Jump to content

Dahiyatu Bairut

Daga wikishia
Dahiyatu Bairut
Abubuwa na musammanCibiyar gudanarwar Hizbullahi
ƘasaLabanun
Jimlar yawan jama'aKusan mutum miliyan ɗaya da rabi
HarsheLarabci
ƘabilaLarabawa
AddinaiMuslunci da Kiristanci
MazhabaShi'a
Yawan jama'ar Musulmi85% cikin mazauna wannan yanki
Muhimman abubuwan da suka faruKashe Sayyid Hassan Nasrullah. Harin Isra'ila Kan Kudancin Labanun (2024). Yaƙin Kwanaki 33
Ɗan SiyasaSayyid Hassan Nasrullah


Dahiyatu Junub Bairut m ko Dahiyatu Bairut, (Larabci: الضاحية الجنوبية لبيروت) wani yanki ne da ƴanshi'a suke da rinjaye da yake a kudancin babban birnin Bairut na ƙasar Labanun, wannan wuri ana la'akari da shi matsayin babbar cibiyar Hizbullahi Lubnan. Wannan wuri daɗi kan kasancewarsa mahallin da aka dinga samun rikice-rikice a lokacin yaƙin cikin gida a Labanun shekarar (1975-1990m) miladiyya, a lokuta daban-daban daga 1982 da 2006 da 2024 miladiyya ya fuskanci hare-haren Isra'ila, lamarin da ya lalata gine-ginen ƙarƙashin ƙasa kai hatta gidajen mutane ba su tsira ba. Haka nan Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren Hizbullahi Lubnan a wancan lokacin, a wannan yanki ya yi shahada sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan Hedkwatar shugabanci Hizbullahi Lubnan da yake a wannan yanki.

Dahiyatu Junubi, aksarain mazauna wannan yanki talakawa ne masu rangwamen gata, kuma kashi 85% daga cikinsu ƴanshi'a ne, kashi 10% Kiristoci ne Maruni sannan kashi 4% kuma Ahlus-Sunna, ana ƙaddara ƙididdigar lissafin adadin mazauna wannan yanki da mutum miliyan ɗaya, wanda suke matsayi sulusin adadin baki ɗayan al'ummar Bairut.

Matsayi Da Taƙaitaccen Tarihi

An ce yankin Dahiya Junubi wuri ne da yake yawan fuskantar rikice-rikice sakamakon muhimmiyar rawar da yake takawa a matsayin babbar cibiyar gwagwarmaya ta ƴanshi'a, rushe-rushe mahallai da ya samo asali daga yaƙin basasa da kuma sakamakon hare-haren da Isra'ila da take kai wa daga wajen ƙasar Labanun.[1] Wanan yanki a baya can ana la'akari da shi a matsayin geffan babban birnin Bairut, sai dai kuma sannu-sannu ya sauya ya zama ɗaya daga cikin cibiyoyin tattalin arziƙi da zamantakewa na babban birnin Bairut.[2]


Dahiyatu Junub Bairut, da farko ya kasance wani ƙauye da ake yin noma cikinsa. Sai aka fara tsugunar da ma'aikatan birnin Bairut a wannan ƙauye, bayan nan kuma sannu-sannu sai al'umma da suke rayuwa a ƙauyen suka dinga ƙaruwa, musamman ma bayan hijirar da ƴanshi'a suka yi daga kudancin Labanun Ba'alabak, da kuma Falasɗinawa zuwa wannan ƙauye, da wannan dalili ne, wannan yanki ya canja daga ƙauye zuwa cikin garin Bairut.[3]A tsakanin shekarun 1950 zuwa 1960, ƙarƙashin tasirin gasa tsakanin Jamal Abdul-Nasir shugaban ƙasar Misra da Kumaili Sham'un shugaban ƙasar Labanun, yankin Dahiya ya fi goyan bayan ƙungiyoyin Nasiriyya da Falasɗinawa, sai dai kuma cewa a shekarar 1970 miladiyya, Sayyid Musa Sadar ya assasa Harkatu Amal, sannan ƙungiyar ta taimaka wajen ƙarfafa gwagwarmaya adawa da Isra'ila, da wannan ne Dahiya ta koma ɗaya da cikin muhimman cibiyoyin gwagwarmayar muslunci.[4]

Sayyid Musa Sadar yana yi wa wannan yanki laƙabi da "Dahitul Mahrumin" ma'ana yankin masu ƙarancin gata, amma jam'iyyun hagu suna yi wa wannan yanki laƙabi da "Dahiyatul Bu'usi" ma'ana yankin talakawa, amma ita kuma ƙungiyar Hizbullahi Lubnan tana kiran wannan wuri da laƙabin "Dahiyatul Mustaz'afin" ma'ana yankin raunana.[5]

Haɗin Jama'a Da Matsin Tattalin arziƙi (Talauci)

Kan asasin hasashe da aka yi, adadin al'ummar da suke zaune a Dahiyatu Junub Bairut sun kai kusan mutane miliyan ɗaya, kusan kaso ɗaya cikin uku na baki ɗayan al'ummar Bairut babban birnin ƙasar Labanun, haka kuma an ce kasu biyu cikin uku na mazauna wannan yanki ƴan gudun hijira ne.[6]

Aksarin mazauna Dahiyatu Junub Bairut ƴanshi'a ne, amma tare da haka akwai tsirarun daga sauran mazhabobi da suke zauna a yankin. Bisa hasashe, an bayyana cewa kashi 85% na mazauna wannan yanki ƴanshi'a ne, kashi 10% Kiristoci Maruni sannan kashi 4% Ahlus-Sunna. Dahiyatu Junub wuri ne da galibi talakawa masu rangwamen gata ne ke rayuwa ciki..[7]

Rakiyar jana'izar Fu'ad Shukur daga cikin kwandojin gwagwarmaya a Dahiya Bairut 2024 miladiyya

Cibiyoyin Da Al'adun Shi'a A Yankin Dahiya

A Dahiyatu Junub Bairut akwai masallatai da husainiyoyi da aka gina domin sallah da zaman makokin Ashura a sauran ayyukan addini. daɗi kan raya munasabobin addini a wannan gine-gine, ana shirya tarurrukan zamanakewa, haka zalika akan yi taron neman taimakon jin ƙai duka ta wannan hanya.[8] A wannan yanki daɗi kan gine-ginen muslunci akwai majami'ai da coci-coci ta kiristoci.[9]

Mujamma Sayyidush Shuhada,shi ne mahallin da Hizbullahi suke shirya tarurruka da bayanan Sayyid Hassan Nasrullah da yake a Dahiya Bairut. wannan dakin taro ya rushe sakamakon harin da Isra'ila ta kai a shekarar 2024 miladiyya.

Muhimmiyar rawa cikin samarwa da gudanar da cibiyoyin al'adu da addini a yankin Dahiyatu Junub Bairut, ta hanyar amfani da husainiyoyi da masallatai, an ƙarfafa samuwar mahzaba da siyasa da zamantakewa al'ummar Shi'a, da wannan ne Dahiya ta zama kamar misalin gunduma dake nuna samuwar Shi'a a Bairut cikin ayyukan zamntakewa da siyasa da ake yaɗawa da raya su da taimakon Hizbulahi Lubnan.[10]

Lambun Shahidan Hizbullah (Maƙabarta)

Lambun Shahidan Hizbullahi wata maƙabarta ce da take yankin Dahiyatu Junub Bairut, wanda a wannan wuri ne ake binne shahidan Hizbullahi Lubnan waɗanda suka yi shahada a lokacin yaƙi da gwamnatin Sahayoniyya. Imad Mugniyya, da ɗansa Jihad, Musɗafa Badrud-dini, Sayyid Hadi Nasrullah,[11] Nabil Faruƙ, Fu'ad Shukur, Ibrahim Aƙil da Ali Karki duka an binne su ne a wannan maƙabarta.[12]

Dahiya Bairut A Watan Muharram

Kusa da Raudatul Shahidaini (Dausayin shahidai guda biyu), akwai wani wuri daban da ake kira da suna Raudatul Haura'i Zainab (A.S), wuri da aka ware domin binne shahidan masu ba da kariya ga harami da ma sauran shahidai, kabarin Samir Ƙanɗar yana nan a wannan wuri.[13]

Yaƙoƙi Da Rikice-rikice

Fuskar cikin makabartar Rawdat al-Shuhada
  • Yaƙin basasa (1975-1990): a wannan daura yankin Dahiya Junub Bairut ta kasance ɗaya daga cikin asalin yankuna da aka dinga samun rikice-rikice da rigingimun addini da siyasa, Dahiya ta zama matsugunin da yawa daga ƴanshi'a, sakamakon yaƙin cikin gida da kuma hare-haren da Isra'ila ta dinga kai wa kudancin Labanun, wannan yanki ya kasance mafakar ƴan gudun hijira, sannan kuma ya kasance yanki da yake cike da mutane daban-daban daga talakawa masu rangwamen gata.[14]
  • Hare-haren Isra'ila: An ce farmakin da Isra'ila ta ƙaddamar a shekarar 1982 miladiyya da kuma tsayuwa kyam da Hizbullahi Lubnan suka yi gaban keta alfarmar Isra'ila, ya mayar da wannan yanki cibiyar Hizbullahi Lubnan. Bayan nan kuma sai Dahiya ta canja ta zama cibiyar siyasa, soja da al'adu ta Hizbulahi Lubnan, Bayan nan kuma ta zama yanki da Isra'ila ta zaɓa ta zafafa kai hare-hare kai tsaye.[15] A lokacin yaƙin kwanaki 33 da ya faru a shekarar 2006 miladiyya hare-haren Isra'ila sun fi zafafa a wannan yanki, wanda haka ya haifar da lalata gine-ginen ƙarƙashin ƙasa da matsugunan fararen hala.[16] Daɗi kan wannann, sojan Isra'ila cikin hare-hare kan kudancin Labanun, a ranar 27 Satumba 2024, Sojojin Isra'ila sun yi ruwan bamabamai a cibiyar kwamdancin Hizbullahi Lubnan da take yankin matsugunan ƴanshi'a a Dahiya Junub[17]] tare da shahadantar da Sayyid Hassan Nasrullah.[18]
“Hoton yankunan gidaje da suka lalace a Dahiyeh Beirut a lokacin yakin kwanaki 33

Ku Duba

Bayanin kula

  1. Mahana«الضاحية الجنوبية لبيروت بين أمس أخضر وحاضر شاحب»،Independent Arabi.
  2. Kaj، «الضاحية الجنوبية بيعون بيروتي»، Shafin yanar gizo na Alif Lamun
  3. Mahana، «الضاحية الجنوبية لبيروت بين أمس أخضر وحاضر شاحب»، ایندیپندنت عربی؛ حرب، «La Dâhiye de Beyrouth»، Shafinn yanar gizo na Karun.
  4. «الضاحية الجنوبية، بيروت»، Shafin yanar gizo na Almarifa.
  5. Mahana، «الضاحية الجنوبية لبيروت بين أمس أخضر وحاضر شاحب»،Independent Arabi..
  6. «الضاحية الجنوبية، بيروت»، shafin Almarifa Harbi، «La Dâhiye de Beyrouth»، Shafin yanar gizo na Karin.
  7. «الضاحية الجنوبية، بيروت»، shafin Almarifa Harbi، «La Dâhiye de Beyrouth»، Shafin yanar gizo na Karin.
  8. Harb، «La Dâhiye de Beyrouth»، Shafin Karin.
  9. «الضاحية الجنوبية، بيروت»، Shafin Ma'arifa
  10. Harb، «La Dâhiye de Beyrouth»، Shafin Karin
  11. «روضة الشهدا مقاومت اسلامی در لبنان»،Kamfanin dillancin labarai na Mehr.
  12. «پیکر فرماندهان شهید حزب‌الله به خاک سپرده شد»، Kungiyar Matasan ’Yan Jarida.
  13. «روضة الشهدا مقاومت اسلامی در لبنان»،Kamfanin dillancin labarai na Mehr.
  14. مهنا، «الضاحية الجنوبية لبيروت بين أمس أخضر وحاضر شاحب»، Independent Arabi.
  15. «الضاحية الجنوبية، بيروت»،Shafin yanar gizo Almarifa.
  16. Mahana، «الضاحية الجنوبية لبيروت بين أمس أخضر وحاضر شاحب»، Independent Arabi.
  17. «انفجارهای مهیب در بیروت؛ اسرائیل: مقر فرماندهی مرکزی حزب‌الله را هدف گرفتیم»،‌ Kamfanin dillancin labarai na EuroNews؛ «بمباران شدید و پیاپی بیروت/ارتش اسرائیل: هدف، مرکز فرماندهی اصلی حزب الله بود»،Kamfanin Dillancin Labaran Jamhuriyar Musulunci.
  18. «حسن نصر الله.. قائد جعل من حزب الله قوة إقليمية»،Tashar Aljazira.

Nassoshi