Mafatihul Al-Jinan (Larabci: مَفاتیحُ الجِنان) (Ma'ana Maƙullan ƙofofin aljanna) wani sanannen suna ne na littafin addu'a da ya yi matuƙar yaɗuwa tsakankanin ƴan shi'a wanda Shaik Abbas ƙummi, (Ya rayu tsakanin shekaru: 1294-1359) ya wallafa shi, wannan littafi ya tattaro addu'o'i, munajati, ziyarori, keɓantattun ayyukan ibada a kwanakin cikin shekara da watanni da kuma ladubba da munasabobin addini da aka naƙalto su daga Annabin muslunci da Imaman shi'a da kuma malamai. Mawallafin littafin ya ɗauko ɓangarori masu yawa daga daɗaɗɗun litattafai da suka gabace shi misalin Iƙbalul A'amal na Sayyid Ibn ɗawus da Misbah na Kaf'ami da Zadul Al-ma'ad na Allama Majlisi. Matanin addu'o'ida ziyarori ya rubuta su cikin harshen larabci, amma a mafarin ba'arin wasu addu'o'i a cikin littafin ya yi ƙarin bayani da harshen farisanci.

Hotan bangon littafin Mafatihul Al-Jinan

An fara fitar da littafin Mafatihul Al-jinan a shekara ta 1344 bayan hijira, a garin mashad na ƙasar Iran, cikin ƙanƙanin lokaci mutane suka wawasheshi ya ƙare, ana samun wannan littafi a wurare masu albarka a wurin ƴan shi'ar ƙasar Iran, wannan littafi kusan shi ne littafin da ƴan shi'a suka fi riƙo da shi cikin ayyukan mustahabbi da kuma lokacin munasabobin addini, mafi shaharar tarjamar da aka yiwa wannan littafi zuwa daga larabci zuwa farinsa ta kasance tarjama da Mahadi Ilahi ƙumshe ya yi, muhaddis ƙummi ya yi ƙari a ƙarshen Mafatihu da Al-baƙiyatus As-salihat wanda shi ma ya ƙunshi addu'o'i, ziyarori, da sallolin mustahabbi, a cikin mafi yawan kwafin mafatihu za ka samu wannan ƙari cikin hashiyar littafin.

Litattafai guda biyu, Mafatihu Nawin da Minhajul Al-hayat an samar da su domin isnadi da shi kuma littafin Mafatihul Al-hayat dimin kammala mafatihu, akwai kulasosi da taƙaicewa masu yawa da aka yi kan mafatihu waɗanda suka kasance da sunaye daban-daban.

Gabatatarwa Tare da Muhimmanci

Littafin Mafatihul Al-jinan wanda Shaik Abbas ƙummi muhaddisul shi'a ya rubuta shi a ƙarni na 14, ya kasance ɗaya daga cikin mashhuran litattafan addu'o'i da ziyarori kuma mafi yaɗuwa tsakanin jama'ar shi'a a ƙarni na goma sha huɗu musammam ma a ƙasar Iran, haka zalika ƴan shi'a a faɗin duniya suna amfani da wannan littafi a lokutan munasabobin addini, Mafatihul Al-jinan baya ga kur'ani ya kasance littafin da aka fi bugawa da yaɗawa tsakankanin ƴan shi'a[1]a cewar ministan al'adu na ƙasar Iran tsawon shekaru 45, a ƙasar Iran kaɗai an buga kwafi miliyan 28 na wannan littafi[2] ba'arin cibiyoyi da kamfanonin litattafai sun zaɓi wasu ɓangarori daga wannan littafi sannan suka ɗabba'a su ɗauke da sunaye misalin "Muntakhab Mafatihu" ko kuma "Guzideh az Mafatihu". A watan Khordar shekara ta 1402 hijira shamsi, an shirya taron bikin cika shekara ɗari da wallafa littafin Mafatihul Al-jinan a ƙasar Iran[3] an buɗe wannan taro da karanta saƙon Ayatullahi Makarim Shirazi ɗaya daga maraji'an taƙlidi.[4]

 
Tambarin tunawa da shekara 100 da rubuta Mofatih al-Jinan

Game da Marubucin Littafin Mafatihul Al-jinan

Tushen ƙasida: Shaik Abbas ƙummi

Wanda ya tattara Mafatihul Al-jinan shi ne Shaik Abbas ƙummi (Wafati:1359.h.ƙ) ya kasance daga kwararrun malaman shi'a a fagen ilimin hadisi, tarihi da salon jawabi. Ya rubuta litattafai masu yawa gaske, littafin Safinatul Al-bihar da Muntahal Al-amal suna daga cikinsu, an binne Shaik Abbas muhaddisul ƙummi a garin najaf cikin haramin Imam Ali (A.S).[5] ɗansa ya naƙalto cewa mahaifinsa ya rubutu littafin Mafatihul Al-jinan yana tare da alwalarsa.[6] Shaik Abbas ƙummi ya wallafa wannan littafi tare da niyyar yin gyara kan littafin Miftahul Al-jinan,[Tsokaci 1] sakamakon a wancan zamani littafin ya yaɗu ba tare da sanya isnadin addu'o'in da suke cikinsa ba, wasu bayin Allah sun buƙaci ya wallafa littafi guda mai cin gashin kansa da yake tattare da isnadan addu'o'i masu isnadi tare da sauran ingantattun addu'o'i.[7]

Hususiyoyi

Mafatihul Al-Jinan yana da babban sashe guda ɗaya, wanda aka kafa shi a babi uku: addu'o'i, ayyukan shekara-shekara da ziyarori. An ƙara wani sashe da taken Albaƙiyatul As-salihat, Shaik Abbas ƙummi bai kawo addu'o'i ba a cikin wannan littafi tare da isnadinsu, kaɗai ya wadatu da bayani inda ya naƙalto waɗannan addu'o'i.[8] haka nan wasu ba'arin addu'o'in da ya naƙalto a cikin Mafatihu bas a isa zuwa ga Ma'asumai, ya bayyana cewa wallafar ba'arin wasu malamai ne kamar misalin Du'a'u Adila.[9]

Ƙare-ƙare Kan Mafatihu

Shaik Abbas domin hana wasu ƙara wani abu cikin mafatihu, ya yi tsinuwar Allah da Manzonsa da A'imma tsarkaka (A.S) kan duk wani mutum da ya yi masa ƙari cikin littafinsa na Mafatihul Al-jinan,[10] amma tare da haka kamfanonin da suke buga wannan littafi sun ƙara wani sashe da suka kira da suna mulhaƙat na biyu na mafatihu, daga jumlar waɗannan mulhaƙat akwai addu'a bayan sallar Imam Husaini (A.S) da Imam Jawad (A.S) da kuma hadisul kisa'i.[11] ba'arin kamfanonin sun yi ƙara a sashen Albaƙiyatul As-salihat sun ƙara masa sashe biyu, saboda haka mafatihu na yanzu yana da ɓangarori guda shida kaso ɓangarori uku ne kaɗai ainahin abin da Shaik Abbas ƙummi ya rubuta, su ne: Asalin Mafatihu, mulhaƙat mafatihum albaƙiyat as-salihat, sannan ɓangarori uku da aka yi masa ƙari daga baya sun kasance: mulhaƙat na biyu na mafatihu, mulhaƙat na farko baƙiyat salihat, mulhaƙat na biyu baƙiyat salihat.[12]

Tsari Da Abin da Ya Tattaro

Galibi yawancin bugun Mafatihul Al-jinan da farkonsa yana farawa ne da adadin wasu surori masu tsayi da gajejjeru.[Tsokaci 2] abubuwan da Mafatihul Al-jinan ya ƙunsa an rarraba su zuwa adadi babuka rukuni-rukuni: Babi na farko:: Addu'o'i Sun tattaro Takibat addu'o'i da ake yi bayan idar da sallolin farilla, ayyukan dare da rana da kwanakin cikin mako, sanannun salloli misalin sallar Manzon Allah (S.A.W), sallar Amirul muminin (A.S), sallar Sayyida Faɗima (S), sallar Jafar ɗayyar, ziyarorin Imamai a kwanakin mako da ba'arin addu'o'i da munajati kamar haka: munajatin khamsa ashar daga Imam Sajjad (A.S), munajatin Imam Ali a masallacin kufa, du'a'u samat, kumail, jaushan sagir, jaushan kabir, du'a'u makarimul akhlaƙ da sauransu.

Babi na biyu: Ayyukan Shekara Wannnan babi ya ƙunshi ayyukan ibada na mustahabbi tsawon shekara, abubuwan da suke cikin wannan sashe suna farawa daga watan rajab tare da ayyukan ibada na jimada sani, bayan nan sai ayyukan sabuwar shekarar farisawa, suna ƙarƙarewa da watanni rumawa. Munajatin sha'abaniyya a cikin ayyukan watan sha'aban, du'a'u Abi Hamza simali, du'a'u iftita da du'a'u sahar, ayyukan dare lailatul ƙadri a watan ramadan, du'a'u Imam Husaini (A.S) a ranar arafa cikin ayyuka zil hijja, suna daga mafi shaharar ayyukan ibada da wannan babi ya tattaro a cikin Mafatihul Al-jinan.

Babi na uku: sashen ziyarori A wannan babi da farko ya kawo abubuwa game da ladubban tafiya da ziyara da kuma kiran sallah da shiga harami. Ziyara ta farko ta kasance ziyarar Manzon Allah (S.A.W) bayanta sai ziyarar Sayyida Faɗima (S), bayan ita sai ziyarar Imaman da aka binne a maƙabartar baƙi'a, ƙari kan ziyarar imamai sha biyu, wannan sashe ya tattaro ziyarorin ƴaƴan Imamai da ba'arin manyan mutane da kuma malaman shi'a, kamar misalin ziyarar Sayyidina Hamza, Muslim ɗan Aƙilu, Faɗima bint Asad, shahidan yaƙin uhud, Salamnul Farisi da sauransu. Ayyukan ba'arin sanannun masallatai misalin masallacin kufa, masallacin sa'asa'a suma wannan littafi ya kawo su.

Mafi tsayin sashe a wannan babi ya keɓantu ne da ziyarar Imam Husaini (A.S), sannan mafi shaharar takardar ziyarar Imam Husaini(A.S) misalin ziyarar ashura, ziyarar arba'in da ziyarar waris an naƙalto a wannan sashe, du'a'u nudba, du'a'u ahad da ziyaratul jami'a kabira ta zo a sashen da yake da alaƙa da ziyarar Imam Zaman (A.F). bayan ziyarori da suke da alaƙa da Imam Zaman (A.F), ziyaratu anbiya da ziyarar Faɗima Ma'asuma (A.S) da ziyarar Sayyidina Sha Abdul-azim Hasani an naƙalto su a ƙarshen wannan babi, wanda ya kasance ƙarshen abubuwa da Mafatihu ya tattaro a tsohon Mafatihul Al-jinan bugu na farko, waɗannan batutuwa na ƙarshe sun kasance ƙarƙashin taken ziyarorin ƙaburburan muminai da addu'o'i da suke da alaƙa da su.

Mulhaƙat Mafatihu

Shaik Abbas ƙummi cikin bugun kwafi na biyu ya ƙara wani sashe da ya kira da suna Mulhaƙat Mafatihu.[13] cikin wannan sashe akwai batutuwa guda takwas da aka ƙara su cikin Mafatihu, a amannar marubucin wannan littafi, mutane suna tsananin buƙatar wannan addu'a, waɗannan abubuwa guda takwas sun kasance kamar haka:

  • Addu'ar bankwana da watan ramadan
  • Huɗubar ranar idin ƙaramar sallah
  • Ziyaratu Jami'eh A'immatul muminin
  • Addu'a bayan gama ziyara
  • Ziyarar bankwana da Imamai
  • ƙuri'a domin neman buƙata
  • Addu'a a zamanin gaibar Imam Zaman
  • Ladubban ziyarar niyaba.
 
Du'a'u Kumail Cikin Mafatin Rubutun Hannu Na Tahir Afshari

Baƙiyatus Salihat

Baƙiyatus salihat wani littafi ne na marubucin Mafatihu da ya jona cikin hashiyar Mafatihu,[14] yan hijira.[15] a cikin ɗaba'i daban-daban na Mafatihul Al-jinan, an gabatar da wannan littafi haɗe da Mafatihu. Wannan littafi yana ƙunshi babuka guda shida sashe da ake kira da mulhaƙat su kasance kamar haka:

  • Babi na farko: takaitaccen ayyukan dare da yini waɗanda sun kasance ba'arin ladubban rayuwa da yau da gobe da addu'o'in awannin yini da kuma koyar da yadda ake sallar dare, duka an yi bayaninsu.
  • Babi na biyu: ba'arin nafilfilu misalin sallar hadaya ga ma'asumai, sallar daren farko bayan binne mamaci, sallolin neman buƙata, sallolin istigasa, sallolin ranakun mako, suna daga jumlarsu.
  • Babi na uku: addu'o'i da tsari domin magance raɗaɗi da cututtuka, an yi bayani addu'o'in kawar da raɗaɗi da cututtuka daban-daban cikin wannan babi.
  • Babi na huɗu: zaɓaɓɓun addu'o'i daga littafin Al-kafi, addu'o'in wannan sashe su ma galibinsu addu'o'i ne na kawar da matsaloli, misalin ƙarancin arziƙi da buƙatunb duniya.
  • Babi na biyar: kawo ba'arin hirzi da gajejjerun addu'o'i da aka tsamo su daga littafin Muhaj Ad-da'awat da Almujtana. Haka nan wannan babi ya kawo addu'o'i neman nesanta daga bala'i da wasu munajat da addu'o'i na neman arziƙi.
  • Babi na shida: bayanin hususiyar ba'arin surori da ayoyi da ambato ba'arin addu'o'i da abubuwa daban-daban, hususiyoyin ba'arin ayoyin kur'ani da surori suna da tasiri cikin warware matsalolin rayuwa, cikin wannan sashe an kawo addu'a domin yin mafarki, addu'a domin nazarin karatu, ladubban aƙiƙa, istihara da kur'ani suma duka an kawo su cikin wannan babi.
  • Khatima: taƙaitaccen bayani game da hukunce-hukunce matattu

Madogaran Littafi

Ba'arin madogaran da Shaik Abbas ƙummi ya jingina da su cikin wallafa littafin Mafatihul Al-jinan waɗanda aka kawo sunansu cikin wannan littafi su ne kamar haka:

1. Isbatul Al-hudati na Shaik Hurrul Amili

2. Al-Ihtijaj na Ahmad ɗan Ali ɗabarsi

3. Al-Iktira na Ibn Baƙi

4. Arba'atu Ayyam ma Mirdamar

5. Al-Azriya wanda ya shahara da Ha'iyya na Shaik Kazim Azri

6. I'ilamul Alwara na Shaik ɗabarsi

7. Iƙbal na Sayyid Ibn ɗawus

8. Al-amali na Shaik ɗusi

9. Al'aman na Sayyid Bin ɗawus

10. Biharul Al-anwar na Allama Majlisi

11. Baladul Al-amin na Kaf'ami

Shaik Abbas ƙummi ya ambaci wasu madogaran ƙari kan waɗannan a cikin littafin Mafatihu, daga jumlarsu: Tarikh Alamul arayi Abbasi na Mirza Iskandar big munshi, Tuhufatl Az-za'air na Allama majlisi, tahzibul ahkam shaik ɗusi, jami'ul al-akhbar (ba a san marubcinsa ba) Jamalul Usbu na Sayyid Ibn ɗawus.[16]

 
Mafatihu Nawin

Bugawa, Yaɗawa Da Tarjama

A shekarar 1344 bayan hijira ne Shaik Abbas ya wallafa Mafatihul Al-jinan, sannan a karo farko aka buga shi da yaɗa shi a garin Mashad na ƙasar Iran.[17] wannan littafi ya samu kyakkyawan rubutu ta hannun manya-manayn kwararrun a fannin kyawunta rubutu misalin ɗahir khusnawis,[18] Misbabu zadeh[19] Mirza Ahmad zanjani[20] Muhammad Rida afshari[21] sun rubuta shi da salon rubutun hannun na nastaaliƙ, an ɗabba'a miliyoyin kwafin wannan littafi cikin salo daban-daban, sakamakon girman da littafin yake da shi ne ya sanya ba'arin kamfanonin littafi suka zaɓi wasu adadin abubuwa da littafin suka buga shi da taken "Muntakhabul Mafatihu" ko kuma "Guzideh Mafatihu".[22]

Tarjama

ƙarin bayani da Shaik Abbas ya sanya a gefen duk wata addu'a ko ziyara, ya yi wannan ƙarin bayani da harshen farisanci, amma matanin addu'a da ziyara ya rubuta shi tun asali da harshen larabci, sai dai cewa an samu wasu sun tarjama shi zuwa harshen farisanci, mafi yaɗuwa da shaharar tarjamar farisanci ta Mafatihu ta kasance tarjamar Mahadi Ilahi ƙumshe, sauran tarjamomin sun kasance ne ta hannun Sayyid Hashim Rasuli mahallati,[23] Husaini Ustaduli,[24] Muhammad Baƙir Kamra'yi da sauransu.

A ranar 9 ga watan Khordad shekara ta 1402 hijira shamsi, wanda ya yi daidai da 10 ga watan zil ƙa'ada shekara ta 1444 bayan hijira an shirya taron bikin cikar shekara 100 da rubuta Mafatihul Al-jinan.[25]cikin wannan taro an nuna sabun kwafin Mafatihul Al-jinan kan asasin rubutun hannu na ɗahir kyakkyawan rubutun da ya yi gyara kan rubutun Shaik Abbas ƙummi.

Bambance bambance da yake tsakanin nau'uka kwafi daban-daban tare da sanya ƙarin bayan a kasan matanin shafi, an ware addu'o'i an yi musu gaɓa-gaɓa, kowacce gaɓa an sanya mata lamba, haka kuma an yi amfani da alamomin rubutu misalin, alamar tsayawa, alamar dagatawa da ci gaban rubutu.[26] Mafatihul Al-jinan ya samu tarjama zuwa sauran harsuna daga jumlarsu harshen turanci (an tarjama shi har karo huɗu zuwa harshen turanci), harshen faransanci, turkanci, urdu da harshen sipaniyanci.[27]

 
Littafin Minhajul Al-Hayat na Muhammad Hadi Yusufi Garawi

Suka

Malamai masu dandaƙe bincike sun suka kan kan abin da yake cikin Mafatihu da kuma da'awar da Shaik Abbas ya cikin littafi. Alal misali akwai sananniyar waƙa ta jami[28] da ya kawo amma kuma sai ya dnaganta ta zuwa ga nazzami ganjawi.[29] haka nan Nasir makarim shirazi cikin muƙaddimar Mafatihul Nawin kawar da tawaya, ƙara mariskai da madogaran addu'a da ziyarori, kiyaye sharuɗɗa na zamani da mahalli tare da cire wasu abubuwa da ka iya jawo matsala ta hannun masu muguwar niyya, yana ganin wani yanki da ɓangare ne da ya hukunsa sabinta duba da nazari mai faɗi kan littafin Mafatihul Al-jinan..[30]

Litattafai Da Suke Da Dangantaka Da Mafatihu

Tushen ƙasida:Mafatihul Nawin (Littafi)

Mafatihul Nawin na Nasir makarim shirazi, littafi ne da ya rubuta shi da niyyar riskar da sanadai, tantacewa tare kuma kammala Mafatihul Al-jinan.[31] Manufar Ayatullahi Makarim kan wannan littafi ta kasance domin la'akari da zamanin da muke ciki da kuma cire wasu abubuwa da ka iya taimakawa magauta cikin kawo suka da matsaloli cikin Mafatihul Al-jinan.[32] a cewar marubucin ƙara muƙaddima kan kowanne sashe daga addu'a da ziyarori, kawo madogarai da masadir ɗin addu'a a ƙasan shafi, cire ba'arin ayyuka masu kama da juna da raunana, mayar da hankali kan abin da addu'o'i da ziyarori suka tattara akai, rashin wadatuwa da isnadi cikin ɗaɓarsu, na daga abubuw ada wannan littafi ya keɓanta da su.[33]


Minhajul Al-hayat

Tushen ƙasida: Minhajul Al-hayat Fi Ad'iya Waz-ziyarat

Muhammad Hadi Yusufi tare da dandaƙe bincike ya rubuta wannan littafi, cibiyar Majma Jahani Ahlul-baiti ce ta ɗauki nauyi buga wannan littafi, littafi ne da ya yi bincike kan kammalallen isnadin addu'o'i da ziyarori da suke cikin Mafatihul Al-jinan..[34] tace sanadi da isnadin addu'o'i da ziyarorin cikin Mafatihul Al-jinan da kuma cire wasu abubuwa da maye gurbinsu da wasu tare da kawo madogarai masu inganci a wani lokaci kuma ana mayar da addu'o'i da ziyarorin zuwa ga madogaran tarihi.[35]

 
Mafatihul Al-Hayat

Mafatihul Al-hayat

Tushen ƙasida: Mafatihul Al-hayat (Littafi)

Wasu gamayyar masu dandaƙe bincike ne ƙarƙashin kulawar Ayatullahi Abdullahi Jawadi Amoli suka rubutu littafin Mafatihul Al-hayat. Ya kira wannan littafi da sunan mafatihu mujalladi na biyu, haka nan manufar rubuta wannan littafi shi ne koyar da mutane tsari da salon rayuwar muslunci.[36] wannan littafi ya fifita da la'akari da zamani na yau, daidaituwa, za a iya ɗora shi da hali da yanayin da ake cikin a wannan zamani.[37]

Bayanin kula

  1. چاپ نزدیک به ۲۸ میلیون جلد مفاتیح الجنان پایگاه وزارت ارشاد.
  2. چاپ نزدیک به ۲۸ میلیون جلد مفاتیح الجنان پایگاه وزارت ارشاد.
  3. تارنمای وزارت فرهنگ و ارشاد اسلامی
  4. پیام آیت‌الله مکارم شیرازی به همایش مفاتیح الجنان. خبرگزاری ابنا. مرور خبر ۲۹ آذر ۱۴۰۲ش.
  5. Tali, Salishmar Hayat wa Athar Muhaddis Qommi, 1389 AH, shafi na 13-48.
  6. Qomi, Mafatih al-jinan, 1388H, shafi na 28.
  7. Qomi, Mafatih al-jinan, 1388H, shafi na 12.
  8. Sultani, Ishara bih Barāhayāz Mānbiḥ Mafātiḥ al-Jinān, 1389 AH, shafi 450.
  9. Sultani, Ishara bih Barāhayāz Mānbiḥ Mafātiḥ al-Jinān, 1389 AH, shafi 450.
  10. Qomi, Mafatih al-jinan, 1388H, shafi na farko, shafi 869.
  11. Qomi, Mafatih al-jinan, 1376 AH, shafi 985.
  12. Qomi, Abbas, Mafatih al-Jinan, 1387H.
  13. Qomi, Mufatih al-Jannan, 2008, shafi na 869.
  14. Qomi, Mafatih al-jinan, 1388H, Mukaddima Bakhsh Baqiyat al-Salihat, shafi na 903.
  15. Qomi, Mafatih al-jinan, 1388H, shafi na 1115.
  16. Sultani, Isharat bih Barāhayāz Mānbiḥ Mafatiḥ al-Jinān, 1389 AH, shafi 459-472.
  17. Tala’i, Salishmar Hayat wa Athar Muhaddis Qummi, 1389H, shafi na 31.
  18. Qomi, Mufatih al-Jinan, ba khushnawis Taher Khoshnavis, 1375.
  19. Qomi, Koliat Mofatih al-Janaan, Abbas Misbahzadeh khat, 1375.
  20. Qomi, Mafatih al-jinan, wanda: Ahmad bin Muhammad Hussein Zanjani ya rubuta, 1357 BC.
  21. Qomi, Kuliyat Mafatih al-Jinan, Khoshnevis Afshari, 1388H.
  22. Daga cikin su, Qomi, Muntakabul Mufatih al-jinan, 1385, wanda baya ga surorin Alkur’ani, ya tattara tare da buga wasu addu’o’i da ziyarori 40.
  23. Qomi, Kuliyat Mafatih al-jinan, fassarar gaba dayan nassi na Farisa da kuma hashiya na Sayyid Hashim Rasouli Mahallati, 1375 miladiyya.
  24. Ganbari, "mu'arrifi Tarjameh Nahj al-Balaghah"
  25. برگزاری همایش یکصدمین سال نگارش مفاتیح الجنان پایگاه صاحب‌خبران.
  26. ویژگی‌های مفاتیج رونمایی‌شده در همایش یکصدمین سال. پایگاه مصحف.
  27. Yek zikri ba sad zaban 1389 AH, shafi na 32
  28. "Jami" Haft Orang" Tohfa Al-Ahrar".
  29. Mufatih al-jinan, ziyaratu kuburu muminin
  30. مقدمه مفاتیح نوین حضرت آیت‌الله مکارم شیرازی، سایت هدانا.
  31. سیری در کتاب مفاتیح نوین.
  32. Makarem Shirazi, Mofatih Novin, 1390, shafi na 16.
  33. Makarem Shirazi, Mofatih Novin, 1390, shafi na 2
  34. مصاحبه با آیت‌الله یوسفی غروی درباره کتاب منهاج الحیاة.
  35. مصاحبه با آیت‌الله یوسفی غروی درباره کتاب منهاج الحیاة.
  36. مصاحبه با آیت الله استادی درباره مفاتیح الحیات، «کتاب مفاتیح الحیات را باید جلد دوم مفاتیح الجنان بدانیم»، پایگاه اطلاع‌رسانی کتاب‌راه.
  37. مصاحبه با آیت الله استادی درباره مفاتیح الحیات، «کتاب مفاتیح الحیات را باید جلد دوم مفاتیح الجنان بدانیم»، پایگاه اطلاع‌رسانی کتاب‌راه.

Tsokaci

  1. mifathul al-jinan kamar yanda Sayyid Yahaya limamin juma'a a msallacin mashad ya nakalto, marubucin wannan littafi shi ne shaik asadullahi tehrani ha'iri (Wafati:1333.h.q) ya kasance daga daliban Shaik murtada ansari, sannan ya yi tsawon rayuwa ya mutu yana da shekara 120. Ya zo a cikin littafin Fawaed Razwieh cewa shi dan garin Boroujardi ne kuma ma'abocin mimbari, kuma an san shi da gaskiya. (Agha Bozor, Tehrani, Al-Dhari’a, juzu’i na 21, shafi na 324.) A cikin littafin “Fawaed Razaviyeh” na Sheikh Abbas Qomi mai suna “Asadullah bin Abdallah al-Jordi”, ba a ambace shi ba. "Muftah al-Jinan".
  2. Surori sun bambanta a bugu da wallafe-wallafe daban-daban; Gabaɗaya, akwai surori kamar Yasin, Rahman, waqi'ah, Ankabut da Noor domin karanta su a ranaku daban-daban, ciki har da daren lailatul qadari.

Nassoshi