Gidan Sayyada Fatima (S)
Gidan Sayyada Fatima (S) (Larabci:دار السيدة فاطمة عليها السلام) gida ne da yake jikin masallacin Annabi wanda sayyada zahra da Imam Ali (A.S) suke rayuwa a cikinsa, Da yawa daga malaman shi'a suna ganin ƙabarin sayyada fatima yana cikin gidanta, falalar da wannan gida yake dashi ya samo asali ne daga inda Allah ya bada umarnin rufe kowwace ƙofar gida da take haɗe da Masallacin Annabi, banda ta gidan Sayyida fatima (as).
Yazo a hadisi daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa yin Salla a wannan gida yafi yin salla a filin masallacin annabi lada da daraja, an ruguje wannan gida a zamanin banu umayya wajan faɗaɗa masallacin annabi, an zagaye ɗakin da aka binne annabi a ciki da gini mai kyau.
Wasu suna ganin gidan Sayyida fatima (a.s) da aka kaiwa hari , a harin da aka raunata ta shine dai gidan Imam Ali (a.s) da ke unguwar Bani Hashim. Waɗannan masu binciken sun faɗi dalilai da hujjojin samuwar wannan gida a unguwar banu hashim da kuma yanda harin ya kasance.
Matsayin Gidan Sayyad Fatima
Gidan Sayyida Fatima (S) yana nufin gidan da take rayuwa acikinsa a garin Madina, wanda ya zo a cikin ruwayoyi na Shi'a da Ahlus-Ahlus-sunna da kuma na tarihi game da falalarta[1] da abin da ya faru na harin da aka kai mata[2] Har ila yau, wasu malaman Shi’a suna ganin shi ne in da aka binneta.[3]
Ya zo a cikin hadisin Shi'a da Ahlus-sunna cewa Annabi (S.A.W) ya gabatar da gidan Fatima da Ali (a.s) a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun misalan gidaje wanda ya zo a aya ta 36 a cikin suratun Nur:
A cikin gidajen da Allah ya yi musu izini a girmama kuma ɗaukaka ambaton sunansa . A cikin waɗannan gidaje anayi masa tas'bihi kowace safiya da maraice.[4]
Gidan sayyada Fatima shi ne mahaifar ƴaƴanta[5] kuma a bisa abin da yazo a ruwaya shi ne gunda aka haifi Imam Sajjad (a.s).[6] A ruwayar da ta zo a cikin littafin Alkafi, Imam Sadik (a.s) ya ce salla a gidan Fatima (a.s) tafi daraja fiye da yin salla a filin masallacin manzon Allah,[7] an ruwaito cewa Imam Jawad (a.s) ya kasance yana sallah a gidan sayyada Fatima (a.s) kullum.[8] garuruwan Iran, a zamanin Fatimiyya ana gine gine da kwafi na unguwar Bani Hashim da gidan Sayyida Fatima, kuma jama'a suna turuwa don ziyartar gurin kuma su yi kallo.[9]
Yunkuri Sauyawa Sayyada Fatima (S) Gida Bayan Aure
Ibn Sa'ad masanin tarihin ƙarni na 3 hijriyya, ya ruwaito daga Imam Baƙir (a.s) cewa Imam Ali (as) ya gina wani gida da ke da nisa kaɗan da gidan Manzon Allah bayan ya auri Fatima (as) Annabi ya ce musu yana son 'yarsa ta zauna kusa da gidansa. sai dai bai san yaya zaiyi ba tinda babu wani gida da yayai saura a kusa da nasa wanda ba mutane aciki , sai sayyada Fatima (a.s) ta nemi Annabi da ya yi magana da Haris bin Nu’uman domin su zauna a gidansa da yake jikin gidan Annabi[10]saboda abaya ya bada wasu gidajensa Dan Manzo Allah ya zauna da matansa a ciki[11] Sai Annabi yace ba zai iya tambayar sa ba saboda a baya ya bashi , sai labarin abunda yake faruwa ya kai ga haris, Saboda haka, sai ya bai wa Annabi gidan nasa, yace karɓar dukiyarsa da Annabi zaiyi yafi masa Alkhairi da yaƙi karɓa.[12]
A cewar wasu majiyoyin Shi'a, Manzon Allah ya buƙaci Imam Ali (a.s.) ya shirya musu gida da za su zauna shida matar sa bayan aure. sai imam Ali (a.s) ya ce babu wani gida kusa da gidan Annabi sai gidan Haris bin Nu’uman. Annabi ya ce Haris ya ba shi wasu daga cikin gidajensa, sai ya ji kunyar faɗa masa ya kuma bashi wani. Haris ya samii labarin hakan sai yazo wurin Annabi ya ba shi gidansa. Da haka Ali (a.s) da Fatima (a.s) suka tafi gidan Haritha.[13]
Gida Ɗaya Tilo Mai Ƙofa Cikin Masallaci
Gidan Sayyida Fatima yana gabas da masallacin Annabi (S.A.W) kuma a tsakiyar gidajen Manzon Allah (S.A.W.).[14]Wannan gidan yana da ƙofofi guda biyu: ɗaya kofar tana buɗewa daga cikin masallaci, ɗaya ƙofar ta wajen masallacin,[15] da umurnin Allah ya zo sai aka rufe dukkan ƙofofin masallacin Annabi (SAWW) sai wannan aka bari.[16] سَدُّالابواب wata falala ce ta Imam Ali (A.S) shi kadai[17]
Gidan Sayyida Fatima (a.s) yana bayan gidan Manzon Allah (s.a.w) (ɗakin A’isha)[18] A tsakanin waɗannan gidaje biyu akwai wata ƴar ƙaramar taga.[19] daga nan ne Manzon Allah ya ke tambayar `yarsa halin da take.[20] akwai wani dare da aka sami jayayya tsakanin Sayyida Fatima da Aisha matar Manzon Allah (s.a.w) sai hakan ya ɓata ran Fatima (A.S) sai Manzon Allah (saww) ya rufe bisa riƙon sayyada Fatima (S).[21]
Harin Da Aka Kai Gidan Sayyada Fatima (S)
- Asalin Maqala: Waƙi'ar kai Hari Gidan Fatima (S)
Kamar yadda majiyoyin Shi’a da Ahlus-sunna suka ruwaito, bayan wafatin Manzon Allah (S.A.W) da waƙi'ar Saƙifa, wasu daga cikin Sahabbai sun garzaya gidan don karɓar bai'ar dole daga Imam Ali (A.S) da wasu mutanen da suka ki yi wa Abubakar mubaya’a da nuna goyan baya wanda suka taru a gidan Imam[22] A cewar majiyoyin Shi'a, an ƙona ƙofar gidan a wannan harin da aka kai[23] kuma a sakamakon raunukan da sayyada fatima ta samu ne ya janyo zubewar cikin (Muhsin)[24] sannan sanadin ciwon ya zamanto ajalinta, ta yi shahada bayan wani lokaci[25].
Wanne Gida aka Kai Hari?
Wasu masu bincike na ganin cewa harin da aka kai gidan Fatima ba a wannan gidan da ke kusa da masallacin Annabi bane, gidan da aka kai wa hari yana da nisa da masallaci[26] Kamar yadda Muhammad Sadiƙ Najmi (ya rasu: 1390) a cikin littafin "Tarihin Hubbaran Imaman Baƙi'a" wasu rahotannin tarihi sun tabbatar da wannan hasashen. Daga cikin su akwai rahoton cewa lokacin da aka kai Ali (a.s) masallaci don yin mubaya’a ga Abubakar, mutane sun taru suna kallon abubuwan da suke faruwa a titunan Madina[27] Wannan rahoton yana cikin littafin Saƙifa da Fadak na Ahmad bin Abdulaziz Johri Basri (ya rasu 323 bayan hijira).[28] Kuma an ce wannan gida yana gabas da masallacin Annabi, a bayan Baki'a kusa da gidan Abu Ayyub Ansari, gidane mai ɗauke da rumbun ajiya, dakuna da dama da babbar kofar katako.[29]
Samhudi (ya rasu a shekara ta 911 bayan hijira), malamin Ahlus-Ahlus-sunna mai bincike kan tarihin garin madina, shi ma ya yi magana a kan gidan da ke kusa da maƙabartar Baki'a ,wanda yake na Imam Ali (a.s) ne,[30] cikin littafin Thabakat Kubra daga madogaran tarihi da aka rubuta a karni na uku an ambaci sunan gidan Fatima da cewa yana kusa da Baki'a[31] Wasu suna ganin wannan gida shi ne dai wanda haris bin Nu’man ya ba Fatima kyauta dan ta zauna a cikinsa.[32]
Sayyid Jafar Murtada Amili (ya rasu: 1441H), masanin tarihin Shi'a, yana ganin cewa an kai harin ne a gidan da aka ruwaito labarin sad Al-Ab'wab (batun rufe ƙofofin da suke ta masallacin Annabi da barin iya ta gidan sayyada fatima(S)[33]
ASALIN Maƙala:An Binne Sayyada Fatima A Gidanta?
A cewar Sayyid Jafar Murtada amili, masani a tarihin Musulunci da na Shi'a, (ya rasu: 1441), ba zai yiwu a iya tantance inda ƙabarin Sayyida Fatima yake ba.[34] Kamar yanda Isma'il Ansari Zanjani ya ruwaito a cikin littafin Al-Mausuatul-kubra an Fatimatul-Zahra, mafi yawan malaman Shi'a sun yi imani da cewa an binne Fatima a gidanta.[35] an ruwaito a cikin faɗin Imam Ali (a.s.) a lokacin jana’izar Fatima (a.s.) ya ce
wannan yana daɗa tabbatar da an binne Fatima (as) a gidanta.[36]
An Sayna Gaba ɗayan Gidanta Cikin Ginin ƙabarin Annabi (S.A.W)
An ruguje gidan Fatima a zamanin Abdulmalik bin Marwan (mulki: 65-86 AH).[37] ko Walid bin Abdulmalik (mulki: 86 AH-96 AH)[38] domin raya masallacin Annabi. An haɗe ɗakin ta dana annabi a guri ɗaya.[39]
Bayanin kula
- ↑ Misali, dubi Kulaini, al-Kafi, 1407, juzu'i na 4, shafi na 556.
- ↑ Masoudi, Isbatul wasiyya, 1384, juzu'i na 1, shafi na 146
- ↑ Misali, duba: Sheikh Sadouq, Man La Yahdara al-Faqih, 1413 AH, juzu'i na 2, shafi na 572.
- ↑ Siyuti, Durrul al-Manthor, Dar al-Fikr, juzu'i na 6, shafi na 203; Erbali, Kashf al-Ghumma, 1421 AH, juzu'i na 1, shafi na 313.
- ↑ طبسی، «گزارشی از خانه زهرا علیها السلام»، سایت حوزه.
- ↑ Tabari Amoli, Dalai al-Imamah, 1413 AH, shafi na 191.
- ↑ Kulaini, al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 4, shafi na 556.
- ↑ Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 1, shafi 493.
- ↑ «روایتی از «کوچههای مادری»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
- ↑ Ibn Saad, Tabaqat Al-Kubra, 1410, juzu'i na 8, shafi na 132.
- ↑ Ameli, Sahih Mn Sirah Imam Ali (A.S), 2009, juzu'i na 3, shafi na 132-133.
- ↑ Ibn Saad, Tabaqat al-Kubra, 1410, juzu'i na 8, shafi na 132.
- ↑ Tabarsi, Ilamul Al-Wora bi Alam Al-Huda, 1390 AH, shafi na 71; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 19, shafi na 113.
- ↑ طبسی، «گزارشی از خانه زهرا علیها السلام»، سایت حوزه.
- ↑ Qaidan, Darsenameh Amakin mazhabi Makkeh mukarrama wa Madina, 1390, shafi na 177.
- ↑ Ibn Kathir, al-Bidaiya wa al-Nihaya, 1407H, juzu'i na 7, shafi na 342.
- ↑ Hakim Neishaburi, al-Mustadrak Ali al-Sahihin, Beirut, juzu'i na 3, shafi na 125.
- ↑ Qaidan, Darsenameh Amakin mazhabi Makkeh mukarrama wa Madina, 1390, shafi na 177.
- ↑ Al-Sagheer, Tarihin Imam Ali (A.S) Siratuhu wa kiyadatuhu fil al-Manhaj al-Tahlili, 2002. Juzu'i na 1, shafi na 31.
- ↑ Samhoudi, Wafa al-Wafa bi Akhbar Dar Al-Mustafa, 2006, juzu'i na 2, shafi na 57.
- ↑ Sabri Basha, EMasu'atu Mir'ati Al-Haramaini al-Sharifaini wa Jazeera al-Arab, 2004, juzu'i na 3, shafi na 262.
- ↑ Tabari, Tarihin A'umam wa Al-Muluk, 1387 A.H., juzu’i na 3, shafi na 202.
- ↑ Salim bin Qays, Kitabu Salim bin Qays, 1420H, juzu’i na 1, shafi 150.
- ↑ Masoudi, Isbatul Wasiyya, 2004, shafi na 146.
- ↑ Tabari, Dalai al-Imamah, 1413H, shafi na 134.
- ↑ Mousavi, "Pasukh Shubuhate Tarikhi ateshe zadane Khuneh dar Ayineh Tarikhi wa riwayat farikaini ", shafi na 140-141.
- ↑ Najmi, Tarikhi Harame A'immeh wa asare digare dar madinaeh munawarra, 1386, shafi na 166-163.
- ↑ Johari Basri, Al-Saqifa wa Fadak, Tehran, shafi na 72.
- ↑ اللهاکبری، «خانه حضرت فاطمه(س) کجا بوده است؟»، شیعهنیوز
- ↑ Samhoudi, Wafa Al-Wafa, 2006, juzu'i na 2, shafi na 59.
- ↑ Ibn Saad, Tabaqat Al-Kubra, 1410H, juzu'i na 4, shafi na 40.
- ↑ Duba Qazvini, Fatima al-Zahra (a.s.) Man al-Mahd al-Lahad, 2006, juzu'i na 1, shafi na 157
- ↑ Ameli, Musibar Al-Zahra (AS), 1418 Hijira, Juzu'i na 1, shafi na 177.
- ↑ Ameli, Ma'asatu Al-Zahra (AS), 1418 Hijira, Juzu'i na 1, shafi na 252 da 253.
- ↑ Ansari Zanjani, Al-Masu'a al-Kubra Fatima al-Zahra, 1428 AH, juzu'i na 16, shafi na 113.
- ↑ Makarem Shirazi, Payam Imam Amirul Momineen, 2006, juzu'i na 8, shafi na 32.
- ↑ Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib, 1379 Hijira, Juzu'i na 2, shafi na 211.
- ↑ Samhoudi, Wafa al-Wafa bi Akhbar Dar Al-Mustafa, 2006, juzu'i na 2, shafi na 89.
- ↑ Jafarian, Asare Islami Makkeh wa Madina, 2007, shafi na 295.
Nassoshi
- Ibn Jozi, Abd al-Rahman bin Ali, al-Muntazem, bincike na Muhammad Abd al-Qader Atta, Mostafa Abd al-Qader Atta, Beirut, Dar al-Kutb al-Alamiya, bugu na farko, 1412H.
- Ibn Hajr Asqlani, Ahmad bin Ali, Al-Isaba fi Tamy'iz al-Sahaba, bincike na Adel Ahmad Abd al-Mojood, Ali Muhammad Moawad, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, bugu na farko, 1415H.
- Ibn Saad, Muhammad Ibn Saad, Tabaqat Al-Kubra, bincike na Muhammad Abd al-Qadir Atta, Beirut, Dar al-Kitab Al-Alamiya, bugu na farko, 1410 A.H.
- Ibnshahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, Qum, Allamah Publications, bugu na farko, 1379H.
- Ibn Kathir, Ismail bin Umar, al-Bidaiyah wa al-Nihayah, Beirut, Darul Fikr, 1407H.
- Erbali, Ali Ibn Isa, Kashf al-Ghumma fi Marafah al-Imam, Kum, Razi, 1421H.
- Al-Sagheer, Muhammad Hossein, Imam Ali (A.S) Siratuhu wa Kiyadatuhu fi Zau'i al-Manhaj al-Tahlili, Bija, Al-Arif Foundation, 2002.
- Ansari Zanjani Khoini, Ismail, Al-Mausu'a al-Kubra Fatima al-Zahra, amincin Allah ya tabbata a gare ta, Qum, Dilil Ma, 1428 AH/1386.
- Jafarian, Rasul, Asare Islami Makka wa Madina, Tehran, Mashaar, 2007.
- Johari Basri, Ahmad bin Abdul Aziz, Al-Saqifa waa Fadak, bincike da gyara daga Mohammad Hadi Amini, Tehran, Ninoy al-Haditha School, B.T.A.
- Hakim Neishaburi, Muhammad bin Abdullah, Al-Mustadrak Ali Al-Sahihin, Dar al-Marafa, Beirut, Bita.
- Salim bin Qays, littafin Salim bin Qays, Kum, Al-Hadi, 1420H.
- Samhoudi, Ali bin Abdullah, Wafaa al-Wafa bi Akhbar Daril al-Mustafa, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, 2006.
- Siyuti, Jalaluddin, Aldurrul al-Manthor, Beirut, Dar al-Fekr, Bita.
- Sabri Basha, Ayoub, Mausuatu Mirt'a Al-Haramain al-Sharifain wa Jazeera al-Arab, Majdeh Maarouf, Alkahira, Dar al-Afaq al-Arabiya, ya fassara, 2004.
- Tabarsi, Fazl bin Hasan, Ilamul Al-Wori Bi Alamul Al-Huda, Tehran, Darul Kitab al-Islamiya, bugu na uku, 1390H.
- Tabari Imami, Muhammad bin Jarir bin Rostam, Dalai al-Imamah, Qum, Ba'ath, 1413H.
- Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh al-Umama wa al-Muluk, Musa al-Alami, Beirut, 4th, 1403H.
- نجمی، محمدصادق، تاریخ حرم ائمه بقیع و آثار دیگر در مدینه منوره، تهران، نشر مشعر، ۱۳۸۶ش.
- اللهاکبری، «خانه حضرت فاطمه(س) کجا بوده است؟»، شیعهنیوز، تاریخ درج مطلب: ۱۳ دی ۱۴۰۰ش، تاریخ بازدید:۲۱ مرداد ۱۴۰۲ش.
- مکارم شیرازی، ناصر، پیام امام امیرالمومنین، تهران، دارالکتب الاسلامیه، ۱۳۸۶ش.
- موسوی، سید محمدتقی، «پاسخ به شبهات تاریخی آتش زدن خانه وحی در آیینهی تاریخ و روایات فریقین»، تاریخ اسلام در آیینه اندیشهها، سال دوازدهم، شماره۱۸، پاییز و زمستان ۱۳۹۹ش