Musulmi

Daga wikishia

Musulmi (Larabci: المسلم) shi ne mutumin da ya yi Imani da koyarwar Addinin Muslunci sannan kuma yake aiki da koyarwar, a ra'ayin Malaman fiƙihu na shi'a, mutum yana zama Musulmi ta hanyar furta kalmomin Shahada guda biyu sannan yana tafiya ne kan asasin hukunce-hukuncen tsarkin gangar jiki, da kuma mutunta rai da dukiya da mutunci da ingancin Ibada, Imani da Tauhidi da Annabta da Ma'ad (ranar lahira) suna daga aƙidun da dukkanin musulmai suka yi tarayya cikinsu, Sallah, Azumi, Hajji, da ba'arin wasu ayyukan ibada musulmai sun yi tarayya cikin su, Malaman tarihi sun nakalto cewa Hazrat Ali (A.S) da hazrat Khadija (S) sune farkon wanda suka fara muslunta.

Bisa dogara da bayanai da cibiyar bincike ta (PEW) sun bayyana cewa adadin al'ummar musulmai a fadin duniya a shekarar 2015m ya kai kusan mutum bilyan daya da miliyan dari bakwai da hamsin da biyu da dubu ɗari shida da ashirin, sannan addinin muslunci shi ne addini na biyu a yawan mabiya bayan addinin Kiristanci, bisa binciken wannan cibiya kashi biyu cikin uku na Musulmai suna rayuwa ne a yankin Asiya da Akyanusiya (oceania). Musulmi yana nufin wanda ya sallamawa dukkanin umarnin ubangiji, hatta cikin Alkur'ani Kalmar ta zo ne da wannan ma'anar.

Mahalli Da Takaitaccen Tarihi

Addinin muslunci a shekara 610 m, a garin Makka Yankin Jazirar larabawa an aiko Hazrat Muhammad (S.A.W) da Annabta, sannan ana kiran mabiyan sa da sunan Musulmai. [1] an nakalto cewa Hazrat Hazrat Ali (A.S) Imami na farko ga yan shi'a da Hazrat Khadija (A.S) matar Annabi su ne mutane na farko da suka karɓi muslunci. [2] Malamin tarihi Ibn Hisham a cikin littafinsa Siratun Nabawiyya ya nakalto cewa bayan Imam Ali (A.S) akwai mutane misalin Zaidu Bn Harisa,Abukakar Bn Abi Kuhafa, Usman Bn Affan, Sa'ad Bn Abi Wakas, Zubairu Bn Awwam, Abdur-Rahman Bn Aufi, da Dalhatu Bn Ubaidullahi dukkanin sun karɓi Muslunci. [3] Magana ta zo kan taken Musulmi ko muslunci a wasu ba'arin riwayoyin Babukan fikhu [4] galibin su babukan fiƙihu ne misalin, Dahara, Sallah,Zakka,Azumi,Hajji,Jihadi, Kasuwanci, Wakilci,Wasicci,Aure, Farauta da Yanka, Raya Matattu,Haddi, Kisasi. [5] Musulmi shi ne wanda Musulmi suka kubuta daga sharrin harshen sa da hannun sa

Sanin Kalma

gutsiren kyakkyawan zanen rubutun hadisin "Musulmi shi ne wanda mutane suka kubuta daga harshensa da hannunsa.

Larabawan kauye sun ce mun yi Imani ka ce musu baku yi Imani ba sai dai cewa ku ce mun miƙa wuya kuma har yanzu Imani bai shiga zukatan ku ba. [6] Musulmai suna ne ga mutane da suka yi Imani da kowayrwar Muslunci kuma suke aiki da su. [7] wasu Malamai sun tafi kan cewa ana kiran duk mutumin da ya shiga addinin muslunci ya mika wuya ga Annabin Musulunci (S.A.W) da sunan Musulmi. [8] Kalmar Musulmi ta zo cikin Alkur'ani a wurare fiye da guda 40 da ma'ana biyu kebantacciyar ma'ana da gamammiyar ma'ana,[9] ana amfani da ita a kan wanda ya mika wuya ga dukkanin umarnin Ubangiji ya kuma yi Imani da tsantsar Tauhidi kuma bai cudanya da dukkanin Shirka da bautar gumaka ba.[10] ana amfani da Kalmar cikin kebantacciar ma'ana kan mutumin da ya muslunta ya kuma yi Imani da Muhammad (S.A.W) [11] a matsayin bawan sa kuma Manzon sa.

Banbanci Mumini da Musulmi

Template:Ƙuote boɗ Malaman fikhu bisa la'akari da ayoyin. Kur'ani da riwayoyi sun tafi kan cewa akwai banbancin ma'ana tsakanin Mumini da Musulmi [12] da wannan bayani ne ana amfani da Kalmar Mumini a gamammiyar ma'ana ga mutumin da cikin zuciyarsa ya kudurce Imani da dukkanin abin da ya zo daga Annabi (S.A.W) kuma ya furta shi a kan harshensa [13] a daidai lokacin da zama Musulmi ya takaitu da furta kalmar Shahada guda biyu [14] Mumini a kebantacciyar ma'ana a mahangar Malaman shi'a shi ne wanda ya yi Imani da imamanci da wilayar Imaman Shi'a. [15]

Siffofin Musulmi a cikin riwaya

A ba'arin wasu riwayoyi da suka kunshi Aklak, an ambaci wasu siffofi na hakika ga Musulmi. [16] alal misali akwai wata riwaya da aka nakalto ta daga Annabi (S.A.W) Musulmi na hakika shi ne wanda mutane suka kuɓuta daga sharrin harshensa da hannunsa. [17] Imam Ali (A.S) 18 a wata riwaya ya ce hikima mutunci gaskiya da kuma tilawar Alkur'ani, soyayya da kiyayya don Allah, sanin wilayar Ahlil-baiti (A.S) kiyaye hakkokin mutane, kyautata makotantaka da mutane duka wadannan abubuwa suna daga hususiyar Musulmi na hakika [18] Template:Ƙuote boɗ

Asalan addini

Wasu ba'ari daga Asalan Akida da dukkanin musulmai suka yi tarayya cikin su, sune kamar haka:

  • Tauhidi: Asali na tushen Akidar dukkanin Musulmai [19] bisa imanin dukkanin Musulmai Ubangiji shi ne mahalicci duniya kuma bashi da abokin tarayya. [20]
  • Ma'ad: Imani da dawowar rai gangar jiki a ranar Alkiyama da kuma kara dawo da shi a raye domin ya karbi sakamakon ayyukan da yayi a gidan duniya, wanda ya kyautata aiki a saka masa da gidan Aljanna wanda kuma ya munana a kai shi wuta. [21]
  • Annabta: imanin Musulmai da Annabta da farko Magana ce kamar haka: Allah ya zabi Hazrat Muhammad (S.A.W) da Annabta [22] na biyu: an masa Wahayin Alkur'ani daga Allah, [23] na uku: babu wani Annabi da zai zo bayansa. [24]

Ayyukan ibada

Rassan addini Yana daga cikin mafi muhimmancin ayyukan ibada da dukkanin Musulmai suka yi tarayya cikin su, samfurin su shi ne kamar haka:

  • Sallah: Wajibi ce kan dukkanin Musulmai a kowace rana suna sallatar raka'a 17. [25] wannan raka'a guda 17 ana kiran su da sallolin Rana [26] sune kamar haka: raka'a 2 da Sallar Asubahi, raka'a 4 da Azuhur, raka'a 4 La'asar, raka'a 3 Magariba, raka 4 Isha'i, [27]
  • Azumi: wajibi kan dukkanin Musulmai ana yinsa tsawon wata daya a watan Ramadan, ana kamewa daga ci da sha da sauran Abubuwan da suke karya Azumi daga lokacin kiran sallar Asubahi zuwa kiran sallar Magariba. [28]
  • Hajji: dukkanin Musulmi bayan ciki sharudda wajibi yaje aikin Hajji sau daya a tsawon rayuwarsa. [29] Aikin hajji wani aiki ne na ibada da yake kasancewa sau ɗaya a watan Zil Hijja, adadi mai tarin yawa daga Musulmai daga ƙasashe daban-daban suna taruwa domin yin wannan ibada. [30]

Hukunce-hukuncen fiƙihu

Hoton Kur'ani, Littafin Musulmai mai tsarki

A ra'ayin Malaman fiƙihun shi'a, da zarar mutum ya furta Kalmar shahada ko kuma tarjamar ta zai zama Musulmi. [31] Shari'ar muslunci ta sanya wasu kufaifayi ga wanda ya zama Musulmi, sune kamar haka: Imam Sadiƙ (A.S) jini na tsira da muslunci ana kuma sauke amana da shi farji na halasta ta hanyar sa ana kuma samun ladan lahira sakamakon Imani da shi. [32]

  • gangar jikin Musulmi da danshin sa duka tsarkakakku ne. [33]
  • rai da dukiya da mutuncin Musulmi suna da alfarma. [34]
  • wajibi ne Musulmi yayi Kaciya ko da kuwa ya tsufa. [35]
  • kasancewa Musulmi cikin ingancin ibada da ayyukan da ingancinsu ya dogara da niyyar neman kusancin Allah sharadi ne. [36]
  • Aure: tsakanin Musulmai da Kafirai baya inganta [37] mace Musulma baya inganta ta auri Ahlil-kitab. [38]
  • Kafiri bai da wilaya da iko a kan Musulmi, bisa dogara da Ka'idar Nafyul Sabil (kore iko) Allah bai sanya kowanne irin hukunci da zai zama sababi da dalilin da zai sa Kafiri samun iko kan Musulmi. [39]
  • a wurin Malaman fikhun shi'a duk wani Musulmi idan ya yi gangancin fadin cewa ni daga yanzu na bar muslunci ko kuma ya yi inkarin daya daga cikin laruran addini, ko kuma ya yi inkarin daya daga cikin ijma'in Musulmi shi'a da sunna to ya yi ridda kuma za a zartar masa hukucin ridda. [40]

Wurare masu tsarki

Hoton Musulmai masu aikin Hajji a Masallacin Harami

Wasu ba'arin wurare masu tsarki a wurin Musulmai sune kamar haka:

Template:Ƙuote boɗ

Al'ummar Musulmi

Bisa dogara da bayanan cibiyar bincike ta (PEW) adadin al'ummar Musulmi a shekara 2015 ya kai Bilyan daya da milyan dari bakwai da hamsin da biyu da dubu dari shida da ashirin. [48] Addinin da yafi kowanne addini mabiya shi ne bayan Kiristanci shi ne muslunci, [49] Bisa bincken wannan cibiya kusan kashi biyu cikin uku na mabiyan muslunci suna yankin Asiya [50] kan asasin adadin da aka fita a shekarar 2015 m kasashe goma ne suka fi kowa yawan adadin Musulmai. Haka kuma adadin musulman kasar Amrika a shekara 2017 ya kai milyan uku da dubu dari hudu da hamsin, kusan kaso daya da digo daya kenan na al'ummar Amrika. [51] Yankin kasashen Turai adadin Musulmi a kiyasin tsakanin shekara 2010 ya kai kusan milyan sha tara da dubu dari biyar ya tsallaka ya karu zuwa milyan ashirin da biyar da dubu dari takwas a shekarar 2016 kusan ya tsallaka daga kashi takwas da digo uku zuwa kashi tara da digo hudu. [52]

Kididdigar Al'ummar Musulmi
Lamba Ƙasa Adadi Ƙididdigar adadi cikin al'umma Ƙasa
1 Indunusiya 219/960/000 kaso 87 cikin 100
2 Indiya 194/810/000 kaso 14 cikin 100
3 Pakistan 184/000/000 kaso 96 cikin 100
4 Bangaladash 144/810/00 kaso 90/6 cikin 100
5 Najeriya 138/000/000 kaso 60 cikin 100
6 Misra 83/870/000 kaso 95 cikin 100
7 Iran 77/650/000 kaso 99/5 cikin 100
8 Turkiyya 75/460/000 kaso 98 cikin 100
9 Aljaza'ir 37/210/000 kaso 97/9 cikin 100
10 Iraki 36/200/000 kaso 99 cikin 100

Firkoki

Firkokin Shi'a da Ahlus-sunna sune masu mafi yawan mabiya daga kungiyoyin Musulmai, bisa dogara da bayanan cibiyar (PEW) sun fitar bayani cewa yan shi'a sun kashi sha uku cikin kaso dari sannan kaso casa'in cikin dari kuma shi'a. [53] a wani rahoton Shi'a sun hada da Imamiyya Isma'iliyya da Zaidiyya a wannan Zamani sun kai kusan Miliyan 3000

Bayanin kula

  1. Bahramiyan, “Islam”, shafi na 395.
  2. Yaƙoubi, Tarikh Yaƙoubi, Dar Sadir, juzu'i na 2, shafi na 23.
  3. Misali, duba Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyya, Dar Ihya Al-Turath Al-Arabi, juzu'i na 1, shafi na 262-273.
  4. Misali, duba Kulaini, Al-Kafi, 2007, juzu'i na 3, shafi na 68-76.
  5. Muassateh Dairatu Maref Fiƙh Islam, Farhang Fiƙh Farsi, 1385, juzu'i na 1, shafi na 511.
  6. Suratul Hujrat, aya ta 14.
  7. Makonni, Daneshanameh Akwam Musliman, 2003, Mukaddaima, shafi na 2.
  8. Seyyed Sharafuddin,Ayineh Hamzisti Musulmanan, 2014, shafi na 34.
  9. Tabatabai, Al-Mizan, 1393 AH, juzu'i na 18, shafi na 328-329.
  10. Makarem Shirazi, Tafsir Nmuneh, 1374, juzu'i na 2, shafi.703; Mustafavi, Tahaƙiƙ fi Kalemat al-ƙur'an, 1368, juzu'i na 2, shafi na 294-295.
  11. Tabatabai, Al-Mizan, 1393 AH, juzu'i na 18, shafi na 328-329.
  12. Misali, duba Kulaini, Al-Kafi, 2007, juzu'i na 3, shafi na 68-76.
  13. Shahid Sani, Masalik Al-Afham, 1423 AH, juzu'i na 5, shafi na 337.
  14. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 65, shafi na 315.
  15. Shahid Sani, Masalik Al-Afham, 1423 AH, juzu'i na 5, shafi na 338
  16. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 71, shafi na 158-159; Ibn Shuba Harrani, Tohf al-Aƙool, 1404 AH, shafi na 196-197.
  17. Bukhari, Sahihul Bukhari, 1422 AH, juzu'i na 1, shafi na 11; Kilini, Al-Kafi, 2007, juzu'i na 3, shafi na 592.
  18. Ibn Shuba Harrani, Tohf al-Aƙool, 1404 AH, shafi na 196-197.
  19. Yahya, “Sairi mas'ale tauhid dar Alami Islami ta karni haftom Hijiri”, shafi na 196; Safi, Tajalli Tauhid dar Nizameh Imamat, 1392, shafi na 21.
  20. Karimi, Tauhid Az Didgahe Ayat wa Riwayat, 1379, shafi na 19-20.
  21. Alameh Majlisi, Haƙ Al-yaƙin, Intisharat Islami, juzu'i na 2, shafi na 369.
  22. Misali, duba Hilli, Kashf Al-Morad, 1430 AH, shafi na 485-480; Age, Eiji, Sharh Al-Mawakif, 1325 Hijira, juzu'i na 8, shafi na 243-244.
  23. Motahari,Majmu'eh Asar, 2008, juzu'i na 26, shafi 127.
  24. Esƙuii, Nubuwat,1390, shafi na 202-203.
  25. Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 7, shafi na 12.
  26. Mohaghegh Hilli, Shar'i Al-Islam, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 46.
  27. Mohaghegh Hilli, Shara'i al-Islam, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 46.
  28. Mohaghegh Hilli, Shara'i al-Islam, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 139.
  29. Mohaghegh Hilli, Shara'i Al-Islam, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 163; Sheikh Ansari, Kitab al-Hajj, Tarath al-Sheikh al-Azam Ansari, shafi na 6.
  30. Mohaghegh Hilli, Shara'i al-Islam, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 174.
  31. Alameh Majlisi, Bihar al-Anwar, juzu'i na 65, shafi na 315; Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 41, shafi na 630.
  32. Kulaini, Al-Kafi, 2007, juzu'i na 3, shafi na 69.
  33. Dayiratu Maref Fiƙh Islami, Farhang Fiƙh Farsi, 1385, juzu'i na 1, shafi 513
  34. Mohagheƙ Damad,Kawa'id Fikh, 1406 AH, Juzu'i na 1, shafi na 213-214.
  35. Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 31, shafi na 263.
  36. Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 17, shafi na 161.
  37. Shahid Sani, Al-Rawda Al-Bahiya fi Sharh Al-Lama' Al-Damashƙiyyah, 1427 AH, juzu'i na 2, shafi na 412.
  38. Najafi, Jawahirul Kalam, 1362, juzu'i na 30, shafi na 92.
  39. Hosseini, Al-Anawin Al-Fiƙhiyyah, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 350.
  40. Hashemi,Dar Babi TAkfir wa Irtidadi, 1400, shafi na 85.
  41. Kurdi Makki, Kaaba wa Masjid Al-Haram dar Guzare Tarikh, 1378, shafi na 11, gabatarwar littafin.
  42. Tunae, Farhang Nameh Hajji, 2013, shafi na 885-886.
  43. Muassaseh Farhang Honari Mashaar nashar, Masjid Al-Nabi (AS), Mashaar Nashar, shafi na 3..
  44. Muassaseh Farhang Honari Mashaar nashar, Masjid Al-Nabi (AS), Mashaar Nashar, shafi na 3
  45. Musa Ghosheh, Tarihin Majmu'eh Masjid Al-Aƙsa, 1390, shafi na 7.
  46. Hamidi, Tarihin Urushalima, 1381, shafi na 183.
  47. Tonei, Farhanga Nameh Hajji, 2013, shafi na 711-710.
  48. https://www.pewresearch.org/fact-tank/2019/04/01/the-countries-with-the-10-largest-christian-populations-and-the-10-largest-muslim-populations/
  49. https://www.pewresearch.org/fact-tank/2017/01/31/worlds-muslim-population-more-widespread-than-you-might-think/
  50. <a class="eɗternal teɗt" href="https://www.pewresearch.org/fact-tank/2017/01/31/worlds-muslim-population-more-widespread-than-you-might-think/">Desilver, «World's Muslim population more widespread than you might think»، Pew Research Center</a>
  51. <a class="eɗternal teɗt" href="https://www.pewresearch.org/fact-tank/2017/01/31/worlds-muslim-population-more-widespread-than-you-might-think/">Desilver, «World's Muslim population more widespread than you might think»، Pew Research Center</a>
  52. <a class="eɗternal teɗt" href="https://www.pewresearch.org/fact-tank/2018/01/03/new-estimates-show-u-s-muslim-population-continues-to-grow/">Mohamed, New estimates show U.S. Muslim population continues to grow، Pew Research Center</a>
  53. <a class="eɗternal teɗt" href="https://www.pewresearch.org/fact-tank/2017/11/29/5-facts-about-the-muslim-population-in-europe/">Hachett, «5facts about the Muslim population in Europe»، Pew Research Center</a>

Nassoshi

  • Ibn Shuba Harrani, Abu Muhammad Hasan bin Ali, Tohf al-Aƙool, ƙum, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1404H.
  • Ibn Hisham, Abd al-Malik Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyah, Beirut, Dar Ihya al-Tarat al-Arabi, Bita.
  • Pew Religion and Public Life Association, World Population Map, wanda Mahmoud Taghizadeh Davari ya fassara, ƙom, Kimiyyar Shi'a, 2014.
  • Eji, Azad al-Din, Sharh al-Mawakif, ƙum, bugu na farko, 1325H.
  • Biabani Eskoui, Mohammad, Nebuwat, Tehran, Naba Publications, 1390.
  • Tonei, Mojtabi,Farhang Nameh Hajji, Kum, Mashoor Publications, 1390.
  • Bahramian, Ali, "Islam",Daiyreh Maref Buzurg Islami, Volume 8, Tehran, Big Islamic Encyclopedia Center, 1381.
  • Hosseini, Seyed Mir Abdul Fattah, Al-Anawin Al-Fiƙhiyyah, ƙum, Al-Nashar al-Islami Foundation, bugu na biyu, 1417H.
  • Seyyed Sharafuddin, Abdul Hossein, Ayineh Hamzisti Musulmanan, ƙum, Gidan Wallafa na Habib, 2014.
  • Shahid Thani, Zain al-Din bin Ali, al-Rawda al-Bahiya fi Sharh al-Lama' al-Damashƙiya, ƙom, Darul Tafsir, bugu na 7, 1427H.
  • Shahid Thani, Zain al-Din bin Ali, Masalik al-Afham, ƙom, Al-Maarif al-Islamiya Institute, 1423H.
  • Sheikh Ansari, Morteza, Kitab al-Hajj, Kum, Tarath al-Sheikh al-Azam Ansari, Bita.
  • Safi, Lotfollah, tajalli Tauhid dar nezameh Imamat, ƙum, Ofishin Gyara da Buga Hazrat Ayatullahi Safi Golpayegani, 1392.
  • Tabatabaei, Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsir al-ƙur'an, Beirut, Al-Alami Institute for Press, bugu na uku, 1393H.
  • Alameh Majlisi, Mohammad Baƙer, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ahya Trahat Arabi, 1403 AH.
  • Allameh Majlisi, Mohammad Baƙer, Haƙ Al-Yekin, ƙom, Islamia Publications, Beta.
  • Allameh Hilli, Kashf al-Murad fi Sharh Tajrid al-Itƙad, Al-Nashar al-Islami Institute, 1430 AH.
  • Kordi Makki, Mohammad Taher, Kaaba wa Masjid Al-Haram dar Guzare Tarikh, Tehran, Mawallafin Mashaar, bugu na biyu, 1378.
  • Karimi, Jafar, Tauhid Az Didgahe Ayat wa Riwayat (2), Tehran, kare juyin juya halin Musulunci, 1379.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaƙub, Al-Kafi, Kum, Darul Hadith, bugun farko, 1387.
  • Mohaghegh Damad, Seyyed Mostafi, Kawa'id Fikh, Cibiyar Buga Ilimin Kimiyyar Musulunci, bugun 12, 1406H.
  • Mohaghegh Hilli, Jafar bin Al-Hassan, Shara'i' Al-Islam, Tehran, Esteghlal Publications, bugu na biyu, 1409 AH.
  • Mustafavi, Hassan, Tahaƙiƙ fi kalemat Al-ƙur'an, Tehran, Ministry of Culture and Islamic Guidance, bugun farko, 1368.
  • Motahari, Morteza,majmu'eh Asar, ƙom, Sadra Publishing House, 2008.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiya, 1374.
  • Muassaeh Daiyire Maref Fikh Islam, Farhang Fiƙh Farsi, 1385.
  • Najafi, Mohammad Hassan, Jawaher Al-Kalam, Beirut, Farfaɗowar Al'adun Larabawa, bugu na 7, 1362.
  • Weeks, Richard,Daneshnameh Akwam Musliman, Masoumeh Ebrahimi da Peyman Mateen suka fassara, Tehran, Amir Kabir Publishing House, 2003.
  • Hashemi, Seyyed Sadra, dar Babi mas'aleh Takfir wa Irtidad, Tehran, Negah Masares, bugu na farko, 1400.
  • Yahya, Othman bin Ismail, “Sairu mas'aleh tauhid dar Alameh islami Ta karni haftom Hijiri”, wanda Alireza Zakavati Karagzlou ya fassara, a mujallar Maarif, lamba ta 16 da 17, Afrilu da Nuwamba 1368.
  • Yaƙoubi, Ahmed bin Abi Yaƙoob, Tarikh Yakubi, Beirut, Dar Sader, bugu na farko, BTA.

ن اسماعیل، «سیر مسآله توحید در عالم اسلام تا قرن هفتم هجری»، ترجمه علی‌رضا ذکاوتی قراگزلو، در مجله معارف، شماره ۱۶ و ۱۷، فروردین و آبان ۱۳۶۸ش.

  • یعقوبی، احمد بن ابی‌یعقوب، تاریخ الیعقوبی، بیروت، دارصادر، چاپ اول، بی‌تا.

Template:چپ‌چین

Center: 3 January 2018, seen at: 5 February 2022.