Kisan Kiyashi da ya Faru a Asibitin Alma'amadani

Daga wikishia

Kisan kiyashi kan Fararen Hula a Asibitin Ma’amadani, (Larabci: مجزرة مستشفى المعمداني) Hari ne da Isra’ila ta kai kan Falastsinawa a Asibiti A Zirin Gaza a 17 ga watan Oktoba shekara ta 2023 wannan Hari yayi Sanadiyar Mutuwar Fiye da Mutane 500.

Kisan Fararen Hula

Haramtacciyar Kasar Isra’ila a ranar 17 ga watan Oktoba 2023 ta kai Harin cin Zali kan Masu Rauna wadanda suke cikin Ciwo da wadanda suke fake cikin Asibitin Ma’amadani ko kuma muce Mutanen Gaza da suka fake wannan Asibiti, wannan Hari na cin zali yayi sanadiyar mutuwar fiye da Fararen Hula 500 [1] a wani Rahoton an bayyana adadin wanda suka mutu ya kai 800, [2] ko 1000, [3] a cewa Mai Magana da yawun Ma’aikatar lafiya ta Falastinu a Gaza akasarin wadanda wannan hari ya halaka Mata ne da Kananan yara [4] Tashoshin Yada Labarai sun bayyana wannan Harin Zalunci a Matsayin hakikanin Kisan Kiyashi da kisan Kare Dangi. [5] Manufar wannan Harin cin Zali shine Tilastawa Mutane Gaza Barin Garinsu da yin Hijira da Tilashi, Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai wannan Hari ne matsayin ramuwar Gayya kan harin da Kungiyar Gwagwarmayar Hamas ta kai Kansu wanda ake kiransa da Tufanul Al-Aksa wanda ya kasance a 7 ga watan Oktoba, wani hari ne da Hamas ta kai domin `yanto Falastinu daga mamayar Haramtacciyar kasar Isra’ila, Kamfanin yada labarai ta Roterz ta bayyyana cewa harin da Haramtacciyar Kasar Isra’aila ta kai kan Asibitin Ma’amadani shine Hari mafi muni da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta taba kaiwa kan Asibiti wanda ta yi shi matsayin Ramuwar Gayya kan Hari da Hamas ta kai kanta me suna Tufanul Al-Aksa [6] Masu Fashin Baki kan Al’amuran Gabas ta Tsakiya sun bayyana cewa Haramtacciyar Kasar Isra’ila ba za su iya gyara Kashi da suka sha a hannun Hamas ba da wannan Hari da suka kai kan Asibitin Ma’amadani.

Martani

Ganawa da ma'aikatan Asibit tare da `yan jarida a tsakiyar gawarwaki

Ganawar yan Jarida tare da Ma’aikatar lafiya ta Falastsinu cikin tsakiyar Gawawwakin Harin Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila kan Asibitin Ma’amadani Zirin Gaza. Antoniyo Goutresh Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana kasha Fararen Hula sakamakon Harin Ta’addanci da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai matsayin Abu Mai Matukar tayar da hankali sannan yayi Allawadai da shi [7] Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin zai yi zaman Gaggawa don yin bincike kan wannan Harin ta’addanci [8] kasar Rasha ta kira wannan Hari da Mummunan lefi na Rashin Tausayi da Yan Adamtaka [9]

Zanga-Zanga Allawadai kan Harin Ta’addanci daga Sassa daban-daban na Duniya

Kan asasin Rahotan Kamfanin Dillancin labarai na Roterz bisa Martanin Mutane daga kasashe daban-daban na Duniya daga na Musulmai da wanda ba na Musulmai ba dukkaninsu sun fito Kan Tituna suna Zanga-Zangar kan Nuna rashin yarda da wannan ta’addanci [10] a Kasar Jodan Fusatattun Masu Zanga-Zanga sun bankawa Ofishin Jakadancin Isra’ila Wuta [11] da yawan kasashen Duniya daga Faransa, Saudi Arabiya, Qatar,Sipaniya, Turkiyya, , duka sun yi Tofin Alatsine da Allawadai da wannan Ta’addanci na Haramtacciyar Kasar Isra’ila [12] Masu Zanga-Zanga sun nemi Kasashen Musulmi da su yi raddi da martani kan wannan Hari na Ta’addanci don nuna goyan bayansu ga Falastsinu. Hauzozin IlimiA Iran Sun sanar dagatar da Karatu na kwana daya don Alhini da Zaman Makoki kan wannan Hari na Ta’addanci Duka cikin Allawadai da Alhini da zaman Makokin kan kisan Raunana marasa mafaka Kasar Iran ta bada hutun kwana [13] daya, Kasar Irak da [14]Siriya [15] sun bada hutun Kwanaki uku, a Kasar Iran domin nuna jimami an canja Kalar Tutar Hasumiyar Haramin Imam Rida (A.S) [16] haka kuma baki dayan Hauzozin Ilimi na Kasar Iran [17] da Hauzar Ilimi ta Najaf [18] sun dagatar da karatu, a Birnin Qum Dalibai da Malamai sun shiga Zanga-Zangar Allawadai da Haramtacciyar Kasar Isra’ila [19] Ayatullahi Nuri Hamadani daya daga cikin Maraji’an Taklidi da yake zaune a birnin Qum cikin Sakon da ya aika kan Allawadai da wannan Harin Ta’addanci ya bukaci Al’ummar Musulmi da mutanen Iran da kada su kasa a gwiwa cikin bada dukkanin Taimakon da ya dace ga Al’ummar Gaza.

Korar Jakadun Isra’ila daga Kasashen Musulmi

Kasar Kolombiya cikin Martaninta kan wannan Hari na Ta’addanci ta yanke Alakar Diflomaisiyya da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kuma Kori Jakadan Isra’ila daga kasarta [20] haka kuma Ministan Harkokin Waji na Iran cikin ganawarsa tareda Babban Sakataren Kungiyar Aiki da juna ta Muslunci ya bukaci Korar Jakadun Haramtacciyar Kasar Isra’ila daga kasashen Musulmi da kuma haramta sayen kayayyakinsu da dagatar da sayar Musu da Dnayen Man Fetur [21]

Soke Zama Tsakanin Shugaban Kasar Amerika tare da Shugabannin Kasashen larabawa

Kan asasin rahoton Tashar Tauraron `dan Adam ta Aljazeera, bisa ittifain da akai za a yi zama tsakanin Shugaban Kasar Amerika Joe Biden da Shugaban Kasar Misra da Kuma Shugaban Kungiyoytin Sakai na Falastsinawa za a yi wannan zaman ne a Kasar Jodan [22]

Amfani da Bomb Kirar Amerika

Kan asasin Rahotan Tashoshin Labarai da suka nakalto daga Jaridar Wall-Street Amerika, a wannan Hari Isra’ila ta yi amfani ne da Bomb MK-84 kirar Amerika, [23] a gefe guda Amerika sun da’awar cewa tarwatsewar Asibitin Ma’amadani ta faru ne sakamakon fashewar wani Makami Mai Linzami bisa Kuskure na Kungiyar Gwagwarmayar [24] Sai dai kuma Ƙungiyar-Jihadul Islam ta yi watsi da wannan tuhuma ta Amerika mara tushe tare kuma da nesanta kanta daga wannan tuhuma, kuma sun tabbatar da cewa wannan ba aiki kowa bane sai Haramtacciyar Kasar Isra’ila wacce tun kafin harin ta yi kira da Mutanen kan Asibitin Ma’amadani da sauran Asibitocin Zirin Gaza da su fita daga cikin Asibitocin ko kuma da dakarkaresu da Bomb, haka kuma Rahotanninsu masu karo da juna kan wannan Hari suna kara tabbbatar da karyarsu [25] a nakalin Tashar (NBC) sun bayyana cewa Palastsinawa basu da Karfaffan Makami irin wannan da zai darkake Asibiti Haka, dama can Haramtacciyar kasar Isra’ala Kasa ce da ta shahara da sharara karya da aikata miyagun Lefuka da kuma dora tuhuma kan wasu daban https://www.nytimes.com/live/2023/10/17/world/gaza-news-israel-hamas-war haka kuma na nakalto daga Tashar watsa labarai ta BBC bisa la’aka da karfin Makamin zai wahala mu ce ba Makamin isra’ila bane [26]

Bayanin kula

1. https://www.aljazeera.com/news/2023/10/18/what-do-we-know-about-the-strike-on-the-hospital-in-gaza
2. class="external text" href="https://www.mehrnews.com/news/5914565">بیش از ۸۰۰ شهید در بمباران بیمارستان المعمدانی غزه
3. a class="external text" href="https://www.farsnews.ir/news/14020725001268">چهارشنبه در سراسر کشور عزای عمومی است
4. a class="external text" href="https://fa.alalam.ir/news/6727963">وزارت بهداشت غزه: اغلب قربابیان فاجعه بیمارستان المعمدانی زن و کودک هستند
5. هولوکاست واقعی این تصویر است
6. Dubi "Taron yaye daliban jami'o'in sojojin kasa na hadin gwiwa", ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
7. https://www.reuters.com/world/middle-east/quote-box-israeli-air-strike-hits-gaza-hospital-hundreds-dead-2023-10-17/
8. «فاجعه بمباران و کشتار بیمارستان المعمدانی غزه؛ علل و اهداف؟»
9. "Taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan harin bam a asibitin Gaza", DW.
10. "Taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan harin bam a asibitin Gaza", DW.
11. مسکو: حمله به بیمارستان غزه جنایت است
12. https://www.reuters.com/world/middle-east/quote-box-israeli-air-strike-hits-gaza-hospital-hundreds-dead-2023-10-17/
13. آتش زدن سفارت رژیم صهیونیستی در اردن
14. محکومیت گسترده بمباران بیمارستان معمدانی در غزه
15. اعلام عزای عمومی در سراسر کشور
16. لحظه به لحظه با دوازدهمین روز عملیات طوفان الاقصی
17. سوریه سه روز عزای عمومی اعلام کرد
18. "An daga tutar makoki a kan kubbar haramin Razavi", kamfanin dillancin labarai na IRNA.
19. تعطیلی درس‌های حوزه علمیه در واکنش به حمله وحشیانه به بیمارستان در غزه
20. لحوزة العلمية في النجف تعلن الحداد وتعطل دروسها
21. «عکس/ راهپیمایی طلاب قم در محکومیت حمله به بیمارستان غزه»، مشرق نیوز.
22. «کلمبیا سفیر رژیم اسرائیل را اخراج کرد»
23. "Amir Abdullahian: Muna bukatar gaggauta kauracewa gwamnatin sahyoniyawan da kasashen musulmi suke yi," in ji kamfanin dillancin labaran IRNA.
24. "Lardan ya soke taron koli na hanyoyi hudu da Biden, Wal-Sisi da Abbas bayan harin bam a asibitin Baghza", Al Jazeera.
25. وال استریت: بیمارستان المعمدانی غزه با بمب آمریکایی بمباران شد
26. تلویزیون آمریکا: اسرائیل دروغگوست

Nassoshi

«تلویزیون آمریکا: اسرائیل دروغگوست»،‌ Kamfanin Dillancin Labarai na Mashareq, kwanan watan aikawa: 26 Oktoba 1402, ranar ziyarta: 26 Oktoba 1402.

Template:چپ‌چین