Jump to content

Maƙam Ra'asil Husaini (Asƙalan)

Daga wikishia
Wannan wata ƙasida ce game da Kan Imam Husaini da yake garin Asƙalan. domin ƙarin bayani game da sauran wuraren ku duba Maƙam Ra'asil Husaini
Maƙam Ra'asil Husaini (Asƙalan)
Wanda ya kafaBadrul Jamal ko ɗansa mai suna Afzal Shahinsha, waziran Daulaf Faɗimiyyan
KafawaShekarar 484 bayan hijira
Mai amfaniMasallaci. Wurin Ziyara
WuriGarin Asƙalan da yake Falasɗinu
Sauran sunayeMashad Ra'as Asƙala, Masallacin Mashad Husaini (A.S)
Al'amuran da suka shafiWaƙi'ar Karbala, yaƙe-yaƙen Salibiyun
Sabunta giniA cikin shekarun 1990 miladiya


Maƙam ra'asil Husaini (Larabci: (عسقلان) مقام رأس الحسين) Wuri ne da aka jingina cewa a wannan wuri ne aka binne kan Imam Husaini (A.S). Wuri ne da mutane suke ziyarta a Asƙalan cikin ƙasar Falasɗinu, wasu musulmi sun yi imanin cewa sojojin Yazid bayan sun kewaya da kan Imam Husaini (A.S) a garuruwa daban-daban a Sham sun binne shi a wani guri a Asƙalan, daga baya a lokacin gwamnatin Faɗimiyya a Masar aka ɗauki kan Imam Husaini zuwa Masar kuma aka gina maƙami a gurin da aka ajiye kan.

Malaman Shi'a da wasu daga cikin malaman Ahlus-Sunna da wasu daga cikin masu bincike na yammacin duniya sun yi imani cewa kan Imam Husaini (A.S) ba'a binne ba a wannan guri mai suna Asƙalan, amma duk da haka kasantuwar wannan gurin musulmi suna girmamashi, sai aka gina shi a shekara ta 484 hijira ta hannun gwamnatin Faɗimiyya, bayan haka duk da cewa wannan guri na Asƙalan ya faɗa hannun Kiristoci a lokacin yaƙoƙi da aka yi da Kiristoci a loƙuta daban-daban, amma duk da haka wannan guri ba a ruguje gabaɗayansa ba sai a ƙarni na 20 haramtacciyar gwamnatin Isra'ila ta rushe wannan guri a shekara ta 1950, amma daga baya ƴanshi'ar Indiya suka sake gina wannan guri, kuma wannan guri yana karɓar masu ziyara daga ƙasar Indiya da Pakistan duk shekara.


Bayani Kan Wannan Wuri

Bisa abin da malaman tarihi suka faɗa wannan guri na kan Imam Husaini (A.S) ana girmama shi tin daga ƙarni na 5, kuma ya zama ɗaya daga cikin wuraren ziyarar shi'a da Ahlus-sunna, wasu masu bincike suna la'akari da wannan guri a matsayin mafi muhimmanci gurin ziyara na ƴanshi'a a ƙasar Falasɗinu,[1] wannan guri ana kiran shi da Masallacin Mashahad Imam Husaini (A.S)[2] duk da shakku kan samuwar kan Imam Husaini (A.S) a wannan guri ko binne shi a cikinshi duk haka musulmi suna ziyartar wannan guri kuma suna ba da bakancensu[3] a wannana guri. Har ila yau mutane daga garuruwa daban-daban suna ziyartar wannan guri.[4]

Shin An Binne Kan Imam Husaini (A.S) A Asƙalan?

Masu bincike kuma ƴanshi'a suna ganin yiwuwar samun kan da aka binnne a Asƙalan, amma bubu wani dalili da yake nuna cewa wannan kai kan Imam Husaini (A.S) ne,[5] Malaman Shi'a suna ganin cewa kan Imam Husaini (A.S) kwatakwata ba a binne shi ba a Asƙalan,[6] abin da yake akwai shi ne bayan sojojin Yazid sun kewaya da shi a garin Kufa da Sham, to an mayar da shi zuwa Karbala kuma an tare da gangar jikin Imam Husaini (A.S),[7] kamar yadda Ibn Taimiyya ɗaya daga cikin malaman Ahlus-Sunna ya kore cewa an binne kan Imam Husaini (A.S) a wannan guri, ya ce babu wani littafin na tarihi ingantacce da yake tabbatar da wannan Magana.[8] Bisa ra'ayin wasu malaman yammacin duniya sun tafi kan cewa an gina wannan gurin ziyara ne a Tsauni da yake sananne kafin Muslunci da cewa wannan wani guri ne da mutum biyu Kiristoci suka yi shahada a cikinshi waɗanda aka fille musu kai, wasu sun yi tinanin cewa wannan wani guri ne mai tsarki na ziyara gurin Kiristoci, amma aka yi ƙoƙarin mayar da shi na Musulmi.[9] Sai dai cewa kuma wasu masu bincike sun gamsu da cewa bayan sojojin Umar Bin Sa'ad sun gama zagayawa da kan Imam Husaini (A.S) a garuruwa daban-daban a cikin Sham, to a ƙarshe sai suka binne shi a wannna guri na Asƙalan.[10] Wasu sun yi imani cewa Yazid ya bada umarni da gangan da a binne kan Imam Husaini (A.S) a wannan guri saboda ƙarancin ƴanshi'a a can.[11] Amma bisa wata ruwaya ya zo cewa mutanan Asƙalan da kansu suka nemi Yazid cewa a binne kan imam Husaini (A.S) a gurinsu, su kuma daga bayan suka yi gini a gurin.[12]

Gina Wannan Gurin Ziyarar Kan imam Husaini

Ya zo cikin wata ruwaya cewa wani mutum a lokacin Daular Faɗimiyya a Masar a shekara ta 420-487 ya yi mafarki cewa kan Imam Husaini (A.S) yana Asƙalan,[13] sai Badar-din Jamal ya bada umarni a gina wannan wuri, Badru wanda ya kasance waziri a gwamnatin Muntasar ya kasance Kirista, ya rasu a shekara ta 487hijira,[14] ko kuma ya umarci ɗanshi mai suna Afdal Shahinsha (459-515)[15] da ya gina ƙubba (hubbare) a wannan guri, bisa zanan da aka samu a jikin Minbarin masallacin da yake gurin wanda daga baya aka mayar da shi zuwa masallacin garin Khalil wanda shi ma yake cikin Falasɗinu, tarihin gina wannan guri na kan Imam Husaini (A.S) an ginashi ne a shekara ta 484 hijira, ƙari kan haka akwai zanen dutse guda biyar da aka samu cikin masallacin wanda yake tabbatar da wannan tarihi na gina sh,[16] A cikin littafin Asarul Buldan Abu Abdullah Alƙaziwini ya ambaci cewa akwai gurin da aka binne kan imam Husaini (A.S) a garin Asƙalan kuma guri ne mai girma.[17] A wata tafiya da ibni Baɗuɗa ya yi a shekara ta 703-770 ya yi nuni da wannan guri cewa masallaci ne babba kuma mai kyau.[18] Cikin hadisai an ambaci cewa a gurin da aka binne kan imam Husaini (A.S) an gina wasu tiraku masu girma waɗanda aka lulluɓe da wani koran ƙyalle kuma saka ɗora rawani kore kanshi.[19]

Wurin Ziyara Na Asƙalan Bayan Ɗauke Kan Imam Husaini

Masu bincike basu da shakka kan samuwar Kani a Asƙalan wanda daga baya aka canza mishi guri zuwa Alƙahira a Masar[20] A shekara ta 545 hijira a lokacin yaƙin da kirista suka yi suka mamaye wannan guri na Asƙalan,[21] Ɗala'ilu Bin Zuraiki sabon shugaban ƙasar Masar na wancan lokacin ya sami izinin yin amfani da wani kuɗi masu yawa[22] domin mayar da wannan kai da ake jinginawa Imam Husaini (A.S) daga Asƙalan zuwa Al-ƙahira[23] A ƙasar Masar bayan wannan lokaci ne sai garin Asƙalan ya canza zuwa garin Musulmi da Kirista, ana haka har takai ga garin ya zama garin Musulmi a shekara ta 645 hijira,[24] Kuma duk da cewa Kiristoci sun rushe wannan gari na Asƙalan da gina-ginanshi, amma ginin gurin kan Imam Husaini (A.S) yana nan lafiya ƙalau,[25] Litattafan tarihi sun nuna cewa a dukkanin zamanin da ya biyo bayan wannan gini ya kasance abin girmamawa a gun Musulmi na wannan yanki.[26]

Rushe Wannan Gini Da Sake Gina Shi A Ƙarni Na 20

Bisa abin da malaman tarihi suka faɗa, a ƙarshan ƙarni na 19 aka sake gina wannan guri a ƙarin Asƙalan, amma a shekara ta 1950 sojojin haramtacciyar ƙasar Isra'ila sun rushe wannan gini da umarnin Mushe Dayan 1915-1981..[27]Amma bisa abin da jaridar Los Angeles Times ta rawaito a shekara ta 1900 ne ƴanshi'a na ƙasar Indiya suka sake gina amma ƙarami a wannan guri, wanda yanzu huri ne da yake cikin asibitin Asƙalan. Kuma ana cewa wannan gina an yi shi ne bisa buƙatar mai wa'azi Muhammada Burhanud Din a shekara ta 1915-2014,.[28] wanda shi kuma shi ne Imami na 52 na ƴanshi'a Isma'iliyya.[29] Bisa wani rahoto wannan guri yana samun masu ziyara da yawa daga ƙasar Indiya da Fakistan a ko wace shekara.[30]

Ku Duba Masu Alaƙa

Bayanin Kula

  1. Petersen, Bones of Contention: Muslim Shrines in Palestine, p108-110.
  2. «مقام رأس‌الحسین في الأراضي المحتلة»،Shafin yanar gizo na Noor.
  3. Qazwini, Asarul Bilad Wa Akhbarul Ibad, bugu 1998 m, shafi na 222
  4. Petersen, Bones of Contention: Muslim Shrines in Palestine, p109.
  5. Rukunin marubuta, Tarihin Imam Husaini, 1378-1390H, Vol. 5, ku. 553, Littafin Mujallar Larabci ta Iraki [Anastas Al-Karmali] shafi na 557-558.
  6. Baydoun, Mausu'atu Karbala, Al-A’lami Foundation, Vol. 2, ku. 542; Rukunin marubuta, Tarihin Imam Husaini, 1378-1390H, Mujalladi. 5, ku. 553.
  7. Rukunin marubuta, Tarikhu Imam Husaini, 1378-1390H, Mujalladi. 5, ku. 546; Rukunin marubuta, Tarikh Kiyame wa Maqtale Jami'i Sayyid al-Shuhada, 1395H, Vol. 2, shafi na 574 da 587; Al-Fattal al-Nishapuri, Rawdat al-Wa’izin, al-Radi Publications, p. 192; Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, Vol. 45, ku. 145.
  8. Ibn Taimiyyah, Ra'asul Al-Hussein, 1368H, shafi na 8
  9. Petersen, Bones of Contention: Muslim Shrines in Palestine, p109.
  10. Raw material “Ras al-Husayn”, shafi. 188; Rukunin marubuta, Tarikh Imam Husaini, 1378-1390H, Mujalladi. 5, ku. 526.
  11. Rukunin marubuta, Tarikh Imam Husaini, 1378-1390, mujalladi. 5, ku. 518.
  12. Rukunin marubuta, Tarikh Imam Husaini, 1378-1390, mujalladi. 5, ku. 516.
  13. Rukunin marubuta, Tarikh Imam Husaini, 1378-1390, mujalladi. 5, ku. 518.
  14. Khameh Yar, “Ra'asul Hussein,” p. 188.
  15. Rukunin marubuta, Ahlul-Baiti Fi Masar, 1427H, shafi. 77.
  16. Petersen, Bones of Contention: Muslim Shrines in Palestine, p109.
  17. Al-Qazwini, Asarul Bilad Wa Alkhbarul Ibadi, 1998 Miladiyya, shafi na. 222.
  18. Ibn Battuta, TaRehlatu Ibn Battuta, 1417 AD, Vol. 1, p. 252.
  19. Petersen, Bones of Contention: Muslim Shrines in Palestine, p110.
  20. Rukunin marubuta, Tarikh Imam Husaini, 1378-1390, mujalladi. 5, ku. 553
  21. Ibn Taghri Bardi, Annujum Zahira, 1392 AH, Vol. 5, ku. 299.
  22. Rukunin marubuta, Tarikh Imam Husaini, 1378-1390, mujalladi. 5, ku. 562
  23. Rukunin marubuta, Tarikh Imam Husaini, 1378-1390, mujalladi. 5, ku. 516
  24. Abu al-Fida, Tarikh Abul al-Fida, 1417 AH, Vol. 2, ku. 282.
  25. Petersen, Bones of Contention: Muslim Shrines in Palestine, p109.
  26. Petersen, Bones of Contention: Muslim Shrines in Palestine, p110.
  27. Petersen, Bones of Contention: Muslim Shrines in Palestine, p110؛ Rapoport, «History Erased», Haaretz.
  28. SobelmaN, «Sacred surprise behind Israeli hospital», los angeles time.
  29. «مقام رأس‌ الحسين في الأراضي المحتلة»، موقع نورنیوز.
  30. SobelmaN, «Sacred surprise behind Israeli hospital», los angeles time؛ Rapoport, «History Erased», Haaretz.

Nassoshi

  • Ibn Battuta, Muhammad bn Abdullah, Rehlatu Ibn Battuta, Marrakesh, Kwalejin Daular Maroko, 1417 miladiyya.
  • Ibn Battuta, Rehlatu Ibn Battuta, Muhammad Ali Muwahhid ya fassara, Agah Publications, 1370H.
  • Ibn Taghribirdi, Yusuf, Annajumuuz Zahira fi Muluk Masar Wal Alkahira, Ma'aikatar Al'adu da Jagorancin Kasa. Ƙungiyar Masarawa ta Masar, 1392 AH / 1972 AD.
  • Ibn Taimiyyah, Ahmad bn Abdil-Halim, Ras al-Husayn, Jaridar Sunnah al-Muhammadiyah, 1368H/1949 Miladiyya.
  • Abu al-Fida, Ismail bin Ali, Tarikh Abu al-Fida (Takaitaccen Tarihin Dan Adam), Beirut, Darul Kutub al-Ilmiyyah, 1417 AH/1997 Miladiyya.
  • Ibn Shahr Ashub, Muhammad bn Ali, Al-Manaqib, editan Muhammad Hussein Ashtiani, Kum, Allamah, (n.d.).
  • Baydoun, Labib, Mausu'atu Karbala, Beirut, Al-Aalami Foundation for Publications, 1427 AH/2006 AD.
  • Khameyar, Ahmad, “Ra'asul Husaini,” Encyclopedia of the Islamic World, Tehran, Islamic Encyclopedia, 1393 AH.
  • Al-Fattal Al-Nishapuri, Muhammad bin Ahmad, Rawdat Al-Wa’izin, Kum, Al-Radi Publications, (n.d.).
  • Al-Qazwini, Zakariyya bin Muhammad, Asarul Bilad Wa Alkhbarul Ibad, Beirut, Dar Sadir, 1998 Miladiyya.
  • Kungiyar mawallafa, Ahlul-baiti Fi Masar, Tehran, Majalisar Kiyaye Mazhabobin Musulunci, 1427H.
  • Kungiyar marubuta, Tarihin Imam Husaini Samfuri:Abridged/PBUH, Tehran, Kungiyar Bincike da Tsare-tsare ta Ilimi. Hotunan Ofishin Taimakon Ilimi, 1378-1390 AH.
  • Rukunin marubuta, Tarikhu Kiyame Wa Maqtale Jami'i Sayyid al-Shuhada, Qum, Wallafa na Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini, 1395H.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya’ al-Turath al-Arabi, 1403H.
  • Al-Karmeli, Anastas, Littafin Mujallar Larabci ta Iraki, shafi na 557-558.
  • Petersen, Andrew, Bones of Contention: Muslim Shrines in Palestine, Springer, Singapore, 2017.
  • Sobelman, Batsheva, «Sacred surprise behind Israeli hospital», los angeles time. Ranar saka bayanin: 21 Maris 2008, Ranar dubawa: 4 Janairu 2024
  • «History Erased», Haaretz. 5 Yuli 2007, sannan an sake dubawa ko karanta shi a ranar 5 Janairu 2024. Bisa ga bayanan da ke cikin shafin da kake dubawa, wannan yana iya danganta da Makam Imam Husain (A.S.) a birnin Asqalan.
  • "Makam Ra'as al-Hussein Fi Arazi Muhtalla," gidan yanar gizon Noor News, ranar buga buƙatun: Maris 21, 2008, ranar kallo: Janairu 4, 2024.