Ƙawancen Ƴan Gwagwarmaya
Ƙawancan ƴan gwagwarmaya (Larabci: محور المقاومة) wannan wani Isɗilahi ne da ya ke nuni kan ƙawance tsakani wasu hukumomi da ƴan gwagwarmaya a gabas ta tsakiya waɗanda mafi yawan su ƴan Shi'a ne, kamar Iran da Siriya musamman a lokacin Hafizul Asad da Basharul Asad da Iraƙi da Hizbullah ta Lubnan, kuma hadafin wannan ƙawancan shi ne yaƙar haramtacciyar ƙasar Isra'il da kuma kawo ƙarshan ƙarfin fada-aji da ƙasashan yammacin duniya suke da shi a gabas ta tsakiya da kuma kare ƴancin ƙasar Falasɗinu da yaƙar tasirin yammacin duniya a gabas ta tsakiya, masamman tasirin ƙasar Amuruka a yammacin Asiya, da yaƙar hukumomi masu kama-karya da yaƙar ƴan ta'adda kamar su ISIS. Samar da wannan ƙawance ya zo ne sakamakon tasirin juyin juya hali na muslunci da aka yi a ƙasar Iran da sakamakon goyan baya da Jamhuriyar musulinci da Iran ta Iran take bayarwa ga gungiyoyin gwagwarmaya domin yaƙi mulkin danniya da mulkin mallaka.
Ana gani wannan ƙawancen ƴan gwagwarmaya a wannan yanki na gabas ta tsakiya a matsayin wata gamayya da ta ke tarayya kan al'adun mutane da addini da yanayin zaman takewa da suke tarayya a cikinsu, kazalika tasirin siyasa duk sune abubuwa da suka keɓanta da wannan ƙawance, kuma wannan sune abubuwan da suka sa hadin kai tsakanin wannan ƙungiyoyin ƴan gwagwarmaya, daga cikin Shirin wannan ƙawance akwai yawaita sojoji domin fuskantar duk wani kalobale da wannan ƙawance yake fuskanta. ƙarfafar ƴan shi'a da iyankance ci gaba da yaɗuwar haramtacciyar ƙasar Isra'ila da kuma samar da sabon tsasi a yanki yammacin Asiya suna daga cikin abubuwan da wannan ƙawance ya samar, daga cikin abubuwan da ya samar akwai Failaki ƙudus da Hamas da Jihadil Islami a Falasɗinu da Harka Sha'abiyya a Iraƙi, da Hashadush sha'abi, da Hizbullahi Lubnan, da Ansarullah Yaman.
Saboda tattara rahotanni da ayukansu wannan ƙawance ya samar da kafafan watsa labarai, kamar tashar talabihsin ta Al-manar da Shabakatu Al-mayadin da Shabakatu Al-masira da Shabakatu Al-furat. Kazalika tashar radiyo ta jamhuriyyatul islamiyya tana watsa shirye wannan ƙawance.
Matsayin Wannan Ƙawance
Sunan wannan ƙawance da turanci shi ne (Axis of Resistance) ƙawance ne na yankin gabas ta tsakiya sakamakon alaƙa da jamhuriyyamuslunci ta Iran, wanda bisa ra'ayin masu bincike a siyasa suna ganin wannan ci gaban gwamnatin muslunci a Iran shi ne ya kai ga samun canji yadda ake kalo da tafiyar da gwamnatin a yammacin Asiya,[1] kuma haka ne ya kai ga samar da yanayi sabo na yadda ake tafiyar da gwamnati.[2] goyan bayan da gwamanatin muslunci a Iran take bawa ƙungiyoyin gwagwarmaya da ƙungiyoyin masu ƙin jinin mulkin mallaka da mulkin kama-karya da kuma goyan bayan yunkuri da motsawar da al-ummar musulmi suka yi masamman a ƙasashan larabawa, ya kasance dalili na ci gaban da ƙara ƙarfin ƙungiyoyin ƴan gwagwarmaya na shi'a kuma ya kai ga kyautata tsaron Iran a yanki gabas ta tsakiya.[3]
Masu bincike a siyasa suna ganin cewa wannan ƙawance na gwagwarmaya yana tasirantuwa da ayyukan jamhuriyar muslunci ta Iran a bayyane, jamhuriyar muslunci da take ƙoƙarin kin yarda da suka da tasirin ƙasashan masu ƙarfin fada aji a duniya,[4] a cewar masu binciken fitattun alamomi da sirrikan Juyin-juya hali da kafuwarta ya faro ne a lokacin da Saddam Husain ya yaƙi Iran, bayan yaƙin a lokacin yaɗa ra'ayin juyin-juya-hali sai wannan ra'ayi na juyin-juya-hali ya yaɗu a lokacin motsawar al'umma a yankin gabas ta stakiya.[5]
Daga cikin sakamako na ƙarfafa samuwar wannan ƙawance a yammacin gabas ta tsakiya shi ne samun ƙarfin da ƴan Shi'a suka yi a yammacin gabas ta tsakiya,[6] da ƙarfafa neman haƙƙin Falasdinawa da fuskantar jagorancin wasu gwamnatoci a yankin gabas ta stakiya da tabbatar da mutincin jamhoriyar musulinci ta Irana.[7] Da kifar da gwamnatin wasu ƴan kama-karya a gabas ta tsakiya,[8] da koma bayan tasirin Amuruka a gabas ta stakiya da kuma ƙalobalantar sulhu da harmatacciyar ƙasar Isara'il da kuma fitar da sojojin Isra'il daga ƙasar Lubnan,da kuma rashin nasarar gwamnatin Isra'ila ta yi a yakin kwana 33 da 22 da yaƙar gungun ƴan ta'adda kamar ISIS.[9]
Kafuwa Da Sa Suna
Kalmar "Mihiwarul Muƙawama" ko "Mihwarul Mumana'a" ana amfani da shi ne ga rukunin kasashe da gwamnatoci, da kuma ga gungun ƙungiyoyin Islama da na Shi'a masu ɗauke da makamai da ke da nufin kawo ƙarshen mulkin da ƙasashan yamma ke yi kan yankin Gabas ta Tsakiya, da nuna adawa da ɗaukar matakin da yaƙar ƙasar Isra'ila, da kare ƴancin Falasɗinu.[10]
Ƙawancen gwagwarmaya ana ɗaukar shi ƙawance ne na yanki da yanki (ƙawancen soja da na siyasa) wanda ya ƙunshi ƙungiyoyin da gwamnati da yawa (Iran da Siriya).[11] A lokacin mulkin (Hafizul Asad da Bashsharul Asad) da wasu da waɗanda basa ƙarƙashin gwamnati da Hizbullah a Lubnan.[12] da Hamas da Hartul Jihadul Islami a ƙasar Falasɗinu,[13] ana cewa duk shugabancin wannan tarayya yana hannun Iran ne,[14] kuma ana gani wannan ƙawance ya faru ne sakamakon abubuwa da suka faro a tarihi a ƙarni na ashirin da farkon ƙarni na ashirin da daya domin ƙalubalantar abin da haramtacciyar ƙasar Isra'ila take yi a ƙasar falasɗinu da Lubnan fuskantar kungiyar ƴan ta'adda a Siriya da Iraƙ, da fuskantar tasirin Amuruka a yanking abas ta tsakiya.[15]
Bisa abin da masu bincike a siyasa suka ce, ƴan gwagwarmaya suna da alfanu na ƙasa da aƙida da ta haɗa su, kuma suna ƙoƙarin fuskantar tasirin Amurka ta hanyar siyasarsu mai zaman kanta da gwagwarmaya,[16] a yammacin Asiya, da yaƙar haramtacciyar gwaamnatin Yahudawa da kuma bada kariya ga Falasɗinawa,[17] wannan ƙawance ya faɗaɗa sakamakon wasu abubuwa da suka faro a yammacin Asiya, kamar samuwar ƙungiyar ta'addanci Isis da kuma harin da wasu ƙasashan larabawa suka kai a Yaman a farkon ƙarni na 21, kuma wannan ne ya haifar da samun ƙungiyar Hashadush Sha'abi ta Iraƙi, kazalika gungiyar Ansarullah ta Yaman ta haɗe da wannan ƙawance na ƴan gwagwarmaya.[18]
Ƙawancan Gwagwarmaya Ya Samu Domin Ƙalubalantar Ƙawancen Sharri
Wannan kalma ta ƙawancan ƴan gwagwarmaya an fara amfani da ita ne bayan jawabin da Joj Bush ɗa ga Joj Bush babba ya yi a lokacin da ya ke shugaban ƙasar Amruka a ranar 29-1-2002, inda ya ce Iran da Iraƙi da Koriya ta arewa taran masu sharri ne a duniya[19] bayan haka sai ministan harkokin ƙasashan waje Jon Bultan ya ƙara ƙasar Siriya da Libya a lis ɗin ƙasashan da suke sharri ga ƙasar Amruka kamar yadda suke gani.[20] To bayan hakan sai wata mujalla mai suna Azzahaful Akda ta ƙasar libiya ta yi raddi kan kiran waɗanna ƙasashe madadin taran sharri, sai ta kira su da ƙawancan ƴan gwagwarmaya, kuma sune waɗanda suke tsayawa a gaban tasirin Amuruka a duniya.[21]
Bayan haka ne sai ministan cikin gida na Falasɗinawa a gwamnatin Hamas Sa'id Siyam ya yi amfani da wannan suna a ya yin gidan tibi na Al-alam ya yi hira da shi, domin nuna tarayya kan manufofin siyasa domin yaƙar Amurka da Isra'ila, ya kuma ƙara da cewa Iran da Siriya da gungiyar Hizbullah ta Lubnan da Hamas a Falasɗin sun samar da wannan ƙawance domin yaƙar Amuruka da Isra'ila,[22] Kazalika tsohon ministan harkokin wajen Iran Ali Wilayati wata Magana da ya yi a shekara ta 2010 ya ce yana ganin gwagwarmaya yaƙar ƙasar Isra'il taƙunshi Iran da Siriya da gungiyar Hizbullah ta Lubnan da gwanatin Iraƙi saabowa da gungiyar Hamas. Kuma yana ganin cewa ƙasar Siriya tana taka muhimmiyar rawa ga wannan ƙawaance.[23]
Sayyid Ali Khamna'i shugaban addinin muslunci a ƙasar Iran ya yi amfani da wannan kalma ta gwargwarmaya a shekara ta 1993 a lokacin ganawar shi da shugaban ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar lubnan Sayyid Hassan Nasarullah, ya ce wannan ƙawanci an kafashi ne sakamakon zalinci ƙasar Isra'il wadda bawai kawai takasa cima hadafinta na siyasa bane, a'a abin da take yi kai ga haɗin kai tsakanin alumar ƙasar lubnan da haɗewar alummu domin yaƙar ƙasar Isra'il.[24]
Ƙungiyoyin Ƙawancen Gwagwarmaya
Ƙungiyoyin da suka haɗa wannan ƙawance suna ƙasashe daban-dabana, Iran a kwai Failaƙul ƙudus da waɗanda suke ƙarƙashinshi, sojojin Zainabiyyawa da Faɗimiyyawa. Iraƙi: akwai Hashadush sha'abi da Failaƙu Badar da Kata'ib Hizbullah da Hizbu Da'awa Al'islamiyya da Majalisul A'ala Al'islami da kuma Tayarus Sadari. A Siriya akwai sojojin gwamanati da Dafaul Waɗani a lokacin Hafiz da Basharul Asad. A Yaman akwai Ansarullah A Lubnan akwai Hizbullah A Falasɗin akwai Jihadul Islami Alfalasɗiniya da Hamas.[25]
Sahu | Suna | Shekarar Da Aka Kafa | Wanda Ya Kafa | Fitattun Mutane | Jagora | Mazhaba | Inda Ya Taso | Take (Logo) | Kafafen Watsa Labarai |
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
1 | Harkatul Amal | 1974 miladi | Imam Musas Sadar | Mustafa Shimran | Nabi Birri | Shia | Lubanun |
![]() |
Tashar NBN |
2 | Harkatul Jihadil Al-islami | 1981 miladi | Fatahish Shiƙaƙi | Ramadan Abdullahi Abu Harbid | Ziyad Nakhala | Ahlus-sunna | Gaza |
![]() |
Tashar Falasɗinul Yaumi |
3 | Hizbullahi Lubnan | 1982 miladi | Sayyid Abbas Musawi | Sayyid Hassan Nasrullah | Na'im Ƙasim | Shi'a | Labanun |
![]() |
Tashar Al-manar. Radiyon An-nur |
4 | Munazzamatul Badar | 1985 miladi | Adnan Ibrahim Abu Mahadi Al-muhandis | Hadi Al-amiri | Shi'a | Iraƙ |
![]() |
Tashar Al-ghadir | |
5 | Harkatu Hamas | 1977 miladi | Shaik Ahamd Yasin | Abdul-Aziz Rantisi Isma'il Haniyye Yahaya Sinwar | Majalisar Zartarwa ta wucin gadi ta Hamas | Ahlus-sunna | Falasɗinu |
![]() |
|
6 | Failaƙ Kudus | 1990 miladi | Sayyid Ali Khamna'i | Ahmad Wahidi | Ƙasim Sulaimani Isma'il Ƙa'ani | Shi'a | Iran |
![]() |
|
7 | Ansarullah Yaman | 1990 miladi | Sayyid Husaini Husi | Badrud-dini Al-husi | Abdul_malik Al-husi | Zaidiyya | Yaman |
![]() |
Tashar Al-masira |
8 | Kata'ibu Hizbullah Iraƙ | 2003 miladi | Abu Mahadi Al-muhandis | Abu Husaini Al-humaidawi Abu Baƙir Al-sa'idi | Ahmad Muhsin Farhu Al-humaidawi | Shi'a | Iraƙ |
![]() |
Tashar Al-ittija |
9 | Kata'ibu Sayydush Shuhada Iraƙ | 2003 miladi | Abu Mustafa Khaz'ali Alhaji Abu Yusuf | Abul Ala'i Al-wala'i | Shi'a | Iraƙ |
![]() |
||
10 | Isabu Ahul Haƙƙi | 2004 miladi | Ƙaisu Khaz'ali | Abdul-Hadi Darraji Muhammad Al-bahaduli | Ƙaisu Khaz'al | Shi'a | Iraƙ |
![]() |
Tashar Al-ahad |
11 | Harkatul Nujaba | 2013 miladi | Akram Ka'abi | Abu Isa Iƙlim Mushtaƙ Kazim Al-hawari | Akram Ka'abi | Shi'a | Iraƙ | ||
12 | Liwa'u Zainabiyyun | 2013 miladi | Wasu gungun jama'a daga Fakistan | Zainab Ali jafari Aƙid Malik Muɗahhar Husaini | Shi'a | Fakistan |
![]() |
||
13 | Liwa'u Faɗimiyyun | 2013 miladi | Wasu adadin mutane daga mujahidan shi'ar Afganistan | Ali Rida Tawassuli Sayyid Muhammad Hassan Al-husaini Sayyid Ahmad As-sadat | Shi'a | Afganinstan |
![]() |
||
14 | Hashadush Sha'abi | 2014 miladi | Hadi Al-amiri Abu Mahadi Al-muhandis | Falihu Fayyaz | Shi'a | Iraƙ |
![]() |
Dabaru Da Halaye Na Musamman
Mambobin ƙawance gwagwarmaya sun yi ittifaki akan dabaru da halaye masu yawa. Haka kuma, an ce mambobin wannan ƙungiya suna ƙoƙarin cimma burinsu ta hanyar ƙarfafa karfin soja.
Shaidar Yanki
Halayya ta gari da al'adu na alumma da na addini da al'adun da ƴa'yan wannan ƙawance suka yi tarayya, suna daga cikin abubuwa da suka kai ga samar da wannan ƙawance inji masu fashin baƙi a siyasa, duk da nisan guri da rashin iyaka a tsakanin wasunsu daga cikin ƴa'yan wannan ƙawance,[26] duk da haka suna riƙo da cewa su ƴan wannan yanki ne, kuma akayi la'akari da cewa shi wannan ƙawance na ƴan wannan yanƙi ne, duk da banbanci da yake tsakani kuma suna ƙoƙari wajan nuna halayya ta gari da al'ada gama gari ga waɗanda suke da tasiri a yankin.[27]
Bisa ra'ayin masu hankali shi wannana ƙawance yana ƙoƙarin isa ga hadafin shi ta hanyar kafa hujja da koyarwa ta addini, kamar yaƙi da masu mulkin kama-karya da dogaro kan haɗin kan duniyar musulmi da yaƙar manya ƙasashe masu babakere a duniya,[28] An kuma ce daga cikin abubuwa da suka yi tasiri kan samar da wannan ƙawance akwai al'adar yin shahada,[29] da taimakon waɗanda aka zalinta da ƙoƙarin samar da adalci da neman ƴanci da goyan bayan duk wannan motsi domin ƴanci da aƙidar imam Mahadi da fata da siyasa irin ta addini, irin wadda aka kafa a Iran bayan juyin-juya-hali a ƙasar Iran.[30]
Wasu masu bincike suna ganin samar da wannan ƙawance na yanki yana ƙaro da wani ƙawance da aka samar a gabashin Asiya wanda wasu ƙasashe na Larabawa suka samar wanda ya ke ƙoƙarin samar da dai-daito tsakaninsu da haramtacciyar ƙasar Isra'il da kuma tsayar da tasirin Iran.[31]
Tasirin Siyasar Muslunci
Ana ɗaukar siyar muslunci a matsayin abu mafi tasiri kan abubuwan da suke faruwa a yammacin gabas ta tsakiya a shekarun baya-bayannan, kazalika amfani da ɓangaranci na aƙida a gurin Salafawa da masu kafirta mutane ya sabbaba rashin tsari da amfani da ƙarfi da saɓani na addini a yankin gabas ta tsakiya,[32] a hannu guda kuma an samar da wani yanayi sabo wanda ake kira da gwagwarmayar ƴan shi'a wadda ta samo a lokacin da aka yi juyin-juya-hali na muslunci a Iran da kafa gwamnatin ƴan shi'a a Iran, tare da haɗewar wasu gungun ƴan gwagwarmaya kamar Hizbullah da wasu na ƴan shi'a a Iraƙi da Ansarulalh a Yaman kai da ma wasu gungun ƴan gwagwarmaya na Ahlus-sunna kamar Hamas da Jihadul Islami duk waɗannan abubuwa sun haifar da wani yanayi na masamma a gabas ta tsakiya.[33]
Ƙara Yawan Sojoji Da Makami Domin Samun Dai-daito a Varfin Soja
Ƙara yawan sojoji da makami ga ƙasashan ƴan gwagwarmaya da ƙarfafar ƙungiyoyin da suke tare da su saboda ƙalubalan da ƙawancan ya ke samu, kuma ya yi ƙaranci ga wannan ƙawance ya takali ko ya tsokani ƴan hamayyarshi a wannan a yanki, kuma wannan ɗaya ne daga cikin tsarin wannan ƙawance.[34] bisa abin da masu bincike na ƙasa da ƙasa kan harkar tsaro suka ce, ƙara ƙarfin soja ga wannan ƙawance na ƴan gwagwarmaya da kusantar manya ƙasashe masu ƙarfin soja yasa kaiwa wannan ƙawance hari yana da wahala saboda asarar da hakan zai jawo ga ƙasashan da suke gaba da wannan ƙawance, ko kuma idan suka kuskura suka kai hari to fa ba ƙaramar asara hakan zai jawo musu ba.[35]
Matakai Da Abubuwan Da Aka Yi Nasara
Tun da aka kafa wannan ƙawance ya ɗauki kwararan matakai da suka kai shi ga matsayin mai taka muhimmiyar rawa a yanki gabas ta tsakiya da duniya baki ɗaya.[36] daga cikin irin matakan da wannan ƙawance ya ɗauka akwai yaƙi da kuma fatattakar da masu gwagwarmayar Falasɗinawa suke yi ga ƙasar Isra'il da Hizbullah, kazalika ƙasar Iran da Iraƙi da kuma Siriya da kuma yaƙar ƙungiyoyi na ta'addanci kamar su Da'ash a Iraƙi da Siriya, a ƙarshe kuma fuskantar ƙasashan larabawa sanda suka kai hari a ƙasar Yaman da Ansarullah suka yi.
Ƙarfafar Shi'a A Gabashin Asiya
Yin gwagwarmaya ɗaya ne daga cikin abubuwa da suka yi tasiri kan ƙarfafar shi'anci a yankin gabas ta tsakiya,[37] sojojin Jamhuriyyar muslunci ta Iran ɗaya ne daga cikin abin da ya ƙarfafi ƴan shi'a da samar da tasiri ga ƙasashe irin Iraƙi,[38] da Yaman,[39] da wani sashi na ƙasar Lubnan,[40] kamar yadda ɗaukaka matsayin ƴan shi'a a cikin aluma da cikin siyasa da alaƙa domin amfanin ko wane ɓangare bisa ra'ayin masu bincike a siyasa ya ƙarfafa wannan ƙawance na ƴan gwagwarmaya, masamman a Iraƙi bayan tinɓuke gwamnatin Saddam, kuma hakan ya fitar da ƴan shi'a daga cikin takurawar Jam'iyyar ƴan Ba'as, hakan ya basu damar yin siyasa da bada gudunmawa a cikin al'umma.[41]
Ƙin Amincewa Da Mamayar Isra'ila
Bisa ra'ayin masu fashin baƙi a siyasa suna ganin cewa kasancewar Isra'ila ƙasa ce mai mamaya da rashin tsayawa iya yankin da aka keɓe mata, ya sa Falasɗinawa su karkata wajan yaƙar ta,[42] da kafa ƙungiya domin yaƙar ta irin su Jihadul Islami da Hamas, wannan gungiyoyin guda biyu sune akakafa domin ƴantar da ƙasar Falatsinawa wadda Isra'il ta mamaye,[43] kuma wannan ƙungiyoyi guda biyu sunyi rigima sosai da Yahudawa,[44] mafi muhimmaci daga cikin akwai bure na ɗaya da na biyu da Falatsinawa suka yi,[45] da yaƙin kwana 22 a Gaza,[46] tsakaninsu Falatsinawa da harin buɗe masallacin Aƙsa.[47]
Fuskantar Yahudawa bai taƙaita ga ƴan gwgwarmayar Falasɗinawa ba, sai da abin ya kai ga cewa Hizbullah ta Lubnan ta kai ga cewa ta kawo ƙarshan mamayar soja da Isra'ila ta yiwa ƙasar Lubnan har tsawan shekara 18 a kudancin Lubnan a shekara ta 2000.[48] haka aka ci gaba da gwabzawa tsakanin Isra'ila da gungiyar Hizbullah a yaƙin da sukayi na kwana 33 a ƙarshan 2005.[49] bayan yaƙin buɗe masallacin Aƙsa gungiyar Hizbullah ta shiga yaƙi da Isra'ila domin taimakawa Gazza, inda aka gwabza mummuna yaƙi a tsakanin ɓangare biyun.[50] inda a wannan fafatawa ne Sayyid Hasan Nasarullah shugaban Hizbullah ya yi shahada da wasu daga cikin shugabanni.[51]
Mamayar Isra'ila wani yanki wanda akafi sani da Tuddan Jaulan a lokacin da akayi yaƙi kwana shida tsakanin Larabawa da Isra'ila a shekara ta 1967 ya kai ga nuna ƙiyayyar ƙasar Isra'ila ga Siriya,[52] ƙila kuma ance ƙiyayyar ta yi muni ne bayan nasara da muslunci ya yi a ƙasar Iran ne, masamman a farkon mulkin Hafizul Asad da ɗanshi Bassharul Asad, kuma hakane ya kai ga samar da wannan ƙawance mai kyau tsakanin Iran da Siriya,[53] amma bisa ra'ayin wasu masu bincike suna gani cewa ɗaya daga cikin babban dalilin da ya sa ƙawance ya kyautata tsakanin Iran da Siriya akwai abubuwan da suke tarayya kansu, yaƙar Isra'ila da taimakawa ƙungiyar Hizbullah ta Lubnan.[54]
Fuskantar gungiyoyin ƴan ta'adda a Iraƙi da Siriya Mamayara ƴan Da'ish, ƴan ta'adda ga wani yanki na ƙasar Siriya da Iraƙi ya sa ƙawancan gwagwarmaya ya ƙara kyautata ƙawancan shi domin fuskantar ƙalubale na soja da na siyasa na tattalin arziƙi da kuma zaman takewa ga ƙasashan wannan ƙawance,[55] kuma hakan ne yasa Iran ta fara tura sojoji da masu bada shawara zuwa Iraƙi da Siriya, domin hana yaɗuwar ƴan Da'ish,[56] kuma kare gurare masu tsarki a Iraƙi da Siriya daga cikin hadda hubbaran Sayyida Zainab (A.S) yana cikin dalilin samuwar Iran a wannan ƙasashe.[57]
Bada Kariya Ga Ansarullah A Yaman A Lokacin Da Ƙasashan Larabawa Suke Yaƙar su
An kafa gungiyar Ansarullah a shekara ta 1990,[58] ita wata ƙungiya ce ta siyasa a Yaman,[59] ana cewa ta tasirantu da Imam Khomaini da gwamnatin muslunci ta Iran.[60] wannan yunƙuri na Ansarullah ya yi nasarar kifar da gwamnati a Yaman a shekara ta 2011 bayan farkawar da al-ummar musulmi suka yi, Ansarullah sun sami damar mamaye wasu yankuna na Yaman, kuma hakan ne yasa Mansur Hadi ya sauka daga kan Mulki na shugabancin Yaman a wancan lokacin, ya koma yankin kudanci inda ya kafa gwamnatin wucin gadi.[61] Sakamakon wasu abubuwa da Mansur Hadi ya yi a bayan kafa gwamnatin a kudanci Yaman kawai sai wasu ƙasashan larabawa suka kai harin soja a Yamana kan Anssarullah domin kwace Mulki daga Ansarullah,[62] amma a ƙarshe wannan hari bai yi nasara ba sakamakon jajircewar Ansarullah.[63]
Yaɗuwar ƙin-jinin Amurka a yammacin Asiya Daga cikin nasarorin da wannan ƙawance ya samu akwai ƙin-jinin Amurka da taƙaita tasirinta a yammacin Asiya,[64] bisa ra'ayin wasu masu bincike suna ganin tin bayan faɗuwar tarayyar Sobiyat Amurka take ƙorin jibge sojojinta a yammacin Asiya domin samar da tsaro ga Isra'la da kare muradunta,[65] saboda haka Amurka ta kafa ƙungiyoyi na ƴan ta'adda da rura wutar saɓani na addini wanda a ƙarshe ya kai ga girgiza tsaron ƙasashan wannan yanki,[66] A hannu ɗaya hakan yasa ƴan gwagwarmaya suka kyautata alaƙarsu ta siyasar yaƙar ƙasashe nasu danniya da fara yaƙar ƴan ta'adda da Isra'ila wanda hakan ya sabbabawa Amurka asara ta fuskar tattalin arzuƙi, wannan ƙawance na ƴan gwagwarmaya ya yaɗa ƙin-jinin Amurka a yankin gabas ta tsakiya kuma a dai-dai lokacin ya iyakance muradun Amurka a wannan yanki.[67]
Harka Watsa Labarai
Wannan ƙawance ya gaggauta samar da kafafe na watsa labarai domin yaɗa ayyukan wannan ƙawance, daga cikin wannan kafafe akwai tashar Al-Manar ta Hizbullah a Lubnan,[68] da tashar Al-mayadin (Wace take Bairut),[69] da tashar Almasira ta Ansarullah a Yaman,[70] da tashar Al-furat Mallakar Majalisul Islami Al'a'ala a Iraƙi,[71] gidan tibi Algadir na Munazzamatul Badar Al'iraƙi,[72] da tashar tibin Tainadat ta Kata'ib Hizbullah a Iraƙi,[73] da tashar Al'ahad ta Asa'ibi Ahlul Haƙa a Iraƙi.[74]
Bugu da ƙari akwai wasu kafafe da suke wa wannan ƙawaance aiki, daga cikin akwai gidan tibi na Jamhuriyar Islamiyya Al'iraniyya shi ma ya kasance yana yaɗa ayyukan wannan ƙawance, kamar yaɗa labarai ko hira kan ayyukan wannan ƙawance masamman baya Tufanul Al-aƙsa,[75] daga cikin akwai Shirin mai suna Bi Ufiƙil Falasɗin,[76] kazalika tashar talabishin ta Al-alam da Press Tv da Shabake Khabar suna cikin tashoshi na Jamhoriyya Islamiyya ta Iran waɗanda suka bada gudunmawa wajan yaɗa ayyukan wannan ƙawance na gwagwarmaya.[77]
A Duba Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Kwaja Saravi wa Suri, "Jumhuriye Islami Iran, Mihwar mukawamat wa shakle dahi be nazme madike garbe Asiya," shafi na 41; Qasemi, "Geopolitics mihwar mukawamat wa amniyat milli jamhuri islami Iran bar asase gufteman inkilb islami," shafi na 28; Shirudi da abokan aikinsa, "Guftemane mukawamat wa tasir an bar nazme amniyati garbe Asiya...," shafi na 226-227.
- ↑ Sadati-Nejad, "Baztabhaye huzur jabhe mukawamat dar mandike garbe Asiya,shafi na 94.
- ↑ Qasemi, "Geopolitics mihwar mukawamat wa amniyat milli jamhuri islami Iran bar asase gufteman inkilb islami," shafi na 29
- ↑ Sadati-Nejad, "Baztabhaye huzur jabhe mukawamat dar mandike garbe Asiya,shafi na 94.Postinchi da Motaghi, "Zabane Siyasi mukawamat islami dar Siyasat bainal milali," shafuffuka na 124-125.
- ↑ Postinchi da Motaghi, "Zabane Siyasi mukawamat islami dar Siyasat bainal milali," shafuffuka na 124-125
- ↑ Abbasi da Mahmoudzadeh, "Tahlili bar himayat ideoloji Iran az mihwari mukawamat dar garbe Asiya," shafi na 117.
- ↑ Arab Amiri wa Emami, "Izztalabi be masabat siyasat kariji ceharcubi baraye tahlil siyasat karijiji Iran mihwari mukawamat," shafuffuka na 104-105; Bagheri da abokan aikinsa, "Tabyin manafi ideoloji Jumhuriyar Islami Iran dar ittihad mausum mihwari mukawamat," shafuffuka na 11-17.
- ↑ Qasemi, "Geopolitics mihwar mukawamat wa amniyat milli jamhuri islami Iran bar asase gufteman inkilb islami," shafi na 29
- ↑ Mahmoudi Raja da abokan aikinsa, "Barrasi mihwari mukawamat wa ayande nizam sulta ba istifadeh az nazariyye nizame jahani," shafuffuka na 7-8 da 23-25.
- ↑ محور المقاومة.. النشأة والتطوّر ووحدة المصير، shafin yanar gzi na Al-mayadin.
- ↑ قائد الثورة الإسلامية المعظم خلال إستقباله الرئيس السوري: نعتبر دعم سوريا دعماً لمحور المقاومة ونفتخر بذلك، الموقع الرسمي لمكتب السيد الخامنئي.
- ↑ حزب الله من المقاومة إلى ما بعد المقاومة، Shafin yanar gizo na Al-manar.
- ↑ Reza Khwah, "Bidari Islami wa ayandeh Mihwari mukawamat," shafi na 32.
- ↑ Jafari-Far da Ahrami, "Tasiri mandikiy dakalat Hezbollah wa Isra'ila dar buhrane Suriya," shafi na 78.
- ↑ Khamenei, "Jawabin a wajen bikin kammala karatun daliban jami'ar kimiyya ta tsaro," wanda aka wallafa a shafin ofishin kiyaye da wallafa ayyukan Ayatollah Khamenei; Basiri, "Wakaye Tahdidat Amniyati Da'ish bar mihwari mukawamat wa tasir an bar amniyate kan barazanar tsaro da ISIS ke yi wa tsayin daka da tasirin Jumhuriya Islami Iran," shafuffuka na 7 da 11 da 13-14 da 20; Karimi, "Nakshe Iran dar huwiyate bakshi beh majmu'eh amniyati mihwar mukawamat," shafuffuka na 12-13.
- ↑ Reza Khwah, "Bidari Islami wa ayandeh Mihwari mukawamat," shafi na 32.Hashimpour da abokan aikinsa, "Huwiyat bakshi Inkilab Islami Iran beh mihwarie mukawamat Islami," shafi na 33; Salimi da Shariati, "Manafi milli Jumhuri Islami Iran, Tadawum ya inkita himayat az nizame kanuni Siriyi," shafi na 77.
- ↑ Karimi, "Nakshe Iran dar huwiyate bakshi beh majmu'eh amniyati mihwar mukawamat," shafuffuka na 3-5.
- ↑ Bagheri da abokan aikinsa, "Tabyin manafi ideoloji Jumhuriyar Islami Iran dar ittihad mausum mihwari mukawamat," shafi 8.Moradi da Shahramnia, "Bohran Syria wa amniyate mandikeyi Jamhuriye Islami Iran," shafuffuka na 129-130.
- ↑ بوش يواصل حربه ضد دول محور الشر، shafin yanar gizo na Al-jazira.
- ↑ محللون: واشنطن تصعد التوتر مع دمشق، shafin yanar gizo na Al-jazira
- ↑ Karimi, "Nakshe Iran dar huwiyate bakshi beh majmu'eh amniyati mihwar mukawamat," shafi 2
- ↑ Khosrow Shahin, "Bazdarandagi Mihwar mukawamat," akan gidan yanar jaridar "Sazandegi."
- ↑ ولايتي : سوريا تمثل الحلقة الذهبية في محور المقاومة، Hukumar Labarai ta Duniya ta Tasnim..
- ↑ Taron Jagoran Juyin Juya Hali na Musulunci da Sakataren Janar na Hezbollah, a shafin hukuma na Sayyid Ali Khamenei.
- ↑ Ayoozi da Nawazani, "Mihar Mukawamat beh masabat huwiyye mandikeyi Shaidar Yanki," shafi na 13.
- ↑ Ayoozi da Nawazani, "Mihar Mukawamat beh masabat huwiyye mandikeyi Shaidar Yanki," shafi na 6-7
- ↑ Ayoozi da Nawazani, "Mihar Mukawamat beh masabat huwiyye mandikeyi Shaidar Yanki," shafi na 8-9
- ↑ Karimi, "Nakshe Iran dar huwiyatebakshi beh majmu'eh Amniyati Mihwari Mukaamat", shafi 7.
- ↑ Qassemi, "Farhange shahadat talabi Inkilabe Islami Dar jahan islam wa arse bainal milali", shafi na duniya 106.
- ↑ Hashempour vaqiqi, "Rabiteh Inkilab Islami Iran wa mihwar Mukawamat dar huwiyat bakshi beh husi Yemen", shafi 221; Karimi, "Nakshe iran dar huwiyat bakshi beh majmu'eh amniyat mihwar mukawamat shafi na 7-9
- ↑ Sadatinejad, "Baztabehaye Huzur mukawamat dar madike garbe Asiya", shafi na 97-96.
- ↑ Shiroudi da Abokan , "Guftemane Mukawamat (Shi'a) wa tasir an bar nizame hermanatik garbe Asiya dar muwajahe ba guftemane salafi ikhwani Asiya", shafi na 236-237.
- ↑ Shiroudi da Abokan Juriya, "Guftemane Mukawamat (Shi'a) wa tasirin an bar nizame hermanatik garbe Asiya dar muwajahe ba guftemane salafi ikhwani Asiya", shafi na 236-237.
- ↑ Bagheri da abokan aiki., "Tasir Mihwar mukawamat bar umki istiratajik Jamhuri Islami Iran", PP. 84-84.
- ↑ Bagheri da abokan aiki., "Tasir Mihwar mukawamat bar umki istiratajik Jamhuri Islami Iran", shafi na 86-87.
- ↑ Sadatinejad, "Baztabehaye Huzur mukawamat dar madike garbe Asiya", shafi na 89-
- ↑ Shiroudi da Abokan , "Guftemane Mukawamat (Shi'a) wa tasir an bar nizame hermanatik garbe Asiya dar muwajahe ba guftemane salafi ikhwani Asiya", shafi na 219
- ↑ Darju Hidayati, "Tasir Kudrat Jamhuriye islami Iran dar takwaiyate kudrat dar sakhtare siyasi irak (2013-2020), shafi na 82.
- ↑ Hashempour vaqiqi, "Rabiteh Inkilab Islami Iran wa mihwar Mukawamat dar huwiyat bakshi beh husi Yemen", shafi 230-238
- ↑ Shiroudi da Abokan , "Guftemane Mukawamat (Shi'a) wa tasir an bar nizame hermanatik garbe Asiya dar muwajahe ba guftemane salafi ikhwani Asiya", shafi 185-187
- ↑ Qasimii, Zarfiyate sanji Shi'ayani Irak wa tasiri an bar mihwar mukawamat »shafi na 185-187
- ↑ Karimi, "Nakshe Iran dar huwiyatebakshi beh majmu'eh Amniyati Mihwari Mukaamat", shafi 12.
- ↑ Nubzatu Al -jihad al -Islami fi Palestin », al Jazera News Network; Maliki, "Hamas, Motsa", shafi na 9.
- ↑ Hadas Sa'a .. Bayani cewa sha'awar ka san cewa MusulunciJihadul Islami wanda ya haifar da yantar da fursunonin Jalbua. Faydi, "al-jazira
- ↑ Al -sharif, "Harkatul Jihad Islami palastin", Adireshin Nutalat Islami Palastine ... Labarin Jihad da sirri yaƙar Isra'ila dai niyya tare da yakinsa na ƙarshe."
- ↑ Karimi, "Nakshe Iran dar huwiyatebakshi beh majmu'eh Amniyati Mihwari Mukaamat", shafi 12.<
- ↑ "Rana ta goma ta aikin Tsawa ta Al-Aqsa," tashar Al-Alam; "Menene Harakatul Jihad Islamiyya wanda Isra'ila ta zarge shi da harbin asibitin Baptist a Gaza?" shafin yanar gizo na France24
- ↑ Mebini da Qasemi, "Dasteawardehaye mukawamat islami Lebanon dar manzumeh fikri Sayyid Hassan Nasrallah wa Tasirin an bar amniyate mihware mukawamat," shafi na 28.
- ↑ Karimi, "Nakshe Iran dar huwiyatebakshi beh majmu'eh Amniyati Mihwari Mukaamat", shafi 12.
- ↑ "Lokaci zuwa lokaci tare da rana ta biyu na Ayyukan Tsawa ta Al-Aqsa," tashar Al-Alam; "1038 Ayyukan Hezbollah akan Yahudawa cikin kwanaki 133 na yaki," tashar Al-Alam.
- ↑ "Shaidar Sakataren Janar na Hezbollah, Mai Girma Sayyid Hassan Nasrallah," shafin yanar gizo na Al-Manar
- ↑ Karimi, "Nakshe Iran dar huwiyatebakshi beh majmu'eh Amniyati Mihwari Mukaamat", shafi 12.
- ↑ Karimi, "Nakshe Iran dar huwiyatebakshi beh majmu'eh Amniyati Mihwari Mukaamat", shafi na12
- ↑ Roustayi, "Tahlil Bar Himayat Iran az mihwar mukawamat dar buhrane Syria ba takid bar royekad armane gerayi wa waki'i gerayi," shafi na 79.
- ↑ Bisserie, "Wakawi Tahdidat Da'ish bar Mihware mauakwamat wa tasiri an bar amniyat milli Jamhuriye Islami Iran," shafi na 21-22.
- ↑ Bisserie, "Wakawi Tahdidat Da'ish bar Mihware mauakwamat wa tasiri an bar amniyat milli Jamhuriye Islami Iran," shafi na 21-22.
- ↑ Bisserie, "Wakawi Tahdidat Da'ish bar Mihware mauakwamat wa tasiri an bar amniyat milli Jamhuriye Islami Iran," shafi na 21-22.
- ↑ Muhammad Yahya Azan, "Tanzimul Shabab al-Mu’min bil Yemen," wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na tashar labarai ta Al-Jazeera.
- ↑ Sayyid Kamil, "Al-wijud Al-Houthi fil Yemen: Dirsa Jegrofioyya As-siyasa," shafi na 19.
- ↑ "Dawafi Musanadati Iran Lil Husiyin Fil Yemen," shafin yanar gizo na Cibiyar Bincike na Manufofin Siyasar Iran na Larabawa.
- ↑ Sayyid Kamil, "Al-wijud Al-Houthi fil Yemen: Dirsa Jegrofioyya As-siyasa," shafi na 27
- ↑ Sayyid Kamil, "Al-wijud Al-Houthi fil Yemen: Dirsa Jegrofioyya As-siyasa," shafi na 31.
- ↑ "Haka'ik La ta'arifuha an Abdul-Malik al-Houthi," wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na mujallar Was’ih Sadrak; Sadatizadeh, "Baztabhaye Huzur Jabhe muakawamat dar mantikeh garbe Asiya," shafi na 104-97-99.
- ↑ Sadatizadeh, "Baztabhaye Huzur Jabhe mukawamat dar mantikeh garbe Asiya 97-97
- ↑ Parsai da Motaharnia, "Asre Guzarui mihwar Iran, Syria wa Hezbollah bar Manafi Amrika dar garbe Asiya," shafi na 115-119.
- ↑ Sadatizadeh, "Baztabhaye Huzur Jabhe mukawamat dar mantikeh garbe Asiya 97-97
- ↑ Parsai da Motaharnia, "Asre Guzarui mihwar Iran, Syria wa Hezbollah bar Manafi Amrika dar garbe Asiya," shafi na123-131.Sadatinejad, "Baztabehaye Huzur mukawamat dar madike garbe Asiya", shafi na 97-99
- ↑ "Tashar Al-Manar," shafin yanar gizo na Al-Jazeera; Umar al-Farouq, "Adda'aya Shi'a," 2017, shafuka 70-71.
- ↑ Hakim da Mohammadpour, "Barrasi Mukayase'i fushesh Khabari Buhrane Syria dar sayithaye khabari Al-jazira wa Al-mayadin," shafi na 57; "Matsayin tashar Al-Mayadeen da ra'ayoyin 'yan wasan larabawa game da ita," hukumar labarai ta IRNA.
- ↑ "Kafofin Al-Nahar Al-Arabi: Labaran rufe ofisoshin tashoshin Houthawa a Lebanon ba gaskiya bane," shafin yanar gizo na jaridar Al-Nahar Al-Arabi; Rizeq, "Tashar Al-Masirah: Shekaru bakwai na bayarwa da ci gaba da fuskantar kalubale," shafin yanar gizo na Yemeni Press.
- ↑ "Gano Wasu Daga cikin Gidajen Talabijin na Shi'a," hukumar labarai ta IQNA.
- ↑ Muhammad Ibrahim, "Sabon Kwatancen Gidan Talabijin na Al-Ghadir na 2024 a Nilesat," shafin yanar gizo na Maqalatak.
- ↑ Hamdi Malek; Crispin Smith, "Bayanin Gaba ɗaya na Al-Itijah TV Channel," shafin yanar gizo na Washington Institute.
- ↑ Hamdi Malek, "Bayanin Gaba ɗaya na Channel na Al-Ahed TV," shafin yanar gizo na Washington Institute.
- ↑ "Hadaddiyar Gidan Watsa Labarai na Tsayin Daka," wanda aka buga a jaridar Jame Jam.
- ↑ "Labari na sa'o'i 24 tare da 'To the Horizon of Palestine'," wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na Fars News.
- ↑ "Kungiyar Hadin Kan Gidan Watsa Labarai na Tsayin Daka," wanda aka wallafa a jaridar Jame Jam.
Nassoshi
- حسيننا في هذا الزمان، "Shafin Yanar Gizo na Bayar da Ayyukan Imam Khomeini, Ranar Buga." "10/09/2019, Ranar Buga; 31/10/2023, Ranar Dubawa."
- جنرالات سابقون في جيش العدو: الانسحاب عام 2000 كان كارثة استراتيجية"Shafin Yanar Gizo na Al-Manar TV Channel.""Ranar Buga: 27/05/2022, Ranar Dubawa: 31/10/2023.".
- وزير الدفاع العراقي : إيران وقفت إلى جانب العراق في الحرب ضد داعش،"Hukumar labarai ta IRNA, Ranar Buga: 24/11/2020, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- ال صادق : محور المقاومة اضحى اكثر قوة وتماسكا ..العراق لديه شعب غيور ومساند للقضية الفلسطينية، "Hukumar labarai ta IRNA, Ranar Buga: 13/04/2023, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- حزب الله من المقاومة إلى ما بعد المقاومة،"Shafin Yanar Gizo na Al-Manar TV Channel, Ranar Buga: 13/02/2015, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- أهداف ونتائج الحرب على غزة 2008-2009، "Hukumar labarai da bayanai ta Falasdinu (WAFA), Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- محور المقاومة في ميزان الفلسفة والصراع الدولي، "Mujallar Kayhan Al-Arabi, Ranar Buga: 08/02/2021, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- تسلسل العلاقات الاسرائيلية السورية،"Hukumar labarai ta Reuters, Ranar Buga: 21/05/2008, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- حقائق-من هم الحوثيون في اليمن، "Hukumar labarai ta Reuters, Ranar Buga: 11/01/2021, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- ولايتي : سوريا تمثل الحلقة الذهبية في محور المقاومة،"Hukumar labarai ta Tasnim International News Agency, Ranar Buga: 16/08/2015, Ranar Dubawa: 31/10/2023."*الله الاراكي يهنئ قائد الثورة بالانتصار على داعش الإرهابي، "Majalisar Duniya na Ahlul Bayt, Ranar Buga: 23/11/2017, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- محللون: واشنطن تصعد التوتر مع دمشق،"Shafin Yanar Gizo na Al-Jazeera, Ranar Buga: 10/05/2002, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- بوش يواصل حربه ضد دول محور الشر، "Shafin Yanar Gizo na Al-Jazeera, Ranar Buga: 26/01/2003, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- العلاقات السورية الإيرانية، "Shafin Yanar Gizo na Al-Jazeera, Ranar Buga: 08/08/2012, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- روحاني يؤكد عزم إيران الدفاع عن المراقد الدينية،"Shafin Yanar Gizo na Al-Jazeera, Ranar Buga: 18/06/2014, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- السيد نصر الله : في تاريخ الصراع مع اسرائيل يعد انتصار تموز الإنجاز الأهمّ، "Shafin Yanar Gizo na Al-Manar TV Channel, Ranar Buga: 13/08/2016, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- محور المقاومة.. النشأة والتطوّر ووحدة المصير،"Shafin Yanar Gizo na Al-Mayadeen TV Channel, Ranar Buga: 06/07/2021, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- قائد الثورة الإسلامية: نعتبر دعم سوريا دعماً لمحور المقاومة ونفتخر بذلك،"Majalisar Duniya na Takaitawa, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- سعيد جليلي في دمشق للتباحث مع الرئيس الأسد وكبار المسؤولين السوريين، "Hukumar labarai ta Tabnak, Ranar Buga: 07/08/2012, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- ماذا يعني وصف نصرالله للإمام الخامنئي بـ’حسين زماننا’؟، "Hukumar labarai ta Taqrib, Ranar Dubawa: 31/10/2023."
- Basiri, Muhammad Ali da Abokan aiki, Wakawi Tahdidat Amniyati Da'ish Bar Mihware mukamawat wa tasir an bar amniyate milli Jamhuri Islami Iran."A cikin mujallar Nazarin Juyin Juya Hali na Musulunci, lamba 48, bazara 1396 Hijira Shamsi."