Ƙungiyar Jihadul-Islam

Daga wikishia

Ƙungiyar Jihadul-Islam (Larabci:حركة الجهاد الإسلامي في فلسطين) ta Palasɗinu ɗaya ce daga cikin ƙungiyoyin gwagwarmayar Palasɗinawa, wanda aka gina bisa tasirin hanyar da Imam Khumaini ya bi, wadda ya yi imanin cewa hanya ɗaya tilo wadda za'a `yantar da yankunan Palasɗinu gaba daya ita ce tsayawa tsayin daka da gwagwarmaya kan mamayar Isra'ila. Tushen wannan yunƙuri shi ne imani da koyarwar Musulunci da kuma haramta imani da Isra'ila a matsayin ƙasa mai zaman kanta.

Fathi Shaƙiƙi ne ya kafa ƙungiyar Jihadul-Islam a shekarar 1981 a Gaza. Har ila yau, reshen sojojinta ya kai hare-hare da dama kan Isra'ila, haka ita ma Isra'ila ta kashe wasu kwamandojinsu, Babban sakataren wannan ƙungiya shi ne Za'ad Nakhale. kafinsa Ramadan Abdullah, kafin ramadan, Fathi Shaƙaƙi ne ke ɗaukar wannan nauyi. Wasu ƙasashe kamar Amurka da Ingila da kuma Tarayyar Turai sun sanya wannan ƙungiya cikin jerin ƙungiyoyin 'yan ta'adda.

Gabatarwa da Kafa Wannan Ƙungiya

Harkar Jihadul-islam na ɗaya daga cikin muhimman ƙungiyoyin gwagwarmayar Palasɗinawa, waɗanda suke ganin juriya da haƙuri shine hanya ɗaya tilo ta 'yanta masallacin Ƙudus.[1] kuma Bata goyan bayan yarjejeniya da Isra'ila.[2] wannan ƙungiyar batakai hamas da fath samun magoya bayaba,[3] samuwar wan kungiyar a garin ƙudus ya temaka mata wajan cigaba sosai [4] Kamar yanda wasu kafafan yaɗa labarai sukace , wannan ƙungiyar ta ƙunshi ɓoyayyan tsari na sirri .

adawa da yarjejeniyar Oslo (2003), ƙauracewa zaɓen majalisar dokoki (2006), adawa da yarjejeniyar zaman lafiya ta Misra a shekara ta 2014, da matakin warware rikici tsakanin Hamas da gwamnatin Misra (2014) na daga cikin muhimman ayyukan siyasa da kungiyar Jihadul-Islam ta aiwatar[5]

An kafa ƙungiyar Jihadul islam a birnin Gaza a shekara ta 1981 a hannun Fathi Shaƙaƙi, likitan Falasɗinu[6] tare da haɗin gwiwar mutane irin su Abdul Aziz Awda,, Ramadan Abdullah da Nafiz Azzam.[7]a shekarar 1987 a ka kori shuwagabannin ƙungiyar zuwa Lebanon a can suka haɗu da ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon suka sami horo daga dakarun IRGC na iran.

Mossad ta Isra'ila ta kashe Fathi Shaƙaƙi babban sakataren ƙungiyar Jihadul-Islam a shekara ta 1995,[8] daga nan Ramadan Abdullah Shalah (ya rasu: 2020) ya gaje shi. Ramadan Abdullahi ya taka rawar gani a fagen siyasar wannan yunƙuri.[9] Bayan rashin lafiyar Ramadan Abdullah, an nada Ziad Nakhala a matsayin babban sakataren ƙungiyar a shekarar 2018.[10]

Ƙa'idoji da Mamufofi

Jihadul islam ta ayyana ƙa'idojin ta , waɗanda da ta ginu a kansu : addinin Musulunci shi ne tushen imani da ayyukan wannan yunƙuri. A bisa waɗannan ƙa'idoji, dukkanin ƙasar Palasɗinu kasa ce ta Musulunci da Larabawa, sannan kuma amincewa da gwamnatin Isra'ila a wannan ƙasa haramun ne, kuma kasancewar Isra'ila a cikin Palasɗinu yana nufin mamayewa da rarraba ƙasashen Musulunci gaba ɗaya,[11] Sannan duk wani tsarin mulki da zai nuna Isra'ila ce mai wannan ƙasar , ana ganin ba za a yarda da shi ba[12]

Ƙungiyar Jihadul-Islam ta Palasɗinu ta bayyana babbar manufarta a matsayin 'yantar da Palasɗinu gaba ɗaya, ruguza gwamnatin Isra'ila da kafa gwamnatin Musulunci. Sauran manufofin wannan yunƙuri dai su ne: shirya al'ummar Palasɗinu zuwa jihadi na soji da na siyasa, da tsara al'ummar musulmin duniya da kwadaitar da su wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ga Palasɗinu, da ƙarfafa alaƙa tsakanin Musulmi da 'yantar da su da haɗin kai da Kira zuwa ga Musulunci da yaɗa koyarwarsa[13]

Harkar Jihadul Islam tana da haɗin gwiwar siyasa da soja da ƙungiyar Hamas,[14] Amma bata da dangantaka da ƙungiyar 'yantar da Falasɗinu saboda tsarin ita wannan ƙungiya ta ba ruwansu da addini da kuma son yin sulhu da Isra'ila da kuma amincewa da ita.[15]

Juriya kan Mamayar da Isra'ila Ta yi wa Palasɗinu

Ƙudus Brigades (Larabci: Saraya Al-ƙuds),shine reshen soja da tsaro na ƙungiyar Jihadul-islam, an kafa shi ne a ƙarni na ashirin. Kafin wannan sunan ana kiransa da dakarun Mujahidul-Islam kafin wannan ana kiransa da Kataib Saif al-Islam[16] Sarayal-ƙuds ita ce mafi girman rundunar soji a Gaza bayan reshen soja na Hamas[17] Isra'ila ta kashe wasu kwamandojin Jihadul-islam, waɗanda suka haɗa da: Fathi Shaƙaƙi(1995), Isam Barahma (1992), Hani Abid (1994), Mahmud Al-Khawaja (1995), Mahmoud ɗiwaliba (2002), Mahmoud Zamɗa(2003). , Bashir Al-Dabsh (2004 AD), Khalid Al-Dahduh (2006 AD), Daniyal Mansur (2014 AD)[19] da Hassam Abu Harbid (2021), kwamandan reshen soji na Sarayal-ƙuds [18]

Hare-Hare da Ofireshin

Ɓangaran soja na Jihadul-islam ya kai hare-hare da dama kan guraran da Isra'ila ta mamaye, Irin su Beit Lid, Dizengoff, Kafer Darum, Netsarim, Gabashin Jabaliya, Moraj[19] da Bashaer al-Intisar.[20]

Gwagwarmayar Neman Haƙƙi ta Shekarar 1987 m

A shekarar 1987 Harkar Jihadul-islam ta taka rawar gani a intifada ta farko ta Falasdinu (1987).

Jawabin Abd al-Aziz Ouda a masallacin Izzud-din Ƙassam na daga cikin muhimman abubuwa a farkon wannan intifada.[21] Isra'ila ta bayyana Ramadan Abdullah a (2000) a matsayin shugaban aiwatar da hare-hare gare ta.[22] Shigar da dakarun sojan Jihadul-islam cikin wannan intifada[23] shine musabbabin kisan wasu kwamandojin rundunar sojansu da Isra'ila ta yi.

Tarayya a Cikin Yaƙin ɗufanul Al-Aƙsa

Asalin labarin: Ɗufanul-aƙsa. A cewar wasu kafofin watsa labarai na Turai, ƙungiyar Jihadul-Islam ta shiga cikin yaƙin ɗufan Al-aƙsa (2023), wanda ya yi sanadin mutuwar Isra'ilawa 1,400 tare da kame wasu daruruwan Isra'ilawa[24] inji Isra’ila[25] Wannan ƙungiyar ta bayyana cewa ta kama mutane sama da 30 kuma ta hanyar musaya kaɗai zata sake su.[26]

Ba'arin wasu kasashe misalin Amurka, Ingila, Kanada da Japan da kuma tarayyar kasahsen turai sun sanya Kungiyar Jidaul Islam cikin jerin Kungiyoyin ta'addanci.[27]

Tasirantyuwa da Juyin Juya hakin Muslunci na Iran

Tun Farko kafa Kungiyar Jihadul Muslunci ta tasirantu da tunanin juyin juya halin muslunci na Iran karkashin jagorancin Imam Khomaini[28]bisa wannan tunani ne suka rike muslunci da koyarwarsa matsayin fitila da jagora cikin gwagwarmaya da jihadi.[29] Fathi shakaki gabanin kafa wannan kungiya, ya rubuta littafi mai taken (Imam Al-Khomaini Al-Halli Al-Islami Wal Al-Badil) ma'ana Imam Khomaini hanya samun warwara ta muslunci, da wannan dalili ne Kasar Misra ta kama shi ta tsare shi[30] Ya bayyana tunanin Imam Khumaini da juyin juya halinsa a matsayin mafi kyawun madadin sauran hanyoyin cimma manufofin duniyar musulmi musamman 'yancin Falasɗinu[31] Jihadi domin wannan yunƙuri na goyon bayan Imam Khumaini da tunaninsa da ƙarfafa haɗin kan Shi'a da Ahlus-Sunna ana zarginsa da cewa ya zama shi'a.[32] kungiyar jihadil Islami ta nesanta kanta da wannan zargi tare da bayyana cewa sun dora dukkanin ayyunkansa kan koyar mazhabobin Ahlus-sunna[33]

A cewar khalid al-Baɗsh, memba a ofishin siyasa na ƙungiyar Jihadul-Islam, Iran ita ce babbar mai goyon bayan wannan yunƙuri na gwagwarmayar palasɗinu,[34] Taimakon iran ya kama daga kuɗi, makaman yaƙi, koyar da sojoji dabarun yaƙi, da al'amuran siyasa[35]Cibiyar Nazarin Siyasar Larabawa, ta bayyana cewa ,wannan yunƙuri ya kasance cikin tsaka mai wuya a yaƙin basasar Siriya (farawa: 2011). da kuma harin da ƙawancen ƙasashen Larabawa suka kai wa ƙungiyar Ansarullah ta Yaman (farawa: 2015), wanda ya sa dangantakarta da Iran ta yi sanyi na wani lokaci[36]

TasharTalabishin

Cibiyar sadarwar tauraron dan adam ta Falasdinu Alyowm tana da alaƙa da ƙungiyar Jihadul-slami, wanda babbar cibiyarta ke a Gaza. An sanar da matsalolin kuɗi a matsayin dalilin rufe ofishin wannan cibiyar sadarwa na Urushalim (2015),.[37] daga nan a shekarar 2016 Isra'ila ta rufe ta gabaki ɗaya.[38]

Bayanin kula

  1. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.
  2. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»، وبگاه عربی پست.
  3. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»، وبگاه عربی پست.
  4. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»، وبگاه عربی پست.
  5. «رویکرد جهاد اسلامی فلسطین در مبارزه با اسرائیل و تفاوت‌هایش با حماس در چیست؟»، وبگاه یورونیوز.
  6. «حرکة الجهاد الإسلامی»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.
  7. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»، وبگاه عربی پست.
  8. «تاریخ حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین موضوعًا لمحاضرة وحدة الدراسات الاستراتیجیة»، وبگاه مرکز عربی پژوهش‌ها و مطالعات سیاسی.
  9. «ما هی حرکة "الجهاد الإسلامی" التی تتهمها إسرائیل بقصف المستشفی المعمدانی فی غزة؟»، وبگاه فرانس۲۴.
  10. «ما هی حرکة "الجهاد الإسلامی" التی تتهمها إسرائیل بقصف المستشفی المعمدانی فی غزة؟»، وبگاه فرانس۲۴.
  11. «نبذة عن حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.
  12. «نبذة عن حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.
  13. «نبذة عن حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.
  14. «ما هی حرکة الجهاد الإسلامی وما علاقتها بحماس؟»، وبگاه الحره.
  15. «رویکرد جهاد اسلامی فلسطین در مبارزه با اسرائیل و تفاوت‌هایش با حماس در چیست؟»، وبگاه یورونیوز.
  16. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.
  17. «حرکة الجهاد الإسلامی»، وبگاه TRT عربی.
  18. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.
  19. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.
  20. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»، وبگاه عربی پست.
  21. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»، وبگاه عربی پست.
  22. «نشأت بمصر، ولعبت دوراً کبیراً بالانتفاضة.. قصة حرکة الجهاد وسر استهداف إسرائیل لها بحربها الأخیرة»، وبگاه عربی پست.
  23. الشریف، «حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین»، وبگاه مرکز مطالعات فلسطین.
  24. «ما هی حرکة "الجهاد الإسلامی" التی تتهمها إسرائیل بقصف المستشفی المعمدانی فی غزة؟»، وبگاه فرانس۲۴.
  25. «رویکرد جهاد اسلامی فلسطین در مبارزه با اسرائیل و تفاوت‌هایش با حماس در چیست؟»، وبگاه یورونیوز.
  26. «ما هی حرکة "الجهاد الإسلامی" التی تتهمها إسرائیل بقصف المستشفی المعمدانی فی غزة؟»، وبگاه فرانس۲۴.
  27. «درباره جهاد اسلامی فلسطین و گردان‌های قدس چه می‌دانیم؟»، وبگاه شبکه خبری یورو نیوز.
  28. «حرکة الجهاد الإسلامی»، وبگاه TRT عربی.
  29. ابو طه، «تأثیر امام خمینی و انقلاب اسلامی در اندیشه و عملکرد جنبش جهاد اسلامی فلسطین»، پورتال امام خمینی.
  30. عرب‌سرخی، «جنبش جهاد اسلامی فلسطین از آغاز تا امروز»، وبگاه جمعیت دفاع از ملت فلسطین.
  31. ابو طه، «تأثیر امام خمینی و انقلاب اسلامی در اندیشه و عملکرد جنبش جهاد اسلامی فلسطین»، پورتال امام خمینی.
  32. ابو طه، «تأثیر امام خمینی و انقلاب اسلامی در اندیشه و عملکرد جنبش جهاد اسلامی فلسطین»، پورتال امام خمینی.
  33. ابو طه، «تأثیر امام خمینی و انقلاب اسلامی در اندیشه و عملکرد جنبش جهاد اسلامی فلسطین»، پورتال امام خمینی.
  34. «فی حوار مع الجزیرة نت خالد البطش یوضح مکاسب الجهاد من الحرب ودور حماس والعلاقة مع إیران»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.
  35. «فی حوار مع الجزیرة نت خالد البطش یوضح مکاسب الجهاد من الحرب ودور حماس والعلاقة مع إیران»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.
  36. «تاریخ حرکة الجهاد الإسلامی فی فلسطین موضوعًا لمحاضرة وحدة الدراسات الاستراتیجیة»، وبگاه مرکز عربی پژوهش‌ها و مطالعات سیاسی.
  37. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.
  38. «حدث الساعة.. معلومات تهمک معرفتها عن الجهاد الإسلامی التی أنجبت أسری عملیة جلبوع»، وبگاه شبکه خبری الجزیره.

Nassoshi