Jump to content

Likkafani

Daga wikishia


Likkafani (Larabci: الكفن) lulluɓe jikin mamaci Musulmi kafin binne shi. Tufafin da za a suturce shi da shi alal aƙalla ka da ya gaza ƙyalle guda uku: Mi'izar (Wani yanki ne na likkafani da ake ɗaura shi daga cibiya zuwa gwiwa), Riga da izari (Ƙyalle da ake lulluɓe baki ɗayan jikin mamaci). Wajibi ne sanya wa duk wani mamaci Musulmi likkafani amma wajibi kifa'i. Bai kamata a yi amfani da ƙyalle na ƙwace ko najasa ba. Mustahabbi ne mutum ya tanadi likkafaninsa tun yana raye.

Gabatarwa Da Kuma Wajibai

Likkafani, wani ƙyallen yadi ne da ake amfani da shi cikin suturce jikin mamaci Musulmi kafin binne shi.[1] Sanya likkafani ga mamaci namiji ko mace wajibi kifa'i ne.[2] Samar da likkafanin mace wajibi ne kan mijinta,[3] Amma samar da likkafanin sauran mutane yana wuyansu saboda abin da yake wajibi shi ne yin likkafani ga gawa ba wai ba da likkafani ba[4] Ba awajabta kan kowa ba[5] Bisa fatawa malaman fiƙihu idan dukiyar mamaci ba za ta isa a saya masa likkafani ba, za a iya fitar da kuɗin likkafanin daga dukiyar zakka.[6]

Ana yin likkafani da ƙyallen yadi guda uku:[7]

  1. .Mi'izar, za a ɗaura shi daga cibiyar mamaci zuwa gwiwa, yana lulluɓe baki ɗayan geffan jiki, zai fi kyau a ɗaura shi daga ƙirji zuwa saman ƙafafuwa.[8]
  2. .Riga, wajibi a ɗaura ta daga saman kafaɗu zuwa rabin ƙwaurin ƙafafuwa, a lulluɓe dukkan geffan jiki[9] zai fi kyau ta kai har saman ƙafafu.[10]
  3. .Izari, wajibi a lulluɓe tun daga kai har zuwa ƙafafuwa, kuma faɗinsa wajibi ya kasance da girman da gefansa zai rufe saman ɗaya gefan.[11] Zai fi kyau tsayinsa zai kai tun daga kan mamaci har zuwa ƙafafunsa a ɗaure shi.[12]

Baya halatta cikin halin samun zaɓi yin likkafani ga mamaci da yadin ƙwace ko najasa haka ƙyallen tsuran yadin alharir ko ƙyalle yadi da yake cuɗanye da ulu ko gashin dabbar da namanta ya haramta.[13]

Kafin likkafani ga mamaci ko yayin yi masa, wajibi ne a shafa Kafur kan wurare bakwai na jikinsa waɗanda yake ɗora su kan ƙasa yayin da yake sujjada.[14] Ana kiran wannan aiki da sunan hanuɗ kuma yinsa wajibi ne.[15]

  • Shahidi a fagen yaƙi bayan shahada ba ya buƙatar likkafani sai idan babu tufafi tare da shi, a irin wannan hali wajibi ne a masa likkafani.[16]

Mustahabbai Da Makaruhai

Mustahabbi ne tanadar likkafani tun mutum yana raye[17] daga ƙyallen burdul yamani[18] ana so ya kasance tare da ƙamshi mai daɗi (Ƙamsasa shi da turare makaruhi ne, amma ƙamsasa shi da Kafur mustahabbi ne).[19] Saɓanin wannan magana, an ce makaruhi ne amfani da ƙyallen yadi daga jinsin kitani[20] da kuma amfani da kayan aiki na yanka shi da suka kasance daga ƙarfe misalin almakashi, daga cikin makaruhai a likkafani an yi ishara da abubuwa misalin: likkafin ya kasance tare da hannu da maɓallin riga, baƙin launi ko kuma a yi rubutu jikin likkafanin da baƙin launi, rawani ba tare da ɗaura shi ƙasan haɓar mamaci ba, likkafani ya kasance mai datti, lokacin sayen likkafani a dage neman sauki ba tare da larurar hakan ba, ɗinka ƙyallen likkafani. Na'am an ce idan an yi masa likkafani daga rigar da yake sawa lokacin da yake a raye to wajibi ne a cire maɓallan jikin rigar, sannan hannun rigar babu matsala, amma wajibi ne rigar ta zama za ta wadatar cikin lulluɓe miƙdarin da ya zama wajibi a lulluɓe..[21]

Ku Duba

  • Binne Gawa
  • Sallar Gawa
  • Tahniɗ
  • Talƙin

Bayanin kula

  1. Duba: Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi na 402-403.
  2. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi. 402; Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1426 AH, juzu'i. 2, shafi. 456.
  3. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi. 405; Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1426 AH, juzu'i. 2, shafi na 531-533.
  4. Najafi, Jawaher al-Kalam, 1426 AH, juzu'i. 2, shafi na 535-536; Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi. 407.
  5. Najafi, Jawaher al-Kalam, 1426 AH, juzu'i. 2, shafi na 535-536; Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi. 407.
  6. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi. 409; Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1426 AH, juzu'i. 2, shafi. 539.
  7. Najafi, Jawaher al-Kalam, 1426 AH, juzu'i. 2, shafi. 456.
  8. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi. 402; Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1426 AH, juzu'i. 2, shafi na 457-458.
  9. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi na 402-403; Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1426 AH, juzu'i. 2, shafi na 461-462.
  10. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi na 402-403.
  11. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi na 402-403; Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1426 AH, juzu'i. 2, shafi. 463.
  12. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi na 402-403.
  13. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi. 404; Najafi, Jawaher Al-Kalam, 1426 AH, juzu'i. 2, shafi na 465 da 469.
  14. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi na 413-414.
  15. Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1409 AH, juzu'i. 1, shafi na 413-414.
  16. Tabatabaei Yazdi, Al-Arwa Al-Wuhtga, mawallafin Ayatollah Uzma Al-Sayed Al-Sistani, juzu'i. 1, shafi. 294.
  17. Hurrul Ameli, Wasa’il al-Shi’a, 1395 AH, juzu’i. 2, shafi. 755.
  18. Najafi, Jawaher al-Kalam, 1932, juzu'i. 4, shafi. 196; Muassase Da'iratul Ma'arifil Fiqhil Islami, Farhange Fiqhe Farsi, 1385, juzu'i. 2, shafi. 98.
  19. Al-Musawi Al-Khomeini, Tahrir Al-Wasilah, 1390 AH, juzu'i. 1, shafi na75.
  20. Najafi, Jawaher al-Kalam, 1426 AH, juzu'i. 2, shafi na 465 da 469.
  21. Yazdi, Al-Urwa Al-Wughati, Al-Nasher Makarantar Ayatullah Azami Sayyid Al-Sistani, juzu'i. 1, shafi na 316;https://www.sistani.org/persian/book/26575/6114/

Nassoshi

  • Hurru Ameli, Muhammad bn Hassan, Wasa’il al-Shi’a: Zuwa ga isar sha’anin Shari’a, Beirut, Dar Ihya’ al-Turat al-Arabi, Beirut, 1412 Hijira.
  • Khomeini, Sayyid Ruhollah, Tahrir al-Wasilah, Najaf, Al-Adab Press, 1390H.
  • Najafi, Muhammad Hassan, Jawaher al-Kalam fi Thobeh al-Jadeed: Sabuwar hanyar nazarin bincike na littafin Jawaher al-Kalam da gabatar da shi da tsarin maudu'i, Kum, sashen ilimin fikihu musulunci bisa akidar Ahlul Baiti (AS), 1426 AH/2005 AD.
  • Najafi, Muhammad Hassan, Jawaher al-Kalam, Mai bincike: Quchani, Abbas, Mawallafi: Beirut, Dar Ihya’ al-Turat al-Arabi, bugu na bakwai, 1362H.
  • Tabata’i Yazdi, Muhammad Kazem, Al-Urwa al-Wuthqa, Beirut, Al-Alami Publishing House, 1409 AH/1988 Miladiyya.
  • Farhange fiqhe Mutabiq mazhabar Ahlul-baiti alaihimus salam, ta yi bincike kuma ta hada da Mu'assasar Fikihu akan Mazhabar Annabi (saw); karkashin kulawar Mahmoud Hashemi Shahroudi, Qum, bugu na biyu 2003.