Mubahala
- Wannan maƙala ce game da gamammiyar ma'anar mubahala. Domin sanin waƙi'ar mubahala, ku duba shafin Mubahalar Annabi (S.A.W) Tare da Kiristocin Najran
Mubahala, (Larabci: المباهلة) tana nufin roƙon tsinuwar Allah da azabarsa da niyyar tabbatar da gaskiyarka da ƙaryata da'awar abokin rigimarka. Ana yin mubahala a lokacin da tattaunawa da kafa hujja da dalili suka gaza ba da ma'ana, ko wane ɓangare ya kafe kan maganarsa da ra'ayinsa. An ce tun kafi muslunci ana yin mubahala cikin wasu al'ummu.
Mubahalar Annabi (S.A.W) tare da Kiristocin Najran, ɗaya ce daga cikin mubahaloli da aka yi a farkon Muslunci. Bisa ba'arn rahotanni, Ahlul-Baiti (A.S) sun kasance suna gayyatar ɗaiɗaikun wasu mutane zuwa ga mubahala; daga cikinsu akwai Imam Baƙir (A.S) ya gayyaci Abdullahi Bin Umar Lisi mubahala. Haka nan malaman Shi'a misalin Mir Findiriski, Jafar Kashiful Giɗa da Allama Ɗabaɗaba'i, su ma sun koyi da Imamansu cikin gayyatar masu saɓani da su zuwa mubahala.
Ma'anar Mubahala Da Matsayinta
"Mubahala" tana nufin mutane biyu da suke da saɓani da juna, domin tabbatar da gaskiya ko wane ɗaya daga cikinsu zai roƙi Allah ya saukar da tsinuwa kan abokin rigimarsa[1] ya tona asirin maƙaryaci ya kuma saukar masa da azaba.[2] Ana yin mubahala a lokacin da tattaunawa da kawo dalili da hujja suka gaza ba da ma'ana.[3]
A rahotan majiyoyin tarihi da hadisi, a farkon Muslunci, an yi mubahala ko kuma dai an yi gayyaci wasu ɗaiɗaikun mutane zuwa ga mubahala[4] daga cikin mubahaloli da aka yi akwai mubahalar Annabi (S.A.W) tare da Kiristocin Najran wace magana kanta ta zo a Kur'ani.[5] Annabi ya yi haka domin tabbatar da gaskiyar Muslunci.[6] Sayyid Muhammad Husaini Ɗabaɗaba'i, malaman fiƙihu da falsafa na Shi'a ya bayyana wannan mubahala a matsayin dawwamammiyar mujizar.[7]
Taƙaitaccen Tarihin Mubahala
Bisa rahotan ba'arin masana, al'adar mubahala tana da samuwa tun kafin zuwan Muslunci; alal misali mutanen al'ummar Sam, a lokacin wayewar Babil, duk sanda suke son tabbatar da gaskiyarsu ko tabbatar da da'awarsu, suna yin rantsuwa da tsinuwa idan har ƙarya suka faɗa to Allah ya sauka musu da azaba;[8] Haka nan bisa wata riwaya da Allama Majlisi ya naƙalto a littafin Biharul Al-Anwar, a cikin al'adar Yahudawa da Nasara akwai mubahala.[9]
Du'a'u Mubahala'
Imam Sadiƙ (A.S): Ya Allah idan wane ya yi inkarin wani haƙƙi ya bayyana ƙarya, ka jarrabe shi da wani bala'i daga sama da wata azaba daga wurinka
Ladubban Mubahala
Muhammad Yaƙub Kulaini, malamin hadisi na Shi'a ya kawo wata riwaya, wace bisa abin da ta ƙunsa, a lokacin mubahala za mu sanya yatsun damanmu cikin yatsun abokan rgimarmu.[11] A wata riwayar kuma ya zo cewa za a yi tsinuwa har sau saba'in kan abokin rigima.[12] A wani hadisin daban, lokacin da yafi dacewa a yi mubahala shi ne (Bainal Ɗulu'ani) tsakanin huduwar alfijir sadiƙ da hudowar rana.[13]
Mutanen Da Suka Yi Mubahala
Tun daga farkon Muslunci mutane ne daban-daban suka yi amfani da mubahala domin tabbatar da da'awarsu, ba'arinsu sun kasance kamar yadda bayani zai zo a ƙasa:
Mubahalar Annabi (S.A.W) Tare da Kiristocin Najran
Bisa rahotanni marbuta tarihi, Annabi Akram (S.A.W) cikin wasiƙar da ya aika zuwa malaman kiristanci, da suke zaune a Najran ya kira su zuwa addinin Muslunci. Sun zo Madina sun tattauna tare da shi, sai dai kuma ba su tuba daga aƙidarsu ba ta danganta allantaka ga Sayyidina Isa (A.S). bayan dogon bahasi da jidali, sai suka yanke shawarar yin mubahala tare da shi. A ranar mubahala Annabi (S.A.W) ya ɗauko Imam Ali (A.S), Sayyida Faɗima (S) da Hasanaini (A.S); sai dai cewa Kiristoci ba su yarda an yi wannan mubahalar ba, daga ƙarshe dai sun nemi a yi sulhu, Annabi ya karɓi buƙatarsu ta sulhu amma tare da sharaɗin za su dinga biyan jiziya.[14]
Mubahalar Ahlul-Baiti (A.S) Tare da Masu Adawa Da Su
Bisa naƙalin Allama Ɗabaɗaba'i a cikin Tafsirul Almizan, cikin ba'arin litattafan hadisi ya zo cewa Annabi (S.A.W) ya gayyaci Yahudawa mubahala; amma sai suka ƙi amsa gayyata,[15] Haka nan a cikin littafin Al-Jafariyyat, an ambaci cewa Imam Ali (A.S) cikin tabbatar da rashin ziharin kuyanga, ya gayyaci wasu mutane zuwa mubahala.[16] A rahoton Kulaini, lokacin da Imam Baƙir (A.S) ya kasance yana bahasi tare da Abdullahi Bin Umar Lisi kan wani maudu'i, Ibn Lisi ya kafe kan ra'ayinsa, sai Imam Baƙir (A.S) ya nemi su yi mubahala.[17]
Mubahalar Sahabban Ahlul-Baiti (A.S) Tare da Masu Saɓani Da Su
Bisa rahotan Abu Mukhnif, marubucin Maƙtal na Shi'a, a cikin waƙi'ar Karbala, Burairu Bin Khudairi Hamdani, daga cikin shahidan Karbala da Yazid Bin Ma'aƙal, daga sojojin Umar Bin Sa'ad, sun yi mubahala kan halifancin Imam Ali (A.S).[18] A cewar Faizul Kashani a cikin Tafsirul As-Safi, Abdullahi Bin Abbas, sahabin Annabi (S.A.W) a lokuta daban-daban ya gayyaci wasu ɗaiɗaikun mutane misalin Zaidu Bin Sabit, daga marubuta Kur'ani,[19]zuwa mubahala.[20]
Shaikh Mufid a cikin Al-Irshad ya naƙalto cewa baban Khairani, hadimin Imam Jawad (A.S) ya gayyaci Ahmad Bin Muhammad Bin Isa wanda ya kasance yana inkarin halifancin Imam Hadi (A.S), zuwa ga mubahala, amma sai ya tsorata daga ƙarshe dai ya miƙa wuya ya yi iƙrari da halifanci Imam Hadi (A.S).[21] Haka nan Shaik Ɗusi a cikin littafin Al-Gaiba ya rubuta cewa Husaini Bin Ruhu Naubekti, na uku cikin Nuwwabul Arba'a, ya yi mubahala da Shalmagani, bayan wani gajeren lokaci sai Shalmagani ya mutu.[22] Najashi shi ma ya yi bayani cewa Abu Abdullahi Safwani ya yi munazara da mubahala da alƙalin garin Mosul game da imamanci, bayan wasu ƴan kwanaki sai alƙalin ya mutu.[23]
Mubahalar Malaman Shi'a Da Masu Saɓani Da Su
Mulla Ahmad Naraƙi, marubucin Mi'irajus Sa'ada, a cikin Khaza'in ya rubuta cewa Abul Ƙasim Findiriski, a cikin wata tafiya da ya yi zuwa wani garin Kafirai, ya yi bahasi da su, sai suka bayyana masa cewa wanzuwar wuraren ibadarsu da rushewar masallatan musulmi dalili ne kan gaskiyar addininsu. Mir Findiriski ya yi watsi da wannan da'awa ta su, sannan domin tabbatar da maganarsa sai ya yi kiran sallah ya kuma yi sallah a cikin wurin ibadarsu wanda hakan ya janyo faɗowar rufin ginin wurin ibadar ta su.[24]
An ce Jafar Kashiful Giɗa, daga maraji'an taƙlidi na ƙarni na 13 ƙamari, ya gayyaci Mirza Muhammad Ikhbari, daga sanannun Akhbariyawa a Iran mubahala, sai dai kuma shi Mirza ɗin bai zo mubahalar ba.[25]Bisa wani rahoto, Allama ɗabaɗaba'i shi ma ya yi tayin mubahala ga wasu ba'rin Ahlul-Kitabi, ya yi imani da cewa ita mubahala rayayyiyar hujja ce, duk sanda sharuɗɗa suka cika tana bayar da sakamako mai kyau.[26]
Ku Duba
Bayanin kula
- ↑ Majlisi, Mir'atul al-Aqool fi Sharh Akhbar Al-ul-Rasoul, 1404 AH, juzu'i. 12, shafi. 185
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir al-Numno, 1374, juzu'i. 2, shafi. 578.
- ↑ Mohammadi Ray Shahri, Farhangenameh Mubahele, 2016, shafi na 11.
- ↑ Misali, duba Abu Mukhnif, Waqqa al-Taffi, 1417 AH, shafi. 221; Faiz Kashani, Tafsir as-Safi, 1415 AH, juzu'i na 2, shafi na 17; Ibn Abd al-Barr, Jame al-Ilim wa Fazlihi, 1421 AH, shafi na 381; Mufid, Al-Irshad fi Marifah Hajajillah Alal Al-Abad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 298; Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 307.
- ↑ Suratul Ale-Imran, aya ta 61.
- ↑ Paknia, "Mubahala, Roshantarin Bawarehaye Shi'eh," shafi. 51.
- ↑ Tabataba'i, I'ijaz qur'an, 1362, shafi na 127-128.
- ↑ Luyi, Mubahala Dar Madina, 1378, shafi. 65.
- ↑ Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i. 10, shafi. 65.
- ↑ Al-Kulaini, Kafi, 1407 AH, juzu'i. 2, shafi. 514.
- ↑ Al-Kulaini, Kafi, 1407 AH, juzu'i. 2, shafi. 514.
- ↑ Al-Kulaini, Kafi, 1407 AH, juzu'i. 2, shafi. 514.
- ↑ Al-Kulaini, Kafi, 1407 AH, juzu'i. 2, shafi. 514.
- ↑ Ibn Sa’ad, Tabaqat al-Kubra, Khamisa 1, 1410 AH, shafi na 391-392.
- ↑ Tabataba'i, Tafsir al-Mizan, 1417 AH, juzu'i. 3, shafi. 234.
- ↑ Ibn Ash'ath, Al-Ja'fariyyat, Maktaba al-Nin al-Hadithah, shafi. 115.
- ↑ Al-Kulaini, Kafi, 1407 AH, juzu'i. 5, shafi. 449.
- ↑ Abu Mokhnif, Waqqa al-Taffi, 1417 AH, shafi. 221.
- ↑ Ibn Abd al-Barr, Jame al-Ilim wa Fadlihi, 1421H, shafi na 381.
- ↑ Fayz Kashani, Tafsir al-Safi, 1415 AH, juzu'i. 2, shafi. 17.
- ↑ Mufid, Al-Irshad fi Marifah Hajajillah Alal Al-Ibad, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 298.
- ↑ Tusi, Al-Ghaybah, 1411 AH, shafi. 307.
- ↑ Najashi, Rijal al-Najashi, 1365, shafi na 393.
- ↑ Naraqi, Khazaen, 2001, Shafi na 48.
- ↑ «مباهله راهکاری برای مقابله با افراد بی منطق است»،Kamfanin Dillancin Labarai na Rasa
- ↑ Bostan Kitab, Marzuban Wahayi Wa Kherad, 2002, shafi. 290.
Nassoshi
- «مباهله راهکاری برای مقابله با افراد بی منطق است»، Kamfanin Dillancin Labarai na Rasa, ranar shigarwa: Maris 5, 2010, kwanan wata ziyara: Disamba 17, 2024.
- Ibn Abdul Bar, Yusuf bn Abdullah, Jame’ al-Ilim wa Fadlihi, Mas’ad Abdul Hamid Sa’dani ya yi bincike a Beirut, Darul Kutb al-Ilmiyah, 1421H.
- Abu Mukhnaf, Lut ibn Yahya, Waqa’at al-Taffi, Muhammad Hadi Yusuf al-Gharavi ya yi bincike, Qum, Jamia al-Modrasin, bugu na uku, 1417H.
- Ibn Ash’ath, Muhammad ibn Muhammad, Al-Ja’fariyat, Tehran, Maktaba al-Ninwi al-Hadithah, bugu na farko, bi-ta.
- Ibn Sa’ad, Muhammad bn Sa’d, Al-Tabaqat al-Kubra, Muhammad Abdulkadir Atta, ya yi bincike a Beirut, Darul Kutb al-Ilmiyah, bugu na farko, 1410H.
- Bustan al-Kitab, Marzuban al-Wahayi wa Kherad, Qom, Bustan al-Kitab, bugu na farko, 1381H.
- پاکنیا، عبدالکریم، مباهله روشنترین دلیل باورهای شیعه، Muballigan, fitowa ta 50, Maris 2003.
- Tabatabai, Sayyid Mohammad Hossein, I'ijaz Qur'an, Tehran, Cibiyar Buga Al'adun Raja, bugu na farko, 1362H.
- Tabatabai, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsiril Al-Qur'ani, Qum, Ofishin Buga Musulunci na Kungiyar Malaman Makarantar Qum, bugu na biyar, 1417H.
- Tusi, Muhammad bn Hassan, Al-Ghaybah, Mai bincike: Ebadallah Tehrani da Ali Ahmad Naseh, Qum, Darul Ma'arif al-Islamiyya, bugu na farko, 1411H.
- Fayz Kashani Mulla Mohsen, Tafsir al-Safi, wanda Hossein A'alami ya yi bincike a Tehran, Sadr, bugu na biyu, 1415H.
- Kulaini, Muhammad bn Ya'qub, Al-Kafi, wanda Ali Akbar, Ghaffari da Muhammad Akhundi suka yi bincike a Tehran, Darul Kutb al-Islamiyya, bugu na hudu, 1407H.
- Louis, Massignon, Mubahala Dar Madina, Mahmoud Reza Iftikharzadeh, Tehran, Resalat al-Qalam, ya fassara, 1378H.
- Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, kungiyar masu bincike ta Beirut, Dar Ihya al-Turat al-Arabi, bugu na biyu, 1403 AH.
- Majlisi, Muhammad Baqir, Mirat al-Uqol fi Sharh Akhbar Ale-Rasul, Mai bincike: Rasuli Mahallati, Seyyed Hashim, Tehran, Dar al-Kutb al-Islamiya, bugu na biyu, 1404H.
- Mohammadi Ray Shahri, Muhammad, Farhange Mubahla, Qum, Dar al-Hadith, 1395H.
- Mufid, Muhammad ibn Muhammad, Al-Irshad fi Ma’rifat Hujajllah Alal al-Ibad, Mai bincike: Cibiyar Al-Bait (AS), Qum, Sheikh Mufid Congress, bugu na farko, 1413H.
- Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugun farko, 1374.
- Najashi, Ahmed bin Ali, Rijal al-Najashi, Qom, Al-Nashar al-Islami Institute of the University of Madrasin Baqm al-Mushrafah, Jap 6, 1365.
- Naraghi, Ahmad, Khazain, bincike na Hasan Hassanzadeh Amoli, Qom, Qiyam, 1380