Masallacin Sakra

Daga wikishia

Masallacin Sakra ko kuma Sakra mai tsarki, masallaci ne a cikin masallacin Al-aƙsa dake ƙudus a wannan guri da ake kira da Hadabatun Muriya a Baitul Muƙaddas, kuma shi wannan masallaci yana kan wani babban dutse, shi wannan dutse yana da girma da matsayi a addinin Yahudanci da Musulinci da Nasaranci (Kiristanci), kuma musulmi sun yi imani cewa Annabi amincin Allah ya tabbata a gareshi ya yi Mi'iraji daga ƙasa zuwa sama ta kan wannan dutse, kuma Yahudawa sun yi imani da cewa an shinfiɗa ƙasa ne daga kan wannan dutse, kuma annabi Adam an halice ne daga ƙasar wannan gurin, shi kuma Annabi Ibrahim an umarce shi da ya yanka ɗanshi a wannan guri.

Wannan rifin sananne na zinare da mutane suke zaton na masallacin ƙudus ne, to a haƙiƙa na mmasallacin Sakra ne, kuma shi wannan masallaci a ginashi ne a shekara ta ɗaya hijira a zamani Abdulmalik ɗan Marwan, sanna daga baya aka ƙara ginashi a kokuta daban-daban.

ٍSanya Wannan Suna

Shi dai wannan masallaci an san shi da masallacin Sakra, saboda an ginashi kan wannan dutse da ake kira Sakra a gurin mai suna Hadabatu Muriya a cikin masallacin Baitul Muƙaddas, saboda haka kuma ake ce mishi ƙubbatus Sakra.[1] kuma wani lokacin kira ƙubbatus Sakra da masallacin Al-aƙsa bisa kuskure, a dai-dai lokacin da samar masallacin Sakra da zinare aka yi ta, amma samar masallacin Aƙsa kalar baƙi-baƙi[2]

Gurin Da Aka Gina Wannan Masallaci

Masallacin Sakra ko ƙubbas Sakra yana cikin masallacin Aƙsa a wannan guri da ake kira da Hadabatu Muriya a cikin Baitul Muƙaddas, kalar rufinsa ruwan zinare ne kuma gini masallaci yana da gida-gida guda takwas.,[3] kuma yana da ƙofofi huɗu ana buɗesu ta ɓangarori guda hudu.[4]

A ɓangaran kudu masu yamma na masallacin shi gurin da Annabi ya yi Mi'ira daga ƙasa zuwa sama,ana kirashi da sawun Muhammad, a kusa da ƙubbatus Sakra, gurin da aka saanshi ƙubbar Annabi [5] a rukuni na arewa a kwai maƙamin Annabi Kidir,[6] kuma ƙubbatus Sakra yana cikin gurare masu girma a Musulinci.

Muhimmancin Wannan Masallaci== Masallacin ƙubbatus Sakra da Masalacin Umawi a Dimashiƙ da Masallacin Ammar ɗan As a ƙahira da Masallacin ƙiran wanda yake a Tunus suna daga cikin masallatai da gine-gine da akayi tin a ƙarni naɗaya na hijira[7] kuma wannan masallatai suna girma a gun Yahudawa da Kiristoci da Musulmai.[8]

Kuma dutsan da aka gina masallacin ƙubba a kanshi,shi ne yazamo Alƙiblar Musulmi a ƙarni na biyu na hijira, [9] kuma Musulmi sun yi imani da cewa Annabi amincin Allah ya tabbata a gareshi ya yi Mi'iraji zuwa sama daga kan wannan Sakra ɗin.[10] Yahudawa sun yi imani da an shifiɗa ƙasane daga wannan guri, kuma Annabi Adam An haliceshi ne daga ƙasar wannan guri, kuma shi ne gurin da Annabi Ibrahim ya so ya yanka ɗanshi saboda Allah.[11]

Tarihi

An fara gina wannan masallaci na Sakra a shekara ta 66 na hijira a lokacin kalifancin Umayyawa a mulkin Abdulmalik ɗan Marwan, na ginashi a gikin Sakra (duste) da yake kan Hadaba Muriya a cikin Baitul Muƙaddas, an gama ginashi a shekara ta 72 hajira[12] a wannan lokacin ne Abdullahi ɗan Zubair ya yi iƙrarin kalifanci a Makka, ya kasance yana tilastawa alhazai kan yimishi bai'a, sai shi kuma Abdulmaliƙ ɗan Marwan ya hana mutane zuwa hajji, kuma ya yi ƙoƙarin canza zuwa hajji da zuwa ziyarar ƙubbatus Sakra.[13]

An sake gina ƙubbatu Sakra a lokacin Ma'amun Al-abbasi a shekara ta 216 hijira, aka kuma canza suna da yake a rubuce na Ma'amun dana Abdulmalik ɗan Marwan alhalin suna ya kasance a rubuce a jiki, amma ba'agoge shikarar da aka sake ginashi ba, wato shekara ta 72 hijira ba'a canza tarihin sake ginawar ba.

A shekara ta 407 bayan hijira[14] an yi wata girgizar ƙasa mai tsanani a birnin Kudus[15]. Wani bangare na ƙubbatu Sakra [Dutse] ya faɗo, [16] kuma a shekara ta 413 bayan hijira, musamman a zamanin kalifanci Fatimiyun Azzahir, an sake gina Masallacin Masallacin Sakra [Dutse] [17]. Wata girgizar ƙasa ta sake afkuwa a shekara ta 460 bayan hijira a lokacin mulki Ahakim bi Amrullah Albatimi[18], wanda ya yi sanadin rushe masallacin, aka sake gina shi a shekara ta 467 bayan hijira ta hannun Halifan Abbasiyawa Alƙa'm. bi Amrullah.

Dalilin Sanyawa Masallacin Wannan Suna

Abin da yasa aka sawa wannan masallaci,Masallacin Sakra, shi ne saboda ginashi da akayi a kan duste wanda yake kan Hadabatu Muriya a cikin Baitul Muƙaddas kuma saboda haka nema ake kirashi da ƙubbatu Sakra.[19] Wasu basa ban-ban cewa tsakanin masallacin Al-aƙsa da masallacin ƙubbatus Sakra, shi masallacin ƙubbatu Sakra rufinsa kalar zinare ne, amma shi masallacin Aƙsa rufinsa baƙi ne wulik.[20]