Hashadush Sha'abi
| Shuwagabanni | Falihu Fayyaz. Hadi Al-Amiri. Abu Mahadi Al-Muhandis |
|---|---|
| Ƙungiyoyi | Ƙungiyoyin addini da al'ummu daban-daban na ƙasar Iraƙ |
| Ayyuka | Soja |
| Yankin ayyuka | Yankunan da suke kasance ƙarƙashin ikon Da'ish a Iraƙ |
| Dakaru | Fiye mutum dubu 100 |
| Ya canja zuwa | Sashen sojojin ƙasar Iraƙ |
| Masu adawa | Da'ish. Amurka. Saudi Arabiyya |
| Gidan yana giza gizo | https://al-hashed.gov.iq |
Hashadush sha'abi ko haɗakar sa kai na mutanen Iraƙi, (Larabci: الحشد الشعبي) wasu dakarun soja ne da suke ƙarƙashin hukumar tsaron ƙasar Iraƙi, waɗanda suke ƙarƙashin kulawar babban kwamandan dukkanin jami'an tsaro na Iraƙ, wannan ƙungiya tana aikin taimakawa sojojin ƙasar Iraƙi, aksarin membobin wannan ƙungiya ƴanshi'a ne. An ƙirƙiri wannan ƙungiyar lokacin da aka shiga mummunar matsala rashin tsaro a ƙasar Iraƙi sakamakon farmakin da ƙungiyar ta'addanci ta ISIS ta kai cikin Iraƙi a shekarar 2014 miladiyya, bayan fitar da fatawar jihadi kan Da'ish da marja'in taƙlidi Ayatullahi Sayyid Ali Sistani ya yi, wannan ƙungiyar ta kasance halastacciyar ƙungiya ta kuma samu ƙarfafuwa.
Hashadush sha'abi ta ƙunshi fiye da ƙungiyoyin sojojin sa kai guda arba'in, sannan tana da dakaru fiye da dubu ɗari da suka tattaro ƴanshi'a, Ahlus-Sunna, Kiristoci, Larabawa, Turkimanawa da Ƙurdawa. Rassan sojojin sa kai na Failaƙ Badar, Asa'ibu Ahlil Haƙƙi, Kata'ibu Hizbullahi da Saraya Atbat, suna cikin jumlar ƙungiyoyin sojojin sa kai da suke haɗe da Hashadush sha'abi.
Hashadush sha'abi sun samu ɗaukaka da tasiri a yaƙin da suka yi na fatattaka ISIS daga ƙasar Iraƙ, wannan ƙungiya bayan faɗuwar gwamnatin Saddam Husaini, sun himmatu da tsarkake ƙasar Iraƙi daga ragowar diddigar ƴan ta'addan ISIS da suke rage, haka zalika ba su yi ƙasa a gwiwa ba cikin ayyukan hidima ga jama'a. Kan asasin kundin dokoki, haƙiƙa ƙungiyar Hashadush sha'abi daidai take da sauran dakarun tsaro na ƙasar Iraƙi, su ma an hana su shiga harkokin siyasa.
Ƙasar Amurka da Saudi Arabiyya sun nemi rushe wannan ƙungiya tare da narkarta da ita cikin sojojin ƙasar Iraƙi, a shekarar 2018-2022 miladiyya, Amurka ta kai farmaki kan sansanonin Hashadush sha'abi. A gefe guda kuma ƙasashen Siriya, Jamhuriyar Muslunci ta Iran da ƙungiyar Hizbullahi Lubnan sun bayyana goyan bayansu ga Hashadush sha'abi. Muƙtada Sadar malamin Shi'a, kuma ɗan siyasa a ƙasar Iraƙi, shi ma ya bayyana buƙatar rushe wannan ƙungiya da narkar da ita cikin sojojin ƙasar Iraƙi, kishiyarsa Sayyid Kazim Ha'iri, marja'in taƙlidi ya yana ganin larurar wanzuwar dakarun Hashadush a matsayin ƙungiya mai cin gashin kanta domin tabbatar da tsaro da amincin ƙasar Iraƙi.
Falihu Fayyaz shi ne kwamandan wannan ƙungiya, sannan Hadi Al-Amiri shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar, kafin shi, Abu Mahadi Al-Muhandis ne ya kasance mataimakin shugaban ƙungiyar wanda ya yi shahada tare da Ƙasim Sulaimani babban kwamandan Dakarun Ƙudus, sakamakon harin ta'addanci da Amurka ta kai kansu.
Matsayi
Hashadush sha'abi waɗanda ake kira da dakarun sa kai na al'umma da kuma ƙasar Iraƙi[1] wasu dakaru ne da suke ƙarƙashin hukumar tsaro ta Iraƙi,[2] waɗanda suke ƙarƙashin kulawar babban kwamandon jami'an tsaro, wannan ƙungiya tana taimakawa sojojin Iraƙi kan harkokin tabbatar da tsaro.[3] Aksarin dakarun wannan ƙungiya ƴanshi'a ne.[4] Hashadush sha'abi sun samu ne cikin halin larura ta matsalar tsaro da aka tsinci kai a cikin sakamakon harin ƙungiyar ta'addanci ta ISIS cikin Iraƙi, bayan jawabin majalisar ministocin Iraƙi game da samar da dakarun sa kai ne aka kafa wannan ƙungiya.[5] Haka nan bayan fatawar jihadi kan Da'ish (ISIS) da Sayyid Ali Sistani da ya yi, wannan ƙungiya ta zamo halastacciyar ƙungiya a Iraƙi,[6] tare da samun ƙarfafa.[7]
Kafa Wannan Ƙungiya
Majalisar ministoci a ranar 10 ga watan Yuni 2014, cikin wani jawabi da suka gabata ga Firaministan ƙasar Iraƙi Nuri Maliki, sun miƙa buƙata ga al'ummar ƙasar Iraƙi cikin samar da dakarun sa kai na al'umma domin yaƙar ƴan ta'adda.[8] Wannan jawabi ya kasance daidai lokacin da ƴan ta'addan ISIS suka kwace iko a yankunan yammacin Iraƙi, sannan suka fara barazanar tunkarar Bagdad babban birnin Iraƙi da kuma yunƙurin kwace shi.[9]
Fatawar Jihadi Kifa'i Da Sayyid Ali Sistani Ya Bayar
Sayyid Ali Sistani, ɗaya daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a da yake zaune a Najaf, a ranar 13 ga Yuni 2014, kwanaki uku bayan barazanar da ISIS suka yi da kuma jawabin majalisar ministocin ƙasar Iraƙi ga Nuri Maliki Firaministan Iraƙi game da kafa dakarun sa kai.[10] Ya fitar da fatawar yaƙar ƴan ta'addan ISIS a matsayin wajibi kifa'i.[11] Wannan fatawa ta samarwa da ƙungiyar Hashadush sha'abi halasci a Iraƙi[12] Kuma shigar mutane wannan ƙungiyar ya yi matuƙar tasiri.[13] Ta yadda wasu masana suna da ra'ayin cewa Hashadush sha'abi ta samu kafuwa ne bayan fatawar da Ayatullahi Sayyid Ali Sistani ya yi.[14]
Halasci Na Doka
Bayan rattaba hannu kan dokar halasci "ƙungiyar Hashadush sha'abi"a majalisar dokokin Iraƙi a ranar 26 ga watan Nuwanba 20016, wannan ƙungiya aka fara lissafa ta matsayin ɗaya daga cikin dakarun tsaron ƙasar Iraƙi da suke ƙarƙashin kulawa da sa idon kwamandancin dukkanin hukumomin tsaron ƙasar Iraƙi. Kan wancan asasi, dokokin ƙungiyar Hashadush sha'abi ba su da bambanci da dokokin sauran hukumomin tsaro na Iraƙi, ma'ana wannan ƙungiya an haramta mata shiga harkokin siyasa.[15]
Tsari
Hashadush sha'abi tana cikin ƙungiyoyin soja da aka kafa, adadin ƙungiyoyin da suke ƙarsƙashinta ya kai 42[16] zuwa 68[17] sannan game da adadin dakarunta an ba da mabambantan rahotanni tsakanin dubu sittin[18] zuwa duba 160,[19] Na'am majalisar Iraƙi bisa la'akari da bajet da ta ware musu, kaɗai dakaru dubu 110 ta sani.[20]
Wasu suna ganin zuwa watan Satumba 2021 miladiyya, adadin dakarun Hashadush sha'abi ya kai dakaru dubu 130, daga cikinsu dubu 90 Larabawa ne ƴanshi'a, dubu uku kuma Turkumanawa Kiristoci.[21] Haka nan an bada rahoton samuwar mutanen Ƙurdawa cikinsu..[22]
Ba'arin masana sun ba da rahoto cewa dakarun Hashadush sha'abi sun ƙunshi gungu uku, daga ƴan amanar Sayyid Ali Khamna'i jagoran jamhuriyar Muslunci ta Iran, da na Sayyid Ali Sistani da kuma mutanen Muƙtada Sadar.[23]
Falihu Fayyaz shi ne kwamandan Hashadush sha'abi tun daga farkon kafa ta har zuwa 2023 miladiya, sannan Hadi Al-Amiri shi ne yake matsayin mataimakinsa. Gabanin Amiri, Abu Mahadi Al-Muhandis ne ya kasance mataimakinsa, wanda ya yi shahada tare da Ƙasim Sulaimani babban kwamandar Dakarun Ƙudus na Iran, a shekarar 2019 miladiyya a wani harin ta'addanci da Amurka ta kai kansu.[24] Kan asasi doka da aka rattabawa hannu a majalisar Iraƙi, ayyana babban kwamandan "Ƙungiyar Hashadush sha'abi”, daidai yake da sauran jami'an tsaron ƙasa, yana kasancewa bayan gabatarwa Firaministan da kuma sa hannu majalisa.[25] Na'am kana sasin Kundin tsarin Mulki doka mai lamba 331 wace aka sawa a hannu ta hannun Firaministan Iraƙi Adil Abdul-Mahadi a ranar 17 ga watan Satumba 2019 miladiyya, shugabanci Hashadush sha'abi yana da zaɓi da dama ƙarƙashin wakilcin Firaministan Iraƙi, za su iya naɗa kwamandoji da shuwagabanni, sannan su miƙa sunayenmsu ga babban kwamandan sojan ƙasar domin tabbatarwa.[26]
Ba'arin ƙungiyoyin da suka yi haɗaka da Hashadush sha'abi sune kamar haka:
- Failaƙ Badar (Reshee na soja)
- Asa'ibu Ahlil Haƙƙi
- Kata'ibu Hizbullahi
- Saraya Khurasani
- Kata'ibu Abul Fazlil Abbas
- Saraya Atbat
- Liwa'u Aliyul Akbar[27]
- Kata'ibu Sayyidush Shuhada[28]
- Saraya Salam (Harkatu Al-Mahadi a da can)[Tsokaci 1]
- Saraya Jihad
- Saraya Al-Aƙida
- Saraya Shura[29]
- Sojojin Shahid Sadar
- Harkatu Nujaba[30]
Ayyuka
An yi la'akari da rawar da Hashadush sha'abi ta taka wajen yaƙi da ƴan ta'addan ISIS da muhimmancin da yake da shi.[31] Daga jumlar gudummawarsu akwai karya mamaya da kewaye garuruwan Samarra da Amrili da ƴan ta'addan ISIS suka yi da kuma kwato Jurfu Sakhar, Tikrit, Beji da kuma garin Diyala.[32] Kan asasin rahoton shafin yanar gidan giza gizo na Hashadush sha'abi, wannan ƙungiya zuwa ƙarshen shekarar 2015 miladiyya, sun samu nasarar fatattakar ƴan ta'addan ISIS daga garuruwa guda goma sha tara na Iraƙi, tare kuma da tabbatar da tsaron manyan hanyoyi da titununa da suke sadarwa tsakanin garuruwan wannan ƙasa, wannan shafin labarai na Hashadush sha'abi ya ƙiyasta girman garuruwan da ya kwato daga ISIS da kusan murabba'in kilomita 17,500 (Kashi ɗaya cikin uku daga yankunan da ISIS ta mamaye a Iraƙi)..[33]
Bayan faɗuwar daular ISIS, Hashadush sha'abi sun mayar da hankali kan tsarkake yankunan Iraƙi daga sauran diddigar ƙazantar ƴan ta'addan ISIS da suka rage musammam ma a Bagdad babban birnin Iraƙi da Salahuddin, Diyala, Kirkuk, Ninawa da Anbar.[34] Hashadush sha'abi ba su yi ƙasa a gwiwa ba cikin ayyukan hidima[35] daga gina hanyoyi,[36] kawar da hamada,،[37] ba da tsaro a tarukan addini[38] daga ciki har da Tattakin Arba'in[39] da ƙoƙarin shawo kan bala'o'i da suke afkuwa ba zato ba tsammani[40] kamar misalin ambaliyar ruwa.
Matsayar Wasu ƙasashe Kan ƙungiyar Hashadush Sha'abi
Reksi Tillerson, ministan harkokin waje na Amurka a wancan lokacin, bayan kusan shekara guda da rattaba hannu a dokar da ta tabbatar da "Ƙungiyar Hashadush sha'abi" ya kira wannan ƙungiya da sunan ƙungiyar mayaƙan haya na Iran a Iraƙi.[41] sannan ya buƙacia rushe wannan ƙungiya tare da narkar da ita cikin sojojin Iraƙi.[42] Ba'arin masu fashin baƙi suna ganin cewa babban dalilin rashin amincewar Amurka da wannan ƙungiya ta Hashadush sha'abi ya faru ne sakamakon samuwar wasu ƙungiyoyi masu matuƙar tasiri cikin Hashadush sha'abi misalin Failaƙ Badar, Asa'ibu Ahlil Haƙƙi da Kata'ibu Hizbullahi, waɗanda su waɗannan ƙungiyoyi ƙarara sun bayyanar da buƙatarsu ta korar sojojin Amurka daga ƙasar[43][Tsokaci 2] sauran dalilan akwai kusancin da waɗannan ƙungiyoyi da suke shi da ƙasar Iran da kuma babban marja'in ƙasar Iraƙi watau Sayyid Ali Sistani da kuma tsoron tasiri da za su iyayi cikin harkokin siyasa da zaɓen ƙasar.[44] Ministan harkokin waje na Saudi Arabiyya na lokacin shi ma a watan Yuni 2016 ya bayyana cewa ƙungiyar Hashadush sha'abi za ta haifar da rikice-rikicen addini a Iraƙi, saboda haka ya kamata ne a rushe wannan ƙungiya.[45]
Bashar Asad shugaban ƙasar Siriya a ranar 3 ga watan Maris 2022 miladiyya, ya gana da shugaban Hashadush sha'abi, cikin wannan ganawa ta su ya jaddada larurar ƙalubalantar ƙasashen da suke ɗaukar nauyin ta'addanci.[46] Har ila yau a cewar Hadi Al-Amiri, mataimakin shugaban Hashadush sha'abi a ranar 16 ga watan Nuwanba 2016 miladiyya, Bashar Asad ya gayyaci Hashadush sha'abi bayan ƴantar da Iraƙi da suka kammala da su zo su taya shi fatattakar ISIS a Siriya.[47] Sayyid Ali Khamna'i, jagoran juyin juya halin Muslunci na Iran, cikin wata tattaunawa da ya yi tare da Sayyid Ammar Hakim, shugaban Harkatul Hikima Al-Wataniya Al-Iraƙiyya, shi ma ya kira ƙungiyar Hashadush sha'abi matsayin wani babban hannun jari na ƙasar Iraƙi da ya zama wajibi a ba ta dukkanin kariya da goyan baya.[48] Har ila yau Sayyid Hassan Nasrullah a ranar 19 ga watan Ogusta 2021 miladiyya, ya bayyana cewa ƙarfafa ƙungiyar Hashadush sha'abi domin tabbatar da tsaron ƙasar Iraƙi wani abu ne da ya zama larura.[49]
Hare-haren Amurka Kan Sansanonin Hashadush Sha'abi
A ranar 29 ga watan Disamba 2019 miladiyya ne ƙasar Amurka ta ƙaddamar da hare-hare da jiragen sama kan sansanonin ƙungiyar Hashadush sha'abi a garin Anbar da kan iyakar Iraƙi da Siriya. Wanda hakan ya haifar da asaar rayukan mutanen 25. Ma'aikatar harkokin tsaro ta Amurka ta bayyana wannan hari da ta kai matsayin amsa kan harin da Hashadush sha'abi suka kai mata kan sansanoninta da suke a Iraƙi.[50] Kishiyar haka, Hashadush sha'abi har zuwa yau ba ta ɗauki alhakin harin da Amurka ta ce ta kai mata kan sansanoninta a Iraƙi.[51]
A ranar 8 ga watan Yuni 2021 miladiyya, Amurka ta sake kai hare-hare kan sansanonin Hashadush sha'abi da suke kan iyakar ƙasar Iraƙi da Siriya tare da kashe mutane biyar. Amurka ta sanar da cewa wannan hari amsa ce kan harin jirgi mara matuƙi da yaran Iran suka kai kan muradunta a Iraƙi.[52] Kishiyar haka, Hashadush sha'abi ta bayyana cewa dakarun da Amurka ta kaiwa hari, ba su kai farmaki kan ko da mutum guda ba daga sojojin ƙasashen waje da suke zaune a Iraƙi.[53]
Matsaya A Cikin Iraƙi Game da Hashadush Sha'abi
Muƙtada Sadar, malamin Shi'a kuma ɗan siyasa a Iraƙi, a shekarar 2017 miladiyya, ya buƙaci a rushe Hashadush sha'abi da shigar da su cikin sojojin Iraƙi[54] a shekarar 2022 miladiyya ya buƙaci a haramtawa wannan ƙungiya shiga harkokin siyasa da kasuwanci.[55] Kishiyar haka, Sayyid Kazim Ha'iri, ɗaya daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a a Najaf, ya bayyana larurar ci gaba da wanzuwar ƙungiyar Hashadush sha'abi matsayin ƙungiya mai cin gashin kanta domin tabbatar da tsaron ƙasar Iraƙi.[56]
Shaik Bashir Najafi marja'in taƙlidi a Najaf, ya yi la'akari da Hashadush sha'abi a matsayin dantsen Iraƙi da marja'iyya.[57] Na'am shi da Muhammad Is'haƙ Fayyaz sun yi wa Hashadush sha'abi nasiha da nesantar harkokin siyasa.[58]
Ba'arin masu fashin baƙia Iraƙi su ma sun bayyana ci gaba da samuwar Hashadush sha'abi domin yaƙar barazana daga waje da kuma ƴan ta'adda.[59] Haka nan Sayyid Ammar Hakim, shugaban Harkatul Wataniyya Al-Iraƙiyya, ya yi la'akari da Hashadush sha'abi matsayin larura ta tsare-tsaren tabbatar da tsaro a Iraƙi, ya kuma bayyana adawarsa da yunƙurin rusa su ko shigar da su cikin sojojin Iraƙi; duk da cewa ya yi suka kan alaƙarsu da ƴan siyasa.[60] Falihu Fayyaz, shugaban Hashadush sha'abi, ya musa shigar wannan ƙungiya cikin harkokin siyasa.[61]
Tuhume-tuhume
Hukumar Afuwa ta duniya (Amnesty International) a shekarar 2016 sa'ilin yunƙurin tsarkake garin Falluja daga sauran diddigar ƙazantar ƴan ta'adda, ta tuhumi ƙungiyar Hashadush sha'abi da sace mutane 650 daga mutanen garin Falluja tare da rashin sani cikakkiyar makomarsu.[62]Ahmad Ɗayyid, shugaban jami'ar Al-Azhar shi ma ya tuhumi Hashadush sha'abi da aikata lefin yaƙi a kan Ahlus-Sunna a lokacin da suke tsarkake garin Tikrit daga diddigar ƴan ta'adda.[63] Jama'atu Ulama'i Iraƙ ƙarƙashin shugabancin Khalid Abdul-Wahab Al-Mulla, malamin Ahlus-Sunna,[64] da Shaik Bashir Najafi, marja'in taƙlidi a Najaf,[65] sun yi watsi da da'awar da Shaikul Azhar Shaik Ahmad Ɗayyid ya yi, tare da bayyana cewa wannan ƙungiya ta ƙunshi Shi'a da Ahlus-Sunna.
Taƙaitaccen Nazari
Littafin "Tasirat Hashadush Sha'ab Iraƙ Bar Siyasathaye Raheburdi Iran"na Kiwan Aga Babayi, wannan littafi bayan bincike kan sasanni da taƙaitaccen tarihin Hashadush sha'abi da siyasar harkokin wajen Iran da Saudi Arabiyya cikin sauye-sauyen da aka samu a siyasar Iraƙi tsakanin shekarar 2014 da 2017.[66]
Littafin "Saye Roshan Hashadush Sha'abi"na Amir Hamid Azad, cikin wannan littafi ya yi bahasi kan tsarin tafiya, tarihin kafuwa da ƙalubale da Hashadush Sha'abi suka fuskanta.[67] "Hashadush Sha'abi"na Shiirzad Dadashi shi ma littafi ne da aka rubuta shi kan wannan ƙungiya cikin harshen Farsi.[68]
Al-Hashadush Sha'abi: Al-Istiratijiya Al-Amirikiyya Wal Hashadush Sha'abi Fil Iraƙ, na Zainab Shu'aibu,[69] Al-juyush Al-muwaziya: Milishiyat Hashadush Sha'abi Fil Iraƙ, na Ahmad Adli,[70] da Wal-hashadush Sha'abi Arrihanil Akhir, na wasu gungun marubuta,[71] su ma suna daga cikin jumlar litattafan da aka rubuta cikin harshen Larabci game da wannan ƙungiya.
Har ila yau «Iraƙi Security Forces and Popular Mobilization Forces: Orders of Battl, (Jami'an Tsaron Iraƙi da Shahararrun dakarun Hashadush Sha'abi).[72] Da kuma «The Popular Mobilization Forces and Iraƙ's future.[73] suna daga cikin ba'arin litattafan harshen Ingilishi da aka wallafa game da wannan ƙungiya.
Ku Duba
| Layi | Suna | Kafawa | Wanda Ya Kafa | Fitattun Mutane | Shugaba | Mazhaba | Tushe | Logo | Kafofin Labarai |
|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
| 1 | Harkatu Amal | 1974m | Imam Musa Sadar | Musɗafa Camaran | Nabihu Birri | Shi'a | Labanun |
|
Tashar Talabijin Ta NBC |
| 2 | Ƙungiyar Jihadul-Islam | 1981m | Fatahi Shaƙaƙi | Ramadan Abdullahi Husam Abu Harbid | Ziyad Nakhala | Ahlus-Sunna | Gaza |
|
Tashar Falasɗinil Yaumi |
| 3 | Hizbullahi Lubnan | 1982m | Sayyid Abbas Musawi Sayyid Hassan Nasrullah | Na'im Ƙasim | Shi'a | Labanun | Example | Tashar Al-Manar | |
| 4 | Failaƙ Badar | 1985m | Adnan Ibrahim Abu Mahadi Al-Muhandis | Hadi Al-Amiri | Shi'a | Iraƙ |
![]() |
Tashar Al-Ghadir | |
| 5 | Hamar (Harkar gwagwarmayar Muslunci) | 1987m | Shaik Ahmad Yasin | Abdul-Aziz Rantisi Isma'il Haniyye | Kwamitin wucin gadi na Hamas | Ahlus-Sunna | Falasɗinu |
|
|
| 6 | Dakarun Ƙudus (Failak Ƙudus) | 1990m | Sayyid Ali Khamna'i | Ahmad Wahidi Ƙasim Sulaimani | Isma'il Ƙa'ani | Shi'a | Iran |
![]() |
|
| 7 | Harkatu Ansarullahi Yaman | 1990m | Husaini Al-Husi | Badrud-Dini Al-Husi | Abdul-Malik Al-Husi | Zaidiyya | Yaman |
|
Shabakatu Al-Masira |
| 8 | Kata'ibu Hizbullahi Iraƙ | 2003m | Abu Mahadi Al-Muhandis | Abu Husaini Humaidawi Abu Baƙir As-sa'idi Arzan Allawi | Ahmad Muhsin Farhi Alhumaidawi | Shi'a | Iraƙ |
|
Shabakatu Al-Ittija |
| 9 | Kata'ibu Sayyidush Shuhada Iraƙ | 2003m | Abu Musɗafa Khazali Haj Abu Yusuf | Abu Ala Al-wala'i | Shi'a | Iraƙ |
|
||
| 10 | Asa'ibu Ahlil Haƙƙi | 200m | Ƙaisu Khazali | Abdul_hadi Addaraji Muhammad Al-bahadili | Ƙaisu Khazali | Shi'a | Iraƙ | Example | Shabakatu Al-Ahad | |
| 11 | Harkatu Nujaba | 2013m | Akram Ka'abi | Abu Isa Iƙlim Mushataƙ Kazim Alhawari | Akram Ka'abi | Shi'a | Iraƙ |
|
|
| 12 | Dakarun Zainabiyyu | 2013m | Wasu jama'a daga Fakistan | Zainab Ali Jafari Aƙid Malik Muɗahhar Husaini | Shi'a | Fakistan |
|
||
| 13 | Dakarun Faɗimiyyun | 2013m | Wasu mutane daga mayaƙan Afganistan | Ali Rida Tawassuli Sayyid Muhammad Husaini Sayyid Ahmad Sadat | Shi'a | Afganistan |
|
||
| 14 | Hashadush Sha'abi | 2014m | Hadi Amiri Abu Mahadi Al-Muhandis | Falihu Fayyaz | Shi'a | Iraƙ |
|
Bayanin kula
- ↑ «حشد الشعبیها چه افرادی هستند؟»، Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan.
- ↑ Salumi, "Tadhitut Zat Ladai Muntasib Al-Hashd al-Shaabi al-Iraqi", shafi na 241
- ↑ Brisom, "Asbab Tadawwu al-Shabaab a al-Hashd al-Shaabi", shafi na 621.
- ↑ Khashan, "Al-Hashd al-Sha'bi Dirasa geopolitics Annaqdiyya", Shafi. 486.
- ↑ Nasser, "Al-Hashd al-Shaabi fi al-Manzoor al-Amiriki", shafi. 116.
- ↑ «سیستانی در صدد برچیدن بساط حشد شعبی از زیر پای شبهنظامیان عراقی»، Kamfanin Dillancin Labaran Farisa mai zaman kansa.
- ↑ Hattab, "Tauzifil Al-hashadush Sha'abi FI Almadrakis Siyasi Iraki," shafi. 108.
- ↑ Nasser, "Al-Hashd al-Shaabi fi al-Manzoor al-Amiriki", shafi. 116.
- ↑ Hattab, "Tauzifil Al-hashadush Sha'abi FI Almadrakis Siyasi Iraki," shafi. 108.
- ↑ Hattab, "Tauzifil Al-hashadush Sha'abi FI Almadrakis Siyasi Iraki," shafi. 108.
- ↑ Kati Nahed, "InzimamAl-Hashd al-Shaabi Ila Al-mu'assasa Al-Askariyya", shafi. 437.
- ↑ «سیستانی در صدد برچیدن بساط حشد شعبی از زیر پای شبهنظامیان عراقی», Kamfanin Dillancin Labaran Indefandan Farsi.
- ↑ Nasser, "Al-Hashd al-Shaabi fi al-Manzoor al-Amiriki", shafi. 116; Hattab, "Tawzif al-Hashd al-Shaabi in al-Madark al-Siyasi al-Iraqi", shafi. 108.
- ↑ Alal misali, duba Hattab, "Tauzifil Al-Hashadush Sha'abi Fil Almadrak Assiyasi Iraqi," shafi. 108; Katee Nahid. 437.
- ↑ Hattab, "Tauzifil Al-Hashadush Sha'abi Fil Almadrak Assiyasi Iraqi, shafi na 108
- ↑ Kati Nahed, "Inzimam Al-Hashd al-Shaabi Ila Al-Mu'assasa Al-Askariya", shafi. 440.
- ↑ «الحشد الشعبی فی العراق. قوة عسکریة و سیاسیة»،Kamfanin Dillancin Labarai na Al Jazeera.
- ↑ Hattab, "Tauzif Al-Hashadush sha'abi Fil Almdark Assiyasi Iraki," p. 108.
- ↑ Mansour da Abdul Jabbar, Al-Hashd al-Shaabi wa Mustaqbal Al-Iraki, 2017, shafi na 20.
- ↑ Mansour da Abdul Jabbar, Al-Hashd al-Shaabi wa Mustaqbal Al-Iraki, 2017, shafi na 20.
- ↑ Khashan, "Al-Hashd al-Sha'bi Dirasa Fi geopolitics Annaqdiyya", shafi. 486.
- ↑ ساختار حشد شعبی عراق؛ مهمترین گروههای تشکیل دهنده آنYanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ Mansour da Abdul Jabbar, Al-Hashd al-Shaabi Wa Mustaqbal Al-Iraki, 2017, shafi na 7.
- ↑ درباره ابومهدی المهندس, Kamfanin Dillancin Labarai na Jamhuriyar Musulunci (IRNA).
- ↑ Azad, "Aulguye Tashkili Wa Tahdid Hashadsuh Sha'abi Dar Iraki," shafi. 89.
- ↑ Azad, "Aulguye Tashkili Wa Tahdid Hashadsuh Sha'abi Dar Iraki," shafi. 96.
- ↑ Mansour da Abduljabbar, Al-Hashd al-Shaabi wa Mustaqbal Al-Iraki, 2017, shafi na 21 da 22.
- ↑ Kati Nahed, "Inzimam Al-Hashd al-Sha'bi Ila Al-mu'assasa Al-askariyya", shafi. 441.
- ↑ Mansour da Abduljabbar, Al-Hashd al-Shaabi wa Mustaqbal Al-Iraki, 2017, shafi na 21 da 23-24.
- ↑ ساختار حشد شعبی عراق؛ مهمترین گروههای تشکیلدهنده آن، Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ Mansour da Abdul Jabbar, Al-Hashd al-Shaabi wa Mustaqbal Al-Iraki, 2017, shafi na 7.
- ↑ Halfi, “Hashd al-Shaabi, Basij Mardomi Iraq,” shafi. 48.
- ↑ پایگاه اینترنتی الحشد الشعبی.
- ↑ «آغاز عملیات امنیتی حشد الشعبی در دیالی»،Kamfanin Dillancin Labarai na Daliban Iran (ISNA).
- ↑ «تنفیذ حملة خدمیة فی مقام الإمام السجاد(ع)», Gidan Yanar Gizon Yanar Gizo na Hashadush sha'abi
- ↑ KU duba«اللواء ۲۸ بالحشد یستجیب لمناشدة خدمیة فی شمال خانقین»، , Gidan Yanar Gizon Yanar Gizo na Hashadush sha'abi.
- ↑ «الحشد الشعبي يحصي عدد قواته وجرحاه ويؤكد على الضرورة الملحة لبقائه»، Al-Anba Iraqi Agency.
- ↑ برای نمونه نگاه کنید به «طرح ویژه امنیتی حشد شعبی عراق برای اعیاد مذهبی»،Kamfanin labarai na Mehr«طرح امنیتی حشد شعبی برای مراسم سالروز شهادت امام علی(ع) در نجف اشرف»،Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ «الحشد الشعبي يحبط مخططاً لاستهداف الأمن خلال زيارة الأربعين»، Almayadeen.
- ↑ برای نمونه نگاه کنید به «بالانفو کرافک: هذا ما شارکت به الهندسة العسکریة للحشد فی المحافظات الجنوبیة لاحتواء أزمة السیول والفیضانات (نسخه بایگانیشده)»، Yanar Gizon Yanar Gizo na Hashadush sha'abi.
- ↑ «الجبیر: بحثنا مع تیلرسون خطر إیران و أزمة قطر»، Kamfanin Dillancin Labarai na Al Arabiya.
- ↑ Hattab, "Tauzif Al-Hashadush sha'abi Fil Almadrak Assiyasi Fil Al-Iraki," shafi. 111.
- ↑ Nasser, "Al-Hashd al-Shaabi fi al-Manzoor al-Amiriki", shafi na 118 zuwa
- ↑ Hattab, "Tauzif Al-Hashadush sha'abi Fil Almadrak Assiyasi Fil Al-Iraki," shafi. 111.-112
- ↑ «هل تمنع السعودية مقاتلي الحشد الشعبي من أداء الحج؟»، Kamfanin dillancin labarai na Al-Hurra.
- ↑ «الأسد يبحث مع رئيس الحشد الشعبي القضايا الأمنية المشتركة»، Al-mayadeen.
- ↑ «هادي العامري: الحشد الشعبي تلقى دعوة من الأسد للدخول إلى سوريا»، Tashar labarai ta Rodavo.
- ↑ «خامنئی لقادة الشیعی: لا تثقوا بالامیرکیین»،Cibiyar Bincike da Shawarwari ta Al-Marqas Al-Lebanani.
- ↑ «السيد نصر الله: الحشد الشعبي الضمانة الحقيقية للعراق في مواجهة داعش والتكفيريين»،Tody News.
- ↑ «۲۵ قتیلا و۵۱ جریحا بالهجوم الأمریکی علی مواقع لالحشد الشعبی العراقی»، خبرگزرای روسیا الیوم (RT Arabic)؛ «Dillancin Labarai na Rasha A Yau (RT Larabci)bahesab.ir/time/conversion/ تبدیل تاریخ از میلادی به شمسی»، Yanar gizo na Ba Hisab.
- ↑ «American Airstrikes Rally Iraqis Against U.S»، The New York Times.
- ↑ «القصف الأمریکی: غارات أمریکیة فی العراق وسوریا», Kamfanin Dillancin Labaran Larabci na BBC.
- ↑ «العراق یدین الهجوم الأمریکی علی مواقع للحشد الشعبی»،Anadolu Agency.
- ↑ «مقتدی صدر: حشد شعبی با ارتش عراق ادغام شود»،Kamfanin Dillancin Labarai na ILNA.
- ↑ Shahsavari, "Baz Taze Sadar: Tamami Namayendigan Nazdik beh Beh Muqtada al-Sadr dar Parlaman Iraq Istifa Dadan," shafi na 1999. 4.
- ↑ «بیان سماحة السید الحائری یعلن فیه عدم الاستمرار فی التصدی للمرجعیة بسبب المرض والتقدم فی العمر», Official website of Seyyed Kazem Hosseini Haeri.
- ↑ «المرجع النجفي: الحشد الشعبي ذراع العراق والمرجعية وبهم يعز الإسلام والوطن»،Kamfanin dillancin labarai na Shafaqna.
- ↑ «تأکید آیات عظام نجفی و فیاض بر وحدت بیشتر گروههای مقاومت اسلامی عراق و دوری آنها از سیاست»، Kamfanin dillancin labarai na Shafaqna.
- ↑ Hattab, "Tauzif Al-hashadush Sha'abi Fil Almadrak Assiyasi Al-Iraki," shafi. 117.
- ↑ «در برابر انحلال حشد الشعبی میایستیم»،Kamfanin Dillancin Labarai na Daliban Iran (ISNA).
- ↑ «فالح الفیاض: حشد شعبی در بحثهای سیاسی دخالت نمیکند», Shafaqna News Agency.
- ↑ «Amnesty demands Iraq reveal fate of nearly 650 missing men and boys»، Middle East Eye.
- ↑ «العراق .. المرجع النجفي ينتقد موقف الازهر من الحشد الشعبي»، Kamfanin dillancin labarai na al-Taghrib.
- ↑ «العراق .. المرجع النجفي ينتقد موقف الازهر من الحشد الشعبي»،Kamfanin dillancin labarai na al-Taghrib.
- ↑ «جماعة علماء العراق لالازهر: الحشد الشعبي يتألف من شيعة و سنة»،Tasnim Al-Dawliyya Lil anba agency.
- ↑ «کتابشناسی تأثیرات حشدالشعبی عراق بر سیاستهای راهبردی ایران»،Ƙungiyar Laburare, Gidajen tarihi da Cibiyar Takardun Astan Quds Razavi.
- ↑ Gohari Moghadam da Larabawa, "Jayegahe Al-hashadush Sha'abi Dar Amniyat Iraq Nahwe Baznamayi Rasanehaye Garbi- Sa'udi Az An," shafi. 152.
- ↑ «کتابشناسی حشد الشعبی», Sazimane Asnad Wa Kitabekhune Milli Jamhuri Islami Iran.
- ↑ «کتابشناسی الحشد الشعبی»،Maktabat Noor.
- ↑ «کتابشناسی الجیوش الموازیة»، worldcat.
- ↑ «معرفی الحشد الشعبی الرهان الاخیر»،Kamfanin dillancin labarai na Iraqi Future News Agency.
- ↑ «Iraqi Security Forces and Popular Mobilization Forces»، worldcat.
- ↑ «The Popular Mobilization Forces and Iraq's future»، worldcat.
Tsokaci
- ↑ Wasu ba su dauki Saraya al-Salam a matsayin wani bangare na Hashadus sha'abi ba, ko da yake ta hada kai daHashadus sha'abi a yaki da ISIS. (Katee Nahid, "Inzimam Hashadus sha'abi Ila Al-mu'assasa Al-askaroyyya," shafi na 441.)
- ↑ ƙungiyoyin Kata'ibu Hizbullahi da Asa'ibu Ahlil Haƙƙi sun yi ta yaƙar sojojin Amurka a shekara ta 2003, kafin kafa ƙungiyar Hashadush Sha'abi (PMF) da kuma bayan shigar sojojin Amurka cikin Iraki. (Nasser, “Al-Hashd al-Shaabi FIl Manzuor Amiriki,” shafi na 115.)
Nassoshi
- «۲۵ قتیلا و۵۱ جریحا بالهجوم الأمریکی علی مواقع لالحشد الشعبی العراقی»، Kamfanin Dillancin Labarai na Rasha A Yau (RT Larabci), kwanan buga: Disamba 29, 2019, kwanan wata ziyara: Satumba 7, 1401 AH.
- Azad, Amirhamed، «الگوی تشکیل و تحدید حشد شعبی در عراق»، A cikin Mujallar Siyasar Duniya, juzu'i na 9, fitowa ta 3, Serial Number 33, Disamba 2020.
- «آغاز عملیات امنیتی حشد الشعبی در دیالی»، Ranar shigarwa: Mayu 10, 1401, kwanan wata: Satumba 13, 1401.
- Ibn Ashur, Muhammad Tahir, Tafsir al-Tahreer wa al-Tanvir, wanda aka fi sani da Sharhin Ibn Ashur, Beirut, Al-Tarikh Al-Arabi Foundation, 1421H.
- «الأسد يبحث مع رئيس الحشد الشعبي القضايا الأمنية المشتركة», Al-Mayadeen, Ranar shigowa: Maris 3, 2022, Ranar ziyarta: Satumba 12, 1401.
- «بالانفو کرافک: هذا ما شارکت به الهندسة العسکریة للحشد فی المحافظات الجنوبیة لاحتواء أزمة السیول والفیضانات (نسخه بایگانیشده)»، Gidan Yanar Gizon Yanar Gizo na Hashadush sha'abi, kwanan buga: Afrilu 16, 2019, kwanan wata ziyara: Satumba 5, 1401 AH.
- Brisam, Ghasq Abdolreza,«اسباب تطوع الشباب فی الحشد الشعبی"Al-Tarbiyah,
No. 33, Nuwamba 2018.
- «بیان سماحة السید الحائری یعلن فیه عدم الاستمرار فی التصدی للمرجعیة بسبب المرض والتقدم فی العمر»،Yanar Gizo na hukuma na Seyyed Kazem Hosseini Haeri, kwanan wata ziyara: 7 ga Satumba 1401 AH.
- «تأکید آیات عظام نجفی و فیاض بر وحدت بیشتر گروههای مقاومت اسلامی عراق و دوری آنها از سیاست», Kamfanin Dillancin Labarai na Shafaqna, Ranar aikawa: Yuni 16, 2016, Ranar ziyarar: Satumba 13, 2022.
- «تبدیل تاریخ از میلادی به شمسی»،Yanar Gizona Bahesab, kwanan wata ziyara: 7th Satumba 1401.
- «تنفیذ حملة خدمیة فی مقام الإمام السجاد(ع)»،Gidan Yanar Gizon Yanar Gizo naHashadush Sha'abi, kwanan buga: Agusta 7, 2022, kwanan wata ziyara: Satumba 5, 1401 AH.
- «جماعة علماء العراق لالازهر: الحشد الشعبي يتألف من شيعة و سنة»،Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasa da kasa, kwanan wata: Maris 12, 2015, kwanan wata: Satumba 12, 1401 AH.
- «الجبیر: بحثنا مع تیلرسون خطر إیران و أزمة قطر»،Kamfanin Dillancin Labarai na Al-Arabiya, kwanan watan bugawa: 22 ga Oktoba, 2017, kwanan wata: 6 ga Satumba, 1401 AH.
- «الحشد الشعبی فی العراق.. قوة عسکریة و سیاسیة»، Kamfanin Dillancin Labarai na Al Jazeera, kwanan watan bugawa: Disamba 31, 2019, kwanan wata ziyara: Satumba 6, 1401 AH.
- «حشد الشعبیها چه افرادی هستند؟»،Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan, ranar bugawa: 18 ga Afrilu, 2019, kwanan wata: 30 ga Agusta, 2002.
- «الحشد الشعبي يحبط مخططاً لاستهداف الأمن خلال زيارة الأربعين», Al-Mayadeen, Ranar Shiga: Satumba 8, 2022, Ranar Ziyara: 18 ga Satumba, 1401 AH.
- «الحشد الشعبي يحصي عدد قواته وجرحاه ويؤكد على الضرورة الملحة لبقائه», Kamfanin Dillancin Labarai na Iraki, Ranar shigowa: Yuni 13, 2022, Ranar ziyarta: 18 ga Satumba, 1401.
- Hattab, JavadKazem,«توظیف الحشد الشعبی فی المدرک السیاسی العراقی»،A cikin Mujallar Hammurabi, Shekara ta 7, fitowa ta 29, lokacin sanyi 2019.
- Halfi, Mahdi,«حشد الشعبی بسیج مردمی عراق», a cikin mujallar Pasdar Islam, fitowa ta 411, Mayu da Yuni 2016.
- «خامنئی لقادة الشیعی: لا تثقوا بالامیرکیین»،Cibiyar Bincike da Shawarwari ta Lebanon, ranar shigarwa: Disamba 12, 2016, kwanan wata ziyara: Satumba 1, 1401 AH.
- Khashan, Mohammed Keshish، «الحشد الشعبی دراسة فی الجیوبولیتیک النقدیة»،A cikin Mujallar Cibiyar Nazarin Kufa, fitowa ta 62, Satumba 2021.
- «درباره ابومهدی المهندس»،Kamfanin Dillancin Labarai na Jamhuriyar Musulunci (IRNA), kwanan wata: Janairu 3, 2019, kwanan wata: Satumba 13, 2022.
- در برابر انحلال حشد الشعبی میایستم, Shafin yanar gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Daliban Iran (ISNA), kwanan watan da aka buga: 15 ga Oktoba, 1400, ranar kallo: 1 ga Fabrairu, 1400.
- ساختار حشد شعبی عراق؛ مهمترین گروههای تشکیل دهنده آن،Ranar shigarwa: Yuli 12, 2015, kwanan wata: Janairu 18, 2021.
- Salumi, Salah Adnan Nasser,«تضحية الذات لدى منتسبي الحشد الشعبي العراقي»،A cikin Mujallar Lark don Falsafa, Linguistics da Kimiyyar zamantakewa, No. 22, 2016.
- «السيد نصر الله: الحشد الشعبي الضمانة الحقيقية للعراق في مواجهة داعش والتكفيريين»، Yau Labarai, kwanan buga: Agusta 19, 2021, kwanan wata ziyara: Satumba 12, 1401.
- «سیستانی در صدد برچیدن بساط حشد شعبی از زیر پای شبهنظامیان عراقی», Kamfanin Dillancin Labarai na Indefendan Farsi, Ranar shigowa: Disamba 8, 2010, Ranar ziyarta: Satumba 13, 2012.
- Shasawari«باز تازه صدر: تمامی نمایندگان نزدیک به مقتدی صدر در پارلمان عراق استعفا دادند», Jaridar Etemad, Na 5231, 14 ga Yuni, 1401.
- «طرح ویژه امنیتی حشد شعبی عراق برای اعیاد مذهبی»،Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, ranar shigarwa: Mayu 14, 2020, ranar shigarwa: Yuli 8, 1401, kwanan wata ziyarar: Satumba 8, 1401.
- «طرح امنیتی حشد شعبی برای مراسم سالروز شهادت امام علی(ع) در نجف اشرف», Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, kwanan wata ziyara: Satumba 18, 1401.
- «العراق .. المرجع النجفي ينتقد موقف الازهر من الحشد الشعبي», Kamfanin Dillancin Labarai na Al-Taqrib, ranar shigowa: Maris 13, 2015, Ranar Ziyara: 12 ga Satumba, 1401 AH.
- «العراق یدین الهجوم الأمریکی علی مواقع للحشد الشعبی»،Anadolu Agency, kwanan watan bugawa: Yuni 28, 2021, kwanan wata ziyara: Satumba 7, 1401.
- «فالح الفیاض: حشد شعبی در بحثهای سیاسی دخالت نمیکند»،Kamfanin Dillancin Labarai na Shafaqna, ranar shigarwa: Oktoba 20, 1401, kwanan wata ziyara: 1 ga Satumba, 1402.
- «القصف الأمریکی: غارات أمریکیة فی العراق وسوریا علی قوات موالیة لطهران و الحشد الشعبی یعلن عن قتلی و جرحی»، Kamfanin Dillancin Labaran Larabci na BBC, Ranar bugawa: Yuni 28, 2021, Ranar ziyarta: Satumba 7, 1401 AH.
- Kateh Nahez«انضمام الحشد الشعبی الی المؤسسة العسکریة», a cikin Mujallar Al-Siyasiya da Al-Dawliyya, lamba 45, Disamba 2020.
- «کتابشناسی تأثیرات حشدالشعبی عراق بر سیاستهای راهبردی ایران»،Ƙungiyar Laburare, Gidajen tarihi da Cibiyar Takardun Astan Quds Razavi, ranar shigarwa: Satumba 17, 2019, kwanan wata ziyara: Agusta 2, 2022.
- «کتابشناسی الحشد الشعبی», Maktaba Noor, Ranar Ziyara: 2 Mordad 1401 AH.
- «کتابشناسی حشد الشعبی», Kungiyar Rukunin Rukunin Tarihi da Laburare ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ranar da aka buga: 2 ga Agusta, 1401.
- «کتابشناسی الجیوش الموازیة»، worldcat، Ziyarar kwanan wata: Agusta 2, 1401.
- Gohari Moghadam, Abuzar da Mohammadreza Arab, «جایگاه الحشدالشعبی در امنیت ملی عراق و نحوه بازنمایی رسانههای غربی-سعودی از آن»،A cikin Jaridar Bincike Kan Kafofin Watsa Labarai na Duniya, Shekara ta 3, fitowa ta 3, Faɗuwar 2018.
- «اللواء ۲۸ بالحشد یستجیب لمناشدة خدمیة فی شمال خانقین»،Yanar Gizon Yanar Gizo na hashadush sha'abi, ranar bugawa: Oktoba 4, 2021, kwanan wata ziyara: Satumba 5, 1401 AH.
- «المرجع النجفي: الحشد الشعبي ذراع العراق والمرجعية وبهم يعز الإسلام والوطن»، Kamfanin Dillancin Labarai na Shafaqna, ranar ziyarar: Afrilu 25, 2017, ranar shigarwa: 1 ga Satumba, 1401.
- «معرفی الحشد الشعبی الرهان الاخیر», Kamfanin Dillancin Labarai na Almusatqabal Iraqi, ranar shigarwa: Janairu 30, 2015, kwanan wata: Satumba 3, 1401 AH.
- «مقتدی صدر: حشد الشعبی با ارتش عراق ادغام شود»Kamfanin Dillancin Labarai na ILNA, kwanan watan bugawa: Disamba 10, 2017, kwanan wata ziyara: Agusta 11, 2022.
- Mansour, Raynad and Faleh Abduljabbar,الحشد الشعبی و مستقبل العراق (E-littafi), Beirut, Cibiyar Gabas ta Tsakiya ta Carnegie, 2017.
- Nasser, Karrar Anwar,«الحشد الشعبی فی المنظور الامیرکی»،A cikin Mujallar Nazarin Hamurai, Shekara ta 4, fitowa ta 13, lokacin sanyi 2015.
- «هادي العامري: الحشد الشعبي تلقى دعوة من الأسد للدخول إلى سوريا»، Rodavu Media Network, ranar shigarwa: Nuwamba 16, 2016, kwanan wata: Satumba 12, 1401 AH.
- «هل تمنع السعودية مقاتلي الحشد الشعبي من أداء الحج؟»، Kamfanin dillancin labarai na Al-Hurra, kwanan wata: 13 ga Yuni, 2016, kwanan wata: 1 ga Satumba, 1401.
- «Amnesty demands Iraq reveal fate of nearly 650 missing men and boys»، Middle East Eye، Ranar shigarwa: Yuni 4, 2021, kwanan wata: Satumba 12, 1401.
- «American Airstrikes Rally Iraqis Against U.S»، The New York Times، Ziyarar kwanan wata: Satumba 7, 1401.
- «Iraqi Security Forces and Popular Mobilization Forces»، worldcat، Ziyarar kwanan wata: Agusta 2, 1401.
- The Popular Mobilization Forces and Iraq's future»، worldcat،Ziyarar kwanan wata: Agusta 2, 1401.











