Isra'ila
- Wannan wata ƙasida tana da ƙasida Falasɗinu. da Mamaye Falasɗinu.
| |||
| Babban birni | Urshalim (Ƙudus da aka mamaye)/Tel Aviv | ||
|---|---|---|---|
| Harshen hukuma | Ibraniyanci | ||
| Adadin mutane | 9,824,000 a ƙididdigar shekarar 2024 miladiyya[1] | ||
| Kashi daga cikin yawan al'ummar ƙasa | musulmi sun kai1,728,0000 ƙididdigar shekarar 2022 m,/akwai ƴanshi'a 6000-10000 | ||
| Kashi daga cikin yawan musulmi | kaso 18% musulmi ne a ƙididdigar shekarar 2022 miliadiyya | ||
| Muhimman abubuwa da suka faru a tarihi | Mamaye Falasɗinu a shekarar 1948 miladiyya | ||
| Wuraren ziyara | Maƙam Ra'asil Husaini (Asƙalan) | ||
Isra'ila ko kuma tsarin sahayoniyanci da ya kasance kan asasin tunanin sahayoniyanci, a shekara ta 1948 tare da mamayar garuruwan ƙasar Falasɗinu sun shelantawa duniya samuwarsu, musulmi suna ɗaukar Isra'ila matsayin ƙagagaggiyar hukuma kuma maƙiya na asali ga muslunci, maraji'an taƙlidi na shi'a sun haramta duk wata irin alaƙa da mu'amala tare da Isra'ila, kuma sun buƙaci korar Isra'ila daga garuruwan musulmai.
Ba'arin cibiyoyi da wuraren ziyara na shi'a da suke cikin Isra'ila sune: muƙamu ra'asil Husaini a Asƙalan, muƙam Imam Ali (A.S) a hanyar Ƙudus zuwa Yafa, wurin ziyara da ake danganta shi da Faɗima Ƴar Imam Husaini (A.S) da wani wurin ziyarar daban da ake danganta shi ga Sukaina Ƴar Imam Husaini (A.S).
An ce a cikin ba'arin jami'o'in ilimi na Isra'ila, akwai sashen muɗala'a da zurafa nazarin muslunci da kuma nazarin shi'anci, jami'ar Urshalim, Haifa, Tel Abib da Bar'ila sune muhimman cibiyoyin bincike da nazarin muslunci a cikin Isra'ila. da yawa daga ƙasashen musulmi misalin Indunusiya, Fakistan, Siriya, Iraƙ, Saudi Arabiyya, Yaman da Iran ba su yarda da halascin samuwar hukumar Isra'ila ba, kuma ba sa yin alaƙoƙi da hulɗar siyasa da kasuwanci tare da ita. Kafa haramtacciyar ƙasar Isra'ila ya haifar da saƙonni daga kisa da korar Falasɗinawa daga garuruwansu, da kuma samuwar gwagwarmayar kwato ƴanci da miƙewar al'ummar Falasɗinu da kewayenta dama al'ummun duniya cikin nuna rashin amincewa da mamayar da Isra'ila take yi kan garuruwan Falasɗinawa, kan asasin rahotanni har zuwa shekarar 2023 miladiyya ƙasa da kashi sha biyar cikin ɗari ne kaɗai ya ragewa Falasɗinawa wanda ya haɗa da zirin gaza da wasu ɓangarori daga gaɓar kogin Jodan.
Ƴansahayoniya domin kafa Isra'ila cikin garuruwan Falasɗinawa, sun kawo dalilai da uzurori: Daga jumlarsu akwai da'awar da suke yi cewa Yahudawa zaɓaɓɓun mutane ne a gurin Allah, kuma mamaye Falasɗinu alƙawari ne da Allah ya yi musu, da wannan dalili ne korar Falasɗinawa daga garuruwansu haƙƙi ne na Yahudawa da ƴansahayoniya, kisan ƙare dangi na Holokos (Holocust) da kuma da taken "Ƙasar da ba ta da mutane da mutanen da ba su da ƙasa" suna cikin uzorori da suka kawo kan kwace garuruwan Falasɗinawa.

Rashin Amincewar Shi'a Kan Kafa Isra'ila
Malaman shi'a ba su taɓa amincewa da kafa Isra'ila ba, kodayaushe sun kasance suna Allah wadai da zaluncin da sahayoniyawa suke aikatawa kan Falasɗinawa. A mahangar wasu adadi daga maraji'an taƙlidi, misalin Sayyid Muahammad Hadi Milani,[2] Imam Khomaini,[3] da Muhammad Fadil Lankarani,[4] sun haramta duk wata mu'amala da Isra'ila da amfani da kayayyakin da take san'antawa, wasu jama'a daga malamai misalin Sayyid Muhsin Ɗabaɗaba'i Hakim, Sayyid Abul Ƙasim Khuyi, Ayatullahi Burujardi, Sayyid Abdul-Husaini Sharafud-dini da Sayyid Abul Ƙasim Kashani,[5] da Imam Khomaini[6] cikin Allah wadai da ta'addanci Isra'ila sun buƙaci korar wannan haramtacciyar hukuma daga garuruwan Falasɗinawa, Abdul-Karim Zanjani, daga malaman fiƙihu na shi'a a ƙarni na sha huɗu bayan hijira, bayan shelanta kafa haramtacciyar hukumar Isra'ila da yaƙin da Isra'ila ta yi da ƙasashen Larabawa a shekara 1948 miladi, ya fitar da fatawar jihadi kan Isra'ila.[7]
Imam Khomaini ya bayyana Isra'ila a matsayin maƙiyar muslunci, kur'ani da Annabi (S.A.W) na asali da basu bar duk wani ƙazanta ba cikin kwace ƙasashen musulmai[8] A ra'ayin Murtada Muɗahhari, Isra'ila ce mafi tsanani da hatsari cikin maƙiyan muslunci.[9]
Imam khomaini:
Ina ganin goyon bayan shirin 'yancin kai na Isra'ila da kuma amincewa da ita a matsayin wani bala'i ga musulmi da fashewa ga gwamnatocin Musulunci, kuma ina kallon adawa da shi a matsayin wani babbar farilla a musulunci.
Imam Musa Sadar yana kallon haramtacciyar gwamnatin Isra'ila cikakkiyar alama da mulkin mallaka, zalunci, mamaya da rashin kunya.[11] Ayatullahi Khamna'i shima ya bayyana gwamnatin Isra'ila matsayin gwamnatin kwance, lefi,،[12] ƙarya[13] kashe ƙananan yara.[14] Ƙagaggiyar hukuma ta ƙarya,[15] Mafi ƙazantar maƙiyan muslunci da mutuntaka.[16]
Alaƙar Ƙasashen Musulmai Tare da Isra'ila
Dangantakar da ke tsakanin kasashen musulmi da Isra'ila ta samu koma baya. ƙasashe da dama na Musulunci kamar Indunusiya, Fakistan, Siriya, Iraƙ, Afganistan, Aljeriya, Bangaladash, Kuwait, Labanun, Libya, Malaisiya, Oman, Qatar, Somaliya, Saudi Arabiyya, Tunisiya, Yaman da Iran (Bayan juyin juya halin Musulunci), basu yarda halascin gwamnatin Sahayoniya ba.[17]
Amma tare da haka ba'arin wasu matattun shugabannin ƙasashen muslunci sun daidaita alaƙarsu da Isra'ila, daga jumlarsu akwai: Misra, Jodan, Bahrain, Imarat, Sudan, da Maroko.[18] Ƙasar Turkiyya ita ce ƙasar musulmi ta farko da ta fara daidaita ƙulla alaƙa tare da Isra'ila a watan maris shekarar 1949 miladiya, ƙasar Turkiyya ta amince da halascin samauwar Isra'ila, a shekarar 1952 suka ƙulla alaƙoƙin diplomasiyya tsakanin juna.[19]
A watan isfandi shekara ta 1328, hijira shamsi, daidai da watan maris shekarar 1950 miladi, ƙasar Iran ta bayyana amincewa da halascin gwamnatin Isra'ila tare da ƙulla dangantakar siyasa.[20] Bayan shekara biyu daidai fara aikin muhammad musaddaƙ ƙasar Irana hukumance ta shelanta yanke hulɗa da Isra'ila.[21] a lokacin mulkin rida shah pahlawi, ya ƙara dawo da hulɗa da Isra'ila, a watan shahriwar shekara ta 1346, hijra shamsi, Isra'ila a hukumance ta buɗe ofishin jakadanci a iran, wannan ofishin jakadanci ya cigaba da aiki har zuwa lokacin nasarar juyin juya halin muslunci,[22] bayan nan Irana ranar 22 ga watan bahman shakarar 1357,hijra shamsi, ta sake yanke hulɗa tare da Isra'ila, sannan aka mayar da ofishin jakadancin Isra'ila zuwa ofishin jakadancin Falasɗinu.[23]
Cibiyoyin Muɗala'a Da Nazarin Muslunci Da Shi'anci A Isra'ila
Shi'anci da Iransuna cikin batutuwa da ake zurfafa bincike kansu a jami'o'in Isra'ila.[24] cikin littafin "Islam pajuhi dar isra'il" An bayyana cewa, Isra'ila ta sadaukar da dimbin ayyukanta na bincike ga musulunci da kungiyoyin musulunci da musulmi da kuma al'ummomin musulunci ta hanyar haɗa cibiyoyin kimiyya da dama da fitattun mutane a duniya.[25]
Kan asasin rahotan da ya zo cikin littafin shi'eh pajuhi wa shi'eh pajuhane ingilis zaban, an bayyana cewa jami'ar urshalim ibari ɗaya ce daga mafi muhimmancin jami'o'in Isra'ila da take a baitul muƙaddas, sun samar da sashe na bincike kan shi'anci.[26] jami'ar Tel Abib (Tel Aviv), mafi girman jami'a a cikin Isra'ila ita ma tana da sashen nazari kan muslunci da shi'anci.[27]
Littafin Aƙideh wa fiƙhu dar shi'eh imamiyyeh, tare da alƙalamin atan kulbirag,[28] da littafin Shi'eh Imamiyeh be negahe be sunnate riwayi anan, na josep ilyas,[29] da littafin Kalam Falsafe wa Irfane Shi'eh Dawazda Imami, na Zabine ishmitikeh wanda a shekarar 2002 ya samu lambar yabo ta littafi na shekara a jamhuriyar muslunci ta iran,[30] suna daga muhimman rubuce-rubuce kan nazarin shi'anci a Isra'ila.
Shi'a Da Wurarensu A Cikin Falasɗinu Da Aka Mamaye
Babu cikakken rahotan ƙididdigar adadin ƴanshi'a da suke zaune Isra'ila Ana lissafa muƙamu ra'asil husaini da yake Asƙalan cikin cikin cibiyoyin shi'a da suke Isra'ila, cibiyar ƙididdiga ta birnin ƙudus da aka mamaye, a shekarar 1386 hijra shamsi, sun fitar da cewa a hukumance akwai ƴanshi'a mutum 600, sai dai cewa wannan ƙididdiga ba ta kasance dandaƙaƙƙa ba, saboda da yawan ƴanshi'a suna ɓoye kawukansu saboda tsoro hatsarin da yake tattare da gano su ko su wanene daga ma'akatan tsaro na Isra'ila, suna ɓoye kasancewarsu ƴanshi'a, amma sayit na tashar hafte yaman sun bayyana cewa adadin ƴanshi'a ya kai mutum 6000, a wani rahotan daban an bayyana cewa sun kai 10,000.[31]
An ce tun lokacin da aka shelanta samar da Isra'ila akwai ƴanshi'a da suke rayuwa cikin ƙasar, Kuma akwai kungiyoyin ‘yan Shi'a irin su ‘Ya'yan Abdul Rafi' da `YanShi'a na hakika suna rayuwa a ɓoye cikin ƙasar.[32] Adadin musulmai da suke zaune a mamayayyiyar ƙasar Falasɗinu (Isra'ila) a shekarar 2022, miladiya sun kai miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai da ashirin da takwas.[33]
Wuri Da Ake Danganta Shi Da Ahlul-Baiti A Mamayayyar Ƙasar Falasɗinu

Daga cikin wurare masu tsarki a wurin ƴanshi'a da suke cikin Isra'ila akwai muƙamu ra'asil husaini da yake garin Asƙalan wanda wasu ba'arin masu bincike suna ɗaukar wannan wuri matsayi wurin ziyara mafi muhimmanci da ake danganta shi ga ahlul-baiti da yake palasɗin da aka mamaye.[34] Dalili shahara da muhimammancin wannan wuri ya samo asali ne kan maganar da ake yaɗawa cewa an binne kan Imam Husaini (A.S) a wannan wuri.[35] A wani ƙaulin an bada rahoto cewa a rabin ƙarni na shida bayan hijira, an kai Imam Husaini (A.S) birnin alƙahira na ƙasar Misra, amma muƙam ra'asil Husaini (A.S) yana nan a garin Asƙalan, kuma ya cigaba da kasancewa wuri abin girmama a wurin mutane.[36]
Ana danganta wurare daban-daban ga Imam Ali (A.S) daga jumlarsu akwai muƙam da wurin ziyarar Imam Ali (A.S) kan hanyar ƙudus zuwa yafa (Tel Aviv) wanda aka rusa, akwai muƙamu Imam Ali (A.S) a garin nabulus, garin akka da garin lud.[37] a birnin khalil akwai wani wurin ziyara da ake danganta shi ga fatima ɗiyar Imam Husaini (A.S), haka nan a garin ɗabriyya akwai wurin ziyara da ake danganta shi ga sukaina ɗiyar Imam Husaini (A.S).[38]
Mamaye Falasɗinu Da Shelanta Samuwar Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila
A ranar 14 ga watan mayu shekara ta 1948 tare da kawo ƙarshen mulkin mallaka na birtaniya kan Falasɗinu[39] David Ben-Gurion, uba kuma mai zanen kasar Isra'ila[40] A cikin ɗakin taro na birnin Tel Abib, ya miƙe ya shelanta kafa ƙasar Isra'ila.[41] bayan nan ne mamayar garuruwan Falasɗinu ya fara a hukumanc.[42]

Bayan kwana ɗaya daga shelanta kafa ƙasar Isra'ila, sojojin ƙasashe biyar na larabawa (Misra, lubnan, siriya, Jodan da iraƙi).[43] Cikin yunƙurin bada kariya da goyan ga Falasɗinu sun tsunduna yaƙi tare da Isra'ila.[44] bayan wannan yaƙi ne sai aka wayi gari Isra'ila ta mamaye kaso 78%100 cikin garurun Falasɗinu.[45]
Kan asasin rahotanni zuwa shekarar 2023 miladiyya kaɗai kaso shabiyar ne cikin ɗari ya rage daga Falasɗinu,(Wanda ya haɗa da zirin gaza da yankuna a rarrabe daga ɓangaren gaɓar kogin Jodan), sauran yankunan duka Isra'ila ta kwace ta mallakawa kanta.[46] Ranar shelanta kafa ƙasar Isra'ila cikin mamayar garuruwan Falasɗinawa ana kIranwannan rana da ranar "Nakba" ko ranar (Faji'a) kowacce shekara Falasɗinawa suna yin jerin gwano don tunawa da wannan rana ta baƙin ciki da takaici.[47] An san Isra'ila a matsayin gwamnatin mamaya na birnin Kudus ko kuma gwamnatin haramtacciyar ƙasar Isra'ila saboda mamayar ƙudus da Falasɗinu.[48]


Saƙonni Da Suka Biyo Bayan Ayyana Isra'ila A Matsayin Ƙasa
Shelanta kafa ƙasar Isra'ila a hukumance tare da mamayar ƙasar Falasɗinu ya haifar sabbin saƙonni a cikin Falasɗinu da ma duniya bakiɗaya, ba'arin waɗannan saƙonni sun kasance kamar haka:
- Kisa da korar Falasɗinawa daga garuruwansu: kan asasin rahotannin cibiyar sadar da bayanai ta palasɗin, cikin mamaye Falasɗinu daga shekarar 1948 miladi zuwa shekara 2023, an kashe sama da Falasɗinawa dubu ɗari.[49] Wannan cibiya tare da naƙalin hukumar "UNRWA" adadin korarrun Falasɗinawa zuwa shekarar 2020 miladiyya sun kai miliyan shida da dubu ɗari huɗu.[50]
- Samar da gwawagrwamayar kwato ƴanci da miƙewar mutane: bayan mamayar Falasɗinu da yankunan da suke kewaye da ita, an samu ɓullar ƙungiyoyin gwagwarmayar kwato ƴanci daban-daban misalin ƙungiyar fatahu a shekarar 1959 miladiyya,[51] ƙungiyar kwaton ƴancin Falasɗinu me suna "Safu" a shekarar 1964 miladiyya.[52] ƙungiyar jihadul islami a shekarar 1979 miladiyya.[53] ƙungiyar gwagwarmayar kwato ƴanci ta hamas a shekarar 1987 miladiyya.[54] duka cikin Falasɗinu da kuma ƙungiyar amal a shekarar 1975 miladiyya.[55] ƙungiyar hizbullahi a shekarar 1982 miladiyya waɗannan guda biyun na ƙarshe suna ƙasar lubnan.[56] an samar da su ne domin ƙalubalantar mamayar Isra'ila da kuma kwato ƴanci.
Falasɗinawa tsawon tarihin mamayar ƙasarsu da Isra'ila take yi lokuta daban-daban sun tashi kan fafutikar dawo da ƙasarsu daga hannun Isra'ila.[57] Intifada uku kuma sun faru a Falasdinu: Intifada ta farko (Intifadar Dutse) a 1987, intifada ta biyu (Al-Aƙsa Intifada) a watan Satumba 2000, intifada ta uku (ƙudus Intifada) ranar 1 ga Oktoba, 2015..[58]
- Ku duba: Ƙawancen Ƴan Gwagwarmaya
Hadafin Kafa Isra'ila

An ambaci kafa wata babbar ƙasa (Great Israel) wacce take da asalin Yahudawa da rinjayen yanki a yankin gabas ta tsakiya a matsayin manufa ta farko kuma mafi muhimmanci na gwamnatin Isra'ila..[59] Rouge Garaudy, marubuci ɗan siyasa wanda yai istibsari da ya kasance ɗan asalin ƙasar faransa. ya yi amanna cewa manufa ta asasi a gurin sahayoniyawa game da kafa Isra'ila shi ne hijirar bakiɗayan Yahudawa daga ƙasashen daban-daban na duniya zuwa ƙasar da aka yi musu alƙawari.[60] tare da samar da daular Yahudawa a Falasɗinu.[61] A imanin Imam Khomaini, hadafi na tushe game da kafa Isra'ila a kan garuruwan Falasɗinu shi ne samun iko da ƙarfi kan duniyar muslunci da mulkin mallaka kan ƙasashen musulmai.[62]
Dalilan Sahayoniyawa Kan Kafa Isra'ila
Murtada Mutahhari
“Suna da’awar cewa shekaru dubu uku da suka gabata, mutane biyu daga garemu (Dawuda da Sulemanu) sun yi sarauta a can na ɗan lokaci... A cikin waɗannan shekaru dubu biyu, yaushe ne ƙasar Falasdinu ta zama ta Yahudawa? gabanin Musulunci kasar palastinu ba ta kasance ta yahudawa ba , kuma ba nasu ba ne bayan Musulunci. A ranar da musulmi ya ci kasar Falasdinu, Falasdinu tana hannun kiristoci ne, ba a hannun Yahudawa ba. Kuma wallahi Kiristocin da suka yi sulhu da Musulmai, daya daga cikin abubuwan da suka sanya a cikin yarjejeniyar zaman lafiya shi ne ba ku kyale Yahudawa a nan ba. Yaya aka yi ba zato ba tsammani ya ɗauki sunan ƙasar Yahudawa?"
Sahayoniyawa sun kawo dalilai da uzurori kan mamayar Falasɗinu da kafa daular Isra'ila, abin da ake gani matsayin wata tatsuniya ta Isra'ila.[64] Waɗannan dalilai sun kasance tattare da ɓangare na addini da kuma wanda ba na addini ba, ɗaya daga dalilansu na addini shi ne da'awarsu ta cewa Falasɗinu ita ce ƙasar nan da aka yi musu alƙawarin dawowa hannunsu.[65] Cikin littafin tafiyar halitta [Tsokaci 1] an yi magana game da kyautar wannan ƙasa ga zuriyar Annabi Ibrahim (A.S).[66] A ra'ayin sahayoniyawa, korar waɗanda ba su daga garuruwansu da suke raya cewa Allah ya yi ma Yahudawa alƙawarinsu, bawai kaɗai suna ganin hakan matsayin haƙƙin Yahudawa ba kawai, bari dai suna ganin haka matsayin taklifi da Allah ya ɗora shi a kansu.[67]
Waƙi'ar holokos (Holocust) yana daga cikin dalilai wanda ba na addini ba da suka kawo su game da kafa ƙasar Isra'ila.[68] ta kai ga suna cewa kafa ƙasar Isra'ila amsa ce ta Allah kan babbar sadaukarwa.[69] Yahudawa sun yi imani kan cewa Hitla ya kashe Yahudawa miliyan shida a wannan waƙi'a da ta faru a lokacin yaƙin duniya na biyu.[70] Wannan waƙi'a ce ta bawa Yahudawa damar koken cewa su mutane ne da ake zalunta, kuma suka nemi al'ummar duniya su biya su diyya, ƙasashen turawa sun fake da uzurin gyaran asara cikin kafa cikakkiyar daular yahudawa.[71] tare da haka mutane daban-daban sun nuna shakku kan wannan da'awa da Yahudawa suka dama ƙididdigar lissafin adadin yahudawan da aka kashe a waƙi'ar holokos.[72]
Yaƙoƙi Da Kashe-kashe Da Ta'addanci
- Tushen ƙasida: Fihirisar Yaƙoƙi Da Musulmai Suka Yi Kan Isra'ila
Lokuta da dama Isra'ila ta kai hare-hare kan musulmai da suke a palsɗinu da lubnan, an yi yaƙi tsakanin juna lamarin da ya haifar da asarar dubban fararen hula tare da rusa dubunnan wurare.[73]

Haka nan Isra'ila ta kai hare-hare a lokuta da daman gaske kan mutane da suke rayuwa a zirin gaza; daga jumlarsu akwai yaƙin kwanaki 22 da ya faru a shekarar 2008, yaƙin kwanaki 8 a shekarar 20012 da kuma yaƙin kwanaki 51 shekarar 2014.[74] a watan oktoba shekarar 2023 nan cikin raddin da Isra'ila ta yi kan ofireshin ɗin Tufanul Al-Aksa, ta kai hare-hare kan zirin gaza, zuwa ranar 13 ga watan jun 2024 miladiya Isra'ila ta kashe Falasɗinawa mutum 37232, tare da raunata mutane 85037.[75]
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Khamenei ya yi jawabi a ranar Kudus ta duniya: br> “Daga cikin laifuffukan da mutane ke aikatawa na zamani kusa da wannan zamani, babu wani laifi na wannan juzu’i da irin wannan tsanani. Kwace kasa da korar mutane daga gidajensu da kasashen kakanninsu har abada, tare da munanan nau'ikan kisan kai da aikata laifuka da lalata kwadayi da tsararraki, da ci gaba da wannan zalunci na tarihi shekaru da yawa, hakika sabon tarihi ne. na muguwar dabi’ar dan Adam.
Kashe-kashe Na Gungun Jama'a
- Tushen ƙasida: Fihirisar Kashe-Kashen Da Isra'ila Take Yi
Tsawon tarihin mamayar Falasɗinu da Isra'ila ta yi ta dinga kashe dubban mutane a Falasɗinu da yankunan da suke kewaye da ita. ba'arin kamfanonin dillancin labarai sun kawo sunayen 120 daga ayyukan kisan kiyashi da Isra'ila ta aikata[77] kan asasin rahotannin cibiyar sadar da bayanai ta Falasɗinu, daga shekarar 1948 zuwa 2023 miladiyya Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da mutum dubu ɗari.[78] an bayyana lefukan rashin kunya da Isra'ila take aikatawa kan mutanen Falasɗinu tare da kashe fararen hula da ƙananan yara matsayin kisan kiyashi.[79]
Kisan Mummuƙe
Kan asasin ƙididdiga ta kamfaninnukan dillancin labarai, sahayoniyawan Isra'ila tun shelanta kafa Isra'ila sun aikata ta'addancin kisa fiye da sau 2700.[80] Jaridar birtaniya ta harshen turanci mai suna ze irish indifendan (The Irish Independent) cikin rahotonta mai taken "Waɗanda suka fi aikata kisan gilla a duniya" hukumar leken asiri ta Isra'ila da ake kira da mosad (Mossad) ana siffanta wannan hukuma da injin aikata kisan rashin tausayi na Isra'ila..[81] Ayyukan kisa da Isra'ila suke aikata bai iyakantu kan shugabanni Falasɗinawa da fitattun mutane masu rajin neman ƴanci ba kaɗai, bari dai hatta jagororin siyasa da masana masu yawa a duniya basu tsira daga hannun Isra'ila ba.[82] Ba'arin mutanen da Isra'ila ta aikata ta'addancin kashe su sun kasance kamar haka: Sayyid Abbas Musawi sakatare na biyu a ƙungiyar Hizbullahi Lubnan, Imad Mugniyya ɗaya daga kwamandojin hizbullahi, Ragib Harbi sananne malamin addini ɗanshi'a wanda ake kira da shugaban shahidan gwagwarmayar lubnan, Samir Ƙinɗar daga membobin ƴanto Falasɗinu, Fatahi Shaƙaƙi wanda ya assasa Harkatu Jihadul Islami, Shaik Ahmad Yasin daga jagororin ƙungiyar Hamas.[83] Kan asasin sanadai da rahotanni, haƙiƙa hukumar leƙen asiri ta Isra'ila watau Mosad tana da hannun cikin kashe masana kimiyyar nukiliya na Iran misalin Ali Muhammadi, Shahriyari, Ahmadi Roshan, Rida Nejad da Fakhri Zade.[84]
Karya Dokoki Da Ƙudururrukan Majalisar Ɗinkin Duniya

Isra'ila ta shahara da keta dokokin da ƙudirorin majalisar ɗinkin duniya.[85] An ce kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya tun daga shekara 1948 sun fitar ƙudiri fiye 102, kwamitin kare haƙƙoƙin ɗan adam na majalisar ɗinkin duniya shima ya fitar da takardar ƙudiri guda 104 daga shekara 2006 zuwa 2023 duka kan alawadai[86] Sai dai kuma tare da haka ƙasar amurka cikin ƙoƙarinta na kare Isra'ila tun daga shekarar 1972 zuwa 1996 kusan karo 36 tana hawa kujerar naƙi (Veto) a majalisar ɗinkin duniya don nuna watsi da waɗannan takardun ƙudiri na tir da alawai da aka fitar kan Isra'ila.[87]
Cikin jumlar ƙudiri da matakai na tir da alawadai da aka fitar kan Isra'ila sune kamar haka:
- Ƙudiri mai lamba 3236 a ranar 22 ga Nuwamba, 1974: Wannan kuduri ya amince da `yancin cin gashin kai da yancin kai a Falasdinu ga Falasdinu da ‘yancin ‘yan gudun hijira na komawa ƙasashensu; Amma Isra'ila ta keta shi.[88]
- Ƙuduri mai lamba 2334 na kwamitin sulhu na ranar 23 ga watan Disamba 2016: an fitar da wannan kuduri ne domin yin Allah wadai da matsugunan da Isra'ila ke yi a yankunan da ta mamaye da kuma keta dokokin ƙasa da ƙasa.[89]
- Ƙudiri mai lamba 242 na komitin sulhu: A cikin wannan kudiri a ranar 22 ga watan Nuwamban shekarar 1967 kwamitin sulhun ya bukaci janyewar sojojin yahudawan sahyoniya daga yankunan Falasɗinawa da ta mamaye.[90]
Ayatullahi Khamna'i:
Bayan kammala tattaunawa makamashin nukliya, na ji cewa sahayoniya da suka mamaye palasɗinu suna cewa: halin da ake ciki da wannan tattaunawa zmau kuɓuta daga matsalar iran tsawon shekaru 25 masu zuwa, zan basu amsa da cewa nan da shekaru 25 masu insha Allahu ba za a samu wani abu mai suna daular isra'ila ba.
[91]
Fihirisar Littafi
- Tushan ƙasida: Fihirisar Litattafai Game da Falasɗinu Da Isra'ila
Game da takaitaccen tarihin kafa Isra'ila, yaƙoƙi da mas'alolin batutuwanta an wallafa adadin litattafai, ga wasu ba'arinsu kamar haka:
- Daneshnameh Sahayonisim wa isra'il: wannan littafi yana da nufin gano sahyoniyanci da Isra'ila a cikin juzu'i shida da shigarwar 1900 da Majid Saftaj ya tattara kuma gidan bugawa Aron ya buga shi.
- Siyasat wa diyanat dar isra'il, na abdul-fatahi muhammad madi, tarjamar gulam rida tihami: wannan an fara buga a shekarar 2012 ta hannun maɗabba'ar sana.
- Littafi mai mujalladi goma sha huɗu, "To Zudatr Beshikan" na Ronin Bargeman, tarjamar Wahidu Khidab: wannan littafi riwaya ce kan jami'an tsaron leƙen asiri na Isra'ila game da rahotan ayyuka kisa na shekara 60 da mosad suka gudanar.
- Majaraye palasɗin wa isra'il, na majid safataj, tehran, cibiyar yada al'adun muslunci, bugu na farko a shekarar 2001.
- Dah galɗe mashhur darbaraye isra'il (abubuwan da yawan mutane suke tunani daidai ne, amma kuma ba daidai bane): na Ilan Payehe malamin tarihi a Isra'ila, tarjamar Wahidu Khidab, cikin wannan littafi an kawo tatsuniyoyi goma da imani na kuskure da a kan asasinsu ne isra'i ta kafu, waɗannan abubuwa sun fuskanci bincike da suka.[92] cikin fasali na uku a wannan littafi, watsi da abubuwa kamar haka: aƙidar daidaituwar sahayoniyanci da yahudanci, da kuma daidaita ƙiyayya da sahayoniynci daidai yake da ƙiyayya da yahudanci. maɗabba'ar kitabistane marifat ita ta fara buga wannan littafi a shekara ta 2020 miladiyya.[93]
- Islam pajuhi dar isra'il, na Akbar Mahmudi, cikin wannan littafi an bayyana mafi muhimmancin cibiyoyi, mutane, rubuce-rubuce da bincike game da muslunci da sanin muslunci a ƙasar isra'il.[94]
Bayanin kula
- ↑ jewish virtual library. ,«Vital Statistics: Latest Population Statistics for Israel»
- ↑ Paknia Tabrizi, "Ulamye Shi'a wa difa az Quds Sharif", shafi na 160 da 161.
- ↑ Khumaini, Sahifa Imam, 1389, juzu'i na 2, shafi na 139.
- ↑ MuhtashamiFur، «مروری بر شکلگیری رژیم اشغالگر قدس»،shafi na 112
- ↑ Paknia Tabrizi, "Ulamye Shi'a wa difa az Quds Sharif", shafi na 156 da 163.
- ↑ Khumaini, Sahifa Imam, 1389, juzu'i na 2, shafi na 139 da juzu'i na 6, shafi na 469.
- ↑ Sarehaddi، «علمایی که نسبت به مسئله فلسطین واکنش نشان دادند»،Cibiyayr binciken tarihin na zamani.
- ↑ Sarehaddi، «علمایی که نسبت به مسئله فلسطین واکنش نشان دادند»،Cibiyar Tarihin Zamani.
- ↑ Motahari, Majmu asar, 1390, juzu'i na 26, shafi na 340
- ↑ Khumaini, Sahifa Imam, 1389, juzu'i na 16, shafi na 293.
- ↑ «اسرائیل باطل مطلق است», Imam Musa Sadr Cultural Research Institute.
- ↑ «سخنرانی تلویزیونی به مناسبت روز جهانی قدس»،Gidan yanar gizo na bayanai na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei.
- ↑ «بیانات در مراسم گشایش کنفرانس بینالمللی حمایت از انتفاضه فلسطین»Gidan yanar gizo na bayanai na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei
- ↑ «بیانات در دیدار مسئولان نظام و سفرای کشورهای اسلامی»، Shafin yanar gizo na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei; «بیانات در دیدار دستاندرکاران دومین کنگره ملی شهدای ورزشکار», Shafin yada labarai na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei.
- ↑ «بیانات در دیدار مسئولان نظام و سفرای کشورهای اسلامی»،, Shafin yada labarai na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei.
- ↑ «بیانات در دیدار جمعی از خانوادههای شهدا و آزادگان»،, Shafin yada labarai na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei.
- ↑ Dehkan، «آشنایی اجمالی با رژیم غاصب کودککش اسرائیل», Jaridar Atrak, Mayu 9, 1401; Tofigi,«کدام کشورها اسرائیل را به رسمیت نمیشناسند؟»،Lamarin 24 Kamfanin Dillancin Labarai
- ↑ Taukifi، «کدام کشورها اسرائیل را به رسمیت نمیشناسند؟»،Lamarin 24 Kamfanin Dillancin Labarai.
- ↑ Pahuheshgahe wa Pajuheshkede Siyasi-Ilimi, barasi rawabid khariji daulat sahayonisti, 2018, shafi na 337.
- ↑ Sweidan,Dayiratul almarif musawawwar tarikh sahayonissim, 1391, shafi na 388.
- ↑ Sweidan,Dayiratul almarif musawawwar tarikh sahayonissim, 1391, shafi na 388.
- ↑ Sweidan,Dayiratul almarif musawawwar tarikh sahayonissim, 1391, shafi na 389.
- ↑ Sweidan,Dayiratul almarif musawawwar tarikh sahayonissim, 1391, shafi na 399.
- ↑ Rezawi«مرجعیتپژوهی در اسرائیل»، Gidan yanar gizon da ke nuna al'ummar Iran.
- ↑ Mahmoudi, Islam Pajuhi dar Isra'il, 2019, shafi 302.
- ↑ Hosseini, Shi'eh pajuhi wa Shi'eh pajuhan, 2007, shafi na 49
- ↑ «مطالعات اسلامشناسی و شیعهشناسی در دانشگاه تل آویو»،Tushen bayanan Hauza.
- ↑ Hosseini, Shi'eh pajuhi wa Shi'eh pajuhan, 2007, shafi na 49
- ↑ Mahmoudi, Islam pajuhi dar Isra'il, 2019, shafi 233-306.
- ↑ Mahmoudi, Islam pajuhi dar Isra'il, 2019, shafi 217-218.
- ↑ Muutaz، «شیعه در اسرائیل»، Pegah Hawza bi-weekly.
- ↑ Muutaz، «شیعه در اسرائیل»، Pegah Hawza bi-weekly.
- ↑ jewish virtual library. ,«vital Statistics: Latest Population Statistics for Israel»
- ↑ Khameyar, “Mazarat Ahlul-baiti Payambar (s.a.w) dar ordan wa Palastinu ishakali”, shafi na 183.
- ↑ Khameyar, “Mazarat Ahlul-baiti Payambar (s.a.w) dar ordan wa Palastinu ishakali”, shafi na 183.
- ↑ Khameyar, “Mazarat Ahlul-baiti Payambar (s.a.w) dar ordan wa Palastinu ishakali”, shafi na 184.
- ↑ Duba: Khameyar, " Wuraren ziyartar Iyalan gidan Annabi (SAW) a Jordan da Palastinu da Isra'ila ta mamaye," shafi na 182 da 183;«از آثار اسلامی و زیارتی اهلبیت(ع) در فلسطین چه میدانیم؟»، Kamfanin Dillancin Labarai na Razavi.
- ↑ Khameyar, “Mazarat Ahlul-baiti Payambar (s.a.w) dar ordan wa Palastinu ishakali”, shafi na 185-186
- ↑ ،Encyclopedia na Tarihin Falasdinawa da aka kwatanta, 2013, p. 186; ,Sicherman and others «Israel», The Encyclopaedia Britannica.
- ↑ Mehtadi, "Ben-Gurion, Daɓid", p.356
- ↑ Sweidan, Dayiratul Almarif musawwar tarikh yahudiyat wa sahayonisim, 1391, shafi na 261; Kafash wa digaran, Dayiratul Almarif musawwar tarikh palasdinu, 1392, shafi na 186
- ↑ «روز نکبت و جنایات صهیونیستها از سال ۱۹۴۸ تا به الان»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
- ↑ Saftaj, Majaraye Falasdinu wa Isra'ila, 2001, shafi na 199; Kafash wa digaran, lDayiratul amlmarif tarikh musawwar Falasdinawa, 1392, shafi na 187.
- ↑ Nakba Day: What happened in Palestine in 1948?», Al Jazeera Media Network.
- ↑ Kaffash da wasu mutane, Encyclopedia na Tarihin Falasdinawa da aka kwatanta, 2013, p. 201; Safataj, Labarin Falasdinu da Isra'ila, 2002, shafi. 202; Nakba Day: What happened in Palestine in 1948?», Al Jazeera Media Network.
- ↑ «نقشه فلسطین و مساحت غزه»، Tahsar Al-Alam «۷۵ سال از فاجعه نکبت (اشغال فلسطین) گذشت»،Cibiyar Bayanin Falasdinu.
- ↑ Ashly and Hefawi, «Nakba: ‘It remains bitter and continues to burn’», Al Jazeera Media Network؛ «تظاهرات مردم فلسطین به مناسبت روز نکبت»، Anatoly Agency.
- ↑ Misali, duba: Khumaini, Sahifa Imam, 1389, juzu’i na 151, 154, 160 da 162, juzu’i na 16, shafi na 399; Mohtashmipour, "mururi bar shakle giri rejimi ishkalger Qudus", shafi na 100, 116 da 122.
- ↑ «۷۵ سال از فاجعه نکبت (اشغال فلسطین) گذشتCibiyar Bayanin Falasdinu..
- ↑ «۷۵ سال از فاجعه نکبت (اشغال فلسطین) گذشت»،Cibiyar Bayanin Falasdinu.
- ↑ Kafash wa digaran,Dayiratul almarif musawwar tarikh Falasdin, 1392, shafi na 210.
- ↑ Kafash wa digaran,Dayiratul almarif musawwar tarikh Falasdin, 1392, shafi na 212.
- ↑ Maliki da Rashidi, “Jihadi Islami Janbesh”, shafi na 437
- ↑ Maliki da Rashidi, “ Hamas Janbesh”, shafi na 69-80
- ↑ Khosrowshahi، «جنبش امل و امام موسی صدر (قسمت دوم)»،Ofishin kiyayewa da sharhi kan ayyuka da tunanin Farfesa Seyyed Hadi Khosrowshahi.
- ↑ Taufikiyan «حزب الله نماد عزت و اقتدار لبنان»،Shafin Fajuhe.
- ↑ «مروری بر تاریخ مبارزات مردمی فلسطین از ۱۹۶۷ تا ۲۰۲۲»، Yanar Gizo na Cibiyar Takardun Takardun Juyin Musulunci.
- ↑ «مروری بر تاریخ مبارزات مردمی فلسطین از ۱۹۶۷ تا ۲۰۲۲»، Yanar Gizo na Cibiyar Takardun Takardun Juyin Musulunci.
- ↑ Duba: Safataj, Labarin Falasdinu da Isra'ila, 2002, shafi. 164; «رؤیای صهیونیستها در تأسیس اسرائیل بزرگ چگونه بر باد رفت؟»، , Kamfanin Dillancin Labarai na Fars: Khumaini, Shafi na Imam, 2010, vol. 21, ku. 398, shafi na 2.
- ↑ Garodi, Muhakameh Sahiyonisim Isra'il, 2004, shafi na 41.
- ↑ Erodi, Tarikh yek irtida , 1377, shafi na 75, 76 da 82; Garodi, Muhakameh Sihiyonisim Isra'il, 2004, shafi na 66
- ↑ Khumaini, Sahifa Imam, 2009, juzu'i na 3, shafi na 2.
- ↑ Motahari,majmueh asar 1390, juzu'i na 17, shafi na 288.
- ↑ Misali, duba: Garodi, Tarikh yek irtidad, 1377, shafi na 13-17, 33, 35 da 47-50; Pap, yek Idea Isra'il, 2018, shafi na 152.
- ↑ Firouzabadi, Kashfu Asrar Sihiyonisim, 2013, shafi na 25; Sajjadi, paidayesh wa tadawum Sihiyonisim, 2006, shafi na 45.
- ↑ Garodi, Tarikh yek irtidad, 1377, shafi na 37, 38 da 187.
- ↑ Garodi, Mujakemeh Sihiyoni sim Isra'il, 2004, shafi na 41.
- ↑ Garodi, Sihiyoniyancin Isra'ila, 2004, shafi na 76.
- ↑ Garodi, Tarikh yek irtidad, 1377, shafi na 171.
- ↑ Sweidan, dayiratul almarif musawwar tarikh Yahudiyat wa sahayonisim, 1391, shafi na 297.
- ↑ Firouzabadi, kashful Asrar Sihiyonisim, 2013, shafi na 28.
- ↑ Sweidan, Dayiratul almarif tarikh Yahudiyat wa sahyonisim, 1391, shafi 297-298.
- ↑ Ku Duba: از عملیات سلامت الجلیل و شکلگیری حزبالله تا خوشههای خشم»، خبرگزاری تسنیم؛ «پرونده سنگین جنایتهای ارتش اسرائیل»، Kamfanin dillancin labarai na Mehr.
- ↑ Ku Duba: «پرونده سنگین جنایتهای ارتش اسرائیل»،، Kamfanin dillancin labarai na Mehr «دهها جنایت از بزرگترین جانی جهان»، ، Kamfanin dillancin labarai na Mashraq.
- ↑ «الاحتلال يواصل تصعيده بالضفة ويعتقل عددا من الفلسطينيين»، ، Kamfanin dillancin labarai na Aljazira.
- ↑ «سخنرانی تلویزیونی به مناسبت روز جهانی قدس»، Ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei.
- ↑ Ku duba: «دهها جنایت از بزرگترین جانی جهان»، Kamfanin dillancin labarai na Mashraq.
- ↑ «۷۵ سال از فاجعه نکبت (اشغال فلسطین) گذشت»،Cibiyar Bayanin Falasdinu.
- ↑ Ku DUba: «نمایندگان پارلمان اروپا حملات اسرائیل علیه غزه را نسلکشی دانستند»، Kamfanin dillancin labarai na Anatoly«A genocide is under way in Palestine», Al Jazeera Media Network.
- ↑ «مهمترین ترورهای انجام شده توسط اسرائیل در سراسر جهان»، Kamfanin dillancin labarai na Jamaran; «بیش از ۲۷۰۰ ترور هدفمند میراث شوم اسرائیل»، Kamfanin Dillancin Labaran Jamhuriyar Musulunci.
- ↑ «The world's deadliest assassins», Irish independent.
- ↑ «نگاهی بر جنایات رژیم صهیونیستی در ۸۶ سال گذشته»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
- ↑ Duba: Suwaidan, Illustrated Encyclopedia of the History of Judaism and Zionism, 2012, shafi 346 da 347;«بیش از ۲۷۰۰ ترور هدفمند میراث شوم اسرائیل»، Kamfanin Dillancin Labaran Jamhuriyar Musulunci.
- ↑ برای نمونه نگاه کنید به: «Israel teams with terror group to kill Iran's nuclear scientists, U.S. officials tell NBC News», NBC news؛ «The world's deadliest assassins», Irish independent؛ «نقش آمریکا در عملیات تروریستی در ایران بعد از پیروزی انقلاب اسلامی»، Cibiyar Takardun Juyin Musulunci.
- ↑ Chomsky, Fatefull Triangle, 1369, shafi na 122.
- ↑ نگاه کنید به: «نگاهی به جنایات رژیم صهیونیستی در ۸۶ سال گذشته»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
- ↑ Arodi, Tarik yek Irtidad, 1377, shafi na 14
- ↑ «اسرائیل و نقض قطعنامههای بینالمللی درباره بازگشت آوارگان فلسطینی»،Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr.
- ↑ «قطعنامه ۲۲۳۱ و دیگر قطعنامههای شورای امنیت که دولت ترامپ نقض کرد», Analytical News Society website.
- ↑ Dehghani, " Kadhanameh taksim palastin mabanaye rahe halli du daulat da milaki baraye trahe halli hame pursi", shafi na 1029
- ↑ Khamenei, Falasdinu, 2017, shafi na 603.
- ↑ Paparoma, Dah galad mashshure dabraye Isra'il, 1399, shafi na 14.
- ↑ Paparoma, Dah galad mashshure dabraye Isra'il, 1399, shafi na 16.
- ↑ Mahmoudi, Islam pajuhi dar Isra'il, 2019, shafi na 26.
Tsokaci
- ↑ A wannan rana, Jehobah ya yi alkawari da Abram ya ce: “Na ba da wannan ƙasa tun daga kogin Masar har zuwa babban kogi, kogin Yufiretis, ga zuriyarka.”
Nassoshi
- «الاحتلال يواصل تصعيده بالضفة ويعتقل عددا من الفلسطينيين»، Kamfanin dillancin labarai na Aljazeera, ranar da aka sanya labarin: 25 Disamba, 2023M, ranar da aka duba: 4 Dey, 1402H
- «از آثار اسلامی و زیارتی اهلبیت(ع) در فلسطین چه میدانیم؟»،Kamfanin dillancin labarai na Razavi, ranar da aka sanya labarin: 19 Yuni, 1398H, ranar da aka duba: 16 Dey, 1402H
- «از عملیات سلامت الجلیل و شکلگیری حزبالله تا خوشههای خشم»Kamfanin dillancin labarai na Tasnim, ranar da aka sanya labarin: 16 Afrilu, 1396H, ranar da aka duba: 25 Azar, 1402H
- «اسرائیل و نقض قطعنامههای بینالمللی درباره بازگشت آوارگان فلسطینی»، Kamfanin dillancin labarai na Mehr, ranar da aka sanya labarin: 26 Mayu, 1387H, ranar da aka duba: 4 Dey, 1402H
- «بیانات در دیدار جمعی از خانوادههای شهدا و آزادگان»، پایگاه اطلاعرسانی دفتر حفظ و نشر آثار آیتالله خامنهای، تاریخ درج مطلب: ۲ آبان ۱۳۶۸ش، تاریخ بازدید: ۸ آبان ۱۴۰۲ش.
- «بیانات در دیدار مسئولان نظام و سفرای کشورهای اسلامی»Shafin sanarwa na ofishin kiyayewa da wallafa ayyukan Ayatollah Khamenei, ranar da aka sanya labarin: 2 Nuwamba, 1368H, ranar da aka duba: 8 Nuwamba, 1402H
- «بیانات در دیدار دستاندرکاران دومین کنگره ملی شهدای ورزشکار»، Shafin sanarwa na ofishin kiyayewa da wallafa ayyukan Ayatollah Khamenei, ranar da aka sanya labarin: 2 Nuwamba, 1368H, ranar da aka duba: 8 Nuwamba, 1402H
- «بیانات در مراسم گشایش کنفرانس بینالمللی حمایت از انتفاضه فلسطین»Shafin sanarwa na ofishin kiyayewa da wallafa ayyukan Ayatollah Khamenei, ranar da aka sanya labarin: 4 Mayu, 1380H, ranar da aka duba: 27 Nuwamba, 1402H
- Pappe, Ilan, Ra'ayin Isra'ila: Tarihin Ilimi, Hikima da Ƙarfi, fassarar Mohsen Karbasforushan, Tehran, Intisharat Ettelaat, bugu na farko, 1398H.
- Pappe, Ilan, Kurakurai Goma Masu Tasiri Game da Isra'ila, Qom, Littattafan Ma'arifa, bugu na farko, 1399H.
- Abdulkarim Paknia Tabrizi«علمای شیعه و دفاع از قدس شریف»،Mujallar Mubalighan, lamba 155, Satumba 1391H.
- «پرونده سنگین جنایتهای ارتش اسرائیل»Kamfanin dillancin labarai na Mehr, ranar da aka sanya labarin: 21 Fabrairu, 1394H, ranar da aka duba: 4 Dey, 1402H.
- «دهها جنایت از بزرگترین جانی جهان»Kamfanin dillancin labarai na Mashregh, ranar da aka sanya labarin: 27 Satumba, 1393H, ranar da aka duba: 4 Dey, 1402H.
- Mahdi Taufiqi «کدام کشورها اسرائیل را به رسمیت نمیشناسند؟»،Kamfanin dillancin labarai na Rouydad 24, ranar da aka sanya labarin: 13 Agusta, 1401H, ranar da aka duba: 26 Dey, 1402H.
- Sayyid Abulhasan Taufiqiyan «حزب الله نماد عزت و اقتدار لبنان»،Shafin yanar gizo na Pajoohe, ranar da aka sanya labarin: 27 Agusta, 1387H, ranar da aka duba: 30 Dey, 1402H
- Noam Chomsky, Triangle Mai Mahimmanci: Falasdinu, Amurka da Isra'ila, fassarar Izzatollah Shahida, Tehran, Cibiyar Nazarin Siyasa da Kasa da Kasa, bugu na farko, 1369H.
- Husayni, Ghulam Ahya, Binciken Shi'a da Masana Shi'a Masu Yaren Turanci, karkashin kulawar Mohsen Alviri da Abbas Ahmadvand, Qom, Intisharat Shi'a-Shenasi, bugu na farko, 1387H
- Ahmad Khamehyar«مزارات اهلبیت پیامبر(ص) در اردن و فلسطین اشغالی»Mujallar Waqf Mirath Jawidan, lamba 83, kaka 1393H
- Sayyid Hadi Khosrowshahi «جنبش امل و امام موسی صدر (قسمت دوم)»،Ofishin kiyayewa da nazarin ayyuka da tunanin Malam Sayyid Hadi Khosrowshahi, ranar da aka duba: 30 Dey, 1402H.
- Sahifat Imam, shirya da tsara ta Cibiyar Tsara da Wallafa Ayyukan Imam Khomeini, Tehran, Cibiyar Tsara da Wallafa Ayyukan Imam Khomeini, bugu na biyar, 1389H*دهقان، Muhammad Rida، «آشنایی اجمالی با رژیم غاصب کودککش اسرائیل»، Jaridar Atrak, 9 Mayu, 1401H, ranar da aka duba: 25 Dey, 1402H.
- Rida Kamal«مرجعیتپژوهی در اسرائیل»Shafin yanar gizo na Pajwayi Az Jame'e Irani, ranar da aka sanya labarin: 19 Agusta, 1390H, ranar da aka duba: 17 Dey, 1402H
- «سخنرانی تلویزیونی به مناسبت روز جهانی قدس»،Shafin sanarwa na ofishin kiyayewa da wallafa ayyukan Ayatollah Khamenei, ranar da aka sanya labarin: 9 Mayu, 1401H, ranar da aka duba: 27 Nuwamba, 1402H
- Suwaydan, Tariq, Encyclopedia Mai Hotuna na Tarihin Yahudanci da Sihiyoniyanci, fassarar da bincike na wata ƙungiyar masu fassara da masu bincike, Tehran, Sayan, 1391H
- Safataj, Majid, Labari Kan Falasdinu da Isra'ila, Tehran, Ofishin Wallafa Al'adu na Musulunci, bugu na biyu, 1381H.
- Seyyed Hassan Firouzabadi, Bayyanar Asirin Sihiyoniyanci, Tehran, Jami'ar Babban Tsaron Kasa, bugu na biyu, 1393H
- «قطعنامه ۲۲۳۱ و دیگر قطعنامههای شورای امنیت که دولت ترامپ نقض کرد»،Shafin yanar gizo na Jami'ar Labarai da Nazari na Alef, ranar da aka sanya labarin: 7 Yuni, 1397H, ranar da aka duba: 16 Nuwamba, 1402H
- Kafash, Hamed da wasu, Encyclopedia Mai Hotuna na Tarihin Falasdinu, Tehran, Sayan Publishing, bugu na farko, 1392H
- Roger Garaudy, Shari'ar Sihiyoniyancin Isra'ila, fassarar Sayyid Muhammad Taqi Alavi da Jalil Muhammadi, Tabriz, Cibiyar Bincike na Kimiyyar Musulunci da Dan Adam, bugu na farko, 1384H
- Roger Garaudy, Tarihin Wani Ridda: Tatsuniyoyin Da Suka Kafa Siyasar Isra'ila, fassarar Majid Sharif, Tehran, Cibiyar Hidimar Al'adu ta Rasa, bugu na uku, 1377H.
- Muhammad Maliki «حماس، جنبش»،Encyclopedia na Duniya ta Musulunci (Juzu'i na 14), Tehran, Bunyad Daira Al-Ma'arif Islami, bugu na farko, 1389H
- Cibiyar Bincike da Nazarin Siyasa-Ilimi ta Neda, Duban Dangantakar Kasashen Waje na Isra'ila, Tehran, Neda Zaytun, bugu na farko, 1389H
- Mahmoudi, Akbar, Binciken Islama a Isra'ila, Qom, Dar al-Hadith, bugu na farko, 1399H
- «مطالعات اسلامشناسی و شیعهشناسی در دانشگاه تل آویو»،Shafin sanarwa na Hawzah News, ranar da aka duba: 17 Dey, 1402H
- Murtaza Mutahhari, Taron Ayyukan Malamin Shahidi Mutahhari, Tehran, Intisharat Sadra, bugu na farko, 1390H
- Mutaz Ahmad، «شیعه در اسرائیل»،Murtaza Mutahhari, Taron Ayyukan Malamin Shahidi Mutahhari, Tehran, Intisharat Sadra, bugu na farko, 1390H
- Muhammad Ali Mohtadi، «بنگوریون، دیوید»،Encyclopedia na Duniya ta Musulunci, Juzu'i na 4, Tehran, Bunyad Daira Al-Ma'arif Islami, bugu na farko, 1377H
- «نقش آمریکا در عملیات تروریستی در ایران بعد از پیروزی انقلاب اسلامی»،Cibiyar Takardun Juyin Juya Hali na Musulunci, ranar da aka sanya labarin: 20 Afrilu, 1398H, ranar da aka duba: 22 Nuwamba, 1402H
- «نمایندگان پارلمان اروپا حملات اسرائیل علیه غزه را نسلکشی دانستند»Kamfanin Labarai na Anatolu, ranar da aka sanya labarin: 15 Nuwamba, 2023M, ranar da aka duba: 25 Nuwamba, 1402H
- «نگاهی به جنایات رژیم صهیونیستی در ۸۶ سال گذشته»Kamfanin Labarai na Fars, ranar da aka sanya labarin: 22 Nuwamba, 1402H, ranar da aka duba: 20 Disamba, 1402H
- Ayyash, M Muhannad, «A genocide is under way in Palestine», Al Jazeera Media Network, Published: Noɓember 2, 2023, Accessed: November 18, 2023.
- «Israel teams with terror group to kill Iran's nuclear scientists, U.S. officials tell NBC News», NBC news, Published: February 9, 2012, Accessed: Noɓember14, 2023.
- Sicherman, Harɓay and others, «Israel», Encyclopaedia Britannica, Last Updated: Noɓember 22, 2023, ɓisited: Noɓember 23, 2023.
- «The world's deadliest assassins», Irish independent, Published: December 11, 2010, Accessed: Noɓember14, 2023.
- «ɓital Statistics: Latest Population Statistics for Israel», jewish ɓirtual library, Accessed: Feb 14, 2024.

