Yaƙin Isra'ila Da Iran
Wannan wani rubutu ne game da harin da Isra'ila ta kai kan ƙasar Iran, domin samun bayani game da ofireshin na wa'adus sadiƙ 3 sai ku duba Shafin Ofireshin Wa'adus Sadiƙ 3.
| Lokaci | Farawa:23 ga watan Khordad shekara ta 1404 kalandar Farsi/13 ga watan June shekara ta 2025 |
|---|---|
| Wuri | Iran da mamayayyar ƙasar Falasɗinu |
| Dalili | Yunƙurin kawar bakiɗayan shirin makamashin nukiliya na Iran |
| Masu yaƙi | |
| Ɓangarori biyu na yaƙi | Babban kwamandan Iran Sayyid Ali Khamna'i Benjamin Netanyaho |
| Sojoji | |
| Dakarun kare Juyin juya halin muslunci na Iran da sojojin Iran Sojojin Isra'ila | |
| Asara | |
| Hasara | Daga ɓangaren Iran ba'arin kwamandoji da masana makamashin nukiliya sun yi shahada, tare da kashe gomman fararen hula An kashewa Isra'ila gwamman mutane da tare da raunta gomomi |
Yaƙin Isr'aila da Iran, wani harin soji ne da Isra'ila ta kai kan Iran wanda ya faru a ranar 23 ga watan Khordad shekara ta 1404 shamsi,wanda ya yi daidai da 13 ga watan June shekara ta 2025 miladiyya, daga fara wannan yaƙi Isra'ila ta kai hari kan ba'arin cibiyoyin makamashin nukiliya, cibiyoyin soji da gine-ginen gidaje a Iran. Cikin wannan hari wasu adadin manyan kwamandojin soji misalin Muhammad Baƙiri, Husaini Salami da Amir Ali Haji Zade, sun yi shahada, haka nan ba'arin kwararrun masana nukiliya da wasu adadin fararen hula su ma duk sun yi shahada.
Manufar haramtacciyar gwamntatin Sahayoniyya daga wannan hari da ta kai shi ne ganin bayan bakiɗayan shirin makamashin nukiliya na Iran, canja gwamnatin Iran, rage barazanar Iran kan wanzuwar Isra'ila, kawar da hankulan duniya daga yaƙin Gaza da kuma sanyawa a manta rashin nasarar ta a yaƙin da take a Gaza.
Bisa dogaro da rahotan kafofin labarai na yammacin Turai da na Larabawa misalin tashar Aljazira da Aksiyos, haƙiƙa Isra'ila ta jima da shiryawa wannan hari da ta kai kan Iran kaɗai dai ta kasance ta na jiran lokacin da ya fi dacewa da ƙaddamar da wannan shiryayyen hari na ta, bisa ishara da ta samu daga Amurka, Isra'ila ta kai wa Iran hari bayan amincewa da kudurin da Hukumar makamashin nukiliya ta yi na nuna rashin samun nutsuwa da shirin Iran, da ƙarewar kwanaki 60 na ɗaga ƙafa da shugaban ƙasar Amurka ya bawa Iran domin samun daidaitawa da Iran kan shirinta na makamashin nukiliya, farkon safiyar rana ta goma ma'ana 22 ga watan June da fara wannan yaƙi ne Amurka domin nuna goyanta ga Isra'ila, ta shigo kai tsaye cikin wannan yaƙi tare da fara ƙaddamar da hare-haren ruwan bama-bamai kan cibiyoyin makamashin nukiliya nukiliya na Fordo, Natanza da Isfahan.
Iran cikin raddi da martani kan wannan keta alfarma da Isra'ila ta yi kanta ta ƙaddamar da hari mai suna ofireshin wa'adus sadiƙ 3 ta hanyar harba ɗaruruwan makamai masu linzami tare da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan muhimman wurare daga cibiyoyin tsaro da na leƙen asiri da cibiyar Wayizman da Aman da Mosad da sansanonin sojojin sama, duka a cikin haramtacciyar ƙasar Isra'ila.
Wannan hari da Isra'ira ta yi ya fuskanci martani da nuna rashin amincewa daga ɓangarori daban-daban na duniya. Maraji'an taƙlidi na Shi'a da dauloli masu yawa da shuwagabannin ƙasashe daban-daban sun yi Allah wadai da wannan hari tare da bayyana wannan hari a matsayin tauye shugabancin Iran da kuma dokokin ƙasa-ƙasa.
Ayatullahi Khamna'i, Jagoran Jamhuriyar muslunci ta Iran, cikin saƙonsa da aka yaɗa shi a tashoshin talabijin, ya kira hari da Isra'ila ta kai wa Iran da fara yaƙi da kuma wauta mai girman gaske, wace abin da zai biyo baya zai sanya Isra'ila ta shiga uku. Ya ƙarfafa cewa lallai Iran za ta ɗau fansa mai tsananin gaske kan haramtacciyar gwamnatin Isra'ila, kuma lallai Iran ba za ta taɓa laminta da wannan keta alfarma ta wuce ba tare da fuskantar hukunci mai tsanani ba.
Gwamnatin Sahayoniyya tare da kai hare-haren soji kan yankuna, fararen hula, gidajen mutane, gine-ginen ma'aikatun yaɗa labarai, asibitoci da cibiyoyin makamashin nukiliya, lokuta da daman gaske ta kasance tana take dokokin ƙasa da ƙasa, tare da keta yarjejeniyar Jeneba da kuma majalisar ɗinkin duniya.
Soke tattauna ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, asarar bilyoyin daloli ga tattalin arziƙin Isra'ila, hijirar dubban Sahayoniyyawa daga Isra'ila zuwa wasu ƙasashe daban, suna daga jumlolin abin da wannan yaƙi ya jawowa Isr'aila.