Jump to content

Ƙasim Sulaimani

Daga wikishia
Ƙasim Sulaimani
Tarihin Haihuwa20 ga watan Maris, 1957 a kalandar Miladiyya.
Wurin HaihuwaRabor daga yankin Kerman
Tarihin Shahada3 ga watan Janairu, 2020
Wurin ShahadaBagdad
ƘabariKerman
AddiniMuslunci
MazhabaShi'a
AikiJami'in tsaro
MuƙamaiBabban Kwamandan Dakarun Ƙudus
BayanAhmad Wahidi
KafinIsma'il Ƙa'ani


Ƙasim Sulaimani (Larabci: قاسم سليماني) Mutumin da ya rayu tsakanin shekaru (1335-1398 kalandar Farisa wanda ya yi dai-dai da 1957-2020 kalandar Miladiyya) wanda ya shahara da Haj Ƙasim ko kuma Shahid Sulaimani, tsohon Kwamandan Rundunar Sojojin Ƙudus na kare Juyin Juya Halin Muslunci a Iran, a ranar 13 ga watan Diy shekara ta 1398 shamsi, wanda ya yi dai da 3 ga watan Janairu 2020. Haj Ƙasim Sulaimani tare da Mataimakin Rundunar `Yan Sa Kai ta Hashadul Sha'abi sun yi shahada sakamakon Harin ta'addancin da Kasar Amerika ta kai a kansu a bagdad babban birnin Kasar Iraƙ.

Haj Ƙasim Sulaimani ya kasance Kwamandan Rundunar Sarullahi 41 Kerman a lokacin YaƘi tsakanin Ƙasashen Iraƙ da Iran, shi ne ya jagoranci kwamandancin operation wal-Fajar 8, haka kuma Karbala 4 da Karbala 5. a shekara ta 1376 h shamsi, Ƙarkashin umarnin Sayyid Ali Khamna'i an naɗa Haj Ƙasim mukamin babban Kwamandan Rundunar Ƙudus wani bangare ne na wajen iyakokin Ƙasar Iran.

Sulaimani, ya taiamakawa Mujahidan Ƙasar Afganistan a fagen daga, haka kuma bayan gama yaƙin cikin gida ya bada gudummawa cikin sake gina Ƙasar Afganistan, a lokacin yaƙin kwanaki 33 a Ƙasar Lubnan da yaƙin kwanaki 22 a Falasɗinu, ya taimakawa Hizbullahi da Hamas cikin fafatawarsu da haramtacciyar Ƙasar Isra'ila, ya kuma karfafa Mihwarin gwagwarmaya da Makaman zamani, bayan bayyanar Ƙungiyar `Yan ta'addan Da'ish a Ƙasashen Iraƙ da Siriya, haƙiƙa Ƙasim Sulaimani cikin hallarar cikin wannan fage ya bada babbar gudummawar cikin bada horo ga Sojojin Sa kai da suke kokarin fatattakar `yan ta'addan Da'ish, an bada rahotan irin rawar da ya taka cikin kawar da barazar Da'ish a kan garin Samarra Najaf da Karbala, haƙiƙa kari kan gwagwarmaya da ayyukan fagen daga Haj Ƙasim ba a barshi a bayan cikin ayyukan SaƘafa da raya al'adu, a cewar shugabannin cibiyoyin hukumar Jamhuriyar Muslunci ta Iran haƙiƙa Haj Sulaimani ya kasance wanda ya assasa Ma'aikatar kula da gine-gine wurare masu tsarki, ya kasance mai sa idanu da kula da kwangilar faɗaɗa ginin Haramin A'imma (A.S) haka kuma ya taka rawa sosai cikin samar da tsaro ga maziyartan Imam Husaini (A.S) a lokacin Ziyarar Arba'in.

A ranar 13 ga watan Diy shekara ta 1398 h shamsi, Ƙasim Sulaimani lokacin tare da Abu muhandis da wasu adadin mutane sakamakon Harin ta'addancin na jirgi mara matuƙi ƙarƙashin umarnin shugaban ƙasar Amerika na wancan lokaci sun samu rabauta da shahada, Rundunar Sojojin Ƙudus ta yi martani kan wannan ta'addanci na Amerika inda ta harba makamai masu linzami a kan sansanin Sojojin Amerika na Ainul Asad da yake Ƙasar Iraƙ, bayan haka kuma Wakilan Majalisar Ƙasar Iraƙ sun sanya hannun kan Ƙudurin korar Sojojin Amerika daga Iraƙ.

An yiwa Jana'izar Haj Ƙasim Sulaimani da sauran waɗanda suke tare da shi rakiya a garuruwa daban-daban na Ƙasar Iraƙ da Iran, Ayatullahi bashir Husaini Najafi da Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i sun jagoranci yi musu Sallah a Iraƙ da Iran, kan asasin rahotanni daga ba'arin `Yan jarida an bayyana cewa haƙiƙa Jana'izarsa ta kasance daga mafi girman taron jana'iza a tarihi, kusan mutum miliyan 25 suka halarci taron jana'izarsa, a ranar 18 ga watan Diy h shamsi aka binne shi a Makabartar Shahidai da take garin Kerman.

Tarihin Rayuwa

An haifi Ƙasim Sulaimani a ranar 20 ga watan Isfand shekara 1335 shamshi, wanda ya yi dai-dai da 11 ga watan Maris 1957 a wani Ƙauye da ake kira da suna Ƙanatu Malik da yake ƙarƙashin garin Rabor Jahar Kerman cikin dangi da suke cikin tsarin riƘo da al'adu.[1] tun yana ɗan shekara 18 ya fara aiki a ma'aikatar ruwa ta Jahar Kerman.[2] kamar yanda ya bada labari da kansa ya kasance Jagoran Zanga-zanga da yajin aiki da kalubalantar Dakarun Hukumar Shahinshahi a lokacin gwagwarmayar neman Juyin Juya Halin Muslunci.[3] a zamanin Yakin Iran da Iraƙ ya yi aure,[4] kuma Allah ya azurta shi da `ya`ya shida.[5]

A shekarar 1398 kalnadar Farisa, wanda ya yi dai-dai da 2020 kalandar Miladiyya da hukuncin Sayyid Ibrahim Ra'isi an naɗa Ƙasim Sulaimani MuƘamin jibantar Haramin Imam Rida (A.S)[6] na lokacin ma'ana hadimin Imam Rida (A.S) bayan ya yi shahada ya samu shahara da lakabin Kwamandan zukata, haka kuma cibiyoyin Tabligi daban-daban sun ta yaɗa shi.[7] Haka kuma, hotuna da abubuwan da suka shafe shi an haɗa su a cikin littattafan karatu na matakai daban-daban na ilimi a Iran.[8]

Halaye

Siffofinsa, Jarumta, neman shahada, soyayya da kuma riƘo da Ahlil-baiti (A.S) ya kasance mutum Mai tsantsar sallamawa, yawan Ibada da ma'aniwiyya, kwarewa cikin harkar tsaro, tsari da kiyaye doka da kuma kasancewa Mutum na mutane ana kidaya su daga siffofin Ƙasim Sulaimani,[9] haka kuma Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i ya bayyana Ƙasim Sulaimani da unwanin fuska gwagwarmaya ta Ƙasa da Ƙasa wacce bata takaitu iya Iran ba, kuma mutum da ya samu tarbiyya da horo daga Muslunci da Makarantar Imam Khomaini..[10]

Lokacin yaƙin Iran Da Iraƙ

bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Muslunci a Iran Haj Ƙasim Sulaimani ya zama Memba a Rundunar Dakarun Ƙudus, ya kasance cikin Membobin sashen Horar da Dakarun Rundunar Ƙudus, kuma Mai bada horo a Jahar Kerman.[11] a shekara ta 1360 ƙarƙashin hukuncin Muhsin Rida'i babban Kwamandan Rundunar Dakarun Ƙudus a wancan lokacin an naɗa Ƙasim Sulaimani Muƙamin Kwamandan Dakarun Sarullahi 41 a jahar Kerman.[12] a lokacin yaƙin Iraƙ ta yi kan Iran, Haj Ƙasim ya jagoranci kwamandanci ofireshen wal-Fajar 8, karbala 4, Karbala 5,[13] ya ji rauni har karo biyu ɗaya daga cikin ya kasance mai tsanani.[14] Bayan gama yaƙi tsakanin Iran da Iraƙ a shekara ta 1367 h shamsi, ya kasance Kwamandan Rundunar Dakarun Ƙudus 7 Sahibuz Zaman zuwa wani lokaci.[15] bayan kuma aka Ƙara naɗa shi Kwamandan 41 Sarallahi, gabanin naɗa shi babban Kwamandan Rundunar Dakarun Ƙudus ya jagoranci sashen yaki da fataucin miyagun kwayoyi a kan iyakoki tsakanin Iran da Afganinstan.[16]

Kwamandancin Rundunar Dakarun Ƙudus

Tushen Makala:Dakarun Ƙudus (Failak Ƙudus)

Asalin Makala: Dakarun Ƙudus Masu kare Juyin Juya Halin Muslunci

A shekarar 1376 kalandar Farisa, wanda ya yi dai da 1997 kalandar Miladiyya. Jagoran Juyin Juya Halin Muslunci a Iran ya fitar da hukuncin naɗa Haj Ƙasim Sulaimani MuƘamin babban Kwamandan Rundunar Dakarun Ƙudus a wajen Iyakokin Ƙasar Iran,[17] Wannan bangare an Ƙara shi cikin ayyukan Dakarun Ƙudus a shekarar 1369 h shamsi, Kwamanda na farko da ya fara jagoranta wannan bangare shi ne Ahmad Wahidi, bayansa sai Haj Ƙasim Sulaimani ya karbi ragama, bayan Shahadarsa sai aka naɗa Isma'il Ƙani kwamandancin wannan bangare.[18]

Yaki Da `Yan Talban Da Al-Ƙa'ida A Ƙasar Afganistan

Naɗa Ƙasim Sulaimani kwamandanci Rundunar Dakarun Ƙudus bangaren wajen iyakokin Iran ya zo lokaci ɗaya da habbakar ayyukan Talban a cikin Afganistan,[19] Haj Ƙasim Sulaimani ya haɗa kai da Mujahidan Ƙasar Afganistan daga jumlarsu akwai Shah Mas'ud,[20] bisa rahotan wasu ba'arin Mujahidai Ƙasim Sulaimani a lokuta da daman gaske ya hallara a fagen daga cikin Ƙasar Afganinstan don ɗauki ba daɗi da fafatawa da `yan Talban da Al-Ƙa'ida[21] Akwai Fim da yaɗu da yake nuna shi a garin Panjishir tare da ganawarsa da Ahmad Shah Mas'ud cikin fafatawa da gwabzawar Mujahidun da Talban.[22]

A cewar Dakarun Sojojin Afganistan haƙiƙa zuwan Ƙasim Sulaimani Afganistan ya kawo nasara mai yawa, saboda mutum mai fara-fara da mutane cikin sauki zai iya samun yarda abokin Mu'amalarsa, kuma ya kasance tare da tanadi mai tarin yawa cikin samar da yanayin tsagaita wuta da kuma samar da haɗin kai tsakanin Rundunoni.[23]

Ƙasim Sulaimani tare da Ahmad Shah Mas'ud

Gwabzawa tare da Isra'ila a Ƙasar Lubnan da Falasɗinu

Ƙasim Sulaimani a lokacin da Isra'aila ta kai Harin tsokana kan Lubnan ya kasance cikin cibiyar kwamancdancin Hizbullahi, wannan hari ya jirkice ya zama Yaƙi tsakanin da Ƙungiyar gwagwarmayar Hizbullahi Lubnan, tareda Haramtacciayr Ƙasar Isra'ila, haƙiƙa wannan yaƘi da ya ja lokaci har tsawon kwanaki 33 ana fafatawa a yankin kudancin bairut.[24]

A cewar daya daga cikin Jagororin Hamas haƙiƙa Ƙasim Sulaimani yana da alaka mai Ƙarfin gaske tare da Ƙungiyar gwagwarmayar Ƙwato `yanci ta Hama, kuma yana bada dukkanin goyan bayansa kan gwagwarmayar Falasɗinu,[25] kan wannan asasi ne ya samu damar Ƙarfafa su da makaman zamani,[26] aka haka dogwayen ramuka domin cigaba da yaƙar Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila, wannan tunani na dogwayen Ramuka yana daga gudummawa da Ƙasim Sulaimani da kuma Imad Muniyya suka kaiwa Falasɗinawa.[27]

Dauki Ba Daɗi Da Ƴan Ta'addan Da'ish A Ƙasar Iraƙ

Ƙasim Sulaimani ya kasance cikin Kwamandojin yaki da `yan ta'addan Da'ish a cikin Ƙasar Iraƙ,[28] da Ƙasar Siriya,[29] Da'ish wata Ƙungiya ce ta masu Kafirta duk wanda ba na su ba, kuma sun bayyana ne tsakar rana bayan Faɗuwar Saddam da kuma rikicewar Gabas ta tsakiya.[30] a shekarar 2014 shekarar da Garin Mosul ya faɗa hannunsu haka kuma babban birnin bagdad kaɗan ya rage shima ya faɗa hannunsu, Ƙasim Sulaimani ya je ya gana da babban Marja'in Taklidi Sayyid Ali Sistani, bayan wannan ganawar sai Sayyid Ali Sistani ya bada fatawar Jihadi kan Da'ish.[31] haƙiƙa Ƙasim Sulaimani ya taka babbar rawa cikin korar Da'ish daga Iraƙ, daga cikin akwai daidaita Ƙungiyar Dakarun Sa kai ta Hashadul Sha'abi, wannan rawa da ya taka da kuma gudummawar da ya bayar ta kai haddi da bababan Firaministan Iraƙ a lokacin Haidari Abadi ya siffanta Ƙasim Sulaimani da matsayin daya daga Asalin samun haɗin kan Iraƙ cikin Fafatawa da Da'ish.[32]

Tare da sayyid Hassan Nasrallah da Imad Mugniyya

Ƙasim Sulaimani ya bada gudummawar Shawarwari ga Dakarun Sa kai na Hashadul Sha'abi da Sojojin Yankin Kurdistan Iraƙ cikin yakinsu tare da `yan ta'addan Daish, daga jumlar gudummawarsa akwai kwato garin Amirli na yankin Salahuddin daga hannun `yan ta'adda[33] kwato garin Tikrit[34] taka burki kan ƙarfin ikon Da'ish cikin Erbil Arewacin Iraƙ.[35] da kuma fafatawa da Da'ish a Samarra.[36]

Dauki ba Daɗi da Ƙungiyoyin Takfiri a Ƙasar Siriya

Ƙasim Sulaimani ya bada gudummawar shirya Dakarun kare Kai a Ƙasar Siriya domin fatattakar yan ta'adda,[37] a shekarar 2011 m an samar da Dakarun ƙarƙashin Jagorancinsa waɗanda ake kira da Masu kare Harami, daga jumlarsu akwai Rundunar Fatima da Rundunar Zainabiyyun, sun shiga Siriya,[38] suka kwato garin bukamal,[39] kwato garin Tarihi na Tadammur a kuda Masu Gabas na Himmas Siriya,[40] sannan kuma kwato garin Al-Ƙasir ana ƙidaya su cikin nasarorin da ya samar da yaƙin Siriya.[41]

Sanar Da Kawo Ƙarshen Yaƙi

Ƙasim Sulaimani cikin wasiƙarsa zuwa ga Sayyid Ali Khamna'i Jagoran Jamhuriyar Muslunci ta Iran, ya aika da wasiƙar a ranar 30 ga watan Aban shekara ta 1396 h shamsi, tashoshin Labarai na Ƙasar Iran sun yaɗa wannan Wasiƙa, cikin wannan wasiƙa ya shekanta kammala yaƙi da Da'ish tareda ɗaga Tutar Siriya a garin bukamal cikin garuruwan da suke da iyaka da Ƙasar Iraƙ.[42] haka kafin bayyanar da wannan wasiƙa dama tuntuni a ranar 30 ga watan Shahriwar shekara ta 1396 ya faɗi cewa Ƙasa wata uku masu zuwa zai kawo Ƙarshen ikon hukuma yan ta'addan Da'ish a Ƙasar Siriya.[43]

Wani bangare daga Amsar Da Ayatullahi Khamna'i ya bayar ga wasiƙar Ƙasim Sulaimani dangane da Kawo Ƙarshen Ikon Hukumar Da'ish A Siriya:
Kawo Ƙarshen Kansar Da'ish Mai halakarwa da ka yi, ka bada babbar gudummawa bawai kaɗai ga wannan yanki na gabas ta tsakiya bari ka bada gudummawa ga baki ɗayan duniyar Muslunci.

[44]

Hukumar Kula da Gine-ginen Wurare Masu Tsarki Da Kuma Tattakin Arba'in

Hukumar kula da gine-ginen wurare masu tsarki ta samu ne sakamakon taimako na kai tsaye daga Dakarun Ƙudus a lokacin Kwamandancin Ƙasim Sulaimani, kuma ta hannunsa ne aka ayyana Shugaban Hukumar.[45] Ƙasim Sulaimani ba a barshi a baya ba a fagen samar da tsaro ga Maziyarta a lokacin Tattakin Arba'in, haka kuma cikin samar da tallafi da dabaru da kuma tanade-tanaden saukakawa Masu ziyara.[46] kamar yanda da ƘoƘarinsa ne aka cire biza kan Maziyarta Iraniyawa a lokacin Arba'in.[47]

Shaidar Darajar Muƙami Na Soja

Bayar da tambari Zulfiƙar ta Ayatullahi Khamenei jagoran Jamhuriyar Musulunci a Iran ga Qasem Soleimani a shekara ta 1397

Ayatullahi Khamna'i Jagoran Jamhuriyar Muslunci ta Iran ya bada Shaidar Zul-fiƘar ga Ƙasim Sulaimani. A watan Bahman shekara ta 1389 a kalandar Farisa (wanda yayi daidai da Fabrairu shekara ta 2011 a kalandar Miladiyya). Sayyid Ali Khamna'i babban Kwamandan dukkanin Jami'an tsaro a Ƙasar Iran,a watan bahman shekara ta 1398 ya bada Shaidar MuƘamin Mejo Janaral ga Haj Ƙasim Sulaimani.[48] haka kuma a ranar 19 ga watan Isfand shekara ta 1397 Khamna'i ya ba shi Shaidar Darajar Zul Fiƙar,[49] Ana ba da kyautar ga Manya-manyan kwamandoji da Manya-manyan hafsoshin soji waɗanda matakansu na tsarawa da jagorantar ayyukan yaƙi ya sami kyakkyawan sakamako.[50] shi ne Mutum na farko da samu wannan Daraja tun bayan Juyin Juya Halin Muslunci.[51] haka a shekarar 1398 h shamsi bayan ya yi shahada ya kai matakin Muƙamin Laftanal Janar.[52]

A shekarar 2019 m, cikin wasiƙa ta musammam da jaridar Farin Palis ta Ƙasar Amerika take fitarwa duk shekara-shekara domin gabatar da Mutane guda 100 Mafi fifitar tunani a duniya, sunan Ƙasim Sulaimani ya zo cikin jerin mutane goma da suka fifita a fagen harkokin tsaro da kare kai.[53] a cewar ɗaya daga Kwamandojin Sojan Amerika haƘiƘa Janaral Ƙasim Sulaimani yana da kwarewa MatuƘa kuma mai aiwatar da ofireshin wanda ya karfafa Alaƙoƙin dankon zumunci da kuma matsayin Iran a yankin Gabas ta tsakiya tare da samun nasarar hada kan 'yan Shi'a da Ƙarfafa su.[54] Wasu ba'arin masu fashin baƙin harkokin Siyasa sun tafi kan cewa Ƙasim Sulaimani zai iya kasancewa babban Janaral na duk duniya.[55]

Kashe Shi A Kusa Da Filin Tashi Da Saukar Jirage Na Birnin Bagdad Iraƙ

Tushen Maƙala: Kisan Gillar Ƙasim Sulaimani

A 13 ga watan Diy shekara ta 1398 cikin harin da Jirgi Mara matuki na Amerika ya kai kan motar da ta ke ɗauke da Ƙasim Sulaimani, wannan hari ya kasance kusa da Filin tashi da saukar Jiragen Sama birnin bagdad Iraƙ. Sakamakon wannan Ƙasim Sulaimani tare da Abu Mahadi Muhandis Mataimakin Kwamandan Dakarun Sa kai na Hashadul Sha'abi Iraƙ suka rabauta da samun Shahada..[56] Ma'aikatar Tsaron Amerika tareda fitar da bayani ta shelanta cewa wannan hari ya faru ƙarƙashin umarnin Donal Turum Shugaban ƙasar Amerika na wancan lokacin.[57]

Sayyid Ali Khamna'i:
“A gaban abin da tushensa da dabi'arsa da halayensa shi ne cigaban kasa da wannan yanki, lallai ina rusunawa.

"Kisan gillar Ƙasim Sulaimani ya haifar da zanga-zanga a ƙasashe daban-daban na duniya kuma an gudanar da taruka don tunawa da shi a cikin biranen daban-daban na Iran da sauran ƙasashen duniya. Haka kuma, shugabannin siyasa da addini na Iran da sauran ƙasashen duniya sun mayar da martani ga kisan gillar shi.[58]

Wannan al'amari ya haifar da sakamako daban-daban da suka hada da harin makami mai linzami da Hukumar Kula da Juyin Juya Halin Islama ta kai kan sansanin Ain al-Asad, hedkwatar sojojin Amurka a Iraƙi.[59] "Haka kuma, majalisar Iraƙ ta amince da korar Amurkawa daga Iraƙ." [60]

Ƙasim Sulaimani an yi yunkurin kashe shi sau da dama a baya; karo na farko ya kasance a shekarar 1360 Hijiri Shamsi wanda wani likita da ke da alaka da ƙungiyar Mujahedin ta yi yunƙurin kashe shi.[61]

A farkon watan Mehr na shekarar 1398 Hijiri Shamsi, Husaini Taib, shugaban Hukumar Kula da Bayanan Sirri ta Sojojin Juyin Juya Halin Islama, ya sanar da cafke wasu mutane da suka yi yunkurin kashe Ƙasim.[62] Sulaimani a Kerman.[63]

"Jana'izar Ƙasim Sulaimani a Kerman a ranar 17 ga watan Day na shekarar 1398 Hijiri Shamsi."

Takardar Wasiyya

Kan asasin Wasiyyar wacce a 24 ga watan bahman shekarar 1398 kalandar Farisa, wanda ya yi dai-dai da 13 ga watan Fabrairu 2020 kalandar Miladiyya, Isma'il Ƙani ya karantata a taron kwanaki Arba'in bayan Shahadar Ƙasim Sulaimani,[64] wannan Wasiƙar Wasiyya ta Ƙunshi wasiccin kira zuwa ga biyayya ga Sayyid Khamna'i da karfafa Wilayatul Al-Fakihi, kula ta musammam ga Iyalan Shahidai da girmama Sojojin Ƙasar Iran, wani bangare daga Wasiyyar ya tunatar da himmatuwar Jamhuriyar Muslunci ta Iran kan Makwancin Imam Husaini, ya kuma ja kunne da cewa idan Maƙiya suka nasarar samu rushe wannan Harami to fa babu wani sauran Harami da zai rage, daga Haramin Ibrahimi ko Haramin Muhammadi (S.A.W),[65] an gudanar Taron kwanaki Arba'in da shahadar Haj Ƙasim Sulaimani a garuruwa daban-daban cikin Ƙasar Iran da ma wasu Ƙasashen daban.[66]

Taron Jana'iza

Taron Jana'izar Ƙasim Sulaimani a garin Kerman shekarar 2019

Taron Jana'izar Ƙasim Sulaimani tare da Abu Mahadi Mahandis da sauran waɗanda suke tare da su a ranar 14 ga watan Diy kalandar Farisa, (wanda ya yi dai-dai da 4 ga watan Janairu shekara ta 2020 a kalandar Miladiyya) tare da hallarar Manya-manya mutane daga `yan siyasa da Malaman Addini da kuma sauran mutane a biranen bagdad, Najaf, Karbala.[67] A garin Karbala Sayyid Ahmad Safi ne ya jagorancin Sallar Jana'iza a Haramin Hazrat Abbas.[68] A Najaf kuma Shaik bashir Najafi ne ya jagoranci sallar Jana'iza.[69] sai kuma aka kawo gawar shahid Ƙasim Sulaimani da Abu Mahadi Muhandis Iran inda anan ne aka Ƙara yi musu sallatar Jana'izar a garuruwan Ahwaz da Mashad , 15 ga wata, ranar 16 ga wata kuma aka musu sallah a Tehran da Ƙum.

Sayyid Ali Khamna'i Jagoran Jamhuriyar Muslunci ta Iran shi ne ya yi sallah kan gawar Haj Ƙasim Sulaimani da Sauran waɗanda suka yi Shahada daga cikinsu harda Abu Mahadi Muhandis a ranar 16 ga watan shekara ta 1398 a Tehran.[70] A lokacin Jana'izarsa shugaban bangaren siyasa na Ƙungiyar Hamas Isma'il haniyye cikin bayanansa da ya yi ya bada labarin irin gudummawar da Ƙasim Sulaimani ya bayar ga Falasɗinawa kan yaƙar `Yan Mamayar Sahayoniya na Isra'ila sannan ya bayyana shi matsayin Shahidin Ƙudus.[71] cibiyar labarai ta Rasha a yau sun bayyana cewa taron Jana'izar Ƙasim Sulaimani bayan taron Jana'izar Imam Khomaini yana daga mafi girman Taron Jana'iza a tarihi.[72] A cewar Kakakin Dakarun Kare Juyin Juya Halin Muslunci a Iran, kusan Mutane miliyan 25 ne suka halarci taron Jana'izarsa.[73]

An yi taron jana'izar Ƙasim Sulaimani a ranar 17 sannan kuma aka binne shi a ranar 18 ga watan Diy a garin Kerman.[74] Raka Jana'izar Ƙasim Sulaimani a ranar 17 ga watan Diy shekara ta 1398h shamsi.

Bikin tunawa da shahadar Ƙasim Sulaimani a karo na uku

Ayyukan Fasaha Da Jarida

bayan Shahadar Haj Ƙasim Sulaimani, An gudanar da wani taron bitar ƙarawa juna sani a Fannin fasaha mai suna Naksh Negin Soleimani a birnin Ƙom a ranar 23 ga Disamba, 2018. A cikin wannan taron karawa juna sani, Malaman Jami'a tare da daliban ilmin zane-zane sun samar da ayyukan fasaha tare da taken "juriya da shahidan da gwamnatin ta kashe su cikin harin ta'addanci da ta aikata"[75] "An gudanar da taron tunawa da kayayyakin watsa labarai da taken 'Makarantar Haj Ƙasem Sulaimani' a watan Dey na shekarar 1399 kalandar Farisa a Ahwaz.[76]

Haka kuma An shirya fina-finai dadama game da rayuwa da ayyukan Ƙasim Sulaimani; kamar 'Ƙasim.[77] d aKhatirat An Mardi,[78] 72 Sa'at,[79] Awa'ilu January,[80] haka kuma an tarjama Fim ɗin (Ƙasim) zuwa yaren Sipaniyanci, haka Tashar Talabijin ta Hispan Tb ta nuna wannan Fim ga masu Jin Harshen Sipaniyanci,[81] talabijin ɗin Ƙasar Finlan ita ta nuna Fim ɗin (Ƙasim).[82]

Shirya Taron Tunawa Da Shahadarsa

Kowace shekara a lokacin tunawa da shahadar Haj Ƙasim, ana gudanar da bukukuwa a Kerman da wasu biranen Iran. A Kerman, ana gudanar da bukukuwa tare da halartar mutane daga biranen daban-daban na Iran da wasu ƙasashen duniya.

Harin Ta'addanci A Maƙabartar Shahidai A Kerman

Tushen Maƙala: Harin Ta'addanci A Maƙabartar Shahidai A Kerman

A ranar 13 ga watan Day na shekarar 1402, an kai harin ta'addanci a hanyar da ke kaiwa zuwa maƙabartar shahidai ta Kerman. Wannan harin ya haifar da mutuwar mutane 368 da raunata wasu.[83] A cikin wannan harin, mutane 94 sun mutu; 56 daga cikinsu mata ne kuma 13 daga cikinsu 'yan ƙasashen Afghanistan ne.[84] Da'ish ce ta ɗauki alhakin kai wannan hari,[85] A ranar 26 ga watan Day na shekarar 1402, a martani ga wannan harin, Hukumar Kula da Juyin Juya Halin Islama ta kai hari kan sansanonin da ke da alaƙa da ISIS a wurare daban-daban na Siriya.[86]


Nazari

Hotan Littafin Hajj Ƙasim

An yi rubuce-rubuce masu tarin yawa dangane da Ƙasim Sulaimani an buga su da yaɗa su, waɗannan rubuce-rubuce sun kasance kamar haka:

  • Az cizi Nami Tarsidam: tarihin rayuwarsa wanda shi da kansa ya rubuta shi, littafin da yake da shafi 136 wanda ka buga shi a shekarar 1399 h shamsi, wannan littafi ya tattaro rubuce-rubuce da ya yi da hannunsa tun yana yaro da kuma rayuwarsa a Ƙauyen Ƙanatu Malik da yake a Jahar Karman har zuwa lokacin Fafatwa da Hukumar Pahlawi a shekarar 1375 h shamsi.[87]
  • Haj Ƙasim: bahasi ne cikin tarihin rayuwar Haj Ƙasim, wannan littafi yana da shafuka 167 an tattaro ba'arin wasu bayanansa a lokacin kallafaffen yaƙi da Iraƙ ta tilasta Iran kansa, cibiyar Intisharat Ya Zahra sun buga wannan littafi a shekarar 1394.[88] "An fassara wannan littafi zuwa harshen Larabci kuma kungiyar Ma'arifa a Lebanon ta wallafa shi.[89]
Hotan littafin "Ni babu wani abu da nake tsoro
  • Sarbazane Sardar, Talifin Murtada Karamati, shima littafi ne da yake bayanin wane ne Ƙasim Sulaimani da kuma Shahidan Kare Haram, cibiyar (Ayikut pazar bashi) sun tarjama wannan littafi zuwa Harshen Turkanci da kuma yaɗa shi, littafi da yake ɗauke da shafuka 208..[90]
  • Suluk dar Maktab Sulaimani, rubutun Muhammad Jawad Rudgerd an buga shi da yaɗa shi ta hannun cibiyar Mu'assaseh Farhangi Danesh wa Andishe Mu'asir Fajuheshgahe Farhang Mu'asir Islami cikin shafi 264 a shekara ta 1399 h shamsi. An yi bayanin Asalan da uslubin Irfanin Zamantakewa cikin wannan littafi.[91]
  • Akalu Surk, wasu zababbun Ƙasidu ne da Mudawwanonin Ma'abota sanin ilimin ɗan Adam da zamantakewa cikin babin sanin Halaye da Mahangar Ƙasim Sulaimani kan duniya.[92]
  • Sulaimani Aziz, rahotan rayuwarsa ne daga aikin Soja da kuma matanin wasiyyarsa, littafi ne da yake ɗauke da shafi 256, an buga shi da yaɗa shi.[93]
  • Shakishaye Maktabe Sulaimani, littafi ne da ya Ƙunshi Akidu da Al'adun Ƙasim Sulaimani, kuma an buga shi a shekarar 1399 h shamsi.[94]

A Duba Masu Alaƙa

Bayanin kula

  1. «روایت زندگی و کارنامه سردار قاسم سلیمانی»، Shafin labarai na Asre Iran.
  2. Soleimani,man az cizi nami tarsidam, 1399, shafi na 59.
  3. Soleimani, man az cizi nami tarsidam, 2019, shafi na 64-65.
  4. «روایت ازدواج سردار سلیمانی در دوران جنگ»، Shafin Khabar Online.
  5. «حاج قاسم چند فرزند دارد؟»،Shafin Mashraq News.
  6. سردار حاج قاسم سلیمانی خادم حرم امام رضا(ع) شد،Kahbar Hauza.
  7. «چرا حاج قاسم را سردار دل‌ها می‌نامند؟»، Kahbar Difa Mukaddas.
  8. «"سردار قاسم سلیمانی" به کتاب‌‌های درسی آمد + تصاویر»، Kamfanin Labarai na Tasneem.
  9. «۲۵ ویژگی شاخص حاج قاسم سلیمانی»، Kamfanin dillancin Labarai na barna.
  10. نگاه کنید به «پیام تسلیت رهبر انقلاب در پی شهادت سردار شهید سپهبد قاسم سلیمانی و شهدای همراه او»،Ofishin Ayyukan Ayatullahi Uzma Khamna'i.
  11. Mirzaei, Nabarde Karkheh Kor, 2010, shafi na 82.
  12. «روایت زندگی و کارنامه سردار قاسم سلیمانی»، Shafin labarai na Asre Iran.
  13. «سردار سلیمانی و کسانی که لقب "مردی در سایه" را به او می‌دهند»، Cibiyar Labaran Matasa ta Ƙasar Iran..
  14. Mirzaei, Nabarde Karkheh Kor, 2010, shafi na 82.
  15. Mirzaei, Nabarde Karkheh Kor, 2010, shafi na 82
  16. «سردار سلیمانی و کسانی که لقب "مردی در سایه" را به او می‌دهند»،Cibiyar Labaran Matasa ta Ƙasar Iran.
  17. «حکم انتصاب سرتیپ قاسم سلیمانی به فرماندهی سپاه قدس سپاه پاسداران انقلاب اسلامی»"Gidan yanar gizo na Ayatollah Khamenei.".
  18. نیروی قدس سپاه چگونه شکل گرفت؟، Shafin Kudus online.
  19. «قاسم سلیمانی و افغانستان»،Shjafin Hashte Subhi.
  20. «قاسم سلیمانی و افغانستان»، Jaridar Hashte Subhi.
  21. «حضور جدی سردار سلیمانی در کنار مقاومت‌گران افغانستان»، Jaridar Hashte Subhi.
  22. «فیلمی دیده نشده از حضور سردار سلیمانی در دره پنجشیر افغانستان»، Hukumar labarai ta barna.
  23. «قاسم سلیمانی از زبان میزبان‌های افغانش» Shafin talabijin International.
  24. «نقش حاج قاسم سلیمانی در جنگ تموز لبنان»، Hukumar labarai ta Rasa.
  25. «حمدان للميادين: الشهيد سليماني لعب دوراً مهماً في تعبئة صفوف المقاومين»، Shafin tahsar Al-mayadeen.
  26. «حمدان للميادين: الشهيد سليماني لعب دوراً مهماً في تعبئة صفوف المقاومين»، Shafin tahsar Al-mayadeen.
  27. «قاسم سلیمانی فی غزة»، Shafin tashar Al-alam.
  28. «حقایقی ناشنیده از حضور سردار قاسم سلیمانی در عراق»، Hukumar labarai ta Fars.
  29. «تصاویری از سردار سلیمانی در نبرد با داعش»، Shafin Aftab News.
  30. Nabatian, zaminahaye fikri wa siyasi Juryane Takfiri ba'asi Daish, 2014, shafi na 87.
  31. «شهید سلیمانی مشاور آیت‌الله سیستانی در صدور فتوای جهاد کفایی بود»، "Shafin yanar gizo na ofishin jakadancin jamhuriyar Muslunci na Istalkom.
  32. «اعترافات مامور سابق FBI درباره سردار سلیمانی»، Hukumar labarai ISNA Soufan, «Qassem Soleimani and Iran's Unique Regional Strategy», 2018.
  33. الإعلام الإیرانی یؤکد أن الجنرال الإیرانی قاد متطوعی الحشد الشعبی فی معارک مهمة.
  34. حقائق عن عملیات تحریر تکریت .
  35. قائد بالحرس الثوری: سلیمانی استطاع مع ۷۰ شخصا صد هجوم داعش علی اربیل، Hukumar labarai Fars.
  36. العبادی :لم التقِ سلیمانی فی سامراء وواشنطن لیست قلقة من الدعم الإیرانی.
  37. «بازخوانی نقش سردار سلیمانی در برقراری ثبات و آرامش؛ از میدان جنگ تا میز مذاکره»، Kamfanin labarai na Tasneem.
  38. «اعترافات مامور سابق FBI درباره سردار سلیمانی.»؛ Soufan, «Qassem Soleimani and Iran's Unique Regional Strategy», 2018.
  39. «روایت دست‌اول از آزادسازی بوکمال»، Shafin yanar gizo na hukumar labarai Mehr.
  40. «عملیات آزادسازی شهر تدمر»، "Gidan yanar gizo na Kamfanin Dillancin Labaran Tsaron Kasa.".
  41. «کدام سردار ایرانی پیروزی طلایی ارتش سوریه را رقم زدند؟»، سایت قدس آنلاین.
  42. «نامه سرلشکر قاسم سلیمانی به رهبر انقلاب درباره پایان سیطره داعش»، "Gidan yanar gizo na Ayatollah Khamenei.".
  43. «وعده سردار سلیمانی؛ جشن نابودی داعش تا دو ماه دیگر»، "Gidan yanar gizo na Kamfanin Dillancin Labaran Sada da Sima."
  44. «پاسخ رهبر انقلاب به نامه سرلشکر قاسم سلیمانی درباره پایان سیطره داعش»، "Gidan yanar gizo na Ayatollah Khamenei.".
  45. «صفر تا صد فعالیت‌های ستاد بازسازی عتبات با تدبیر حاج قاسم بود»، "Gidan yanar gizo na Kwamitin Gyaran Masarautu.".
  46. ناگفته‌هایی از نقش حاج قاسم در احیای مراسم اربعین، Hukumar labarai ISNA.
  47. «نقش سردار سلیمانی در پیاده‌روی اربعین»، "Gidan yanar gizo na Kamfanin Dillancin Labaran Al-Qur'ani na Duniya.".
  48. «همه سرلشکرهای نیروهای مسلح ایران/ قاسم سلیمانی، رشید، ایزدی، شمخانی و...»، "Gidan yanar gizo na KhabarOnline.".
  49. «سردار سلیمانی نشان ذوالفقار را از رهبر انقلاب دریافت کرد+ تصویر نشان»،Cibiyar labarai Jawan.
  50. ««نشان عالی ذوالفقار» به چه کسانی داده می‌شود؟»، Hukumaar labarai Fars.
  51. «سردار سلیمانی نشان ذوالفقار را از رهبر انقلاب دریافت کرد+ تصویر نشان»، ،Cibiyar labarai Jawan
  52. درجه نظامی که سردار سلیمانی قبل از شهادت برای خود تعیین کرد، باشگاه خبرنگران جوان.
  53. «سردار سلیمانی جزو ۱۰ متفکر برتر حوزه دفاعی نشریه فارن پالیسی شد»، Hukumar labarai Fars.
  54. «ژنرال آمریکایی: قاسم سلیمانی مورد احترام دوستان و دشمنانش است»، سایت خبرگزاری دانشجو.
  55. «কাসেম সোলাইমানি: দুনিয়ার এক নম্বর জেনারেল!»، در سایت خبرگزاری پروتوم آلا.
  56. «سردار قاسم سلیمانی به شهادت رسید»، Asre Iran.
  57. «جزئیات و جنبه‌هایی از چگونگی و چرایی کشته شدن قاسم سلیمانی»، "Gidan yanar gizo na Deutsche Welle Farsi.".
  58. «پیام تسلیت رهبر انقلاب در پی شهادت سردار شهید سپهبد قاسم سلیمانی و شهدای همراه او»، پایگاه اطلاع‌رسانی آیت‌الله خامنه‌ای؛«پیام‌های تسلیت مراجع تقلید، علما و شخصیت‌های حوزوی به شهادت سردار سلیمانی»، Hukumar labarai hauza.
  59. «انتقام سخت با شلیک دهها موشک به پایگاه آمریکایی عین‌الاسد»، Hukumar labarai Barna.
  60. «مفاد تصمیم پارلمان عراق درباره اخراج نیرو‌های آمریکایی»، Shafin yanar gizo na Tabank.
  61. «ماجرای ترور نافرجام حاج قاسم در مشهد»، Cibiyar labarai ta Jawan.
  62. «شکست طرح ترور سردار سلیمانی در کرمان»، سایت تابناک.
  63. «شکست طرح ترور سردار سلیمانی در کرمان»، Shafin Tabank.
  64. «متن وصیت‌نامه سردار سلیمانی منتشر شد»، Shafin yanar gizo na Tabank.
  65. «وصیت‌نامه سردار حاج قاسم سلیمانی منتشر شد+ متن کامل»، Hukumar labarai Hauza
  66. «متن وصیت‌نامه سردار سلیمانی منتشر شد»، Shafin yanar gizo na Tabank.
  67. «پیکرهای پاک سردار سلیمانی و المهندس وارد نجف شدند»، Hukumar labarai Fars.
  68. «نماز میت به امامت احمد صافی بر پیکر سردار سلیمانی»،Shafin Shahr ara News.
  69. «گریه آیت‌الله بشیر النجفی هنگام اقامه نماز بر پیکر شهید حاج قاسم سلیمانی و یارانش»، Shafin tashar Kausar.
  70. «اقامه نماز بر پیکر شهید سپهبد قاسم سلیمانی و یاران مجاهد او»، "Gidan yanar gizo na Ayatollah Khamenei.".
  71. «إسماعيل هنية: قاسم سليماني "شهيد القدس"»، Tahsar labarai Al-jazira.
  72. «طهران تودع سلیمانی بأکبر جنازة منذ تشییع الخمینی»، Tashar labarai ta Russia today.
  73. «سردار شریف: ۲۵ میلیون نفر در مراسم تشییع «حاج قاسم» شرکت کردند»، Hukumar labarai Fars.
  74. «پیکر سردار سلیمانی به خاک سپرده شد»، Shafin yanar na tahsar Khabar.
  75. «اثر هنری سردار آسمانی حاوی نمادهای مقاومت، شهادت و آسمانی شدن سردار سلیمانی است»، Hukumar labari ta Ana.
  76. «نخستین یادواره تولیدات رسانه‌ای مکتب شهید سلیمانی»،Shafin yanar gizo na tashar Khabar.
  77. «مستند "قاسم"، شهید قاسم سلیمانی از تولد تا شهادت و چهار دهه فعالیت مرد میدان»، Hukumar labarai ta Sida Wa Sima.
  78. «مستندساز حوزه مقاومت: مستند "خاطرات آن مرد" را به عشق سردار سلیمانی ساختم»، Hukumar labarai ta IRNA.
  79. «ساخت مستند "۷۲ ساعت‌" با موضوع سه روز پایانی زندگی سپهبد شهید حاج قاسم سلیمانی»، Hukumar labarai ta Daneshju.
  80. «مجاهدت‌های شهید سلیمانی در "اوایل ژانویه" از شبکه یک»، IRNA.
  81. «پخش "قاسم" برای اسپانیایی‌زبان‌ها/ فرماندهی میدانی سردار مستند شد»، Hukumar labarai Mehr.
  82. «پخش مستند شهید حاج قاسم سلیمانی از تلویزیون فنلاند + فیلم»،Cibiyar Labarai ta Jawan.
  83. «اخبار لحظه به لحظه از حادثه تروریستی کرمان/ بازداشت برخی عوامل مرتبط با انفجارها + تصاویر»، Hukumar labarai IRNA.
  84. نگاه کنید به: «اسامی شهدای حمله تروریستی کرمان تا امروز»،ISNA.
  85. «العربیه: داعش مسئولیت حمله تروریستی کرمان را بر عهده گرفت»، Hukumar labarai Fars
  86. «انهدام مقر موساد و پایگاه داعش این گام اول انتقام است»، Jaridar Kehan.
  87. «کتاب از چیزی نمی ترسیدم»، Adireshin yanar gzo na Iran Kitab.
  88. «بخش‌های خواندنی کتاب حاج قاسم»، Hukumar labarai Mehr.
  89. «انتشار ترجمه عربی کتاب "حاج قاسم" در لبنان»،Shafin yanar gzo Mashraq News.
  90. «انتشار کتاب سربازان سردار»، Hukumar labarai ISNA.
  91. «سلوک در مکتب سلیمانی منتشر شد»، Hukumar labarai Mehr.
  92. «عقل سرخ؛ یادنامه علوم اجتماعی ایران برای حاج قاسم سلیمانی و جهان پس از شهادتش منتشر شد»، INtisgaran Daneshgahe Imam Sadik (A.S).
  93. Tahmasabi, Soleimani Aziz, 2019, shanasnameh.
  94. Shirazi, Shakishaye Maktaba Soleimani, 2019, shafi 11-9.

Nassoshi

  • Soufan، Ali، «Qassem Soleimani and Iran's Unique Regional Strategy»، The Combating Terrorism Center، NObEMbER 2018، bOLUME 11، ISSUE "10, Ranar Ziyara: 24 ga watan Day na shekarar 1397."
  • «سردار سلیمانی جزو ۱۰ متفکر برتر حوزه دفاعی نشریه فارن پالیسی شد»، خبرگزاری فارس، "Ranar rubuta labarin: 7 Bahman 1397 Hijiri Shamsi, Ranar ziyara: 29 Azar 1399 Hijiri Shamsi."
  • کتاب «از چیزی نمی ترسیدم»،"Gidan yanar gizo na Iran Book, Ranar ziyara: 9 Tir 1400 Hijiri Shamsi."
  • «Who Is Ƙasem Soleimani, the Head of Iran's Ƙuds Force That Attacked Israel»،"A cikin gidan yanar gizo na jaridar Haaretz, ranar rubuta labarin: 13 Mayu 2018, ranar ziyara: 24 Day na shekarar 1397 Hijiri Shamsi."
  • "Ikrarin tsohon jami'in FbI game da Sardar Soleimani", a cikin kamfanin dillancin labarai na ISNA, kwanan wata da aka buga: 28 ga Nuwamba, 2017, 11 ga Fabrairu 2017.
  • "buga "Sarbazan Sardar" a Istanbul Turkish", a cikin kamfanin dillancin labarai na ISNA, ranar shigarwa: Afrilu 15, 2019, ranar shiga: Yuni 15, 2019.
  • "buga littafin "Hajji Ƙasim" a cikin harshen Larabci a cikin gidan yanar gizon MasreƘ Khabari, ranar shigar labarin: Maris 07, 2016, ranar ziyarta: Fabrairu 14, 2017.
  • «پخش «قاسم» برای اسپانیایی‌زبان‌ها/ فرماندهی میدانی سردار مستند شد»، "Mehr, Ranar rubuta labarin: 5 Day na shekarar 1400 Hijiri Shamsi, Ranar ziyara: 8 Day na shekarar 1400 Hijiri Shamsi."
  • «پخش مستند شهید حاج قاسم سلیمانی از تلویزیون فنلاند + فیلم»، "Kungiyar Matasa, Ranar rubuta labarin: 8 Shahrivar 1400 Hijiri Shamsi, Ranar ziyara: 8 Day na shekarar 1400 Hijiri Shamsi."
  • "Hotunan Sardar Soleimani a yakin da ISIS", a cikin shafin labarai na Aftab, ranar shigar da labarin: 01 Disamba 2018, ranar ziyarta: 11 ga Fabrairu 2018.
  • "bayanan da ba a ji ba game da kasancewar Janar Ƙassem Soleimani a Iraki", a cikin Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, ranar shigarwa: 7 Disamba 2014, ranar shiga: 11 Fabrairu 2017.
  • "Labari mai ban sha'awa na Serdar Soleimani na taimakon Allah a cikin Karbala 5", a shafin yanar gizon kungiyar 'yan jarida na matasa, ranar da aka buga: 19 Disamba 2017, ranar ziyarar, 13 Fabrairu 2017.
  • "Labari na rayuwa da aikinsa na Sardar Ƙassem Soleimani", akan shafin Asr Iran, ranar shigar abun ciki: 2 Disamba 2016, ranar ziyarta: 7 ga Fabrairu 2017.
  • "Yaya aka kafa rundunar Ƙuds?", Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA, kwanan watan shiga labarin: Janairu 15, 2018, ranar shiga: Fabrairu 19, 2018.
  • "Yaya Sardar Soleimani yake rayuwa?" a shafin yanar gizon wakilin kungiyar Jagora na Jami'ar Ƙazbin Islamic Azad, ranar ziyarar: 8 ga Fabrairu, 2017.
  • "Sardar Soleimani da wadanda suka ba shi lakabin "mutumin da ke cikin inuwa", a shafin yanar gizon kungiyar 'yan jarida na matasa, ranar shigarwa: Maris 17, 2016, sun ziyarci: Fabrairu 7, 2017.
  • "Abokansa da abokan gaba suna girmama Ƙassem Soleimani", a shafin yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Student, ranar ziyarar: 7 ga Fabrairu 2018.
  • "Wasikar Major Janar Ƙassem Soleimani ga jagoran juyin juya halin Musulunci dangane da kawo karshen ikon ISIS", a cikin ma'ajiyar bayanai na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatullah Khamenei, ranar shiga: 30 Nuwamba 1396, ranar shiga: 11 Fabrairu 1397.
  • "Dukkanin Manyan Janar na Sojojin Iran / Ƙassem Soleimani, Rashid, Yazidi, Shamkhani da...", akan gidan yanar gizon Khabaronline, kwanan watan shigarwa: 1 Shahribar 1396, ranar ziyarta: 11 bahman 1397.
  • Aikin zane na "Serdar Asemani" yana dauke da alamomin juriya, shahada da hawan Sardar Soleimani, kamfanin dillancin labarai na Anna, ranar bugawa: 25 bahman 2018.
  • bahman, Shoaib, "Gudunwar Ƙuds Force wajen magance rikice-rikicen yammacin Asiya", a cikin mujallar nazarin dabarun duniyar Musulunci, lamba ta 69, bazara 2016.
  • bayanin bikin zagayowar ranar shahadar Sardar Soleimani, kamfanin dillancin labarai na barna, ranar da aka buga: 11/10/2019.
  • Jan hankali; Littafin tunawa da Ilimin zamantakewa na Iran na Hajj Ƙassem Soleimani da Duniya bayan an buga shahadarsa, Jami'ar Imam Sadegh Publications.
  • [https://snn.ir/fa/news/986279/Sakht-mostand-72-hours-with-the-top-of-the-last-days-uku-of-the-life-of-Saheb- bord-Shahid-Haj-Ƙassem-Soleimani "Making the documentary" 72 Saat" tare da taken kwanaki uku na karshe na rayuwar Laftanar Janar Hajj Ƙassem Soleimani", kamfanin dillancin labarai na dalibai, kwanan wata: 7 Janairu 1400 Hijira, kwanan wata. na shiga: 8 Janairu 1400 AH.
  • An gudanar da taron bitar aikin Negin Soleimani a Ƙom, cibiyar bayanai ta Khabar Ƙom, ranar bugawa: 23 Disamba 2018.
  • Mominian, Masoumeh, ""Shahidi wanda ya danganta Janar Soleimani da masu juyin-juya hali a kan sarki", a cikin kamfanin dillancin labarai na Fars, ranar shigarwa: 8 ga Nuwamba, 1397, an shiga: Fabrairu 8, 1397.*biki mai kayatarwa da tattaki na al'ummar Iraki na tunawa da shahadar kwamandojin gwagwarmaya, gidan yanar gizon labarai na Tabnak, ranar bugawa: 14 ga Disamba 2019.
  • "Mujahedat of Martyr Soleimani a cikin "Farkon Janairu" daga Channel One , IRNA, kwanan wata: Nuwamba 25, 1400, ranar ziyarta: Janairu 8, 1400.
  • "Mai shirya shirin filin juriya: shirin gaskiya"Memories of wannan mutumin" don soyayyar Sardar na gina Soleimani", IRNA, kwanan watan shiga: Janairu 8, 1400, ranar shiga: Janairu 8, 1400.
  • Maidan "Mustand Ƙasim Shahidai Ƙassem Soleimani tun daga haihuwa har zuwa shahada da kuma shekaru arba'in na aiki a matsayin mai fage", Sed and Sima Agency, kwanan watan shigar labarin: 15 ga Mayu, 1400H, da aka ziyarta: 8 ga Janairu, 1400H.
  • Nabatian, Mohammad Ismail da Mukhtar Sheikh Hosseini, mahallin ilimi-siyasa na baathist-Takfiri na yanzu na ISIS, Ahl al-bayt World Forum, Isfand 93.
  • Tunawa da farko na shirye-shiryen watsa labarai na makarantar Shahid Soleimani, gidan yanar gizon cibiyar sadarwar Khabar, ranar bugawa: 8 ga Janairu 2019.
  • Tahmasabi, Alame da sauransu, Soleimani Aziz, Ƙom, Hamaseh Yaran Publications, 2019.
  • Ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatollah Khamenei, Didarname (wasika ta musamman ta shahadar Sardar Soleimani), Tehran, Cibiyar Nazarin Al'adu ta juyin juya halin Musulunci, 2018.
  • Shirazi, Ali, Manuniya na Makarantar Soleimani, Ƙom, Khat Moghadam Publications, 2019.
  • Musafi, Mohammad Mohsen, Sobh Sham, Tehran, Surah Mehr, 1399.
  • Soleimani, Ƙasim, ban ji tsoron komai ba, Tehran, Makarantar Haj Ƙasim, 2019.
  • Me yasa ake kiran Haj Ƙasim Sardar Zuciya? Kamfanin Dillancin Labarai na Tsaro, Ziyara. kwanan wata: 16 Janairu 1400
  • «"سردار قاسم سلیمانی" به کتاب‌‌های درسی آمد + تصاویر»، "Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, Ranar rubuta labarin: 31 Shahrivar 1399 Hijiri Shamsi, Ranar ziyara: 18 Bahman 1402 Hijiri Shamsi."