Husain Badr Al-Din Al-Husi

Daga wikishia
File:حسین الحوثی 6.jpg
Husain Al-Husi

Husain Badr Al-Din al-Husi(Larabci:حسين بدر الدين الحوثي) 1960-2004 shi ne wanda ya assasa kuma jagoran ƙungiyar Ansarullah ta Yemen. Ya kasance ɗaya daga cikin 'yan Shi'a na mazhabar Zaidi, yana ƙarƙashin jagorancin Imam Khumaini ta hanyar sanya adawa Amurka da Isra'ila a matsayin takensa, sannan ya bayyana batun Palasɗinu a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ya sa a gaba. Ya fara ayyukansa na siyasa ne ta hanyar yaƙar tasirin karkatattun aƙidu irin su Wahabiyanci. Shi ne ya ƙagi shahararren taken Husi mai suna Sarkha. Hussein Al-Husi sakamakon adawarsa da Amurka gwamnatin Yaman ƙarƙashin jagorancin Ali Abdullah Saleh sun kashe shi.

Matsayi

Bikin zagayowar ranar shahadar Hossein Badreddin Houthi a birnin Sana'a (2023 AD).

An haifi Sayyid Hussain a shekara ta 1960 (Sha'aban 1379) a yankin Roys na jahar Sa'ada a ƙasar Yaman,[1] Shi ɗan siyasa ne, kuma kwamandan soji, wanda ya kafa ƙungiyar Ansarullah ta ƙasar Yemen kuma jagoran farko na wannan yunƙuri.[2] hakanan maz'habar iyalinsa shi'a ne kuma Jaroudi,[3] Abokansa da malamansa suna kwatanta shi da cewa yana da hankali, fifikon kimiyya da nazari mai zurfi,[4] kuma sun san shi da halaye irin su jajircewa, ƙarfin zuciya, basira da kamala,[5] yana da dangantakar dangin ko nasaba da Imam Hasan.[6] An ce mahaifinsa Badarul-Din al-Husi yana daga cikin fitattun mahukunta kuma maraja'i ne na maz'habar Zaidi[7]

An ganin Hussein Husi a matsayin mai karkata zuwa ga aƙidar Shi'a mai imamai goma sha biyu, ya yi imani da ma'asumin imamai da imani da Mahdin da aka yi alkawarin zuwansa,[8] wasu kuma sun ce ya koma maz'habar Shi'a mai imamai sha biyu.[9]. Kamar yadda wasu masu bincike suka yi nuni da cewa, ruwayoyi daban-daban kamar aƙidar Wahabiyanci, 'Yan Uwa Musulmi, Socialism, Nasiriyyah, da kuma faruwar juyin juya halin Musulunci na Iran, sun yi tasiri wajen kafa tunanin Hussein Husi.[10] wasu dalilai kamar mu'amala da malamai da sauran manyan mutane na ciki da wajan yamen ne suka samar da tsarin tunanin Husain.[11] An tattara jawabansa da taken "Malazem" da 'yan wannan kungiya suke amfani da su a matsayin bayanin Harkar Ansarullah.[12]

Husi ya koyi ilimin addini a wurin mahaifinsa. Bayan kammala karatunsa a fannin adabi,[13] ya je Sudan don kammala karatunsa,[14] ya yi ayyuka da dama, wanda ya fi shahara a cikinsu shi ne Al-Sarkha fi wajhi Al-Mustakbirin.

Tunani da Ra'ayoyi

Hussein Husi ya yi imanin cewa duniyar Musulunci ta lalace kuma hanya ɗaya tilo da za a cece ta ita ce komawa ga Alkur'ani da koyarwarsa.[15]

Ra'ayinsa a Kan Isra'ila da Amurka

Ƙiyayya da masu Girman kai yana daga cikin halayensa. Ya kasance yana faɗakar da al'ummar ƙasar Yemen game da tasirin Amurka a wannan ƙasa,[16] A mahangarsa, 'yantar da Falasɗinu yana daga hanyar farkawa da cigaban da fa'ida ga musulmi.[17] ya sanya takunkumin hana siyan kayayyakin Isra'ila da Amurkawa da raya ranar ƙuds wato jama'ar ƙarshen watan ramadan, Sayyid Husain ba shi da fata ga mahukuntan ƙasashen musulmi na larabawa wajan ‘yantar Falasɗinu,[18] Ya ɗauki duk wani sulhu da Isra’ila a matsayin abin da ba zai taɓa yiwuwa ba saboda munanan nufi da Isra’ila kedashi akan musulmai.[19]

Ra'yinsa Kan Jamhuriyar Muslunci ta Iran da Imam Khomaini

Sayyid Hussein Husi ya ɗauki tafarkin juyin juya halin Musulunci na Iran a matsayin hanya ɗaya tilo ta samun 'yancin al'ummar musulmi,[20] Ya gabatar da tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayin abin koyi da ya dace da musulmi, kuma yana da ra'ayin cewa duk wanda ya yi adawa ko yaƙi da juyin juya halin Musulunci na Iran, Allah zai azabtar da shi.[21]

Husi ya yi imanin cewa, ta hanyar farfaɗo da al'adar bara'a ga mushrikai, Imam Khumaini ya bayyanawa mutane ma'anar Hajji daidai da ma'anar Ƙur'ani.[22] Ya ɗauki Imam Khumaini a matsayin rahamar Ubangiji ga al'ummar Larabawa, ya ce sun hana kansu ko sun haramtawa kansu wannan ni'ima ta hanyar ƙin bin maganganun sa[23] yana ganin imam Khumaini a matsayin imami adali, mai tsoran Allah, kuma wanda Allah ya zaɓa[24]


Ayyukansa na Siyasa da Zamantakewa

Hussein Husain ya fara harkokinsa na siyasa ne ta hanyar yaƙar tasirin wahabiyanci a ƙasar Yemen[25] A shekara ta 1993, da nufin samarwa da yankin Sa'ada.[26]] ƴanci wajan shiga majalisar wakilan Yemen a matsayin wakilin jam'iyyar Haƙ,[27].[28] Ya jaddada a kan samar da sulhu a rikicin jam’iyyar gamayya da jam’iyyun biyu wato Congress da Islah, ya kuma ƙi shiga gwamnati wajen fara yaƙi.[29]

Sayyid Hussein ya ƙi halartar zama na gaba na Majalisar Wakilai inda ya kafa ƙungiyar Shabab Al-Mu'min,[30] wacce daga baya ake kiranta da Harkar Ansarullah ta Yemen,[31] هدف اولیه تشکیل این انجمن، انجام کارهای فرهنگی بود.[32] hadafin wannan ƙungiya a farko shine samar da ayyukan al'adu,[33] Bayan waƙi'a 11 September da harin da Amurka ta kaiwa Afganistan da Iraƙi da kai sojojinta yankin mashigin tekun Aden,[34] sai aka fara ƙiyayya da takun saƙa da Amurka da Sayyid Hussein, inda Amurka ta kai farmaki kan ƙasashen musulmi.[35] Husi ya sanya ranar Palasɗinu a matsayin mafarin yunƙurinsa, kuma da gabatar da jawabinsa na farko a wannan rana ya karanta wa al'umma kalmomin Imam Khumaini game da ranar Ƙudus.[36] ya yi nasihohi masu yawa ga Amurka.sannan ya ƙirƙiri sanannen taken Husi na yaƙi da Amurka da Isra'ila mai suna Sarkha.[37] Hussein Husi ya yi ayyuka da dama na zamantakewa ga al'ummar yankinsa, da suka haɗa da samar da ƙungiyar agaji ta Marran, da kafa makarantun addini, da kafa cibiyoyin kiwon lafiya, da ayyukan gine-gine daban-daban.[38]

Kafirtawa Tare da Kashe Husi

File:مرقد حسین بدرالدین حوثی.jpg
Ƙabarin Husain Badr Al-Din Al-Husi kafin Wahabiyawa su ruguje shi

Ayyukan ƙiyayya ga Isra'ila da Amurka sun kai ga fitar da fatawar kafirci da kashe shi da malaman lokacin sukayi waɗan da ke da alaƙa da tsarin mulkin Yaman.[39] Sun masa ƙazafin yana da'awar cewa shi Annabi ne, Mahadi da Imamanci.[40] a shekarar 2004, an kama mabiyansa 640 wanda ke tafiya a hanyarsa.[41] Sannan gwamnatin Yemen mai mulki ta ba da tukuicin dala 55,000 don karɓar bayanan da za su kai ga kama shi[42]

Bayan da gwamnatin Yaman ta kashe 'yan uwansa 25, adadin ya karu zuwa dala dubu 75.[43] Bayan kwanaki shida da dawowar Abdullah Saleh daga Amurka, akq fara yaƙin da gwamnati take yi da 'yan Husi. An kafa ta ne ta hanyar yarjejeniyar George Bush,[44] shugaban Amurka a lokacin, da Ali Abdullah Saleh a Washington.[45]

Shahada

Kwafin hoto d ayake kan littafin Uwaisu Khomaini

Dakarun gwamnatin Yaman ƙarƙashin jagorancin Ali Abdullah Saleh sun yi wa Hussein Husi ƙawanya a yankin Maran a shekara ta 1425, daidai da shekara ta 2004 miladiyya. sun tsaya tsayin daka na tsawon kwanaki takwas.[46].[47] ya yi shahada bayan yaƙin gaba da gaba , A wani labarin kuma, bayan da ya samu rauni a kai da kafafunsa kuma ya rasa ganinsa, bayan kama shi ya yi shahada.[48] An ce a wannan yaƙin an kashe ‘yan Husi ɗari bakwai da sojojin Yaman dubu goma sha biyar.[49] shugaban sojojin Amurka ya aika da wasiƙa zuwa ga Ali Abdullah Saleh ya taya shi murna da godiya.[50] A shekarar 2013 ne aka miƙa gawar Sayyid Hussein ga iyalansa, aka kuma binne shi a birnin Maran[51] An gina wani wurina kan kabarinsa, wanda aka lalata a shekarar 2015 saboda hare-haren da kawancen Saudiyya suka kai wa garin.[52]

Bayanin kula

  1. Shafukan Masrekha Man Hayat al-Shaheed al-Qaid al-Sayed Hossein Badr al-Din al-Houthi, shafi na 15.
  2. [https://www.rahianenoor.com/fa/news/17187 زندگی‌نامه شهید شاخص راهیان نور سید حسین بدرالدین حوثی
  3. الحوثیون من هم و کیف نشأت حرکتهم
  4. شیعه زیدی جارودی
  5. "الشہید القائد السید حسین بدر الدین الحوثی کی مختصر تفصیل"، انصار اللہ ویب سائٹ۔
  6. جماعة الحوثی (تنظیم الشباب المؤمن/انصارالله) ابرز الشخصیات
  7. حسین الحوثی... من الدعوه الی التمرد
  8. جماعة الحوثی (تنظیم الشباب المؤمن/انصارالله) ابرز الشخصیات»، وبگاه طریق الاسلام.
  9. Al-Mujahid, “Al-Tshi’i fi Sa’ada – tunanin al-Shabaab al-Mu’min fi al-Mizan”, shafi na 196.
  10. Al-Hiyal, Man Fekr al-Shaheed al-Houthi, 1422 AH, shafi na 6.
  11. Al-Hiyal, Man Fekr al-Shaheed al-Houthi, 1422 AH, shafi na 6.
  12. Sheikh Hosseini, janbashe Ansarullah Yemen, 2014, shafi na 245.
  13. "Al-Sayyed Hossein Al-Houthi.. Al-Fikr Al-Jihadi wa Al-intama Al-Alimani", jaridar Al-Wafaq, Satumba 11, 2023, shafi na 7.
  14. السید حسین بدرالدین الحوثی من الولاده.. الی معراج الشهاده»
  15. Sheikh Hosseini, Janbashe Ansarullah Yemen, 2014, shafi na 273.
  16. الشهید حسین بدرالدین الحوثی»، وبگاه الخنادق
  17. رقه، «السید حسین الحوثی.. الفکر الجهادی و الانتماء الیمنی»، وبگاه شبکه خبری المیادین
  18. رقه، «السید حسین الحوثی.. الفکر الجهادی و الانتماء الیمنی»، وبگاه شبکه خبری المیادین
  19. السید حسین الحوثی.. الفکر الجهادی و الانتماء الیمنی»، وبگاه شبکه خبری المیادین
  20. جماعة الحوثی (تنظیم الشباب المؤمن/انصارالله) - حسین الحوثی و الثورة الایرانیه و رموز التشیع»، وبگاه طریق الاسلام
  21. جماعة الحوثی (تنظیم الشباب المؤمن/انصارالله) - حسین الحوثی و الثورة الایرانیه و رموز التشیع»، وبگاه طریق الاسلام.
  22. جماعة الحوثی (تنظیم الشباب المؤمن/انصارالله) - حسین الحوثی و الثورة الایرانیه و رموز التشیع»، وبگاه طریق الاسلام.
  23. جماعة الحوثی (تنظیم الشباب المؤمن/انصارالله) - حسین الحوثی و الثورة الایرانیه و رموز التشیع»، وبگاه طریق الاسلام.
  24. جماعة الحوثی (تنظیم الشباب المؤمن/انصارالله) - حسین الحوثی و الثورة الایرانیه و رموز التشیع»، وبگاه طریق الاسلام.
  25. السید حسین بدرالدین الحوثی من الولاده.. الی معراج الشهاده»، وبگاه انصارالله
  26. حسین الحوثی... من الدعوه الی التمرد»، وبگاه شبکه خبری الجزیره»
  27. الشهید حسین بدرالدین الحوثی»، وبگاه الخنادق.
  28. السید حسین بدرالدین الحوثی من الولاده.. الی معراج الشهاده»، وبگاه انصارالله
  29. السید حسین بدرالدین الحوثی من الولاده.. الی معراج الشهاده»، وبگاه انصارالله
  30. «حسین الحوثی... من الدعوه الی التمرد»، وبگاه شبکه خبری الجزیره».
  31. الحوثیون من هم و کیف نشأت حرکتهم»، وبگاه شبکه خبری BBC.
  32. شیخ حسینی، جنبش انصارالله یمن، ۱۳۹۳ش، ص۲۴۲
  33. Sheikh Hosseini, janbashe Ansarullah Yemen, 2014, shafi na 243.
  34. Sheikh Hosseini, janbashe Ansarullah Yemen, 2014, shafi na 114.
  35. Sheikh Hosseini, janbashe Ansarullah Yemen, 2014, shafi na 114.
  36. حسین الحوثی... من الدعوه الی التمرد»، وبگاه شبکه خبری الجزیره»
  37. رقه، «السید حسین الحوثی.. الفکر الجهادی و الانتماء الیمنی»، وبگاه شبکه خبری المیادین
  38. Safhat Masrekha Man Hayat al-Shaheed al-Qaid al-Sayed Hossein Badr al-Din al-Houthi, shafi na 28-31.
  39. نبذه مختصره عن الشهید القائد السید حسین بدرالدین الحوثی»، وبگاه انصارالله
  40. من حسين الحوثی الی عبدالملک... انصارالله(۲)»، وبگاه آرشیو شبکه خبری المنار
  41. «زندگی‌نامه شهید شاخص راهیان نور سید حسین بدرالدین حوثی»، پایگاه اطلاع‌رسانی ستاد مرکزی راهیان نور
  42. حسین الحوثی... من الدعوه الی التمرد»، وبگاه شبکه خبری الجزیره».
  43. «زندگی‌نامه شهید شاخص راهیان نور سید حسین بدرالدین حوثی»، پایگاه اطلاع‌رسانی ستاد مرکزی راهیان نور
  44. رقه، «السید حسین الحوثی.. الفکر الجهادی و الانتماء الیمنی»، وبگاه شبکه خبری المیادین
  45. رقه، «السید حسین الحوثی.. الفکر الجهادی و الانتماء الیمنی»، وبگاه شبکه خبری المیادین
  46. «السید حسین بدرالدین الحوثی من الولاده.. الی معراج الشهاده»، وبگاه انصارالله.
  47. السید حسین بدرالدین الحوثی من الولاده.. الی معراج الشهاده»، وبگاه انصارالله؛ «جواس لست انا من قتل حسین بدرالدین الحوثی و هذا ما عثرت علیه فی جعبته بعد مقتله»، وبگاه الحکمه نت.
  48. سید حسین بدرالدین الحوثی بنیانگذار انصارالله یمن»، وبگاه اویس قرنی
  49. Sheikh Hosseini, Janbashe Ansarullah Yemen, 2014, shafi na 87
  50. رقه، «السید حسین الحوثی.. الفکر الجهادی و الانتماء الیمنی»، وبگاه شبکه خبری المیادین
  51. رقه، «السید حسین الحوثی.. الفکر الجهادی و الانتماء الیمنی»، وبگاه شبکه خبری المیادین
  52. رقه، «السید حسین الحوثی.. الفکر الجهادی و الانتماء الیمنی»، وبگاه شبکه خبری المیادین

Nassoshi