Jump to content

Kashe-Kashen Sabra Da Shatila

Daga wikishia
Kashe-Kashen Sabra Da Shatila
Wani bango a Labanun da yake da rubutu na tunawa da musibar Sabra da Shatila
Wani bango a Labanun da yake da rubutu na tunawa da musibar Sabra da Shatila
Bayanin Abin da ya faruHarin sojojin Sahayoniyya kan sansanin ƴan gudaun hijira na Falasɗinawa
Lokaci16-18 Satumba 1982
ZamaninAriyal Sharon firaministan Isra'ila
WuriBairut
DaliliFakewa da neman fansar jinin Bashir Jumaili
ManufaKisan kiyashi kan Falasɗinawa da rusa ƙungiyar kwato ƴancin Falasɗinu
Mutanen da suka kai harinSojojin Isra'ila tare da ƴan bindigar Falansar
SakamakoKashe dubban Falasɗinawa
AsaraMutuwar mutane 3000 zuwa 3500
MartaniHukumomi yammacin turai da kafafen watsa labai na duniya sun yi Allah wadai


Kashe-kashen Sabra da Shatila, (Larabci: مجزرة صبرا وشاتيلا) wata waƙi'a ce da ta faru daga ranar 16 zuwa 18 Satumba 1982m a sansanin ƴan gudun hijira na Falasɗinawa da yake a birnin Bairut a ƙasar Labanun.[1] Sansanin ƴan gudun hijira na Sabra da Shatila wanda yake a yammacin Bairut, ya kasance matsugunin Falassɗinawa da suka rasa matsugunansu na asali, wannan sansanin ya tsinci kansa cikin kewaya da ƙawanyar sojojin Isra'ila, tare da haɗin gwiwar sojojin haya na Falansar sun aikata kisan kiyashi kan Falasɗinawa da suke wannan sansani har tsawon awanni 43.[2] A wannan kisan kiyashi an kashe kusan Falasɗinawa mutum 3000 zuwa 3500.[3]

Bayan kashe Bashir Jumaili, a birnin Bairut wanda ya kasance zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Labanun da yake ɗasawa da gwamnatin Sahayoniyya,[4] Isra'ila da ɗora alhakin kashe shi kan wuyan Falasɗinawa, sannan ta fake da haka da sunan ɗaukar fansar jininsa, ta kuma haɗa kai da sojojin haya na Labanun da ake kira da Falansar tare da ƙaddamar da kashe-kashe kan Falasɗinawa.[5]


Cikin wannan kisan kiyashi, an kashe dubban mata da ƙananan yara, wannan harin ta'addanci ya kasance ƙarƙashin kwamandancin Ariyal Sharon, firaministan Isra'ila na wancan lokacin, tun daga wancan lokaci ne ake masa laƙabi da (Haunin Sabra da Shatila).[6] An ce manufar ƙaddamar da wannan kisan kiyashi, ya kasance tarwatsa ƙungiyar nemo ƴancin Falasɗinawa da ake kira da (Saf) wace ta ke a wannan sansani.[7]

Musibar Sabra da Shatila ta zama wata alama ta kausasawa da rashin tausayi ta Isra'ila a cikin ƙwaƙwalen mutane a duniya[8] Ba'arin ƙasashen yammacin duniya da kafofin watsa labarai na ƙasa da ƙasa, wannan kisan kiyashi ya tilasta musu motsawa da yin martani[9] da kuma gabatar da ƙudurin neman hukunta Ariyal Sharon a kotun duniya da take ƙasar Beljiyom, amma sakamakon ƙarfin iko da Sahayoniyyawa suke da shi a duniya babu wani mataki na ku zo mu gani da aka ɗauka a kansa.[10]

Kisan Kiyashin Sabra da Shatila ana la'akari da shi matsayin abu mafi biƙin ciki da takaici da ya faru a tarihin Falasɗinawa, lamari ne da ya wanzu a tarihi wanda duk zagayowar shekara ana zaman tunawa da shi a Falasɗinu da Labanun.[11]

Bayanin kula

  1. Saleh, Palestine, 2002, p. 80; Hazrati, Khorshid Dar Sayeh, 2018, shafi. 89.
  2. Ruzeh shomare, 2011, shafi. 2761.
  3. Sabra and Shatila massacre survivors: 'It can’t be unseen'،Medal Est.
  4. Timeline: At war for decades, Lebanon and Israel edge towards a rare deal، Medal Est.
  5. «کشتار صبرا و شتیلا»، Tarikh Iran.
  6. Faji'eh Sabra Wa Shatila: Nange Abadi Baraye Sahayonistiha”, shafi na 209.
  7. سالروز قتل عام صبرا و شتیلا؛ مروری بر جنایات رژیم صهیونیستی علیه فلسطینیان، Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan.
  8. Faji'eh Sabra Wa Shatila: Nange Abadi Baraye Sahayonistiha”, shafi na 210.
  9. جنایتی تاریخی در قلب فلسطین کشتار صبرا و شتیلا چگونه رخ داد؟، رویداد ۲۴؛ سالروز قتل عام صبرا و شتیلا؛ مروری بر جنایات رژیم صهیونیستی علیه فلسطینیان،Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan.
  10. ««چهل سال از کشتار صبرا و شتیلا گذشت»، Anatoly Agency.
  11. حضرتی، خورشید در سایه، ۱۳۹۷ش، ص۸۹؛ Sabra and Shatila massacre: What happened in Lebanon in 1982?، Aljazira.

Nassoshi