Hizbullahi Lubnan
- Wannan wata maƙala game da Hizbullahi Lubnan. Domin neman ƙarin bayani ku duba Hizbullahi
| Yaƙar Mamayar Isra'ila | |
| Sauran sunaye | Gwagwarmayar Muslunci a Labanun |
|---|---|
| Kafawa | 1982 miladiyya |
| Waɗanda suka kafa | Sayyid Muhammad Husaini Fadlullahi, Subhi Ɗufaili, Sayyid Abbas Musawi, Sayyid Hassan Nasrullah, Na'im Ƙasim, Husaini Kurani da... |
| Salo | Jihadi |
| Nau'in ayyuka | Soja, tattalin arziƙi, saƙafa da zamantakewa |
| Manufofi | Ƴanto da garuruwan da Isra'ila ta mamaye |
| Wuri | Labanun |
| Babban sakatare | Na'im Ƙasim |
| Hali | Tana aiki a yanzu haka |
| Ayyuka da harshen | Larabci |
| Mai alaƙa da | Gidan tarihi Na Malita |
| Adireshin yanar gizo | المقاومة الاسلامیة فی لبنان پایگاه مجازی فارسیزبان مقاومت اسلامی لبنان |
Hizbullahi ko Gwagwarayar Muslunci ta Labanun (Larabci: حزب الله أو المقاومة الإسلامية في لبنان) wata ƙungiyar Shi'a ce ta siyasa da aikin soja a ƙasar Labanun wace aka kafa ta a shekarar 1982 miladiyya, da manufar ƙalubalantar Isra'ila, wannan ƙungiya tana samu ne goyan bayan jamhuriyar Muslunci ta Iran, wannan ƙungiya ta buɗe da fara ayyukanta da ƙalubalantar Isra'ila ta hanyar amfani da ofireshin na neman shahada na ƙunan bakin wake. Bayan nan sai suka juya suka mai da hankali kan ƙarfafa tanadinsu na soja, kuma suka tunkari Isra'ila da makaman rokoki na Katusha da kuma amfani da dabarar yaƙin sari ka noƙe.
Zuwa shekarar 2024 miladiyya, an samu adadin ɗauki ba daɗi da rikici tsakanin Hizbullahi da Isra'ila, daga jumlarsu za a iya ishara da yaƙin kwanaki 33. Wannan yaƙi Isra'ila ce ta fara ƙaddamar da shi da niyyar kwace makaman Hizbullahi da kuma ƴanto sojojinta guda biyu da suke kasance a hannun Hizbullahi, cikin wani ofireshin mai suna Wa'adis Sadiƙ da Hizbullahi ta gabatar wanda cikinsa ta samu nasarar kama sojojin haramtacciyar ƙasar Isra'ila. Har ila yau bayan ofireshin na Tufanul Al-aksa cikin kariya da goyan da Hizbullah ta nunawa Hamas da mutanen zirin Gaza, an samu tsanantar rikici tsakanin Hizbullahi da sojojin Isra'ila, cikin wannan rikici Hizbullahi a yunƙurinta na tsayar da ci gaba da kisan kiyashi kan al'ummar Gaza da Isra'ila take yi, ta ƙaddamar da hare-haren kan sansanonin soja a arewacin mamayayyar ƙasar Falasɗinu, Isra'ila ita ma daga na ta ɓangaren ta kai farmaki kan wasu adadin kwamandojin Hizbullahi tare da kashe su, daga cikinsu akwai Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren ƙungiyar Hizbullahi Lubnan. Bayan shahadar Nasrullah ne Sayyid Abbas Musawi ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar wanda shi ma ba da jimawa ba Isra'ila ta kai masa hari tare da shahadantar da shi. A ranar 29 ga watan Oktoba shekarar 2024 ne bayan kusan wata guda da shahadar Sayyid Hassan Nasrullah sai Na'im Ƙasim ya zama babban sakataren ƙungiyar Hizbullahi Lubnan.
Hizbullahi domin nuna goyan baya da ba da kariya ga gwamnati mai ci a ƙasar Siriya ta shiga yaƙi da ƴan ISIS. ƙungiyar Hizbullahi ƙari kan ayyukanta na siyasa da soja tana yin ayyukan saƙafa da zamantakewa, tashar talabijin ta Al-Manar tasha ce da take yaɗa manufofin ƙungiyar Hizbullahi.
Taƙaitaccen Tarihin Samuwar ƙungiyar Hizbullahi Lubnan
An kafa ƙungiyar Hizbullahi Lubnan a shekarar 1982 miladiyya ƙarƙashin taimakon Jamhuriyar Muslunci ta Iran.[1] Da farko sun fara ayyukansu na yaƙar Isra'ila a ɓoye har zuwa tsawon wasu shekara. A ranar 11 ga watan Nuwamba shekarar 1984, Ahmad Jafar Ƙasir ya ƙaddamar ofireshin na neman shahada ta hanyar ƙunan bakin wake a kan sojojin Isra'ila a kudancin Labanun, sakamakon wannan aiki na sa wasu adadi daga sojojin Isra'ila suka sheƙa lahira. A ranar 16 ga watan Fabrairu shekarar 1985 miladiyya, daidai lokacin da sojojin Isra'ila suke janyewa daga garin Saida kudancin Labanun ne ƙungiyar Hizbullahi Lubnan ta shelanta ɗaukar alhakin harin neman shahada na ƙunan bakin wake da Ahmad Jafar Ƙasir ya ƙaddamar kan sojojin haramtacciyar ƙasar Isra'ila, tare da bayyana aƙida da tsare-tsarensu da ya ginu kan ƙalubalantar Isra'ila da fatattakar ta daga ƙasar Labanun.[2]
A cewar Husaini Dehƙan ɗaya daga cikin kwamandojin Dakarun Kare Juyin juya halin Muslunci na Iran, bayan ofireshin ɗin Baitul Muƙaddas a shekarar 1982 cikin yaƙi tsakanin Iran da Iraƙi, Isra'ila ta kaiwa Labanun farmaki, daidai wannan lokacin wasu gungu daga kwamandojin Dakarun Kare Juyin juya halin Muslunci, aka aika su Labanun domin ba da horo ga sojojin Labanun domin tunkarar Isra'ila. ƙari kan wannan cikin ba da horon soja, sun himmatu kan samar da haɗin kai tsakanin ƙungiyoyi masu alaƙa da Iran wanda daga ƙarshe suka jirkita zuwa ƙungiyar Hizbullahi.[3] A cewar Na'im Ƙasim mataimakin babban sakataren Hizbullahi, Imam Khomaini ne da kansa ya tura waɗannan kwamandoji daga Iran domin ba da horon soja ga mutanen Labanun, na'am gabanin haka dama tuni ƙungiyoyin Harkatu Amal, Hizbud Da'awa, Tajammu'u Ulama'i da kwamitocin Muslunci sun gama cimma matsaya kan samar da da ƙungiya guda ɗaya rak da za ta ƙalubalanci mamayar Isra'ila, sun kuma gabatar da neman amincewa a gaban Imam Khomaini.[4]
Shugabanci
Subhi Ɗufaili shi ne ya kasance farkon babban sakataren Hizbullahi bayan kafa ƙungiyar, an zaɓe shi a ranar 5 biyar ga watan Nuwanba shekarar 1989 miladiyya, gabanin zaɓarsa a wannan muƙami, tsawon shekaru bakwai Hizbullahi suna tafiya kan tsarin majalisar jagoranci.[5] Sayyid Muhammad Husaini Fadlullahi, Subhi Ɗufaili, Sayyid Abbas Musawi, Sayyid Hassan Nasrullah, Na'im Ƙasim, Husaini Kurani, Husaini Khalil, Muhammad Ra'ad, Muhammad Fanish, Muhammad Yazbek, da Sayyid Ibrahim Amin Sayyid suna daga cikin mutanen da suka kafa wannan ƙungiya.[6] A watan Mayu shekarar 1991 miladiyya, sakamakon saɓani da suka da ya yawaita kan Subhi Ɗufaili ne aka zaɓi Sayyid Abbas Musawi matsayin babban sakataren ƙungiyar Hizbullahi Lubnan.[7] A ranar 16 ga watan Fabrairu shekarar 1992 Isra'ila ta kai farmaki kan Sayyid Abbas Musawi, inda ta shahadantar da shi, bayan shahadarsa ne majalisar shura ta Hizbullahi suka zaɓi Sayyid Hassan Nasrullah matsayin sabon babban sakataren ƙungiyar.[8] Sai dai kuma shi ma Sayyid Hassan Nasrullah ya bi sahun wanda ya gabace shi sakamakon farmakin bamabamai da Isra'ila ta ƙaddamar a kansa a ranar 22 ga watan Oktoba shekarar 2024 miladiyya wanda ya yi sanadiyyar shahadarsa.[9]
A ranar 29 ga watan Oktoba ne shekarar 2024, kusan wata ɗaya bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrullah, aka zaɓi Na'im Ƙasim matsayin sabon babban sakataren ƙungiyar Hizbullahi Lubnan..[10]
Fitattun Mutane A Ƙungiyar Hizbullahi Lubnan
Ba'arin fitattun manyan mutane a Hizbullahi Luban sune kamar haka:
Sayyid Hassan Nasrullah

Sayyid Hassan Nasrullah (Shahada: 2024 miladiyya) mutum na uku cikin jerin manyan sakatarorin Hizbullahi Lubnan kuma daga mutanen da suka kafa ta a shekarar 1982 miladiyya, a lokacin shugabancinSa ƙungiyar Hizbullahi ta zama wata babbar ƙungiya mai ƙarfin iko a yankin gabas ta tsakiya, da ta samu iko bayan ƙaddamar da wasu adadin ofireshin a shekarar 2000 miladiyya tare da tilastawa Isra'ila janyewa daga wuraren da ta mamaye a ƙasar Labanun. Sayyid Hassan Nasrullah a ranar 22 ga watan Oktoba shekarar 2024 ne ya rabauta da samun shahada sakamakon harin bamabamai da Isra'ila ta ƙaddamar a kansa.[11]
Sayyid Abbas Musawi

Sayyid Abbas Musawi memba cikin mutane da suka kafa Hizbullahi, mutum na biyu a jerin manyan shugabanni da suka jagorancin ƙungiyar. Bayan murabus da Subhi Ɗufaili ya yi a shekarar 1991 miladiyya ne ya karɓi ragamar jagoranci a matsayin babban sakataren Hizbullahi Lubnan.[12] Kafin haka ya kasance tare da dakarun Falasɗinawa a yaƙin da suka da Isra'ila. A lokacin shugabancinsa a Hizbullahi ya jagoranci ƙungiyar ne ƙasa da watanni 9, sai Isra'ila ta kai masa farmaki tare da shahadantar da shi.[13]
Subhi Ɗufailii
Shaik Subhi Ɗufaili (Haihuwa: 1948 miladiyya) ya kasance farkon babban sakataren Hizbullahi Lubnan, ya kasance a wannan muƙami tun daga 1989-1991 miladiyya.[14] A shekarar 1998 ne ya kafa harkar Sauratu Jiya (Harkar yaƙar yunwa). Magoyan bayansa sun kai hari kan cibiyoyin gwamnatin Labanun, lamarin da ya haifar da rikici mai tsanani tare da asarar rayuka.[15] Subhi Ɗufaili ya jirkice ya zama mutum mai sukan manufofin ƙungiyar Hizbullahi Lubnan da Jamhuriyar Muslunci ta Iran.[16]
Imad Mugniyya

Imad Mugniyya wanda aka fi sani da Haj Ridwan, ya kasance ɗaya daga fitattun kwamandojin kulawa da tsaro na musamman ga manyan shugabannin ƙungiyar Hizbullahi Lubnan, Har ila yau shi ne ya tsara ofirehsin ɗin Wa'adus Sadiƙ tare da jagorancin a filin daga a lokacin yaƙin kwanaki 33 tare da Isra'ila.[17] A ranar 12 ga watan Fabrairu shekarar 2008 ce ya yi shahada a babban birnin Damashƙi na ƙasar Siriya.[18]
Sayyid Hashim Safiyid-dini
Sayyid Hashim Safayid-dini, ya kasance memba a wannan ƙungiya ta Hizbullahi tun daga kafa ta, daga shekarar 1994 miladiyya ya kasance yana jagoranci majalisar zartarwa ta wannan ƙungiya.[19] ana mu'amala da shi a matsayin mutum na biyu a ƙungiyar Hizbullahi,[20] kuma halifan Sayyid Hassan Nasrullah.[21] Sojojin Isra'ila sun sanar da kisan gilla da suka yi masa a ranar 3 ga watan Oktoba shekarar 2024 cikin wani hari da suka kai a Dahiyatu Bairut.[22] Kafofin yaɗa labarai sun bada rahoton gano gawarsa a ranar 22 ga watan Oktoba.[23] Sannan ita kuma ƙungiyar Hizbullahi a nata ɓangaren ta tabbatar da shahadarsa ne a ranar 23 ga watan Oktoba.[24]
Na'im Ƙasim

Na'im Ƙasim wanda aka fi sani da Shaik Na'im Ƙasim (Haihuwa: 1953 miladiyya) shi ne na huɗu cikin jerin manyan sakatarorin Hizbullahi.[25]Ya kasance daga mutanen da suka kafa ƙungiyar Hizbullahi, kuma daga shekarar 1991 miladiyyaya kasance a muƙamin na'ibin shugaban ƙungiyar.[26] Na'im Ƙasim a ranar 29 ga watan Oktoba ne bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrullah aka zaɓe matsayin babban sakataren Hizbullahi Lubnan.[27]
Ƙalubalantar Mamayar Isra'ila
Hizbullahi Lubnan a shekarar 1985 a hukumance sun bayyanar da aƙidu da tsare-tsaren ƙungiyarsu wanda ya ginu kan ƙalubalantar Isra'ila da mamayar da take a Labanun da Falasɗinu.[28] A shekarun farko-farkon kafa wannan ƙungiya sun mayar da hankali kan ayyukan neman shahada wanda aka fi sani da kunan baƙin wake kan sojojin mamaya na Isra'ila; amma sannu-sannu sun sauya daga wannan salo. Dakarun wannan ƙungiya cikin martaninsu kan kashe Sayyid Abbas Musawi, babban sakataren wannan ƙungiya a wancan lokaci, a lokacin na farko sun harba makaman rokoki kiran Katusha kan matsugunan ƴan kama wuri zauna na Sahayoniya arewacin mamayayyar Falasɗinu.[29]
Ba'ari daga muhimman abubuwan suka faru tsakanin Hizbullahi da Isra'ila sun kasance kamar haka:
Ofireshin Wa'adus Sadiƙ
A cikin shekarar 2006 miladiyya, an gwabza yaƙi tsakanin Hizbullahi da Isra'ila, wanda aka fi sani da yaƙin Tamuz ko yaƙin kwanaki 33. Isra'ila ta saɓawa yarjejeniyyarsu da Hizbullahi, ta ƙi sakin fursunonin Lubnan guda uku. Da wannan dalili ne Hizbullahi ta motsa domin kwato su, a shekarar 2006 a yankin Jolan, cikin wani ofireshin da ake kira da suna Wa'adus Sadiƙ, Hizbullahi ta samu nasarar kame sojojin Isra'ila guda biyu. Isra'ila a yunƙurinta na karɓo su da ƙarfin tuwo da kuma kwace makaman Hizbullahi, ta ƙaddamar da hare-hare kan Hizbullahi Lubnan, yaƙi ya tsananta tsakanin Hizbullahi Lubnan da Isra'ila wanda ya ja lokaci har tsawon kwanaki 33.[30]

Rikicin Janairu 1993 Miladiyya
A ranar 25 ga watan Janairu shekarar 1993 miladiyya, Isra'ila da ƙaddamar da hare-hare kan Hizbullahi da niyyar kwace makamai Hizbullahi Lubnan da kuma samar da ɓaraka tsakanin Hizbullahi da al'ummar ƙasar Labanun, da takura gwamnatin Labanun da taka burki ga gwagwarmaya. Wannan hari da ta yi ya fuskanci martanin daga ɓangaren Hizbullahi, daga ƙarshe duka ɓangarorin biyu sun lamince da sulhu a watan Yuli shekarar 1993. Kan asasin wannan sulhu Hizbullahi Lubnan sun amince da cewa idan Isra'ila ta dena keta alfarma, suma za su dagatar da harba rokoki samfurin Katusha kan mamayyun garuruwan Falasɗinawa da Isra'ilawa suka kama suka zauna.[31]

Rikicin Afrilu 1996 Miladiyya
A ranar 11 ga watan Afrilu shekarar 1996 miladiyya, Isra'ila ta ƙaddamar da ofireshin gangamin fushi kan ƙasar Labanun. Wannan ofireshin wanda ya ƙunshi kisan kiyashi kan mutane kashi huɗu a rana ta biyu a Sahmar, a rana ta uku kuma kai hari kan ambulansi Mansuri, a rana ta bakwai Nabɗiyya Fuƙa da Ƙana sune suka shahara, cikin wannan hari Isra'ila ta kashe mutane 25 goma sha huɗu daga cikinsu sun kasance daga dakarun Hizbullahi, wannan ofireshin ya ɗauki tsawon kwanaki goma sha shida, daga ƙarshe, Isra'ila ta yi sulhu da Hizbullahi, cikin wannan sulhu Isra'ila ta amince za ta dena kai hari kan fararen hula, za ta taƙaita da tunkarar dakarun Hizbullahi.[32]
Ofireshin ɗin Ansariyya
A ranar 5 ga watan Satumba shekarar 1992 miladiyya, domin ƙalubalantar keta alfarmar da sojojin ruwan Isra'ila, Hizbullahi ta kai farmaki kansu inda ta yi ajalin da raunata Sahayoniyyawa 17.[33]
Ƴanto Da Fursunonin Gwagwarmaya

Bayan ficewar sojojin Isra'ila daga kudancin Labanun, ba'arin dakarun Hizbullahi misalin Musɗafa Dirani da Shaik Abdul-Karim Ubaidi sun kasance a kurkukun Isra'ila, Hizbullahi cikin ƙaddamar da wani tsararren ofireshin sun samu nasarar cafke sojojin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba shekarar 2000, haka zalika a babban birnin Bairut sun cafke kanal ɗin sojan Isra'ila, domin karɓo wannan sojoji na ta Isra'ila ta amince da musayen fursunoni, inda za ta bayar mutum 400 ƴan ƙasar Labanun da Falasɗinu da take tsare da su da kuma gawarwaki 59 da suka yi shahada a hannunta. Har ila yau dole ne ta bayyanar da makomar mutane 24 da aka neme su aka rasa, kuma ta ba da taswirar wuraren da ta dasa nakiyoyi a kan iyakokin ƙasar Labanun. An gudanar da musayar fursunonin a ranar 29-30 ga watan Janairu shekarar 2004.[34]
A shekarar 2008 miladiyya ne bayan yaƙin kwanaki 33, Hizbullahi suka gudanar da tattaunawa tare da Isra'ila ta hanyar shiga tsakani da ƙasar Jamus ta yi, ta yadda Isra'ila ta sako sauran fusrunonin Labanun. Haka nan an karɓo gawarwakin shahidan yaƙin kwanaki 33 da kuma sauran gawarwakin shahidan gwagwarmayar Labanun da Falasɗinu daga jumlarsu gawar Dallal Magribi da mutane 12 daga hannun Isra'ila.[35]
Goyan Bayan Hamas Da Mutanen Gaza Bayan Ofireshin Na Tufanul Al-aksa
Bayan ƙaddamar da ofireshin na Tufanul Al-aksa da kashe mutanen Gaza da Isra'ila ta fara yi a shekarar 2023 -2024 miladiyya, ƙungiyar Hizbullahi cikin nuna goyan bayanta ga mutanen zirin Gaza, ta ƙaddamar da hari kan cibiyoyin soja na Isra'ila a arewacin mamayayyar ƙasar Falasɗinu, goyan bayan da Hizbullahi ta nunawa Hamas da mutanen Gaza ya haifar da tsanantar rikici tsakaninta da Isra'ila, a rahotan tashar Al-Alam, Hizbullahi cikin kwanaki 133 bayan ofireshin ɗin Tufanul Al-aksa, ta ƙaddamadar hare-hare har guda 1038 kan Isra'ila domin nuna goyan baya ga Falasɗinu da ba su kariya.[36] Anata ɓangaren Isra'ila ta kai adadin wasu hare-hare kan ƙasar Labanun da Siriya tare da kashe wasu adadi daga kwamandojin Hizbullahi. Bisa rahotan kamfanin dillancin labarai na Tasnim, Hizbullahi Lubnan daga farkon ƙaddamar da ofireshin na Tufanul Al-aksa zuwa watan Mayu (Kusan watanni 9) ta ba da labarin shahadar mayaƙanta guda 316 cikin yunƙurinsu na ba da kariya ga Falasɗinu.[37] Haka nan Isra'ila ta hanyar da sa bom cikin na'urar sadarwa ta Pager da Hizbullahi suke amfani da ita, ta kashe fiye membobi dubu uku na Hizbullahi da ji wa wasu munanan raunuka[38] A ci gaban wannan rikici tare da Isra'ila a ranar 27 ga watan Satumba miladiyya, cikin kai farmaki kan Hedkwatar Hizbullahi a Bairut sun shahadantar da Sayyid Hassan Nasrullah mafi girman muƙami a ƙungiyar Hizbullahi.[39]
Bayan wucewar kusan watanni goma sha huɗu ana rikici tsakanin Hizbullahi da Isra'ila, a ranar 21 ga watan Nuwanba an samu tsagaita wuta tsakanin ɓangarori biyu[40] duk da cewa tare da iƙrarin Kakakin sojan Isra'ila a wannan rana da aka cimma tsagaita wuta, ita Isra'ila ba ta mutunta tsagaita wutar ta yadda ta kai hari ta kashe membobin Hizbullahi guda biyu..[41]
Yaƙi Da ISIS A Siriya
Hizbullahi ta ba da haɗin tare da aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Siriya kan yaƙar ISIS. Bayan samun rikici da rashin kwanciyar hankali a Siriya, Hizbullahi tare da sojojin Siriya sun yaƙi ƴan takfiriyya.[42] Kwato garin Al-Ƙasir yana daga cikin mafi muhimmancin nasarorin da Hizbulallahi ta samu a Siriya.[43]
Ayyukan Siyasa
A karon farko a shekarar 1992 miladiyya ne Hizbullahi Lubnan suka fara shiga takarar zaɓe, kuma suka samu nasarar lashe kujeru goma sha biyu. A shekarar 1996 miladiyya, son lashe kujeru goma, a shekarar 2000 suka samu lashe kujeru 12 cikin kujeru 128 na majalisar Labanun.[44] Cikin zaɓen game gari da ya gudana a shekarar 2005 miladiyya, Hizbullahi ita kaɗai ta samu nasara kujeru 14, sannan a iya kudancin Labanun ta lashe bakiɗayan kujeru guda 23 cikin haɗaka da Harkatu Amal, Muhammad Finesh shi ne wanda suka turawa gwamnati a matsayin ministan makamashi da harkokin ruwa na ƙasar Labanun.[45]
Bayan shekarar 2005 miladiyya ne Hizbullahi ta kasance cikin ƙungiyoyi 8 Maris. Kuma a dai wannan shekara lokaci ɗaya da kisan gilla da aka yi kan Hariri, aka samu sabon tsare-tsare da sauye-sauye a fagen siyasar Labanun, ƙungiyoyin 8 ga watan Maris cikin gaggarumin taronsu da suka shirya a shekara 2005 Hizbullahi ta tsaya kyam tare da ƙalubalantar yunƙurin raba ta da makamanta, tare kuma da nuna goyan bayan ga gwamnatin Siriya da gwagwarmayar Muslunci gaban Isra'ila, sauran ƙungiyoyin da suke da haɗin gwiwa da Hizbullahi misalin Harkatu Amal da ƙungiyar Kiristoci da kuma sauran ƙungiyoyi daga Jama'at Islami Lubnan, Harkatu Tauhid Islami (Ahlus-Sunna) da ƙungiyar siyasa ta Dimokrat Lubnan(Doruz) suma sun shigo wannan tafiya.[46]
Daidai wannan lokaci an samu ɓullar ƙungiyar 14 Maris tare da goyan bayan ƙasashen Amurka, Faransam Saudi Arabiyya da Misra, sun wannan sabuwar ƙungiya ta gabatar da buƙatar fitar sojojin Siriya daga ƙasar Labanun da kuma raba ƙungiyar Hizbullahi Lubnan da makamanta, Jam'iyyar siyasa ta Almustaƙbal (Ahlus-Sunna), Hizbu Kata'ib da kiristocin sojojin Labanun daga, da jam'iyyar ƴan gurguzu masu son ci gaban Labanun (Doruz) sune asalin ɓangaorin wannan sabuwar ƙungiyar ta 14 Maris.[47]
Ayyukan Zamantakewa
Mafi muhimmancin ayyukan Hizbullahi shi ne mai da hankali kan ƙalubalantar keta alfarmar da Isra'ila take yi, amma tare da haka, wannan ƙungiya ta Hizbullahi ba su ƙasa a gwiwa ba cikin fagen ayyukan raya zamantakewa, ba'ari daga waɗannan ayyuka sun kasance kamar haka:
- Samar da cibiyar jihadin raya gine-gine domin sabunta gine-gine da suka ruguje sakamakon hare-haren haramtacciyar ƙasar Isra'ila,da kuma bala'o'in ɗabi'a daga misalin ambaliyar ruwa da sauransu
- Kwashe shara da ta taru a cikin Bairut da garuruwan geffan Bairut a shekarar 1988-1991 miladiyya
- Samar da ruwan sha a geffan kudancin Bairut
- Raya fannin noma
- Samar da ƙungiyar lafiya ta Muslunci da cibiyoyin kula da lafiya da gina wasu adadin asibitoci
- Gabatar hidimomi na ilimi da taimako ga ɗaliban firamare da sakandire
- Samar da gidauniyar Shahidi domin gabatar da hidimomi ga iyalan shahidai
- Kafa kwamidin agajin tallafin Muslunci domin taimakon talakawa.[48]
- Mu'assasar jin ƙai ta ƙardul hasana tare da taimako ɗaiɗaikun ahalin alheri suna ba da bashi ga masu ƙaramin ƙarfi, wannan cibiya tana da rassa 9 a yankunan daban-daban a ƙasar Labanun. Sojojin Isra'ila a shekarar 2006 miladiyya da gangan sun kai hari kan rassa guda 6 na wannan cibiya tare da lalata su..[49] Amma tare da haka kan asasin rahotan tashar Aljazira, a shekarar 2023 adadin rassan wannan cibiya ya kai 34..[50] Sojojin Isra'ila cikin harin da ta kai a shekarar 2024 kan Labanun ta yi ruwan bamabamai kan wasu adadin daga rassan wannan cibiya.[51]
Kafafen Watsa Labarai
1.Tashar talabijin Al-Manar: An kafa ta shekarar 1991 miladiyya 2.Radiyo Annur (Kafawa a shekarar 1998 miladiyya) 3.Jarida sati-sati ta Al-Ahad.[52] 4.Shafin yanar giza gizo kudancin Labanun 5. Shafin yanar giza gizo na sashen sadarwa na Hizbullahi Har ila yau Hizbullahi ta mayar da ɗaya daga cibiyoyinta a yankin Malita zuwa gidan adana kayan tarihi.[53]
Masu Goyan Baya Da Ƴan Adawa
Hizbullahi tana masoya masu goyan bayanta a duniya, mafi muhimmancin magoyan bayan Hizbullahi, sune Iran da Siriya. Na'am ƙasar Rasha tana ajiye Hizbullahi a matsayin halastacciyar ƙungiyar siyasa da ayyukan raya zamantakewa[54] Iran ta taka muhimmiyar rawa cikin kafa wannan ƙungiya tare da ba ta horo na soja[55] Har ila yau Iran ta samar da hukumar sabunta gine-gine domin sabunta gine-gine da hare-haren ta'addancin Isra'ila suka lalata a Labanun.[56] Tare da haka ƙasar Amurka, ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Larabawa, majalisar aiki tare da juna na ƙasashen Khalij Farsi da…sun shelanta Hizbullahi ko ace ɓangaren ayyukan soja na Hizbullahi matsayin ƴan ta'adda.[57]Amurka tun shekarar 1997 miladiyya ta sanya Hizbullahi cikin jerin ƙungiyoyin ta'addanci..[58] Tsayawa ƙyam da ƙalubalantar mamaya da barazanar Isra'ila da kuma gazawar soji cikin sojojin Labanun kan ƙalubalantar Isra'ila suna daga cikin dalilan masu inkarin ayyana ƙungiyar Hizbullahi a matsayin ƙungiyar ta'addanci, sun yi imani da larurar kasancewar Hizbullahi tare da makamansu.[59]
Nazarin Littafi
An rubuta litattafai daban-daban game da Hizbullahi, daga cikinsu za a iya ishara da littafin "Hizbullahi Al-Minhajil Tajribatil Mustaƙbal Lubnan Wa Muƙawamatihi Fil Wajiha, wanda Na'im Ƙasim ɗaya daga cikin jagororin Hizbullahi ya rubuta. Cikin wannan littafi, ya kawo taƙaitaccen tarihin ƙungiyar, manufofi da ayyuka.[60] wannan littafi an tarjama shi zuwa harshen Farsi da sunan "Hizbullahi Lubnan Khaɗɗi Mashayi, Guzashte Wa Ayandeye An".[61]
| Layi | Suna | Kafawa | Wanda Ya Kafa | Fitattun Mutane | Shugaba | Mazhaba | Tushe | Logo | Kafofin Labarai |
|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
| 1 | Harkatu Amal | 1974m | Imam Musa Sadar | Musɗafa Camaran | Nabihu Birri | Shi'a | Labanun |
|
Tashar Talabijin Ta NBC |
| 2 | Ƙungiyar Jihadul-Islam | 1981m | Fatahi Shaƙaƙi | Ramadan Abdullahi Husam Abu Harbid | Ziyad Nakhala | Ahlus-Sunna | Gaza |
|
Tashar Falasɗinil Yaumi |
| 3 | Hizbullahi Lubnan | 1982m | Sayyid Abbas Musawi Sayyid Hassan Nasrullah | Na'im Ƙasim | Shi'a | Labanun | Example | Tashar Al-Manar | |
| 4 | Failaƙ Badar | 1985m | Adnan Ibrahim Abu Mahadi Al-Muhandis | Hadi Al-Amiri | Shi'a | Iraƙ |
![]() |
Tashar Al-Ghadir | |
| 5 | Hamar (Harkar gwagwarmayar Muslunci) | 1987m | Shaik Ahmad Yasin | Abdul-Aziz Rantisi Isma'il Haniyye | Kwamitin wucin gadi na Hamas | Ahlus-Sunna | Falasɗinu |
|
|
| 6 | Dakarun Ƙudus (Failak Ƙudus) | 1990m | Sayyid Ali Khamna'i | Ahmad Wahidi Ƙasim Sulaimani | Isma'il Ƙa'ani | Shi'a | Iran |
![]() |
|
| 7 | Harkatu Ansarullahi Yaman | 1990m | Husaini Al-Husi | Badrud-Dini Al-Husi | Abdul-Malik Al-Husi | Zaidiyya | Yaman |
|
Shabakatu Al-Masira |
| 8 | Kata'ibu Hizbullahi Iraƙ | 2003m | Abu Mahadi Al-Muhandis | Abu Husaini Humaidawi Abu Baƙir As-sa'idi Arzan Allawi | Ahmad Muhsin Farhi Alhumaidawi | Shi'a | Iraƙ |
|
Shabakatu Al-Ittija |
| 9 | Kata'ibu Sayyidush Shuhada Iraƙ | 2003m | Abu Musɗafa Khazali Haj Abu Yusuf | Abu Ala Al-wala'i | Shi'a | Iraƙ |
|
||
| 10 | Asa'ibu Ahlil Haƙƙi | 200m | Ƙaisu Khazali | Abdul_hadi Addaraji Muhammad Al-bahadili | Ƙaisu Khazali | Shi'a | Iraƙ | Example | Shabakatu Al-Ahad | |
| 11 | Harkatu Nujaba | 2013m | Akram Ka'abi | Abu Isa Iƙlim Mushataƙ Kazim Alhawari | Akram Ka'abi | Shi'a | Iraƙ |
|
|
| 12 | Dakarun Zainabiyyu | 2013m | Wasu jama'a daga Fakistan | Zainab Ali Jafari Aƙid Malik Muɗahhar Husaini | Shi'a | Fakistan |
|
||
| 13 | Dakarun Faɗimiyyun | 2013m | Wasu mutane daga mayaƙan Afganistan | Ali Rida Tawassuli Sayyid Muhammad Husaini Sayyid Ahmad Sadat | Shi'a | Afganistan |
|
||
| 14 | Hashadush Sha'abi | 2014m | Hadi Amiri Abu Mahadi Al-Muhandis | Falihu Fayyaz | Shi'a | Iraƙ |
|
Bayanin kula
- ↑ سپاه و حزبالله لبنان خاطراتی از شیخ علی کورانی، Shafin Magiran.
- ↑ «احمد قصیر آغازگر عملیات شهادتطلبانه در لبنان»، Hukumar Yada Labarai ta Iran.
- ↑ «نحوه شكلگیری حزبالله لبنان از زبان وزیر دفاع»، Kamfanin Dillancin Labarai na IRNA.
- ↑ Naeem Qasim, Hizbullah, 1423 AH, shafi na 22-25
- ↑ Naeem Qasim, Hizbullah, 1423 AH, shafi. 85.
- ↑ Husaini، ««سیر تحول در رهبری و ایدئولوژی حزبالله»».
- ↑ Qasim, Hizbullah, 1423 AH, shafi na 85-86.
- ↑ Qasim, Hizbullah, 1423 AH, shafi na 85-86.
- ↑ «شهادة الأمين العام لحزب الله سماحة السيد حسن نصرالله»، Shafin Al-Manar
- ↑ «إنتخاب سماحة الشيخ نعيم قاسم أمينًا عامًّا لحزب الله»،Al--Manar.
- ↑ «شهادة الأمين العام لحزب الله سماحة السيد حسن نصرالله»Shafin Al-Manar
- ↑ Labaran nazari na Panjehre na mako-mako, fitowa ta 136.
- ↑ زندگینامه شهید سید عباس موسوی، Shafin Shahid Awini.
- ↑ Labaran nazari na Panjehre na mako-mako, fitowa ta 136.
- ↑ Labaran nazari na Panjehre na mako-mako, fitowa ta 136.
- ↑ سایت خبری- تحلیلی عماریون.
- ↑ زندگینامه شهید مغنیه، Kamfanin Dillancin Labarai na Farsi.
- ↑ روایتهایی از ترور بینالمللی عماد مغنیه، Shafin Haj Rezwan.
- ↑ «من هو هاشم صفي الدين.. الخليفة المحتمل لحسن نصر الله؟»، Euronews.
- ↑ «شبيه نصر الله.. هاشم صفي الدين المرشح لقيادة "حزب الله"»، Shafin RT
- ↑ «صهر قاسم سليماني... من هو هاشم صفي الدين أبرز مرشح لخلافة نصر الله؟»، Sharqe Wusta
- ↑ «حزب الله ینعى رئیس مجلسه التنفیذی هاشم صفی الدین»، Tashar Aljazira.
- ↑ «لبنان.. انتشال جثمان هاشم صفي الدين بالمريجة ومعه 23 شخصا»، Al-Hadas.
- ↑ «حزب الله يزف السيد هاشم صفي الدين شهيداً على طريق القدس»، Gidan yanar giza gizo na Al=Manar.
- ↑ «إنتخاب سماحة الشيخ نعيم قاسم أمينًا عامًّا لحزب الله»، Al-Manar.
- ↑ «السیرة الذاتیة»،Gidan yanar gizon Naeem Qassem.
- ↑ «إنتخاب سماحة الشيخ نعيم قاسم أمينًا عامًّا لحزب الله»، Al-Manar.
- ↑ «احمد قصیر آغازگر عملیات شهادتطلبانه در لبنان»، Hukumar Yada Labarai ta Iran.
- ↑ Naeem Qasim, Hizbullah, 1423 AH, shafi. 158.
- ↑ Vioran, "Daste'awardehaye Hizbullah Dar Jange 33 Ruzeh", shafi na 33
- ↑ Naeem Qasim, Hizbullah, 1423 AH, shafi na 161-162.
- ↑ Naeem Qasim, Hizbullah, 1423 AH, shafi na 162-169.
- ↑ Naeem Qasim, Hizbullah, 1423 AH, shafi na 162-169.
- ↑ Naeem Qasim, Hizbullah, 1423 AH, shafi na 204-210.
- ↑ گزارش کامل «عملیات رضوان»، Cikakken gidan yanar gizon Shahid Avini.
- ↑ «۱۰۳۸ عملیات حزب الله علیه صهیونیستها طی ۱۳۳ روز جنگ»، Tashar Al-Alam.
- ↑ «آمار شهدای حزبالله در راه قدس به ۳۱۶ نفر رسید»،Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «Weaponising ordinary devices violates international law: UN rights chief»، business-standard.
- ↑ «شهادة الأمين العام لحزب الله سماحة السيد حسن نصرالله»، Shafin Al-manar
- ↑ «آغاز رسمی آتشبس لبنان: ایران استقبال کرد، اسرائیل نسبت به بازگشت زودهنگام ساکنان هشدار داد»، Kamfanin dillancin labarai na EuroNews.
- ↑ «اسرائیل آتش بس را نقض کرد: دو عضو حزبالله کشته شدند»، Kamfanin Dillancin Labaran Turkiyya Tribune.
- ↑ صور لـ ۹۰ شهیداً من حزبالله سقطوا أثناء القیام بالواجب الجهادی فی سوریـا، Shafin Kudancin Lebanon.
- ↑ مختصات راهبردی اولین تجربه عملیات برون مرزی حزبالله Shafin Masheq.
- ↑ Naeem Qasim, Hizbullah, 1423 AH, shafi na 273-276.
- ↑ ورق زدن تاریخ پرفراز و نشیب احزاب سیاسی لبنان، Kungiyar Matasan 'Yan Jarida.
- ↑ انتخابات داغ در کرانه شرجي مديترانه مروری بر مشخصات احزاب و جریانات سیاسی لبنان، Rah Analytical Cultural Journal.
- ↑ انتخابات داغ در کرانه شرجي مديترانه مروری بر مشخصات احزاب و جریانات سیاسی لبنان،Rah Analytical Cultural Journal.
- ↑ Naeem Qasim, Hizbullah, 1423 AH, shafi na 114-120.
- ↑ «مؤسسة القرض الحسن.. "بنك حزب الله" في لبنان»، Aljazira.
- ↑ «مؤسسة القرض الحسن.. "بنك حزب الله" في لبنان»، Aljazira.
- ↑ «اسرائیل 11 حمله هوایی به بیروت ترتیب داد»، Anadolu Agency.
- ↑ Zamane Mahjub «تأثیر نگرش معنوی بر پیروزی مقاومت حزبالله»، Tushen saa da bayanin Hauza..
- ↑ «حزبالله يفتتح متحفا عسكريا عن مقاومته لاسرائيل في جنوب لبنان»، Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.
- ↑ .ارتباط ایران، روسیه و حزب الله لبنان سرگرمی جدید کنگره آمریکا، ، Kamfanin Dillancin Labarai na Sputnik.
- ↑ ناگفتههایی از تاسیس«مقاومت اسلامی لبنان»،Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
- ↑ فعالیتهای ستاد بازسازی لبنان به قوت قبل ادامه دارد، Kamfanin Dillancin Labarai na dalibai.
- ↑ «آیا حزبالله لبنان یک سازمان تروریستی است؟»، Gidan yanar gizo na BBC Persian..
- ↑ «آیا حزبالله لبنان یک سازمان تروریستی است؟»،Gidan yanar gizo na BBC Persian..
- ↑ «آیا حزبالله لبنان یک سازمان تروریستی است؟»،Gidan yanar gizo na BBC Persian..
- ↑ "Mu'arrifi Fi KItabe Hizbullahi Khadde Mashayi, Guzashte Wa Ayendehaye An, Mu'arrifi Wa nakze", shafi na 24. 115.
- ↑ حزبالله لبنان خط مشی، گذشته و آینده آن،Patuq KItabe Farda
Nassoshi
- ورق زدن تاریخ پرفراز و نشیب احزاب سیاسی لبنان،Kungiyar Matasan Jarida, ranar shigowa: Mayu 10, 1401, kwanan wata ziyara: Mayu 1, 1402.
- «معرفی کتاب حزب الله لبنان، خط مشی، گذشته و آینده آن معرفی و نقد»، Basij Nazarin Dabarun, Na 29, 2005.
- Imam Khumaini, Sahifa na Imam, Tehran, Cibiyar Tattara da Buga Ayyukan Imam Khumaini, 1999.
- Hizbullah Lebanon: Khattae Mashsyi, Guazshte Wa Ayendhaye An, Sheikh Naim Qassem, Muhammad Mahdi ya fassara. Shariatmadar, Tehran, Etelaat Publications, 2004.
- Naeem Qasim, Hizbullah al-Manhaj al-Taqbara al-Mustakbal, Beirut, Dar al-Hadi, 1423 AH/2002.
- انتخابات داغ در کرانه شرجی مديترانه مروری بر مشخصات احزاب و جریانات سیاسی لبنان،Rah Cultural Analytical Journal, fitowa ta 41, Yuni 2009.
- «آیا حزبالله لبنان یک سازمان تروریستی است؟»
- «مصاحبه با حجةالاسلام سید حسن نصرالله عضو شورای مرکزی حزبالله», Pasdar-e-Islam, No. 67, Farvardin 1367.
- «حزبالله يفتتح متحفا عسكريا عن مقاومته لاسرائيل في جنوب لبنان», Reuters, Mayu 22, 2010, shiga Yuni 12, 2021.
- Hosseini, Seyyed Emad, "Sairi Tahawwul Dar Rahbari wa Idiyoloji Hizbullah," Jama'a, No. 48, Yuni 2008.
- زمانیمحجوب، محمود، «تأثیر نگرش معنوی بر پیروزی مقاومت حزبالله»،Ilimi, No. 58, Agusta da Satumba 2013
- «۱۰۳۸ عملیات حزب الله علیه صهیونیستها طی ۱۳۳ روز جنگ», Al-Alam Network, Ranar shigowa: 17 ga Fabrairu 1402, Ranar ziyarta: 18 Oktoba 1403.
- «آمار شهدای حزبالله در راه قدس به ۳۱۶ نفر رسید»، Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, kwanan watan bugawa: Yuni 26, 1403, kwanan wata ziyara: Oktoba 8, 1403.
- «شهادة الأمين العام لحزب الله سماحة السيد حسن نصرالله»، Gidan yanar gizon Al-Manar, kwanan watan bugawa: Satumba 29, 2024, kwanan wata ziyara: Oktoba 9, 2024.
- «حزبالله کشته شدن علی کرکی را تأیید کرد»، Anadolu Agency, kwanan watan bugawa: Satumba 29, 2024, kwanan wata ziyara: Oktoba 9, 2024.
- «سردار نیلفروشان در بیروت به شهادت رسید+بیوگرافی», Kamfanin Dillancin Labarai na Al-Alam, ranar shigarwa: 8 Oktoba 1403, kwanan wata: 8 Oktoba 1403.
- «۱۱ شهید و ۱۰۸ زخمی آمار حملات روز گذشته به ضاحیه جنوبی بیروت»،Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA, ranar shiga: 27 ga Oktoba, 1403, ranar ziyarar: 18 ga Oktoba, 1403.
- «اسرائیل 11 حمله هوایی به بیروت ترتیب داد»،Anadolu Agency, kwanan watan bugawa: Oktoba 21, 2024, kwanan wata ziyara: Oktoba 21, 2024.* «مؤسسة القرض الحسن.. "بنك حزب الله" في لبنان», Al Jazeera, Anadolu Agency, Ranar shigowa: Oktoba 20, 2024, Ranar ziyarar: Oktoba 21, 2024.
- «Weaponising ordinary devices violates international law: UN rights chief»، business-standard.Published: 21 September 2024, Accessed: 9 October 2024











