Jump to content

Harin Soji Da Amurka Ta Kai Kan Cibiyoyin Makamashin Nukiliya Na Iran

Daga wikishia

Wannan maƙala tare da wani ɓangare na ta, bayani game da wani muhimmi al'amari da ya faru a`yan kwanakin nan. Akwai yiwuwar daga baya bayanan da suke ciki su canja. Akwai yiwuwar labarai na farko-farko su kasance marasa inganci, sabuntawa ta ƙarshe kaɗai za ta iya tantance haƙiƙanin abin da ya faru da ingantattun bayanai na wannan maƙala. Harin Soji Da Amurka Ta Kai Kan Cibiyoyin Makamashin Nukiliya Na Iran

A ranar 22 ga watan June shekara ta 2025 miladiyya ne ƙasar Amurka ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliya na Fordo, Natanza da Isfahan. Amurka ta ƙaddamar da wannan hare-hare da niyyar lalata cibiyoyin makamashin nukiliya na Iran tare da hana Iran samun damar kai wa ga mallakar makamin nukiliya. A cewar babban sakataren hukuma kula da makamashin nukiliya ta duniya, wannan hukuma ba ta da wata shaida da take nuna cewa Iran na Shirin amfani da wannan makamashi domin mallakar makamin nukiliya, Har ila yau duk wani hari ko wata barazana kan cibiyoyin makamashin nukiliya ta Iran za a yi la'akari da matsayin tauye asalan dokokin majalisar ɗinkin duniya, da take haƙƙoƙin ƙasa da ƙasa da kuma watsi da dokokin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya.

Ayatullahi Khamna'i, jagoran jamhuriyar muslunci ta Iran, a shekarar 2010 miladiyya, cikin amsar da ya bayar kan da'awar da Isra'ila ta yi, ya fitar da fatawar haramcin ƙirƙirar makamin nukiliya.[1] Wannan fatawa da ya yi an yi mata rijista a majalisar ɗinkin duniya a matsayin shaida da hujja.[2] da kuma madogarar aiki a jamhuriyar muslunci Ta Iran[Akwai buƙatar kawo madogara]

Bayanin kula

Nassoshi