Sallar gawa

Daga wikishia
wannan wata kasida ce da take takaitaccen bayani game da ra'ayin fikihu wacce ba zata iya zama ma'uni kan ayyukan addini ba, domin ayyukan addini sai a komawa waa madogarar.

Sallahr gawa (Larabci: صلاة الميت) wata sallahh ce ta wajibi Kifa'i (Idan wasu suka yi sun sauke nauyi ga saura) gabanin binne mamaci, wani adadi na Musulmai suna taruwa su masa sallah, ana yin Kabbara hudu cikin wannan sallah, bayan yin kabbara ta farko sai a karanta Shahada biyu, bayan kabbara ta biyu a yi salati, bayan kabbara ta uku sai a nemi gafara ga Muminai da musulmi, bayan kabbara ta hudu sai anemawa mamacin akewa sallah gafara, bayan kabbara ta biyar shiken kuma an gama kowa sai ya tafi. sallahr gawa ta banbanta da sauran sallah, babu karatun Fatiha babu ruku’u babu sujjada babu tahiyya babu sallahma, haka kuma ba wajibi bane ayin dahara, da wannan dalili ne zaka iya yin sallahr ba tareda yin alwala ba, na’am kiyaye sharuddan sauran salloli a cikinta yana da kyau. Za a iya sallahr gawa cikin jam’i za kuma a iya yinta daidaiku; amma cikin jam'i dole ne mamu shima ya yi kabbarori biyar da addu’a. A wurin Ahlus-sunna kabbarori hudu akeyi sannan suna idar da ita da yin sallahma.

Ta’arifi

Addu’a da kabbarorin da ake ma gawa sune ake kira da sallahr gawa wacce take wajibi kan musulmi idan dan’uwansu musulmi ya rasu, bayan wanka da sanya masa likkafani gabanin bizne shi dole su yi masa sallah, kan asasin masadir din fikhu a cikin sallahr gawa, wasu sharudda da suke a cikin sauran salloli da suke wajibi misalin dahara ba sharadi bane cikin sallahr gawa [1] hakama babu sallahma cikin sallahr gawa.[2] sallahr gawa ba sallah bace A fadin Shahidus Sani kan asasin mahangar Mash’hur cikin Malaman fikhu, sallar gawa ba a kirgata cikin sallah a hakika wani Nau’i ce ta addu’a da akewa mamaci, saboda sallar da babu sujjada da ruku’u ai ba sallah ba ce, kuma dahara a sallah sharadi, amma ita sallar gawa babu daya cikin wadanan da take da shi.[3] A cikin littafin Fikhu Rida cikin riwayar daga Imam Rida (A.S) ya zo cewa sallar gawa ba sallah bace a hakika ba koma bace face kabbarori, saboda ita sallah akwai ruku’u da sujjada a cikinta[4]

Yaya ake Sallar gawa

Sallar gawar Muhammad Mahadi Asafi da Ayatullahi Nasir Makarim ya jagoranta

Gabanin sallatar gawa dole a sanya gawar ta kalli Alkibla ya zamana kansa yana bangaren dama kafafunsa na bangaren hagun masu sallah.[5] Dole masu sallah su kalli Alkibla [6] sannan ka da a samu nisa mai yawa tsakaninsu da gawar mamaci,[7] su sallahce shi suna tsaitsaye.[8] Masallatan bayan sun daura niyyar sallatar gawar sai su kawo kabarbari guda biyar bayan kowacce kabbara zuwa ta hudu akwai kebantacciyar addu’a da zasu yi, da sun yi kabbara ta biyar sallah ta kara.[9] Bayan kabbara ta farko zai kawo Shahada guda biyu, bayan ta biyu zai zai yi salati, bayan ta uku zai nemawa Muminai da musulmai gafara, bayan ta hudu zai nemawa mamacin gafara.[10]

Zikiri da addu’ar da ake yi bayan kabbarori hudu sune kamar haka:

Bambance bambance cikin sallah tsakanin Shi'a da mazhabobin Ahlus-sunna
Kabbara Gajeruwar addu'a Doguwar addu'a
Ta farko
اَشْهَدُ اَنْ لا الهَ الَّا اللَّهُ وَ اَنَّ مُحَمَّداً رَسوُلُ اللَّهِ
اَشْهَدُ اَنْ لا اِلهَ الا اللَّهُ
وَحْدَهُ لاشَریک لَهُ وَ اَشْهَدُ اَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَ رَسُولُهُ اَرْسَلَهُ بِالْحَقِّ بَشیراً وَ نَذیراً بَینَ یدَی السّاعَةِ
Ta biyu
اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلی مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّد
اَللّهُمَّ صَلِّ عَلی مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّدٍ وَ بارِک عَلی مُحَمَّدٍ وَ آلِ مُحَمَّدٍ وَارْحَمْ مُحَمَّداً وَ آلَ مُحَمَّدٍ کاَفْضَلِ ما صَلَّیتَ وَ بارَکتَ وَ تَرَحَّمْتَ عَلی اِبْرهیمَ وَ آلِ اِبْرهیمَ اِنَّک حَمیدٌ مَجیدٌ وَ صَلِّ عَلی جَمیعِ الاَنْبِیآءِ وَالْمُرْسَلینَ
Ta uku
اَللَّهُمَّ اْغفِرْ لِلْمُؤْمِنینَ وَ الْمُؤْمِناتِ
للّهُمَّ اغْفِرْ لِلْمُؤْمِنینَ وَالْمُؤْمِناتِ وَالْمُسْلِمینَ وَالْمُسْلِماتِ الاَحْیآءِ مِنْهُمْ وَالاَمْواتِ تابِعْ بَینَنا وَ بَینَهُمْ بِالْخَیراتِ اِنَّک مُجیبُ الدَّعَواتِ اِنَّک عَلی کلِّشَیئٍ قَدیرٌ
Ta hudu idan namji ne:
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِهذَا المَیت
idan mace ce:
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِهذِهِ المَیتَةِ
idan namiji ne:
اَللّهُمَّ اِنَّ هذا عَبْدُک وَابْنُ عَبْدِک وَابْنُ اَمَتِک نَزَلَ بِک وَ اَنْتَ خَیرُ مَنْزُولٍ بِهِ اَللّهُمَّ اِنّا لا نَعْلَمُ مِنْهُ اِلاّ خَیراً وَ اَنْتَ اَعْلَمُ بِهِ مِنّا اَللّهُمَّ اِنْ کانَ مُحْسِناً فَزِدْ فی اِحْسانِهِ وَ اِنْ کانَ مُسیئاً فَتَجاوَزْ عَنْهُ وَاغْفِرِ لَهُ اَللّهُمَّ اجْعَلْهُ عِنْدَک فی اَعْلا عِلِّیینَ وَاخْلُفْ عَلی اَهْلِهِ فِی الْغابِرینَ وَارْحَمْهُ بِرَحْمَتِک یا اَرْحَمَ الرّاحِمینَ
Idan mace ce:
اَللّهُمَّ اِنَّ هذِهِ اَمَتُک وَابْنَةُ عَبْدِک و ابنَةُ اَمَتِکَ نَزَلَتْ بِک وَ اَنْتَ خَیرُ مَنْزوُلٍ بِهِ اَللّهُمَّ اِنّا لا نَعْلَمُ مِنْها اِلاّ خَیراً وَ اَنْتَ اَعْلَمُ بِهامِنّا اَللّهُمَّ اِنْ کانَتْ مُحْسِنَةً فَزِدْ فی اِحْسانِها وَ اِنْ کانَتْ مُسیئةً فَتَجاوَزْ عَنْها وَاغْفِرْ لَها اَللّهُمَّ اجْعَلْها عِنْدَک فی اَعْلا عِلِّیینَ وَاخْلُفْ عَلی اَهْلِها فِی الْغابِرینَ وَارْحَمْها بِرَحْمَتِک یا اَرْحَمَ الرّاحِمینَ
[11]
Ta biyar an gama sallah an gama sallah

Malaman Fikihu

A wurin Malaman Ahlus-sunna sallar gawa ana mata kabbara hutu ne kawai, suna fara sallah da kabbarar farko sai fatiham bayan kabbara ta biyu sai suyi salati, bayan kabbara ta uku kuma sai yiwa mamacin addu’a, bayan kabbara ta hudu sai suyi sallahma shikenan sun gama,[12] na’am a cikin ba’arin wasu juzu’iyat din wannan sallah akwai sabani tsakankanin Ahlus-sunna.[13]

Hukunce-hukunce

Ba’arin wasu hukunce-hukuncen fikihun sallahr gawa sune kamar haka: sallahr gawa wajibi kafa’i, da wannan ne idan wani yayi ya saukewa sauran musulmi nauyin.[14] Cikin fadin Mawallafin littafin Jawahirul Kalam kan asasin Mashhurin Malaman fikihu, yin sallahr gawa fiye da sau daya kan gawa daya Makruhi ne,[15] kan fatwar Ayatullahi Sistani wannan Makruhancin bai tabbatu ba idan jana’izar daga ma’abota ilimi da tsoran Allah babu karhanci cikin yi masa sallah fiye da daya.[16] Za a iya yin sallahr gawa cikin jam’i sai dai cewa dole ne Mamu shi da kansa ya kawo kabbarori biyar da addu’o’i.[17] Wajibi ayi sallahr gaw aga duk wani musulmi da ya kai Shekaru shida.[18] Ba hailasta a sallahci Kafiri da Nasibi Makiyin iyalan Annabi (S.A.W).[19] Cikin sallahr babu wajabcin tsarkin hadasi karami da babba [20] na’am kiyaye sharuddan kamsu salawat da sauran sallolin wajibi abu ne mai kyau cikinta.[21] Dole ne a fara ma gawar sallah gabanin bizneta [22] bayan angama wankan gawa.[23] Idan aka bizne wani musulmi ba tareda yi masa sallah ba dole a yi masa sallah a kan kabarin.[24] Za a iya yiwa wasu adadin gawawwaki sallah daya ta wadatar [25] Makruhi ne ayi sallahr gawa cikin masallahci [26] wasu ba’arin Maraji’ai sun togace masallahcin Harami daga wannan karhanci,[27] amma wasu ba’arin kuma hatta shi kansa masallahcin Haramin bai fita daga wannan karhanci ba.[28] Za a iya yin sallahr gawa da takalmi duk da cewa yinta babu takalmi mustahabbi ne.[29] Jana’izozi da aka ma sallah a tarihin muslunci sallah da akayi kan Jana’izar Hazrat Fatima Zahra (A.S) da wacce aka jagoranta kan gawar Imam Komaini, wasu Jan’izozi ne da kowanne bangare yana dauki hankali, a fadar masana tarihin Hazrat Ali (A.S) hakika yayiwa Matarsa Fatima wankan gawa da cikin dare [30] shine ya mata sallahh,[31] a rahoton Malam Dabarasi, Imam Hassan da Imam Husaini a Mikdadu da Salmanul Farisi da Abu Zar Gaffari, da Ammar Bn Yasir da Akilu Bn Abu Talib da Zubairu Bn Awwam, Buraida Bn Hasib Aslami da wasu adadin Mutane daga Banu Hashim sun yi tarayya cikin sallahr Fatima Zahra (A.S) [32] Dalili da yasa hakan ta faru shine kasancewar Fatima (A.S) ta yima Imam Ali (A.S) wasiyya a kai ta kabari a cikin dare domin kada wanda suka zalunceta su samu damar tarayya cikin jana’izar ta da yi mata sallahh [33] sallahr da aka yiwa Imam Komaini tana daga cikin mafi cikar masu halartar jana’izar a tarihin musulmi, wannan sallah ta kasance a watan Kordad shekara ta 1368 wacce Ayatullahi Golfayagani ya jagoranta [34]

Bayanin kula

  1. Najafi, Jawahirul Kalam, 1404 AH, juzu'i na 12, shafi na 60.
  2. Allameh Hilli, Tazkrat al-Fiqha', 1414q, juzu'i na 2, shafi na 75; Shahid Thani, Al-Rudha al-Bahiya, 1410Q, juzu'i na 1, shafi..
  3. Shahid Thani, Rouz al-Janan, Al El Bayt Institute, shafi na 172 da 173..
  4. Fikhu al-Ridha, 1406 q, 179.
  5. Shahid Thani, Al-Rawdah al-Bahiyah, 1410q, juzu'i na 1, shafi.
  6. Najafi, Jawahirul Kalam, 1404 AH, juzu'i na 12, shafi na 53..
  7. Najafi, Jawahirul Kalam, 1404 AH, juzu'i na 12, shafi na 67.
  8. Shahid Thani, Al-Rawdah al-Bahiyah, 1410q, juzu'i na 1, shafi.
  9. Shahidi Awwal, al-Dros al-Sharia, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 112-113..
  10. Shahidi na farko, al-Dros al-Sharia, 1417 AH, juzu’i na 1, shafi na 113; Shahid Sani, al-Rawda al-Bahieh, 1410 AH, juzu'i na 1, shafi na 428.
  11. .Duba Bani Hashemi Khumaini, Tauzihul Almasa'il, 1424H, Mujalladi na 1, shafi na 337, fitowa ta 608.
  12. Malakhusro, Durar al-Hakim, Sharh Gharar al-Ahkam, Dar Ihya al-Kutub al-Arabiyya, Mujalladi na 1, shafi na 163.
  13. Negah Kaneed Beh Ibn Mazza, Al-Muheet Al-Burhani, 2004 CE, Part 2, shafi na 178; Malakhusro, Durar al-Hakim, Sharh Gharar al-Ahkam, Dar Ihya al-Kutub al-Arabiyya, Mujalladi na 1, shafi na 163.
  14. Mujamu Fiqihu Jawaher, 1417 s, juzu'i na 4, shafi na 172.
  15. Najafi, Jawahirul Kalam, 1404 AH, juzu'i na 12, shafi na 100.
  16. Bani Hashemi Khumaini, Tauzihul Masael Maraji , 1424 Hijira, Juzu'i na 1, shafi na 336, fitowa ta 606.
  17. Shahid Thani, Al-Rawdah al-Bahiyah, 1410q, juzu'i na 2, shafi.
  18. Shahidul Awwal, al-Dros al-Sharia, 1417 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 111.
  19. Shahidul Awwal, al-Dros al-Sharia, 1417 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 111
  20. Najafi, Jawahirul Kalam, 1404 AH, juzu'i na 12, shafi na 60.
  21. Amoli, Misbah al-Hadi, 1380H, juzu’i na 6, shafi na 369.
  22. Amoli, Misbah al-Hadi, 1380H, juzu’i na 6, shafi na 369.
  23. Najafi, Jawahirul Kalam, 1404 AH, juzu'i na 12, shafi na 68.
  24. Amoli, Misbah al-Hadi, 1380H, juzu’i na 6, shafi na 377.
  25. Allama Hali, Tadhkirat al-Fuqaha’, 1414 q, kashi na 2, shafi na 67.
  26. Najafi, Jawahirul Kalam, 1404 AH, juzu'i na 12, shafi na 98-99.
  27. Bani Hashemi Khumaini, Tauzihul Masael Maraji, 1424 Hijira, Juzu'i na 1, shafi na 339, fitowa ta 612.
  28. Najafi, Jawaharlal Kalam, 1404 AH, juzu'i na 12, shafi na 98-99. 98-99.
  29. Najafi, Jawahirul Kalam, 1404 AH, juzu'i na 12, shafi na 84.
  30. Tabari, Tarikh al-Umm da al-Muluk, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 473-474.
  31. Erbil, Kashf al-Ghumma, 1421 BC, Kashi na 2, shafi na 125.
  32. Tabarsi, I'ilamaul Alwara, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 300.
  33. Saduk, Ilalu Sharayi 1385 k shafi na 185.
  34. سایت گینس<

Nassoshi

  • Ibn Maze, Mahmoud bin Ahmad, Al-Muhait al-Burhani fi fiqhu al-Nu'mani fiqhu al-Imam Abi Hanifa, Allah ya kara masa yarda, Abdulkarim Sami al-Jandi, Beirut, Dar al-Kitab al ya yi bincike. -Alamiya, 2004.
  • Erbali, Ali Ibn Isa, Kashf al-Ghamma fi Marafah al-Imam, Qom, Razi, bugu na farko, 1421H.
  • Bani Hashemi Khomeini, Seyyed Mohammad Hossein,Taizihul Masael Mutabik ba-Fatwa Sizda Nafar Az Maraji Taklid Mu'azzam, Qum, ofishin buga littattafan Musulunci mai alaka da al’ummar hauza ta Kum, shekara ta 1424 bayan hijira.
  • Amoli, Mirza Mohammad Taqi, Misbah Al-Hadi fi Sharh al-Arwa al-Waghti, Tehran, 1380H.
  • Shahidul Awwal, Muhammad bin Makki, al-Dros al-Sharia fi fiqhu al-Amamiyyah, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci da ke da alaka da al’ummar hauza ta Qum, 1417H.
  • Shahid Thani, Zain al-Din bin Ali, al-Rawda al-Bahiyyah fi Sharh al-Lama' al-Damashqiyyah, Mohammad Kalantar's margin, Qom, Davari kantin sayar da littattafai, 1410 AH.
  • Shahid Thani, Zain al-Din bin Ali, Roz al-Janan fi Sharh Irshad al-Azhan, Qom, Al-Al-Bait Institute, Jap I, Beta.
  • Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ilalu Sharayi, Bincike na Sayyid Mohammad Sadiq Bahrul Uloom, Al-Najaf Al-Ashraf, Al-Muktaba Al-Haydriya, 1385H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hasan, Al-Wari's Declaration, Qum, Al-Bayt Lahia al-Trath Foundation, 1417H.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarihin Al'ummai da Al-Muluk, Beirut, Mu'assasa Al-alami, 1403H.
  • Allameh Hali, Hasan bin Yusuf, Tazkira al-Fiqha, Qum, wanda ya assasa Al-Bait, 1414H.
  • Faqe al-Reza, Mashhad, Al-Bait institute, 1406 AH.
  • Mullah Khusro, Muhammad bin Faramruz, Darr al-Hakam, Sharh Gharr al-Hakam, Bija, Dar Ehiya Kitub al-Arabiya, Bita.
  • Najafi, Mohammad Hasan, Javaher al-Kalam fi Sharh Shar'e al-Islam, Abbas Quchani da Ali Akhundi, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1404 H.