Kitabu Ali

Daga wikishia
domin kaucewa rudewa ku duba: Jami'atu

Kitabu Ali (Larabci: كتاب علي (ع)) ko kuma ace Aljami’atu wani littafi ne na Hadisi wanda Annabi (S.A.W) ya shifta shi Imam Ali (A.S) ya rubuta shi da Alkalaminsa wannan littafi ya kunshi Ajiyoyin Imamanci da suke shiryarwa kan Imamancin Ma’abocin Littafin, kan asasin Hadisai a cikin Aljami’atu anyi bayani baki dayan hukunce-hukuncen shari’a kai hatta mafi kankantarsu da dikkarsu anyi bayaninsu, daga Aklak, Akida, Kissosin Annabawa Riwayoyin Badini suna daga sauran Bahasosi da wannan littafi ya tattaro. Ya zo cikin Riwayoyi cewa baya ga Ahlil-baiti an samu mutanen da suka taba ganinsa, daga cikinsu akwai Muhammad Bn Muslim, Zuraratu Bn A’ayun da Mansur Abbasi, Shaik Mahadi Muhrizi ya rubuta littafi mai sunan Kitabu Ali kan maudu’in Aljami’atu.

Gabatarwa da kuma Muhimmanci

Kan asasin Hadisan Shi’a Kitabu Aljami’atu wani littafi ne da aka rubuta shi shiftawar Annabi (S.A.W) da kuma rubutun Alkalamin Imam Ali (A.S) [1] a cikin riwayoyi ya zo da wasu sunayen misalin Sahifa [2] Kitabu Ali , [3]wasu ba’arin Masu zurfafa bincike sun tafi kan cewa dukkanin wadannan sunaye suna danganewa da littafi daya, saboda dukkanin siffofin aka ambata suna komawa gareshi ne [4] sai dai kuma a gefe Agha Buzurg Tahrani wanda ya rayu tsakanin shekaru 1293-1389 hijiri Kamari ya tafi kan cewa Kitabu Ali yana da banbanci da Aljami’atu <refAgha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1408H, Juzu'i na 2, shafi na 305-306.</ref>

Aljami’atu Alama ce kan kasancewa Imami

Kan asasin ba’arin wasu riwayoyi hakika Aljami’atu wasu ajiyoyin Imamanci ne da suke shiryarwa kan Imamancin Ma'abocin littafin [5] Agha Buzurg Tahrani ya tafi kan cewa KItabu Ali (A.S) kamar sauran Ajiyoyi ya kasance a hannun Imaman Shi’a daga wancan zuwa wanann hannu da hannu yana zazzagayawa tsakaninsu a yanzu haka yana hannun Imam Mahadi (A.F) [6] Abinda Littafi yake Tattare da shi Kan Asasin Riwayoyi masu yawan gaske, baki dayan hukunce-hujkunce daga Halal da haram kai hatta kananan abubuw misalin Diyyar Yakushi an ambace su cikin littafin Aljami’atu [7] wasu ba’arin Masu zurfafa bincike sun rinjayar da tsammani kan cewa an kirayi wannan littafi da Aljami’atu sakamakon ya tattaro dukkanin hukunce-hukunce [8] Sayyid Husaini Mudarrasi Tabataba’i daga Masu zurfafa bincike a Shi’a a karni na sha biyar tareda jingina da riwayoyi masu yawa ya bayyana cewa littafin ya tattaro bahasi kan wadannan abubuwa kamar haka: hukunce-hukuncen rassan addini da suka hado da sallah, Hajji, Jihadi, Aure, Saki, Alkalanci, shahada, Haddodi, da Diyyoyi, (Aklak, Akidu, Falaloli, Kissoshin Annabawa da riwayoyin Badini [9]

Siffofi

A cikin riwayoyi an bayyana girman littafin Kitabu Ali tsayinsa ya kai Zira’i Saba’in = meter 35 takriban [10] sannan fadinsa kusan daidai yake da cinyar Rakumi [11] an yi maganganu kan fadada da girmansa [12] sai dai cewa a wasu ba’arin riwayoyi ya zo cewa wannan littafi karami ne bai da girma bai wuce a sanya shi cikin Kuben Takobi ba [13] wasu ba’arin Masu bincike tareda jingina da wasu riwayoyin daban sun tafi kan cewa wannan karamin littafi bashi ya kunshi dukkanin Kitabu Ali ba a’a wani bangare ne daga littafin [14] Sayyid Muhammad Kazim Tabataba’i wanda aka Haifa a shekara 1344 hijira shamsi ya tafi kan cewa wannan karamin littafi wani littafi ne daban ba Kitabu Ali (A.S) [15]

Masu bada Rahoto

Kan asasin Binciken Majid Ma’arif wanda aka Haifa shekara ta 1332 shamsi fiye da mutum Arba’in ne suka rawaito asalin samuwar littafin Aljami’atu [16] kan asasin ba’arin wasu Riwayoyi wasu adadi daga Sahabban A’imma misalin Muhammad Bn Muslim [17] Zuraratu Bn A’ayun [18] Abu Basir Muradi [19] Abdul-Malik Bn A’Ayun [20] da Mu’attab [21] da ma wasu ba’ari daga Makiyansu misalin Mansur Abbasi duka sun ga Littafin Aljami’atu [22] a cewar Sayyid Muhammad Kazim Tabataba’i akwai riwaya 70 cikin Wasa’il Shi’a da Aka nakalto su daga littafin Kitabu Ali (A.S) [23]

Mahangar Ahlus-sunna

Wasu ba’arin Masu zurfafa bincike sabanin Rahotannin da suka daga bangaren `Yan Shi’a da suke banbanta abinda littafin Jafaru ya kunsa da abinda Aljami’atu yake kunshe da shi, Rahotannin Ahlus-sunna sun bayyana cewa babu wani banbanci tsakaninsu duk abu daya ne [24] Sayyid Mir Sharif Jurjani daga Malaman Mazhabar Hanafiyya a karni na takwas, ya tafi kan cewa littafin Aljami’atu an rubuta shi da shakali da sura Ramzi da tsarin ilimin Haruffa [25] Haji Khalifa ya bayyana cewa littafin Jafaru ya kunshi ilmin Lauhu Kada, shi kuma Aljami’atu yana kunshi ilimin Lauhu Kadar [26] Kallo da ido daya Mahadi Muhrizi ya wallafa littafi cikin Maudu’in Kitabu Ali (A.S) cibiyar Sahifatu Kiradu ta buga shi a shekara 1`390 shamsi yana dauke da shafuka 220, [27]

Bayanin kula

  1. Safar, Basair Al-Darajat, 1404 AH, shafi na 142-146; Kliny, Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 239.
  2. Safar, Basair Al-Darajat, 1404 AH, shafi na 153-155.
  3. Ahwazi, Al-Zuhd, 1402 AH, shafi na 39; Ash’ari, Al-Nawader, 1408H, shafi na 79; Barki, Mahasen, 1371 AH, juzu'i na 1, shafi na 107 da 273.
  4. Bhardost, "Jafar da Aljami'atu", shafi na 476.
  5. Sheikh Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, 1403 AH, shafi na 102-103; Sheikh Sadouq, Man La Yahzara Al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 4, shafi na 418-419.
  6. Agha Bozur Tehrani, Al-Dhari'ah, 1408H, juzu'i na 2, shafi na 305.
  7. Safar, Basair al-Darajat, 1404 AH, shafi na 142-146; Kliny, Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 239.
  8. Bhardost, "Jafar da Aljam'atu", shafi na 477.
  9. Madrasi Tabatabai, Mirasu Maktub Shi'a, 2006, shafi na 32-36.
  10. Kulainy, Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi na 239; Sheikh Sadouq, Man la Yahzara Al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 4, shafi na 419.
  11. Sheikh Tusi, Al-Tahdhib, 1407H, juzu'i na 9, shafi na 271.
  12. Bhardost, "Jafar da Aljami'atu", shafi na 477
  13. Barqi, Al-Mahasen, 1371 AH, juzu'i na 1, shafi na 17-18; Nasa’i, Al-Sunan Al-Kubra, 1421H, juzu’i na 8, shafi na 56.
  14. Bhardost, "Jafar da Aljami'atu", shafi na 477.
  15. Tabatabai, Tarikh Hadis Shi'a, Mujalladi na 1, shafi na 65-66.
  16. Ma'arif, Fajuheshi dar tarikh hadis Shi'a, 1374, shafi na 43-45.
  17. Sheikh Tusi, al-Tahdhib, 1407H, juzu'i na 9, shafi na 271.
  18. Kulainy, Kafi, 1407 AH, juzu'i na 7, shafi na 94.
  19. Safar, Basair Al-Darajat, 1404H, shafi na 143.
  20. Safar, Basair Al-Darajat, 1404H, shafi na 153.
  21. Safar, Basair Al-Darajat, 1404H, shafi na 145
  22. Al-Jandi, Imam Jafar al-Sadiq, 1397H, shafi na 200.
  23. Tabatabai, Tarikh Hadis Shi'a, 1388, juzu'i na 1, shafi na 69.
  24. Bhardost, "Jafar da Aljami'atu", shafi na 477.
  25. Jurjani, Sharh Al-Mawakif, 1325 Hijira, juzu'i na 6, shafi na 22.
  26. Haji Khalifa, Kashf Al-zunun, 1941, juzu'i na 1, shafi na 591.
  27. Mehrizi, Kitab Ali, 1390.

Nassoshi

  • Agha Bozur Tehrani, Mohammad Mohsen, Al-Dhari'a al-Tsanif al-Shi'a, Qum, Ismailian, 1408 AH.
  • Ash'ari, Ahmad bin Muhammad bin Isa, al-Nawader, Qum, mazhabar Imam Mahdi (a.s) 1408H.
  • Al-Jandi, Abdul Halim, Imam Jafar al-Sadiq, Alkahira, Majlis al-Ali for Islamic Affairs, 1397H.
  • Ahwazi, Hossein bin Saeed, Al-Zuhd, Kum, Al-Matababa Al-Alamiya, 1402H.
  • Barqi, Ahmed bin Muhammad, Al-Mahasen, Qum, Dar Al-Katb Al-Ulamiya, 1371H.
  • بهاردوست، علیرضا، «جفر و جامعه»،A cikin Encyclopaedia na Duniyar Musulunci, Tehran, Mu’assasar Encyclopaedia ta Musulunci, 1385.
  • Jurjani, Mir Seyyed Sharif, Sharh Al-Mawakif, Qom, Al-Sharif al-Razi, 1325H.
  • Haji Khalifa, Mustafa bin Abdullah, Kashf Al-Dhunun akan Sunayen Al-Kitab da Al-Funun, Baghdad, Makarantar Al-Muthani, 1941.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bn Ali, Ma'ani Al-Akhbar, Qum, ofishin da'a na Musulunci, 1403H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man La Yahdrah Al-Faqih, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, 1413H.
  • Sheikh Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Tahdhib, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Safar, Muhammad bin Hassan, Basair Al-Darajat, Qum, Ayatullah Murashi Najafi Library, 1404H.
  • Tabatabai, Seyyed Mohammad Kazem, Tarikh Hadith Shi'a , Tehran, Samt, 2008.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-kafi, Tehran, Dar Al-Kitab al-Islamiya, 1407H.
  • Madrasi Tabatabai, Hossein, Rubutun Gadon Shi'a, Kum, Gidan Buga Tarihi, 2006.
  • Ma'arif, Majid, Bincike a Tarikh HadisShi'a, Tehran, Cibiyar Al'adu da Fasaha ta Zareeh, 1374.
  • Mehrizi, Mehdi, Kitab Ali, Kum, Sahifeh Khard, 1390.
  • Nasa'i, Ahmad bin Shoaib, Al-Sunan Al-Kabari, Beirut, Al-Risalah Foundation, 1421H.