Muhammad Difi
| Cikakken Suna | Muhammad Diyab Ibrahim Almisri |
|---|---|
| Sunan aro | Jikan mutuwa |
| Mazhaba | Ahlus-Sunna |
| Ranar haihuwa | 1965m |
| Wurin haihuwa | Sansanin ƴan gudun hijira na Khan Yunus Gaza |
| Shahada | 13 Yuli 2024 miladiyya |
| Mahallin karatu | Mayayyar Falasɗinu |
Muhammad Diyab Ibrahim Almisri, (Larabci: محمد دياب إبراهيم المصري) wanda ya rayu tsakanin shekaru 1965-2024m, wanda aka fi sani da Muhammad Difi, kwamandan dakarun Izzud-dini ƙassam, sashen soja na harkatu Hamas. Ya kasance mai tsara ofireshin ofireshin na soja da ramukan da Hamas take amfani da su a yaƙi da gwamnatin Sahayoniya.
Muhammad Difi shi ne ya shirya da tsara oforeshin ɗin Tufanul Al-aksa. A ranar 13 Yuli 2024m ne Isra'ila ta kai hari kansa a Zirin Gaza tare da hallaka shi.
Tasiri A Gafen Gwagwarmaya
Muhammad Difi, wanda ake yi wa laƙabi da Abu Khalid, ya kasance ɗaya daga cikin kwamandojin soja na Hamas, ya taka babbar rawa cikin shirya kai hari da zartar da shi a tarihin wannan ƙungiya.[1] Shi ne asalin wanda ya tsara ofireshin ɗin Tufanul Al-Aksa.[2] wanda cikin ƙaddamar da shi aka samu nasarar cafke adadi mai yawa na Isra'ailawa tare da hankaɗo ƙeyarsu zuwa Gaza.[3]
Difi ta hanyar amfani da sabbin dabarun yaƙi, daga jumlarsu samar da hanyoyin ramuƙan ƙarƙashin ƙasa da kuma faɗaɗa ƙarfin makaman rokoki na Izzud-dini Ƙassam, ya sauya zuwa wani samfuri na gwagwarmayar Falasɗinu gaban Isra'ila.[4]
A karon farko a shekarar 1994m, Muhammad Difi ya fara bayyanar da kansa gaban idanun duniya da kyamarorin kafofin watsa labarai ya sanar da labarin kame sojan Isra'ila tare kuma da neman Isra'ila ta saki Ahmad Yasin wanda ya kafa ƙungiyar Hamas. Wannan lamari an yi la'akari da shi a matsayin wani lamari mai motsa zukata da ya faru a tarihin ƙungiyar Hamas da gwagwarmayar Falasɗinawa.[5]
Tarihin Rayuwa
Muhammad Diyab Ibrahim Almisri, wanda ya fi shahara da Muhammad Difi, an haife shi a shekarar 1965m a cikin sansanin ƴan gudun hijira mai suna Khan Yunus a Zirin Gaza.[6]A shekarar 1989m ne sojojin Isra'ila suka cafke shi, bisa tuhumarsa da aiki tare sashen soja na ƙungiyar Hamas, aka ɗaure shi wata goma sha shida a kurkuku. Bayan sakinsa tare da abokansa ne ya kafa dakarun Izzud-dini Ƙassam, sashen soja na Hamas, kafin kashe Salahu Shahad a shekarar 2002m, Difi ya samar da reshen Ƙassam a gaɓar kogin jodan, bayan shahadar Shahad, an naɗa shi matsayin kwamanda na asali a cikin wannan dakaru.[7] Muhammad Difi ya kasance ɗaya daga makusantan Yahaya Ayyash, ɗaya daga cikin wanda suka kafa Hamas, kuma wanda ya taka babbar rawa cikin tsara ofireshin ofireshin da zartar da shi kan gwamnatin Sahayoniyya.[8]
Kisan Gilla
Hukumar leƙen asiri ta gwamnatin Sahayoniyya (Shabak) ta yi yunƙuri daban-daban a lokuta da daman gaske kan ganin ta kashe Muhammad Difi; amma sakamakon gogewa da kwarewarsa cikin tsallake rijiya da baya da kuɓuta daga yunƙurin hallaka rayuwarsa da ɓoye kansa, wannan yunƙuri na su bai yi nasara ba, a ba'arin rahotanni an masa laƙabi da jikan mutuwa.[9]
A shekarar 2006m, cikin wani hari na sama da aka kai kan Zirin Gaza, an jikkata Difi amma tare da haka ya kuɓuta da ransa, bayan wannan hari ne, Muhammad Difi ya koma rayuwa a ɓoye. A ranar 13 Yuli 2024m gwamnatin Sahayoniyya cikin wani ofireshin na musamman da ta shirya ta ƙaddamar da harin makamin mai linzami a kansa tare da shahadantar da shi.[10] Isra'ila a ranar 1 Oktoba 2024m, a hukumance bayan wucewar sati uku da ruwan bama-bamai a kan sansanin ƴan gudun hijira na Khan Yunus ne ta sanar hallaka Muhammad Difi, Kakakin Hamas shi ma a nasu ɓangaren a ranar 30 Janairu 2024m ya tabbatar da shahadar Muhammad Difi.[11]
[[Dakarun Kare Juyin juya halin Muslunci|Dakarun kare juyin juya halin Muslunci na Iran[12] Hizbullahi Lubnan,[13] Ansarullahi Yaman,[14] Ƙungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinu, misalin Hamas da [[Ƙungiyar Jihadul-Islam|Jihadul Islami[15] sun aika da ta'aziyya kan shahadar Muhammad Difi. Mutanen a garuruwan Falasɗinu, Turkiyya, Labanun[16] da Yaman[17] sun yi wa Muhammad Difi salatul ga'ib.
Ku Duba
Bayanin Kula
- ↑ «محمد الضیف مهندس نبرد طوفان الاقصی کیست؟»، Gidan yanar gizon tashar Al-Alam
- ↑ ««محمد الضیف» که امروز شهادتش تأیید شد، که بود؟»، Kamfanin labarai na Tabnak.
- ↑ «لحظه به لحظه با عملیات توفان الاقصیٰ»،Gidan yanar gizon tashar Al-Alam
- ↑ ««محمد الضیف» که امروز شهادتش تأیید شد، که بود؟»Kamfanin labarai na Tabnak.
- ↑ ««محمد الضیف» که امروز شهادتش تأیید شد، که بود؟»،Kamfanin labarai na Tabnak..
- ↑ ««محمد الضیف» که امروز شهادتش تأیید شد، که بود؟»، Kamfanin labarai na Tabnak.
- ↑ «محمد الضیف مهندس نبرد طوفان الاقصی کیست؟»Gidan yanar gizon tashar Al-Alam
- ↑ ««محمد الضیف» که امروز شهادتش تأیید شد، که بود؟»، Kamfanin labarai na Tabnak.
- ↑ «رجل الظل و ابن الموت.. تعرف محمد الضیف قائد ارکان کتائب القسام»، Gidan yanar gizon tashar labarai ta TRT.
- ↑ ««محمد الضیف» که امروز شهادتش تأیید شد، که بود؟»، Kamfanin labarai na Tabnak.
- ↑ «محمد الضیف که بود+فیلم»،Kamfanin labarai na Mehr
- ↑ «بیانیه سپاه در پی به شهادت رساندن محمد الضیف»،Kamfanin labarai na Jahan News.
- ↑ «حزبالله شهادت محمد الضیف و همرزمانش را تسلیت گفت»،Kamfanin labarai na Al-Mizan.
- ↑ «انصار الله یمن: محمد الضیف در دفاع از شرف امت به شهادت رسید»،Tashar talabijin ta Al-Alam.
- ↑ «واکنش گروههای فلسطینی به شهادت محمد ضیف»، Kamfanin labarai na ISNA.
- ↑ «اقامه نماز میت غیابی برای شهید محمد ضیف در شهرهای فلسطین و منطقه»،Kamfanin labarai na Mehr
- ↑ «اقامه نماز برای شهید محمد ضیف در یمن»، Kamfanin labarai na ISNA
Nassoshi
- «رجل الظل و ابن الموت.. تعرف محمد الضیف قائد ارکان کتائب القسام»،Gidan yanar gizon tashar labarai ta TRT, ranar wallafa labarin: 12 ga watan Bahman shekarar 1403 ta Solar Hijri, ranar ziyara: 13 ga Bahman 1403 SH."
- ««محمد الضیف» مهندس نبرد طوفان الاقصی کیست؟»Kamfanin labarai na Al-Alam, ranar wallafa labarin: 11 ga Bahman shekarar 1403 ta Solar Hijri, ranar ziyara: 12 ga Bahman 1403 SH.
- «لحظه به لحظه با عملیات توفان الاقصیٰ»Tashar talabijin ta Al-Alam, ranar wallafa labarin: 15 ga watan Mehr shekarar 1402 ta Solar Hijri, ranar ziyara: 24 ga Mehr 1402 SH.
- ««محمد الضیف» که امروز شهادتش تأیید شد، که بود؟»،Kamfanin labarai na Tabnak, ranar wallafa labarin: 11 ga Bahman shekarar 1403 ta Solar Hijri, ranar ziyara: 12 ga Bahman 1403 SH.