-Adab, Qum, Cibiyar Al-Ghadir, 1416H.
  • Hakeem Neishaburi, Muhammad bin Abdullah, al-Mustadrak Ali al-Sahiheen, Beirut, Dar al-Fikr, 1422H.
  • Hosni, Sayyid Nabil, Al-Mawlud fi Baitullahi al-Haram Ali bin Abi Talib Am Hakim bin Hizam, Karbala, Al-Utbah al-Husainiyyah al-Maqdisa, Qasm al-Shaon al-Fiqriyyah da Al-Thaqafiyyah, 1433 AH/2012 AD
  • Hosseini Tehrani, Mohammad Hossein, Imamology, Mashhad, Allameh Tabatabayi, 1425H.
  • Halabi, Ali bin Burhan al-Din, Al-Sira al-Halabiyyah fi Sira al-Amin al-Ma’mun, Beirut, Dar Al-Marafah, 1400H.
  • Mohammadi Rayshahri, Muhammad, Daneshnameh Amir al-Mominin (amincin Allah ya tabbata a gare shi) bisa Alqur'ani, Hadisi da Tarihi, Qum, Cibiyar Kimiyya da Al'adu ta Darul-Hadith, Kungiyar Bugawa, 2009.
  • Sabat bin Jozi, Youssef bin Farghli bin Abdullah al-Baghdadi, Al-Khwas Taqret, Beirut, Mu'assasa Ahl al-Bait, 1401H.
  • Shami, Yusuf bin Hatem, Al-Dar al-Nazim fi Manaqib na Imaman Allah, Kum, Jamia Madrasin, 1420H.
  • Shushtri, Mohammad Taqi, Al-Rajal Dictionary, Qum, Al-Nashar al-Islami Institute, 1410 AH.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Amali, Tehran, Kitabchi Publications, 1376.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Ma'ani Al-Akhbar, Qum, ofishin yada labaran Musulunci, 1403H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Dokokin Dokoki, Kum, Shagon Littafin Darvri, 1385.
  • Sheikh Mufid, Muhammad bin Muhammad, Al-Irshad fi Marafah Hajjullah Ali Al-Abad, Qum, Al-Bait Foundation, 1414H.
  • Tabari, Muhammad bin Ali bin Rostam Tabari, Bashara al-Mortaza na Shi'a al-Mortaza, bincike na Javad Qayyumi Esfahani, Al-Nashar al-Islami Foundation na Jamaat al-Madrasin a Kum al-Mushrafah, 1420H.
  • Tabari, Emad al-Din Hasan bin Ali, Tohfa al-Abrar, Tehran, rubuce-rubucen al'adun gargajiya, 1376H.
  • Qureshi Asadi Makki, Zubair Bin Bakkar, Jamhara Nasab Quraysh and Akhbars, Research: Mahmoud Mohammad Al Shaker, Madani Press, 1381 AH.
  • Ganji al-Shafa'i, Muhammad bin Youssef, Kefaiya Talib fi Manaqib Ali bin Abi Talib, Tehran, Dar Ayyaya Tarath Ahl al-Bait (AS), 1404H.
  • Morteza Ameli, Seyyed Jafar, Sahih Man Sirat al-Nabi al-Azam (a.s), Kum, Dar al-Hadith, 1426H.
  • Murashi Najafi, Seyyed Shahabuddin, Sharhin Ahqaq al-Haq, Qum, Mazhabar Ayatullah Murashi, Bita.
  • Masoudi, Ali bin Hossein, Promoting Al-Dahab and Maaden Al-Jawhar, Research by Asad Daghar, Qum, Dar Al-Hijrah, 1409 AH.