Sayyid Abbas Musawi

Daga wikishia
File:السيد عباس الموسوي.jpg
Sayyid Abbas Musawi

Sayyid Abbas Musawi (Larabci: السيد عباس موسوي) "Rayuwa: 1952-1992m" ya kasance mutum na biyu cikin jerin sakatarorin ƙungiyar hizbullahi lubnan. Farko-farkon fara ayyukansa na jihadi ya fara ne tare da dakarun palasɗin cikin tunkarar `yan mamayar sahayoniya, lokacin da ya tafi ƙasar iraƙi karatu ya yi gwagwarmaya kan gwamnatin `yan ba'as, yayin da ya koma ƙasarsa ta lubnan tare da samar da ƙungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi yaƙi ya zafafa tsakaninsu da haramtacciyar gwamnatin isra'ila.

Sayyid Abbas Musawi ya kasance mutum da ya yi matuƙar tasirantuwa da tunanin Sayyid Muhammad Baƙir Sadar da Imam Khomaini, a shekarar 1979 lokacin da ya je ƙasar Iran ya gana da Imam Khomaini. Sayyid Abbas Musawi a shekarar 1991m an naɗa babban sakataren ƙungiyar hizbullahi, a shekarar 1992m sojojin haramtacciyar gwamnatin isra'ila suka shahadantar da shi.

Karatu A Lubnan Da Najaf

An haifi Sayyid Abbas Musawi a shekarar 1952m cikin Shisu ƙarƙashin garin Ba'alabak.[1] a shekarar 1966m a garin Sur ne ya fara sanin Imam Musa Sadar kuma bisa shawararsa ne ya shiga hauza ilimiyya ta garin Sur (Ma'ahad Ad-dirasat Al-islamiyya) ya fara karatun hauza a can. .[2]

Sayyid Abbas Musawi a shekarar 1967m domin ci gaba da karatun hauza ya je garin Najaf ya halarci darasin Sayyid Abu ƙasim Khuyi da Sayyid Muhammad Baƙir Sadar..[3] yana ƙarfaffar alaƙa tare da Sayyid Muhammad Baƙir Sadar kuma shi ne mutum da ya bada gudummawa share fage alaƙar Sayyid Hassan Nasrallah tare da Sayyid Muhammad Baƙir Sadar.[4]

Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Labanon, yana Siffanta malaminsa Sayyid Abbas Musawi:
Malami mai ikhlasi, mai bibiyar lamurran ilimi da tarbiyyar dalibai, abin koyi a aikace a takawa, da'a da addini. Jajirtaccen malami,wanda bai san gajiya ba, mai addu'a da kuka da raya dare da ibada. Masoyin manzon Allah da iyalan gidansa, zurfafa alaka da Sayyid Muhammad Bakir Sadar, daukar Imam Khumaini a matsayin wani aiki na biyayya, cikakken biyayya ga Sayyid Ali Khamene'i, ya jajirce wajen yi wa al'umma hidima, da rashin tsoron wanin Allah, da sadaukarwa. a tafarkin tsayin daka na Musulunci har zuwa shahada.[5]

Ayyuka A Labanun

Zamanin da Sayyid Abbas Musawi ya zauna a ƙasar Iraƙi sakamakon ayyukansa na siyasa kan gwamnatin ba'as ta Iraƙi ya fuskan matsanancin matsin lamba da takura daga gwamnatin iraƙi, da wannan dalili a shekarar 1979m ya tattara kayansa ya koma labanun[6] bayan komawarsa ne ya kafa hauza mai suna Madrasatul Al-imam Al-muntazar a garin Ba'alabak, har ila yau matarsa mai sunan Zahra[Tsokaci 1] ita ta gina makaranta domin koyar da `yan uwanta mata[7] haka nan Sayyid Abbas Musawi ya samar da majalisi mai suna taron (Tajammu ulama muslimin) domin ƙarfafa haɗin kai da tafiya tare da juna tsakanin malaman ƙasar lubnan.[8]

A shekarar 1982m bayan mamaye ƙasar labanun da sojojin isra'ila suka yi, shi da wasu adadin matasa sun yi taro a garin Darra Baƙa sun samar da wasu jama'a da za su tunkari isra'ila domin korar ta daga cikin ƙasar labanun, waɗannan jama'a ne daga baya suka juye suka zama ƙungiyar hizbullahi lubnan. [9]

Babban Sakataren Hizbullahi

Tushen ƙasida: Hizbullahi Lubnan

A watan Mayu shekarar 1991m babbar majalisar shura ta hizbullahi lubnan suka naɗa Sayyid Abbas Musawi matsayin babban sakataren ƙungiyar hizbullahi, gabaninsa Subhi Ɗufaili ne ya kasance babban sakataren hizbullahi.[10]

Shahada

A ranar 16 ga watan Fabrairu shekara ta 1992m bayan halartar bikin shekara-shekara da tunawa da shahadar Shaik Ragib Harbi daidai lokacin da shi Sayyid Abbas yake dawowa daga bairut ne Isra'ila ta kai harin kansa da makami ta jirgin sama suka shahadantar da shi tare da ɗansa da matarsa.[11] matuƙin jirgin da ya harba makami ya kashe Sayyid Abbas ya yi bayani filla-filla yadda lamarin ya kasance,[12] jaridar Yedioth Ahronoth ta isra'ila[Tsokaci 2] a shekarar 2012m ta kawo bayani dalla-dalla yadda aka tsara kashe Sayyid Abbas Musawi.[13]


Biyo bayan kashe Sayyid Abbas Musawi, Ayatullahi Khamna'i jagoran jamhiriyar muslunci cikin wani saƙo da ya aiko, ya siffanta Sayyid Abbas Musawi matsayi babban mutum jarumi wanda ya kasance tare da iklasi, tare da nuna cewa shi Sayyid Abbas Musawi ya kasance cikin mutane da suka rayuwa cikin aiki da ilimin da Allah ya ba su tare da sadaukarwa cikin neman yardarsa.[14]

Nazari

Akwai rubuce-rubuce da aka yi game da Sayyid Abbas Musawi, ba'arinsu sun kasance kamar haka:

  • Littafin Zindagi Wa Mubarazati Shahid Musawi (Babban sakataren hizbullahi) talifin Gulam Reza Zawwara. Za a samu littafin cikin wannan sayitاینجا
  • Littafin "Zubrur Al-hadid 2"talifin Fatima Muslih Zadeh.[15]
  • Mujallar wata-wata "Shahid Yaran"rubutu na musammam kan Sayyid Abbas Musawi mai taken "Zaitun Surkh"za ku iya samun kwafin wannan jarida a nan wurinاینجا
  • Documentary: Zindagi Khob, Marge Khob, wanda tashar talabijin ta ƙasar Iran ta shirya da nuna shi, za ku iya samunsa a wannan sayit ɗinجمهوری اسلامی ایران. این مستند را از اینجا

Bayanin Kula

  1. «زندگی شهید سید عباس موسوی دبیرکل سابق حزب‌الله»، خبرگزاری تسنیم.
  2. Goli Zavareh, "Kollatu mukawama", Sayit Farhangiktan Tamaddun Shi'a.
  3. «زندگی شهید سید عباس موسوی دبیرکل سابق حزب‌الله»، خبرگزاری تسنیم.
  4. «روایت سید حسن نصر الله از شهید محمد باقر صدر»، سایت ایمنا.
  5. «خاطرات ناب دبیر کل حزب الله از شهید سید عباس موسوی»، سایت نوید شاهد.
  6. گلی زواره، «قله مقاومت»، سایت فرهیختگان تمدن شیعی.
  7. «زندگینامه شهید سید عباس موسوی»، سایت شهید آوینی.
  8. السید عباس الموسوی من الولادة حتی الشهادة
  9. Gali Zuwarah, Zandiki wa Mubarazat Shahid Sayyid Abbas Musawi, 1388H, shafi na 54-55.
  10. دیوسالار، «تاریخچه و عملکرد حزب الله لبنان و نقش انقلاب اسلامی ایران».
  11. «تشابه شهادت رهبران شهید حزب‌الله»، خبرگزاری ایرنا.
  12. «شرح واقعه ترور سید عباس موسوی توسط خلبان مجری این عملیات تروریستی»، سایت شهید آوینی.
  13. «ماجرای ترور شهید سید عباس موسوی از زبان صهیونیست‌ها»، سایت جهان‌نیوز.
  14. «پیام تسلیت در پی شهادت علامه سید عباس موسوی»، پایگاه اطلاع‌رسانی آیت‌الله خامنه‌ای.
  15. «زبر الحدید (سید عباس الموسوی)»، سایت پاتوق کتاب.

Tsokaci

  1. Ummu Yasir (Saham) Kitabe Wusul talifin Abdul-kudus Amin, riwayar rayuwar matar shahid Sayyid Abbas Musawi, fassarar Ahmad Natanzi karkashin taken "Ham Kasam"
  2. Ma'anar "labarai na baya-bayan nan" ita ce jaridar da aka fi bugawa a Isra'ila tun shekarun 1970

Nassoshi