Jump to content

Ofireshin Na Busharar Nasara

Daga wikishia
Ofireshin Na Busharar Nasara
Sashe daga cikin rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran
Lokaci18 ga watan Yuni 2025 miladiyya
WuriSansanin aludaida na Amurka da yake Qatar
DaliliHarin Soji Da Amurka Ta Kai Kan Cibiyoyin Makamashin Nukiliya Na Iran
Masu yaƙi
Ɓangarori biyu na yaƙiIran
Isra'ila


Ofireshin na busharar basara, (Larabci: عملية بشارة الفتح) wani hari ne na makamai masu linzami da sojojin Iran suka ƙaddamar kan sansanin sojan Amurka mai suna al'udaida da yake ƙasar Qatar, wannan hari ya kasance amsa kan ruwan bama-bamai da Amurka ta yi kan cibiyoyin makamashin nukiliya na Iran a ranar 18 Yuni 2025 miladiyya.[1] Sansanin al'udaida shi ne babbar cibiyar kwamandancin sojan Amurka a yankin yammancin Asiya.[2] Bisa dogara da wasu rahotanni, jirgi mara matuƙi da ya kai hari kan motar Ƙasim Sulaimani ya shahadantar da shi, ya taso daga wannan sansani.[3] Wannan hari na makamai masu linzami shi ne na biyu cikin hare-hare na kai tsaye da Iran ta taɓa kai wa kan sansanin sojan Amurka a yankin yammacin Asiya. A shekarar 2019 miladiyya dakarun kare juyin juya halin Muslunci, cikin martini da suka yi kan kashe Ƙasim Sulaimani kwamandan dakarun ƙudus, sun harba makamai masu linzami kan sansanin sojan Amurka wanda yake Iraƙi da ake kira da suna Ainul Asad.[4] Ofireshin na busharar nasara an buɗe shi da kalmar sirri ta "Ya Aba Abdillahil Husaini (A.S)" adadin makamai masu linzami da aka harba sun ninka adadin bom da Amurka ta yi amfani da shi kan cibiyoyin makamashin nukiliya ta Iran.[5]

Bayan ƙaddamar wannan ofireshin, an samu labarin cewa a a shafukan sadarwa na yanar giza gizo mutane sun fara nuna damuwarsu kan zaman sansanin sojan Amurka a Qatar.[6] Har ila yau, ba'arin fashin baƙi da aka y ikan wannan ofireshin, ance wannan hari na Iran ne sanadiyar tilastawa Isra'ila tsagaita wuta da yaƙin da ta ƙaddamar kan Iran..[7] Bayan wannan ofireshin, shugaban ƙasar Amurka Donal Turom ya buƙaci a tsagaita wuta a yaƙin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila.[8]

Bayanin kula

Nassoashi