Harin Iran kan Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila

Daga wikishia
Harin Iran kan Isra'ila
Wannan maƙala ko wani ɓangare daga gareta, ya ƙunshi wani muhimmin abu da ya faru a ayyananniyar wata rana.

Bayan wani lokaci tana iya yiwuwa cikin gaggawa labarai su canja, labaran farko-farko suna iya kasancewa marasa inganci. Kuma sabbin abubuwan sabuntawa ga wannan labarin na iya yin nuni ga duk abin da ya faru game da wannan al’amari. Da fatan za a inganta wannan labarin.

Harin Iran kan Haramtacciyar ƙasar Isra’ila (Larabci:الهجوم الإيراني على إسرائيل) ko kuma ace ofireshin ɗin wa’adus sadiƙ (Gasgataccen alƙawari) wani ofireshin ne na soja da jamhuriyar muslunci ta Iran ta kai kan haramtacciyar ƙasar Isra’ila. An buɗe wannan ofireshin da kalmar “Ya rasulillah” da asubahin ranar lahadi 14 ga watan Afrilu 2024 miladiyya wanda ya yi daidai da 26 ga watan Farwardin hijira shamsi tare da harba gomman makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan haramtacciyar ƙasar Isra’ila, wannan shi ne karo na farko da Iran ta ƙaddamar da hari kai tsaye kan haramtacciyar ƙasar Isra’ila.

Sharhi kan Wannan Hari

Wannan ofireshin ya zo matsayin ramuwar gayya bayan ita haramtacciyar ƙasar Isra’ila ta kai hari kan ofishin jakadancin jamhuriyar muslunci ta Iran da yake ƙasar Siriya a ranar[1] ga watan afrilu 2024 milidiyya. cikin wannan hari da Isra’ila ta kai kan ofishin jakadancin Iran mutane bakwai sun yi shahada daga dakarun kare juyin juya halin muslunci na Iran, daga cikinsu akwai Muhammad Rida Zahidi, ɗaya daga manyan kwamandojin Sojojin ƙudus.[2]

Me Yasa ta Kai Hari kan Isra'ila

Dakarun ƙudus cikin bayani sun bayyana wannan ofireshin tare da bayyana cewa ya kasance wani ɓangare cikin ladabtar da haramtacciyar ƙasar Isra’ila wanda ya samu sahhalewar majalisar tsaron al’ummar Iran da take ƙarƙashin sojojin ƙasar Iran.[3] haka nan kuma wannan ofireshin ya samu goyan bayan sojojin jamhuriyar ƙasar Iran. kuma ma’aikatar tsaron Iran ta bada labarin wannan ofireshin.[4] dama tun gabani Ayatullah Khamna’i jagoran jamhuriyar muslunci ta Iran ya yi alƙawari sai an ladabtar da haramtacciyar ƙasar Isra'ila,[5] tare da kunyata su,[6] wakilan Iran a majalisar ɗinkin duniya sun shelanta cewa wannan ofireshin wani halastaccen ofireshin ne bisa ƙudurin doka mai lamba 51 ta majalisar ɗinkin duniya [tsokaci 1] [7] Rahotannin kafafen labarai: ba’arin wasu ƙasashe misalin Amurka, Ingila da Jodan sun taimakawa haramtacciyar ƙasar Iran cikin harbo makaman da Iran ta aika kan Isra’ila;[8] amma tare da haka an samu adadi mai yawa daga makaman da Iran ta harba sun faɗa kan Isra’ila.[9]

Bayan ƙaddamar da wannan hari, gungun jama’a daga ƙasashen Iran, Iraƙi, Labanun da gaɓar kogin jodan sun fito tituna suna nuna murna da wannan hari, haka nan cikin garuruwa daban-daban a Iran nam ma mutane sun fito suna nuna murna da goyan bayan wannan hari.[10]

Saukar Makaman Iran kan Cibiyoyin Soja na Haramtaccciyar ƙasar Isra'ila

Kan asasin rahotannin madogaran kafafe yaɗa labarai, wasu ba’arin ƙasashe misalin Amurka, Ingila[11] da Jodan[12] sun taimakawa Isra’ila cikin kakkaɓo makaman Iran masu linzami da jirage marasa matuƙa, amma duk da haka bisa rahotanni lallai wani adadi daga makamai masu linzami sun yi sauka kan tashar filin sauka da tashin jiragen yaƙi na Isra’ila mai suna ramun da na Nawatim[13] bisa rahotan tashar Aljazira cikin naƙaltiwa daga jaridar yadi’ut akaranut ta Sahayoniya, Isra’ila ta yi asarar dalar Amurka biliyan ɗaya da talatin da biyar cikin kakkaɓo waɗannan makamai da Iran ta harba kanta daidai lokacin da Ita iran kaso goma cikin ɗari ta kashe cikin harba waɗannan makamai daga abin da Isra’ila ta yi asara cikin kakkaɓo su.

Martani

Daidai lokacin da dakarun ƙudus suke ƙaddamar da hari kan Isra’ila, gungun mutane daga garuruwa daban-daban na Iran misalin Tehran, Isfahan da Kerman[14] da ma a ƙasar Lubnan[15] Iraƙi 18 sun fito kan tituna suna nuna murna, haka nan a ranar 15 ga watan Afrilu ma sun cigaba murna[16] a wasu ƙasashen ma mutane sun ta nuna goyan bayansu ga Iran kan wannan hari[17] [18] Malamai da fitattun mutane daga ma’abota addini da `yan siyasa sun yi magana kan wannan hari, daga jumlarsu akwai Ayatullah Makarim Shirazi daga maraji’an addini, ya siffanta wannan hari matsayin sababin farin ciki da ɗaukakar al’ummar musulmi.21 Ayatullah Nuri Hamadani shima cikin saƙon da ya aiko ya bayyana cewa wannan hari ya kasance a mahallin da ya dace kuma yana nuna goyan bayansa kansa.[19] haka nan cikin shafin da ake danganta shi da Ahmad bin Hamdi Alkhalili babban mufti a masarautar Oman cikin kafar sada zumunta ta X ya siffanta wannan mataki da Iran ta ɗauka matsayin abin farantawa.[20]

Tambayoyi Masu Dangantaka

  • Tufanul Al-Aksa

Bayanin kula

  1. «حمله گسترده موشکی و پهپادی ایران به اسرائیل آغاز شد»، خبرگزاری تسنیم
  2. «حمله اسرائیل به کنسولگری ایران در سوریه و شهادت ۷ عضو ارشد سپاه (+فیلم و عکس)»،
  3. «ده‌ها فروند پهپاد و موشک به سمت سرزمین‌های اشغالی شلیک شد»، خبرگزاری ایرنا.
  4. «ده‌ها فروند پهپاد و موشک به سمت سرزمین‌های اشغالی شلیک شد»، خبرگزاری ایرنا
  5. «خطبه‌های نماز عید فطر»، سایت دفتر حفظ و نشر آثار حضرت آیت‌الله العظمی خامنه‌ای
  6. «پیام در پی شهادت سرلشکر پاسدار محمدرضا زاهدی و همرزمانش»، سایت دفتر حفظ و نشر آثار حضرت آیت‌الله العظمی خامنه‌ای
  7. «نمایندگی ایران با هشدار به اسرائیل: اقدام نظامی بر اساس بند ۵۱ منشور سازمان ملل بود»، خبرگزاری ایرنا
  8. «الأردن: اعترضنا أجساما طائرة دخلت مجالنا الجوي»، الجزیره.
  9. «مشاهد توثق إصابة مسيرات إيرانية لأهدافها في القصف على فلسطين المحتلة»، المیادین
  10. «إسرائيل أنفقت 1.5 مليار دولار في ليلة واحدة لصد الهجوم الإيراني»، الجزیره
  11. «پیام در پی شهادت سرلشکر پاسدار محمدرضا زاهدی و همرزمانش»، سایت دفتر حفظ و نشر آثار حضرت آیت‌الله العظمی خامنه‌ای
  12. «القوات الأمريكية والبريطانية اعترضت أكثر من 100 مسيرة إيرانية قبل وصولها إلى إسرائيل»
  13. https://www.aljazeera.net/news/2024/4/14/الأردن-اعترضنا-أجساما-طائرة-دخلت «الأردن: اعترضنا أجساما طائرة دخلت مجالنا الجوي»]، الجزیره
  14. «ای. بی. سی نیوز: ۹ موشک ایران به ۲ پایگاه اسرائیل اصابت کرد.»، خبرگزاری ایرنا.
  15. https://www.aljazeera.net/news/2024/4/14/إسرائيل-أنفقت-1-5-مليار-دولار-في-ليلة «إسرائيل أنفقت 1.5 مليار دولار في ليلة واحدة لصد الهجوم الإيراني»]، الجزیره
  16. «حشود إيرانية تحتفي بالهجوم على إسرائيل»، الجزیره
  17. «شادی مردم عراق در خیابان های بغداد از حملات موشکی و پهپادی ایران به اسراییل»، آپارات
  18. برای نمونه نگاه کنید به «حامیان عملیات «وعده صادق» در پاکستان به خیابان‌ آمدند»، خبرگزاری ایرنا
  19. «پیام حضرت آیت الله العظمی مکارم‌شیرازی(مدّظلّه العالی)»، بلیغ‌نیوز
  20. «المفتي العام لسلطنة عمان: الرد الإيراني على الكيان الصهيوني أمر يسر الخاطر حقا + صورة التغريدة»، وکالة أبنا العالمية

Nassoshi