Ofireshin Wa'adus Sadiƙ 3
Wannan rubutu ne game da Ofireshin Wa'adus Sadiƙ. Domin samun bayanai game da Wa'adus Sadiƙ 1, Ku duba: Ofireshin Wa'adus Sadiƙ 1, domin bayan kan Wa'adus Sadiƙ 2 ku duba: Ofireshin Wa'adus Sadiƙ 2.
Wani sashi daga rikici tsakanin Iran da isra'ila da tashar talabijin ta nuna bayan saukowa makamai mazu linzami na dakarun kare juyin juya halin muslunci na Iran, cikin Wa'adus Sadiƙ 3 | |
| Lokaci | 23 ga watan Khordad shekara ta 1404 |
|---|---|
| Wuri | Mamayayyar ƙasar Falasɗinu |
| Dalili | Martani kan harin da Isr'aila ta fara qaddamarwa kan wasu daga cibiyoyin makamashin nukiliya na Iran da sansanonin soji da kwamandojin soja da kuma kan masana makamashin nukiliya |
| Masu yaƙi | |
| Ɓangarori biyu na yaƙi | Jamhuriyar muslunci ta Iran Isra'ila |
| Sojoji | |
| Dakarun kare juyin juya halin muslunci na Iran da
Ƙawancen Ƴan Gwagwarmaya Sojojin Isra'ila, Amurka da Jodan | |
Ofireshin wa'adus sadiƙ 3, wani hari ne na makamai masu linzami tare da jirage marasa matuƙa da jamhuriyar muslunci ta Iran ta ƙaddamar kan Isra'ila a ranar 23 ga watan Khordad shekara ta 1404 shamsi, wanda ya yi daidai da 13 ga watan June shekara ta 2025 domin martani da raddin kan harin da Isra'ila ta fara kai wa kan ita Iran ɗin.
A ranar 23 ga watan Khordad Isra'ila da niyyarta ta ganin bayan Shirin makamashin nukiliya na Iran da kuma canja gwamnati mai ci a Iran, ta ƙaddamar da hari da makamai masu linzami tare da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan ba'arin cibiyoyin makamashin nukiliya ta Iran, sansanonin sojin ƙasa da na sama da unguwanni fararen hula, tare da shahadantar da wasu daga cikin kwamandojin soji misalin Muhammad Baƙiri, Husaini Salami, Amir Ali Haji Zade da wasu adadi daga masana nukiliya na Iran.
Sojojin Iran zuwa ranar 21 ga watan June, cikin oifireshin wa'adus sadiƙ 3, ƙarƙashin marhalolin hare-haren makamai masu linzami har guda 20 da kuma marhala 8 ta harba jiragen yaƙi marasa matuƙa, sun kai hari kan muhimman cibiyoyin soji, cibiyoyin da leƙen asiri da tattara bayanan sirri na Isra'ila daga jumlar cibiyar Wayizma, Mosad, Aman da ba'arin sansanonin sojin sama. Tare da kai hari Yanar giza gizo kan cibiyoyin leƙen asiri da makaman kariyar tsaron sararin samaniya na Isra'ila.
Babban saƙon wannan ofireshi, bisa bayanan dakarun kare juyin juya halin muslunci na Iran, shi ne sanar da Isra'ila da ƙawayenta cewa tsaron Iran jan layi ne da ba a tsallaka shi.
Soke tattaunawa ba ta kai tsaye da take gudana tsakanin Iran da Amurka, sakamakon samun Amurka tana goyan bayan Isra'ila kan duk wata keta alfarma kan Iran. Wannan hari da Iran ta kai ya haifar da asara mai yawan gaske ta biliyoyin daloli kan tattalin arziƙin Isra'ila, tare da guguwar hijirar Sahayoniyyawa daga Isra'ila zuwa wasu ƙasashen daban, suna daga abubuwan da suka biyo bayan wannan ofireshin.