Harkatu Ansarullahi Yaman
| Motsi | |
| Suna | Ansarullahi Yaman |
|---|---|
| Jagorori | Husaini Al-Husi, Abdul-Malik Al-Husi |
| Jagora a yanzu | Abdul-Malik Al-Husi |
| Wanda Ya Kafa | Husaini Al-Husi |
| Fitattun Mutane | Muhammad Ali Al-Husi. Muhammad Abdus-Salam. Abdullahi Yahaya Al-Hakim. Muhammad Al-Bakhiti. Mahadi Al-Mashaɗ[Akwai buƙatar kawo madogara] |
| Manufofi | Kafa gwamnatin muslunci |
| Assasawa | Shekarar 1990 miladiyya |
| Mazhaba | Shi'a zaidiyya jarudiyya |
| Shafin Yanar Gizo | پایگاه رسمی انصار الله |
Harkatu Ansarullahi Yaman ko Husawa(Larabci:
أنصار اللّه اليمنية) wani motsi ne na siyasa haɗe da mazhabar zaidiyya a Yaman wanda aka samar da shi a shekarar 1990 miladiyya, wannan motsi ya samu nasarar karɓe cikakken ikon babban birnin ƙasar Yaman da ma wasu sauran garuruwa ƙasar. Ansarullahi sun tasirantu da juyin juya halin Muslunci na Iran da kuma tunanin Imam Khomaini, ana lissafa kafa hukumar Husawa matsayin ci gaba da kuma miƙewar hukumar imamiyya da zaidiyya a ƙasar Yaman, wanda a ƙarni ya samu tun daga ƙarni na uku bayan hijira, sannan kuma fiye da shekara duba ɗaya yana ta bunƙasa da ci gaba da yaɗuwa.
Adawar wannan harka tare da Amurka da ƙawancen daular Yaman da Amurka, ya haifar da rikici tsakaninsu da daular Yaman. Wannan harka a farko-farkon rikicinsu da daular Yaman ta rasa Husaini Al-Husi ɗaya daga cikin manyan jagororinta, tare da farawar farkon farkawar Muslunci, husawa sun samu nasarar kwace ikon San'a babban birnin Yaman, ƙasar Saudi Arabiyya cikin haɗin gwiwar ƙasar Larabawa da take jagoranta domin kwato wuraren da suke ƙarƙashin ikon Harkatu Ansarullahi Yaman, ta dinga kai zafafan hare-haren soja kan wannan harka, sai dai kuma dakiya da tsayuwar wannan harka ya hanama Saudi Arabiyya da ƙawayenta cimma burinsu.
Ansarullahi Cikin amsarsu kan hare-haren Isra'ila kan zirin Gaza da kashe dubban fararen hula Falasɗinawa, su ma Ansarullahi sun kai hare-hare kan mamayayyan garuruwan Falasɗinu, haka nan sun kai hare-hare kan manya-manyan jiragen ruwa na Isra'ila da suke wucewa ta babban kogin Bahar maliya Khalij Aden (Gulf Aden) wannan harka ta an sanya cikin jerin ƙungiyoyin ta'adda a majalisun shura na tsaro na wasu ƙasashen Larabawa da kuma Amurka.
Matsayi Da Halaye
Ansarullahi Yaman wani motsi ne na addini da yake da tsare-tsare na siyasa da aƙida.[1] mazhabar da membobin wannan harka suke imani da ita, ita ce Jarudiyya, ɗaya daga cikin rassan Zaidiyya wace tafi kusanci da Shi'a Isna Ashari.[2] Wannan harka ana lissafa ta matsayin miƙewar hukumar imamiyya a Yaman wace aka kafa ta hannun Yahaya Bin Husaini wanda ake yi wa laƙabi da Alhadi Ilal Haƙƙi (Rasuwa: 298 h, ƙ), kuma fiye da shekaru 1100 da suka wuce ta ci gaba da bunƙasa da yaɗuwa.[3]
Jigon wannan harka, ya kasance wani dandalin al'adu mai suna Shababul Mumin, wanda aka kafa shi shekarar 1990.[4] Bayan shugabancin Husaini Badrud-dini Al-Husi kan wannan dandali, tare da canja suna zuwa dandalin matasa muminai, sun fara ayyukan siyasa.[5] Ayyukan saƙafa da raya al'adu haɗe da ayyukan soja na wannan dandali ya fara haɓɓaka da bunƙasa sosai a tsakanin shekarun 1992-2004 miladiyya.[6] Sakamakon rashin damuwa da kuma bunƙasa yankunan da husawa ke da rinjaye da gwamnati mai ci a wancan lokaci ta nuna, da kuma ƙarfi da tasirin ƙungiyoyin Salafiyya da Wahabiyawa da yaɗa tunaninsu da aƙidunsu a waɗannan yankuna na husawa,[7] ya zama babbar barazana ga husawa, kuma yana ɗaya daga cikin sababi da dalilin kafa wannan harka ta Ansarullahi Yaman. Adadin al'ummar husawa ya kai kaso 40% cikin al'ummar ƙasar Yama[8] Sunan Husi da ake amfani da shi kan wannan harka da motsi kai dama jagororinta, an ciro shin ne daga sunan wani gari da ake kita Hus wanda yake a kudancin jihar Sa'ada ta Yaman.[9]
Tsarin Zubin Hukuma
Tsarin gwamnatin Ansarullahi Yaman an ciro shi ne daga tsarin tafiyar gargajiya na Zaidiyya, hukumar dangi da ba'arin sassan tsarin zirin salon gwamnatin Jamhuriyar Muslunci ta Iran.[10] Ansarullahi Yaman suna da hukumomi guda uku, na gudanarwa, wanda kai tsaye suna ƙarƙashin kulawar jagoran wannan harka:
- Majalisar siyasa: Wata hukuma ce da gudanarwa da tafiyar da alaƙoƙin wannan harka tare da ƙungiyoyi da jam'iyyun siyasa da tawagogin diflomasiyya da hukumomin yankuna, tare da ba da rahoto da kuma yin fashin baƙi kan harkokin siyasa.
- Majalisar zartaswa: Ya ƙunshi ƙungiyoyi masu alaƙa da mutane, misalin ɓangaren al'adu da tarbiyya, sashen zamantakewa, hukumar kafafen sadarwa, harkokin mata da shugabanci.
- Ƙungiyar kwadago ta gwamnati: Aikin kula da tawagar Ansarullahi a ƙungiyoyin zartaswa na majalisar dokoki ana lissafa shi ɗaya daga cikin ayyukan wannan ƙungiya.[11]
Alaƙa Da Iran

Harkatu Ansarullahi Yaman ta yi matuƙar tasirantuwa da Imam Khomaini da juyin juya halin Iran, Husaini Al-Husi ya gabatar da Imam matsayin abin koyi ga al'ummar Yaman.[12] [12] daga tunanin juyin juya halin Muslunci na Iran.[13] Iran ta kasance uwa mai ba da taimako na kuɗi da soja ga Ansarullahi.[14] An ce a lokacin da Badrud-dini yake zaune a Iran, matasan ƙasar Yaman da suke zaune a Iran sun samu tarbiyar ilimi da aƙida da horon soji da tsaro daga Iran.[15]] Masu adawa da Ansarullahi, suna la'akari da wannan harka a matsayin babban dantsen Iran a ƙasar Yaman.[16]
Takunkumi Na Ƙasa Da Ƙasa Da Na Yanki
Wasu adadi daga membobin Ansarullahi Yaman, daga jumlarsu akwai Abdul-Malik Al-Husi, a shekarar 2014 sun shiga sahun mutanen da kwamitin tsaro ta majalisan ɗinkin duniya ta sanya wa takunkumi, kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya a shekarar 2022 miladiyya, ya sanya takumkumi saye da sayar da makami kan Ansarullahi.[17] A wannan shekara dai ministocin ƙasashen Larabawa, suka sanya wannan harka cikin jerin ƙungiyoyin ta'addanci, sauran ƙasasashe misalin Amurka su ma sun shelanta sanya wannan harka cikin layin ƙungiyoyin ta'adda.[18]
Jagororin Harkatu Ansarullahi Yaman

Harkatu Ansarullahi Yaman tun daga fara motsi da yunƙuri har zuwa kafa hukuma, sun yi shuwagabanni daban-daban, za mu yi ishara zuwa ga ba'arinsu:
Husaini Husi
Husaini Al-Husi ɗa ga Badrud-dini Al-Husi,[19] wanda ya kafa wannan harka, kuma farkon shugaba a wannan harka.[20] Husaini Al-Husi ya yi shahada a farko yaƙi da ya faru tsakanin Husawa da daular Yaman a shekarar 2004.[21] Tunaninsa shi ne tsarin aƙidu da ya kafa tubalin akidar ƙungiyar Ansarullah ta Yaman.[22]
Badrud-dini Al-Husi
Badrud-dini Al-Husi ya kasance ɗaya daga cikin maraji'an Zaidiyya; suna la'akari da shi matsayi uba na ruhaniyya ga Harkatu Ansarullahi Yaman.[23] Ya kasance tare da taimakon wasu malamai Yaman sun miƙe tsaye kan yaƙar tasirin tunanin Wahabiyawa a Yaman.[24] Badrud-dini Al-Husi ya kasance mutum da ya tasirantu da tunanin Imam Khomaini da kuma nuna goyan baya ga tsarin juyin juya halin Muslunci na Iran. Sakamakon matsin lamba da kuma barazanar da Wahabiyawa ke yi wa rayuwarsa ya yi tafiya zuwa Iran, tsawon lokaci ya zauna a birnin ƙum mai tsarki. Wannan zama da ya yi a ƙum ya bashi damar sanin Shi'a Isna ashari da kuma juyin juya halin Muslunci.[25]
Abdul-Malik Al-Husi

Abdul-Malik Al-Husi, na uku cikin jerin jagororin Ansarullahi Yama, bayan ɗan uwanSa Husaini da babansa Badrud-dini, ya naɗa shi shugabanci wannan harka.[26] Daidai da rahotonni da aka samu, babansa ne ya zaɓe kan wannan matsayi.[27] Wasu suna ganin ya fara jan ragamar shugabancin wannan harka a shekarar 2010 miladiyya (Shekarar da Badrud-dini ya rasu).[28]] Wasu kuma suna ganin ya fara ne tun a shekarar 2004 miladiyya, (Shekarar da aka kashe Husaini Al-Husi).[29]] Wasu ba'ari kuma sun ce ya fara ne a shekarar 2006 miladiyya.[30]
Nasara kan daular Yaman,[31] Rashin nasarar hare-haren haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa ƙarƙashin jagorancin Saudi Arabiyya,[32]] hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa na Ansarullahi kan Isra'ila da jiragen ruwanta a babban kogin Bahar Maliya da Kogin Aden[33] da yaƙi da Amurka da Ingila a cikin wannan babban kogi, suna cikin jumlolin abubuwan da suka faru a zaman jagorancin Abdul-Malik Al-Husi.[34]
Rigimar Husawa Da Daular Yaman
Jama'ar husawa, suna la'akari da daular Yaman a matsayin ƴan amshin shatan Amurka, sannan suna kakkausan suka kan wannan daula sakamakon talauci da ta haifar cikin ƙasa da kuma ɗanfaruwar ta da ƙasashen waje da jawo su suna tsoma baki cikin lamurran cikin gidan na ƙasar Yaman.[35] Bayan faruwar harin 11 ga watan Satumba a Amurka da kuma harin da ita Amurka ta kai kan Afganistan da Iraƙi da zuwan sojojin ƙasashen waje wannan yanki da Kogin Aden, wannan harka ta tunkari ƙalubalantar manufofin Amurka kai tsaye a wannan yanki.[36] wannan suna ɗaga murya sa sanannen taken harkatu Ansarullahi Yaman wanda ake kira da Sarkha[Tsokaci 1] kan kishiyantar manufofin Amurka da Isra'ila.[37] Ba'arin masu zurfafa bincike sun bayyana cewa daga cikin dalilan da suka haddasa rikici tsakanin daular Yaman da Ansarullahi, har ma ya janyo yaƙi a tsakanin juna, akwai: ambaton taken "Sarkha" (Iho mai ƙarfin gaske) da ya kasance alama ta nuna adawa da Amurka, wanda shugaban gwamnatin Yaman ya yi la'akari da shi a matsayin wani abu da yake shafarshi kai tsaye. ƙaruwar tsanantuwar ayyukan soja na harkar, ƙin ba da amsa kan tambayoyi ko bayyana matsaya daga ɓangaren Husaini Al-Husi game da ayyukan Ansarullahi.[38] Rikici na soja da Ansarullahi take yi da daular Yaman ya jawo afkuwar wasu adadin yaƙoƙi:
- Yaƙi na farko: Yaƙi na farko da gwamnatin ƙasar Yaman ta fara ƙaddamarwa kan harkatu Ansarullahi, ya jawo kashe Husaini Al-Husi. Kashe sojojin gwamnati guda uku, asalin abin da ya jawo wannan yaƙi shi ne yunƙurin kama Husaini Al-Husi. Wannan yaƙi ya afku ne a shekarar 2004 miladiyya a yankin Marran.[39]
- yaƙi na biyu: ƙin yarda a dakatar da rikice-rikice, shi ne sanadiyyar afkuwa yaƙi na biyu a shekarar 2005 miladiyya, wannan yaƙi ya ɗau lokaci har zuwa watanni biyu, daga ƙarshe daular Yaman ta shelanta cin nasara tare da kawo ƙarshen wannan yaƙi, ana la'akari da wannan yaƙi matsayin wanda ya fi yaɗuwa fiye da na farko.[40]
- Yaƙi na uku: Rikice-rikicen da suka rage daga yaƙi na biyu sune suka kasance sababin faruwar yaƙi na uku, wannan yaƙi da ya fara daga ƙarshen shekarar 2005 kuma ya zo ƙarshe a farkon shekarar 2006 miladiyya, ya yaɗu har zuwa birnin Sa'ada.[41]
- Yaƙi na huɗu: Tilastawa Yahudawan garin Sa'ada da kuma yunƙurin kafa gwamnatin shi'anci a wannan birni ta hannun husawa, shi ne sababin afkuwar yaƙi na huɗu, wannan yaƙi da ya fara daga shekarar 2007 miladiyya, yaƙin ya miƙa har zuwa wajen birnin Sa'ada, tare da shika tsakanin ƙasar ƙatar yaƙin ya zo ƙarshe.
- Yaƙi na biyar: An fara wannan yaƙin a shekarar 2008 miladiyya, ya shafi biranen San'a da Amran, shelanta tsagaita wuta daga iya ɓangaren gwamnati mai ci shi ne ya zama sanadiyyar kawo ƙarshen wannan yaƙi,[42]
- Yaƙi na shida: Zargin husawa da satar ƴan ƙasashen waje shi ne sababi faruwar yaƙi na shi a watan Ogusta 2009 miladiyya, tsananta hare-haren jiragen sama da kuma shigar husawa daular Saudi Arabiyya da kashe sojojinta guda biyu, suna daga cikin abubuwan da suka keɓanci wannan yaƙi, fitar husawa daga ƙasar Saudi Arabiyya a shekarar 2010 ne sababin kawo ƙarshen wannan yaƙi.[43]
Farkarwar Muslunci Da Juyin juya halin 2011 Miladiyya
Tare da fara juyin juya halin farkawar Muslunci a wasu ƙasashen muslunci, al'ummar ƙasar Yaman sun yunƙura domin kifar da hukuma mai ci, husawa sun yi amfani da wannan dama.[44] A ƙarshe da wannan sauyi ne husawa a watan Maris 2011 suka samu nasarar karɓe iko a garin Sa'ada, shugabancin wannan birni ya koma hannunsu.[45] Husawa ba su amince da tsarin yarjejeniyar sulhun siyasa ba, haka nan ba su miƙa wuya ga kiraye-kirayen gaggauta yin zaɓen sabon shugaban ƙasa, kuma ba su amince da halascin sabon shugaban ƙasa da aka kawo ba.[46] Husawa bayan sun yi haɗin gwiwa da tsohon shugaban ƙasa Ali Abdullah Salihu, a shekarar 2014 sun samu kwace babban San'a babban birnin ƙasar Yaman, a shekarar 2017 miladiyya ne tsohon shugaban ƙasar Yaman da ya kulla ƙawance da husawa aka same shi da cin amana ta hanyar tattaunawa da haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa ƙarƙashin Saudi Arabiyya da suke yaƙar husawa, sakamakon rikici ɗauke da makamai ne husawa suka kashe Ali Abdullah Salihu.[47]
Rikicin Soja Tare da ƙasashen Waje
Ansarullahi Yaman sun yi yaƙi tare da wasu adadin ƙasashen waje, za mu yi ishara a ƙasa kan wasu ba'ari daga cikin waɗannan ƙasashe:
Harin Saudi Arabiyya Tare da ƙasashen Haɗin Gwiwa Kan Ansarullahi
Mansur Hadi shugaban jamhuriyar Yaman tare da wazirinsa na farko Khalid Bahah sun yi murabus daga muƙamansu.[48]] Bayan nan sai ya tafi Aden ya kafa gwamnatin wucin gadi.A ranar 26 ga watan Maris shekarar 2015 ne haɗin gwiwar ƙasashen wannan yanki ƙarƙashin jagorancin Saudi Arabiyya, domin nuna goyan baya ga Mansur Hadi, suka fara ƙaddamar da zafafan hare-heren jiragen sama da kuma jiragen ruwa kan Yaman, sanadiyyar wannan hari da yawa-yawan cibiyoyin tsaro da gine-ginen ƙarƙashin ƙasa na tsaro da ma wanda ba na tsaro ba, suka lalace suka tashi daga aiki.[49] Manufar wannan hari, shi ne fitar da garuruwa da biranen Yaman daga ƙarƙashin ikon Ansarullahi da kwato makaman gwamnati da suke hannunsu.[50]
Ansarullahi bayan harin sama da haɗin gwiwar ƙasashen yanki suka ƙaddamar kanta, da farko ta fara da himmatuwa kan yankunan Yaman cikin ƙalubalantar ƙungiyar ta'adda ta Alƙa'ida da sojojin ƙawancen haɗin gwiwa ta kuma dawo da ƙarfin ikonta a waɗannan yankuna, bayan wucewa kusan watannin biyu daga harin keta alfarma da haɗin gwiwar ƙasashen wannan yanki da jagorancin Saudi Arabiyya, Ansarullahi ta ƙaddama da wasu adadin hare-hare kan Saudi Arabiyya, tare da faɗaɗuwar hare-haren haɗin gwiwa, Ansarullahi Yaman da manufar tsagaita wuta, ta yi amfani makami mai linzami samfurin balistik kan ƙasar Saudi Arabiyya.[51] Husawa sun kai hare-hare da dama kan wuraren soji da tashoshin man fetur na Saudi Arabiyya ta hanyar harba makamai masu linzami samfuran balistik da kuma jiragen yaƙi marasa matuƙi.[52]
Kai Hare-hare Kan Isra'ila da Jirangen Ruwanta Cikin Martani Kan Ruwan Bama-bamai Da Take Yi A Gaza
Harkatu Ansarullahi Yaman cikin nuna goyan baya ga mutanen Gaza gaban hare-haren Isra'ila, ta maida zazzafan martani kan Isr'aila ta hanyar kai hare-hare da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi kan garuruwan Falasɗinawa da ta mamaye.[53] Husawa sun dinga kai hare-hare kan jirage Isra'ila da ma jiragen da suka nufi tashoshin jiragen ruwa na Isra'ila daga kogin Bahar Maliya da kogin Aden.[54] Amurka da Ingila su ma sun ƙaddamar da wasu adadin hare-hare kan Ansarullahi, a rahotan wasu jaridun yamma wannan hare-hare na Ingila da Amurka ba su iya takawa husawa birki ba.[55] Wannan mataki da Ansarullahi suka ɗauka cikin martani kan hare-haren da Isra'ila take yi a kan fararen hula, da gine-gine gidaje kai har ma asibitoci da cibiyoyin lafiya ba su tsira ba a Gaza[56]] Hare-haren Isra'aila kan Gaza ya biyo bayan ofireshin da Hamas ta ƙaddamar kan Isra'ila a watan Oktoba shekarar 2023, wanda ake kira da suna Tufanul Al-aksa.[57]
| Layi | Suna | Kafawa | Wanda Ya Kafa | Fitattun Mutane | Shugaba | Mazhaba | Tushe | Logo | Kafofin Labarai |
|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
| 1 | Harkatu Amal | 1974m | Imam Musa Sadar | Musɗafa Camaran | Nabihu Birri | Shi'a | Labanun |
|
Tashar Talabijin Ta NBC |
| 2 | Ƙungiyar Jihadul-Islam | 1981m | Fatahi Shaƙaƙi | Ramadan Abdullahi Husam Abu Harbid | Ziyad Nakhala | Ahlus-Sunna | Gaza |
|
Tashar Falasɗinil Yaumi |
| 3 | Hizbullahi Lubnan | 1982m | Sayyid Abbas Musawi Sayyid Hassan Nasrullah | Na'im Ƙasim | Shi'a | Labanun | Example | Tashar Al-Manar | |
| 4 | Failaƙ Badar | 1985m | Adnan Ibrahim Abu Mahadi Al-Muhandis | Hadi Al-Amiri | Shi'a | Iraƙ |
![]() |
Tashar Al-Ghadir | |
| 5 | Hamar (Harkar gwagwarmayar Muslunci) | 1987m | Shaik Ahmad Yasin | Abdul-Aziz Rantisi Isma'il Haniyye | Kwamitin wucin gadi na Hamas | Ahlus-Sunna | Falasɗinu |
|
|
| 6 | Dakarun Ƙudus (Failak Ƙudus) | 1990m | Sayyid Ali Khamna'i | Ahmad Wahidi Ƙasim Sulaimani | Isma'il Ƙa'ani | Shi'a | Iran |
![]() |
|
| 7 | Harkatu Ansarullahi Yaman | 1990m | Husaini Al-Husi | Badrud-Dini Al-Husi | Abdul-Malik Al-Husi | Zaidiyya | Yaman |
|
Shabakatu Al-Masira |
| 8 | Kata'ibu Hizbullahi Iraƙ | 2003m | Abu Mahadi Al-Muhandis | Abu Husaini Humaidawi Abu Baƙir As-sa'idi Arzan Allawi | Ahmad Muhsin Farhi Alhumaidawi | Shi'a | Iraƙ |
|
Shabakatu Al-Ittija |
| 9 | Kata'ibu Sayyidush Shuhada Iraƙ | 2003m | Abu Musɗafa Khazali Haj Abu Yusuf | Abu Ala Al-wala'i | Shi'a | Iraƙ |
|
||
| 10 | Asa'ibu Ahlil Haƙƙi | 200m | Ƙaisu Khazali | Abdul_hadi Addaraji Muhammad Al-bahadili | Ƙaisu Khazali | Shi'a | Iraƙ | Example | Shabakatu Al-Ahad | |
| 11 | Harkatu Nujaba | 2013m | Akram Ka'abi | Abu Isa Iƙlim Mushataƙ Kazim Alhawari | Akram Ka'abi | Shi'a | Iraƙ |
|
|
| 12 | Dakarun Zainabiyyu | 2013m | Wasu jama'a daga Fakistan | Zainab Ali Jafari Aƙid Malik Muɗahhar Husaini | Shi'a | Fakistan |
|
||
| 13 | Dakarun Faɗimiyyun | 2013m | Wasu mutane daga mayaƙan Afganistan | Ali Rida Tawassuli Sayyid Muhammad Husaini Sayyid Ahmad Sadat | Shi'a | Afganistan |
|
||
| 14 | Hashadush Sha'abi | 2014m | Hadi Amiri Abu Mahadi Al-Muhandis | Falihu Fayyaz | Shi'a | Iraƙ |
|
Bayanin kula
- ↑ Seyyed Kamel, "Alwujud Al-husi fil Yaman: Dirasa Fil Jografiya Assiyasiyya," shafi. 19.
- ↑ Seyyed Kamel, "Alwujud Al-husi fil Yaman: Dirasa Fil Jografiya Assiyasiyya," shafi. 19.
- ↑ Alkazi، «الحوثیین من الداخل.. ما لاتعرفه عنهم»،Gidan yanar gizo na gidan labarai na Al Jazeera.
- ↑ «محمد یحیی عزان.. تنظیم شباب المؤمن بالیمن»، Gidan yanar gizo na gidan labarai na Al Jazeera..
- ↑ Ahmadi, Al-Zahr da Al-Hajr: Al-Tamaruddi al-Shi'i Fil yaman, 2007, shafi na. 130
- ↑ Fa'aliyat Farhangi In Guruhi Baina Salhaye1992 Ta 2004, Tashdid Fa'aliyat Nizami An Agaz Gerdid.
- ↑ «الحوثیون من هم و کیف نشأت حرکتهم»، Gidan yanar gizon BBC Hausa.
- ↑ Muhammadلظاهرة الحوثیه و التحول الفکری من الزیدیه الی الشیعه»،Shafin Al-Qanatir.
- ↑ Muhammadلظاهرة الحوثیه و التحول الفکری من الزیدیه الی الشیعه»، وبگاه القناطیر.
- ↑ «جماعة الحوثیین.. حرکة یمنیه جمعت بین الزیدیه و النهج الایرانی و الحکم العائلی»Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network.
- ↑ «جماعة الحوثیین.. حرکة یمنیه جمعت بین الزیدیه و النهج الایرانی و الحکم العائلیGidan yanar gizon Al Jazeera News Network
- ↑ «دوافع مساندة ایران للحوثیین فی الیمن»،Dandalin Larabawa don nazarin manufofin Iran.
- ↑ «الحوثییون من هم و کیف نشأت حرکتهم», Gidan yanar gizon BBC Hausa.
- ↑ «کیف و متی بدأت علاقة ایران بمیلیشیات الحوثی فی الیمن»، Shafin yanar gizo na Al Arabiya News Network.
- ↑ «دوافع مساندة ایران للحوثیین فی الیمن», Dandalin Al-Arabi don nazarin siyasar Iran.
- ↑ «کیف و متی بدأت علاقة ایران بمیلیشیات الحوثی فی الیمن»، Shafin yanar gizo na Al Arabiya News Network.
- ↑ «جماعة الحوثیین.. حرکة یمنیه جمعت بین الزیدیه و النهج الایرانی و الحکم العائلی» Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network.
- ↑ «جماعة الحوثیین.. حرکة یمنیه جمعت بین الزیدیه و النهج الایرانی و الحکم العائلی» Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network.
- ↑ «حسین الحوثی... من الدعوه الی التمرد»"Shafin yanar gizon Al Jazeera News Network".
- ↑ Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullah Yemen, 2014, shafi. 45
- ↑ «السید حسین بدرالدین الحوثی من الولاده.. الی معراج الشهاده»،Ansarullah website.
- ↑ Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullah Yemen, 2014, shafi. 245
- ↑ Ahmadi, Al-Zahr da Al-Hajr: Al-Tamard Al-Shi'i Fil Yaman, 2007 AD, shafi. 129.
- ↑ «العلامة الربانی بدرالدین الحوثی.. حائط صد امام التکفیریین»،Ansarullah website.
- ↑ Janbashe Ansarullah, shafi na 76-79
- ↑ «عبدالملک الحوثی..من متمرد من الاقالیم الی زعیم وطنی»،Gidan yanar gizon kamfanin dillancin labarai na Reuters.
- ↑ «عبدالملک الحوثی»، Gidan yanar gizo na gidan labarai na Al Jazeera.
- ↑ «عبدالملک الحوثی»،Gidan yanar gizo na Nashru.
- ↑ «عبدالملک الحوثی.. المرشد الاعلی فی الیمن»، Shafin Harka Islamiyya.
- ↑ «حقائق لا تعرفها عن عبدالملک الحوثی»،Gidan yanar gizon Mujallar Wase Sadrak.
- ↑ «عبدالملک الحوثی من زعیم المتمردین الی صانع الملوک»، Gidan yanar gizon labarai na Noon Post.
- ↑ «حقائق لا تعرفها عن عبدالملک الحوثی»، Yanar Gizon Mujallar Wase Sadrak.
- ↑ «السید الحوثی: نرصد السفن الاسرائیلیه فی البحر الاحمر.. سنظفربها و سنستهدفها»، وبگاه شبکه خبری المیادین؛ «راز مقاومت و شکستناپذیری رهبر انصارالله یمن چیست؟»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
- ↑ «الضربات الامریکیه و البریطانیه تفشل فی الحد من هجمات الحوثیین», Gidan yanar gizon BBC Hausa.
- ↑ Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullahi Yemen, 2014, shafi na 153-154.
- ↑ Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullah Yemen, shafi. 243.
- ↑ Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullahi Yemen, 2014, shafi na 153
- ↑ Ahmadi, Al-Zahr da Al-Hijr: Al-Tamaruddush Shia'i Fil Yaman, 2007, shafi na 140-142.
- ↑ Seyyed Kamel, "Alwujud Al-husi Fil Yaman: dirasa Fil Jografiya Assiyasiyya," shafi. 22.
- ↑ Seyyed Kamel, "Alwujud Al-husi Fil Yaman: dirasa Fil Jografiya Assiyasiyya," shafi. 23.
- ↑ Seyyed Kamel, "Alwujud Al-husi Fil Yaman: dirasa Fil Jografiya Assiyasiyya," shafi. 23-24.
- ↑ Seyyed Kamel, "Alwujud Al-husi Fil Yaman: dirasa Fil Jografiya Assiyasiyya," shafi. 24.
- ↑ Seyyed Kamel, "Alwujud Al-husi Fil Yaman: dirasa Fil Jografiya Assiyasiyya," shafi. 24-25.
- ↑ Seyyed Kamel, "Alwujud Al-husi Fil Yaman: dirasa Fil Jografiya Assiyasiyya," shafi. 27.Muhammad, "Zahiraul Husiya Wat tahawwul Fikri Min Zaidiyya Ila Tashayyu," shafi. 75.
- ↑ Muhammad, "Zahiraul Husiya Wat tahawwul Fikri Min Zaidiyya Ila Tashayyu," shafi. 75.Seyyed Kamel, "Alwujud Al-husi Fil Yaman: dirasa Fil Jografiya Assiyasiyya," shafi. 27
- ↑ Seyyed Kamel, "Alwujud Al-husi Fil Yaman: dirasa Fil Jografiya Assiyasiyya," shafi. 27
- ↑ «جماعة الحوثیین.. حرکة یمنیه جمعت بین الزیدیه و النهج الایرانی و الحکم العائلی» Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network.
- ↑ «رئیس جمهور یمن استعفای خود را اعلام کرد»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ خبرگزاری فارس
- ↑ Seyyed Kamel, "Alwujud Al-husi Fil Yaman: dirasa Fil Jografiya Assiyasiyya," shafi. 31
- ↑ «انصارالله برای اولین بار با موشک بالستیک قاهر به عربستان حمله کرد.»،Yanar Gizon Jaridar Kayhan.
- ↑ «ابرز هجمات الحوثیین علی السعودیه»، Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network.
- ↑ «الحوثییون من هم و کیف نشأت حرکتهم»، Gidan yanar gizon BBC Hausa.
- ↑ «الضربات الامریکیه و البریطانیه تفشل فی الحد من هجمات الحوثیین»،Gidan yanar gizon BBC Hausa.
- ↑ «الضربات الامریکیه و البریطانیه تفشل فی الحد من هجمات الحوثیین»،Gidan yanar gizon BBC Hausa.
- ↑ «دهمین روز از عملیات طوفان الاقصیٰ»،Shafin yanar gizo na Al Alam News Network.
- ↑ «دهمین روز از عملیات طوفان الاقصیٰ», Shafin Al-Alam News Network.
Nassoshi
- «دواقع مساندة ایران للحوثیین فی الیمن»،Dandalin Larabawa don nazarin gidan yanar gizon siyasar Iran, ranar shiga: Nuwamba 1, 2019, ranar ziyarar: Fabrairu 24, 2023.
- «حسین الحوثی... من الدعوه الی التمرد»،Gidan yanar gizon Aljazeera News Network”, kwanan shigarwa: Oktoba 4, 2004, kwanan wata ziyara: Fabrairu 18, 2003.
- «جماعة الحوثیین.. حرکة یمینه جمعت بین الزیدیه و النهج الایرانی و الحکم العائلی», Gidan Yanar Gizon Labarai na Al Jazeera, kwanan shiga: 18 Disamba 1402, kwanan wata ziyara: 15 Fabrairu 1402.
- «ابرز هجمات الحوثیین علی السعودیه»،Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network, ranar aikawa: Mayu 14, 2019, kwanan wata ziyara: Maris 2, 2023.
- «محمد یحیی عزان.. تنظیم شباب المؤمن بالیمن»، وبگاه شبکه خبری الجزیره، تاریخ درج مطلب: ۲۱ فروردین ۱۳۸۶ش، تاریخ بازدید: ۲۱ بهمن ۱۴۰۲ش.
- «کیف و متی بدأت علاقة ایران بمیلیشیات الحوثی فی الیمن»،Shafin yanar gizo na Al-Arabiya News Network, ranar shigarwa: Janairu 5, 2017, ranar ziyarar: 14 ga Fabrairu, 2023.
- «دهمین روز از عملیات "طوفان الاقصیٰ"»، Shafin yanar gizo na Al-Alam News Network, kwanan wata: 14 ga Oktoba, 1402, kwanan wata: 24 ga Fabrairu, 1402 (Asabar).
- «من هم الحوثیون», Gidan yanar gizon Mesbar, kwanan watan shigarwa: Disamba 1, 1402, kwanan wata: Fabrairu 1, 1402.
- «رئیس جمهور یمن استعفای خود را اعلام کرد»، Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, ranar shigarwa: Fabrairu 2, 2014, kwanan wata ziyara: Fabrairu 23, 2023.
- «حقائق لا تعرفها عن عبدالملک الحوثی», Gidan yanar gizon Mujallar Vasay Sadrak, ranar shigarwa: Yuli 1, 2019, kwanan wata ziyara: Janairu 15, 2023.
- «السید الحوثی: نرصد السفن الاسرائیلیه فی البحر الاحمر.. سنظفربها و سنستهدفها»،Shafin yanar gizo na Al-Mayadeen News Network, kwanan wata: 13 ga Disamba, 1402, kwanan wata: Fabrairu 2, 1402.
- «السید حسین بدرالدین الحوثی من الولاده.. الی معراج الشهاده»،Gidan yanar gizon Ansarullah, kwanan watan shiga: 14 ga Maris, 1402, kwanan wata: 18 ga Fabrairu, 1403.
- «العلامة الربانی بدرالدین الحوثی.. حائط صد امام التکفیریین», Gidan yanar gizon Ansarullah, kwanan watan shiga: 29 ga Yuli, 1402, kwanan wata: Janairu 17, 1402.
- «الضربات الامریکیه و البریطانیه تفشل فی الحد من هجمات الحوثیین»،Gidan yanar sadarwa na BBC News, kwanan watan shiga: Fabrairu 14, 1402, ranar ziyarta: Fabrairu 23, 1402.
- «الحوثییون من هم و کیف نشأت حرکتهم», Gidan Yanar Gizo na BBC News Network, ranar shiga: Yuli 17, 1402, kwanan wata: 14 ga Fabrairu, 1402.
- «عبدالملک الحوثی من زعیم المتمردین الی صانع الملوک»،Gidan yanar gizon labarai na Noon Post, ranar shigarwa: Janairu 21, 2014, kwanan wata ziyara: Janairu 21, 2023.
- Ansarullah ya kai wa Saudiyya hari a karon farko da makami mai linzami na Qaher, gidan yanar gizo na jaridar Kayhan, ranar shigowa: Disamba 12, 2015, ranar ziyarar: 2 ga Maris, 2023.
Alkazi Muhammad «الحوثیین من الداخل.. ما لاتعرفه عنهم», Gidan Yanar Gizon Labarai na Al Jazeera, kwanan shiga: 16 Fabrairu 1402, kwanan wata ziyara: 18 Fabrairu 1402.
- Sayyid Kamel, Anwar,«الوجود الحوثي في اليمن : دراسة في الجغرافيا السياسية»،A cikin mujallar Cibiyar Bincike da Lexicography (Misira), No. 567, 2017.
- Sheikh Husseini, Mukhtar, Janbashe Ansarullah, Yemen, Qum, Majalisar Duniya ta Ahlul Baiti (AS), bugu na farko, 2014.* محمد، ابراهیم، «الظاهرة الحوثیه و التحول الفکری من الزیدیه الی الشیعه»Mujallar Al-Qunatir, Juzu'i na 23, Lamba 1, Yuli 2021.
- «راز مقاومت و شکستناپذیری رهبر انصارالله یمن چیست؟»،Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, kwanan watan shigarwa: 12 Janairu 1402, kwanan wata ziyara: 13 Janairu 1402.











