Tufanul Al-Aksa

Daga wikishia

Tufanul Al-Aksa, (Larabci: طوفان الأقصى) Hari ne na neman Yanci da Sojojion Rundunar Hamas da ta kai kan Haramtacciyar Kasar Isra'ila a yankin Bakin Iyaka Tsakanin Gaza da Mamayayyar Kasar Falastsinu, wannan hari ya faru a 15 ga watan Mehr shekara ta 1402 h Shamsi daidai da 7 ga watan Oktoba wanda ya dauki wasu kwanaki ana yinsa, da farko dai Dakarun Rundunar Gwagwarmayar Hamas sun fara da Harba Makamai masu Linzani zuwa cikin Mamayayyar Kasar Falastsinu, bayan nan kuma sai suka shiga ta Kasa, Yahudawa yan Mamaya 1400 ne suka sheka Lahira sannan kusan 3000 suka ji rauni sakamakon wannann Hari na Hamas, wannan Hari ya Kunyata Haramtacciyar Kasar Isra’ila kuma hari ne da ba a taba ganin irinsa ba a kansu a tsawon tarihi. Bayan wannan Hari Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai Harin Ramuwar Gayya kan Yankin Zirin Gaza sun dauki tsawon kwanani suna harba Makamai Masu Linzami masu nauyin gaske, lamarin da ya yi sanadiyar kashe Faraen Hula 2600 da kuma raunata mutane 9000, kashe Fararen Hula da Harba Bomb kan Gidajen Mutane da Isra’ila ta yi ya haifar da Tofin Alatsine da Allawadai daga Kasashe daban-daban na Duniya. Ayatullahi Khamna’i Jagoran Jamhuriyar Muslunci ta Iran da sauran Maraji’an Taklidi sun nuna goyan bayansu ga Al’ummar Gaza.

Muhimmanci da Haduffa

Dakarun Hamas sun Kaddamar Harin Soja kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a ranar 7 ga watan Octoba 2023 harin da aka fi sani da sunan Tufanul Al-Aksa, Kafofin yada labaran Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun siffanta wannan hari da harin da ba a taba ganin kamarsa ba a tsawon tarihinsu kuma Babbar Faduwa ce kansu, [1] haka kuma kan asasin rahotan wasu kafafen yada labarai tare da nakali daga Sojojin Haramtacciyuar Kasar Isra’ila da aka kama su fursunan Yaki sun bayyana cewa wannan Hari Hamas ta tsara shi tsawon shekara guda [2]

Manufar da ta sanya Hamas Kaddamar da wannan Hari

Babban Manufa da hadafin Kungiyar Hamas kan wannan Hari shi ne Yantar da Falastsinawa da kuma yakar `Yan Mamayar Sahayoniya da kuma dakile tauye hakkin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take kan Falastsinawa [3] Kafafen Yada Labarai masu goyan bayan Hamas suma sun bayyana cewa wannan Hari na Hamas ya jawo Harin ramuwar gayya daga bangaren Haramtacciyar Kasar Isra’ila ciki kuwa harda keta Alfarmar Masallacin Al-Aksa da cin mutunci masu Gadinsa da bada Kariya da Yan Kama wuri Zaunan Sahayoniya kan cin zarafin Falastsinawa [4] a cikin bayanin Kwamandan Rundunar Hamas wanda aka fitar rana ta uku da fara wannan Yaki ya bayyana dalilin kai Harin da suka yi kan `Yan Keta Alfama Sahayoniya kan Masallacin Al-Aksa da Musulmai da kuma irin zaluncin da suke da keta Alfarmar Kasar Falastsinu [5]

Aiwatar da Hari

Sayyid Ali Khamna'i:
Wannan bala'i ya samo asali ne daga ayyukan sahyoniyawan da kansu. Lokacin da zalunci da aikata laifuka suka wuce iyaka, lokacin da ta'addanci ya kai iyakarsa, sai a jira guguwar ... Jajircewa da kuma sadaukarwar da Falasdinawan suka yi shi ne amsar laifin makiya masu cin zarafi, wanda hakan ya haifar da tashin hankali. ya kasance yana gudana tsawon shekaru kuma ya karu da ƙarfi a cikin 'yan watannin nan; Ita ma gwamnati mai ci da ke mulkin gwamnatin sahyoniyawan da ke cin karenta ba babbaka

[6]

A ranar 15 ga watan Mehr shekara 1402 h shamsi wanda ya yi daidai da 7 ga watan Oktoba 2023 Dakarun Hamas da suke Zirin Gaza sun Kaddamar tsararren Shirinsu na Harin Shammata Kan Mamayayyar Kasar Falastsinu da take hannun Haramtacciyar Gwamnatin Isra’ila, Mintuna kadan bayan wannan Hari Hamas suka samu Nasarar Harba Makamin Mai linzami har guda 5000 cikin Mamayayyar Kasar Falastsinu, bayan nan kuma Dakarun Hamas suka samu Nasarar shiga ta Kasa [7] Muhammad Dhaifu daya daga cikin Kwamdojin Dakarun Rundunar Hizbu Kassam na Hamas ne ya bada Umarnin wannan tsararren Hari, a farko-farkon Harin Dakarun Hamas sun samu Nasarar cafke wasu adadin Mazauna da Sojojin Sahayoniya sannan suka tsallaka da su zuwa yankin Zirin Gaza a matsayin Fursunonin Yaki, Ministan Yaki Na Sahayoniya ya shelanta Shiga Halin matsanancin Yaki [8] Dakaru 1000 suka shiga wannan Yaki daga bangaren Hamas sannan sun shiga Yankuna 15 cikin Mamayayyar kasar Falastsinu [9] Haramtacciyar Gwanatin Sahayoniya ta bayyana cewa kusan mutum 1400 suka mutu sannan mutum 3500 ne suka raunata daga fara wannan yaki zuwa rana ta 12 sannan [10]

Martani

Anthony Guterres. babban Sakataren majalisar dinkin duniya:
"Yana da mahimmanci a san cewa hare-haren Hamas bai faru ba a cikin wani wuri. An shafe shekaru 56 ana mamayar al'ummar Palasdinu. An ci gaba da mamaye ƙasarsu da ƙauyuka da tashin hankali. Tattalin arzikinsu ya lalace; Mutanensu sun yi gudun hijira tare da lalata gidajensu. Fatansu na samun mafita a siyasance ya ruguje

[11]

Bayan yaduwar Labarin wannan Hari a Kafafen Yada Labarai, hakika Musulmai daga Kasashe daban-daban misalin Iran [12] Afganistan [13] Irak [14] sun matukar Farin ciki sun yi Biki kan Samun Nasarar Hamas. Jamhuriyar Muslunci ta Iran [15] da HIzbullahi Lubnan sun nuna goyan Bayansu kan wannan Hari da Hamas ta kai [16] Ayatullahi Khamna’i Jagoran Jamhuriyar Muslunci ta Iran ya bayyana wannan Hari da Matsayin wata faduwa da bata zata taba gyaruwa ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila [17] Ali Rida Arafi Shugaban Hauzozin Ilimi na Iran ya bayyana cewa wannan Hari wani Babban sauyi ne a Duniyar Musulmai. [18] Amerika ta tura Jirgin Ruwa Mai dauke da Jiragen Sama na Yaki don goyan baya da taya Haramtacciyar Kasar Isra’ila Yaki [19]

Harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila kan Zirin Gaza da Kashe Fararen Hula

File:شهدای حملات تروریستی اسرائیل.jpg
Taron manema labarai na ma'aikatar lafiya ta Gaza a cikin gawawwakin shahidan shahidan harin ta'addancin da Isra'ila ta kai a asibitin Al-Momadani da ke Gaza.

Haramtacciyar Kasar Isra’ila cikin nade tabarmar kunya bayan gafalarsu daga tsararren aiki Dakarun Hamas sun tsananta kai hare-hare kan gidajen Fararen Hula tare da yanke musu Ruwan Sha da Fitilar Lantarki, da darkake Gidajen Fararen Hula da Bomb da kashe Fararen Hula daga Mata da Kananan Yara, da harba Bama-bamai kan cibiyoyin kula da Lafiya da Asibitoci, da amfani da haramtattun Makamai wanda hakan ya haifar da tofin Allawadai da tofin Alatsinai kan Isra’ila daga Kasashen Duniya daban-daban [20] Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun sanar da Mutanen Zirin Gaza su gaggauta Kauracewa Arewacin Zirin Gaza har zuwa yanke shawarar ta nan gaba, sai dai kuma Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam sun nuna rashin amicewarsu kan wannan Mataki na Haramtacciyar Kasar Isra’ila [21] Cikin Harin Ramauwar Gayya da Haramtaciyar Kasar Isra’ila ta kai kan Zirin Gaza ta Ruguje gidajen 135000 ta daidaita su da Kasa, Ma’aikatar Kula da Lafiya ta bayyana cewa sakamakon wannan Harin Ta’addanci da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai mutane 3500 suka rasa rayukansu sannan 11000 suka raunata [22] Tashar watsa Labarai ta NBC a ranar 26 ga watan Mehr wanda yayi daidai da 18 ga watan Oktoba sun nakalto daga Ma’aikatar kula da Lafiya ta Falastsinu cewa an kashe mutane 3478 sannan mutum 12000 sun raunata [23] kan asasin Ma’aikatar kula da lafiya ta Falastsinu zuwa rana ta sha biyu da fara Harin Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila an kashe kusan Mata 500 da Kananan Yara 700, [24] haka kuma kan asasin Rahotan Euro News an Ruguje Masallatai 7. [25]

Rashin Nuna Amicewa daga Sannan Duniya kan wanann Harin Ta’addanci

Irin barnar da hare haren Isra'ila ya yi a Gaza

Bayan kai Harin Ta’addanci da Sojojin Sahayoniya suka kai kan Raunanan MUtane Zirin Gaza martanin ya tashi daga sassan duniyar Muslunci da ma Kasashen da ba na Musulmai ba, daga cikin akwai Turkiyya, Iran, Malesiya, Astiraliya, Ingila, da Amerika, Al’ummar wadannan Kasashe sun fito sun Hau kan Tituna suna Zanga-Zangar Nuna rashin Aminta kan wannan Ta’addanci [26]

Martanin Malamai da Maraji’an Taklidi na Shi’a

Zanga-zangar adawa da sahyoniyawan a birnin London na nuna goyon bayan ayyukan guguwar Al-Aqsa, mai taken "'yancin Falasdinu".

Sayyid Ali Khamna’i Jagoran Jamhuriyar Muslunci ta Iran cikin Jawabinsa da Sayyid Ali Sistani daga Maraji’an Taklidi da yake zaune a birnin Najaf tareda fitar takardar Bayani duka sun yi Tofin Alatsine da Allawadai da wannan Ta’addanci na Sahayoniya, Nuri Hamdani, Mukarim SHirazi, Jafar Subhani da Jawadi Amoli daga cikin Maraji’an Taklidi da suka nuna goyan bayansu da Falastsinawa tareda Allawadai da tofin Alatsine kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila [27] Ayatullahi Khamna’i ya siffanta kisan da Sahayioniya suke yiwa Falastsinawa a matsayin Kisan Kare dangi, ya kuma bukaci yin Allawadai da tofin Alatsine kan `Yan Sahayoniya tareda gaggauwa tsayar da Harba Bama-Bamai kan Falastsinawa [28]

Kisan Kiyashi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai kan Asibitin Al-Ma’amadani

Asalin Makala: Kisan Kiyashi da ya faru a Asibitin Al-Ma’amadani A ranar 25 ga watan Mehr h shamsi Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai Harin Ta’addanci kan Asibitin Al-Ma’amadani da yake cike da Marasa Lafiya da masu Rauni da Masu nean mafaka daga yaki a Zirin Gaza, wannan Hari anyi Amfani da Bom kirar Amerika [29] take fiye da Fararen Hula 500 suka mutu [30] da yawa-yawan Kafafen Yada Labarai sun siffanta wannan Harin Ta’addanci da Kisan Kare Dangi, haka kuma ansamu Zanga-Zanga nuna rashin amincewa daga Kasashen Musulmai da ma wanda ba na Musulmai ba kan wannan Ta’addanci, a kasar Jodan Fusatattun Masu Zanga-Zanga sun bankawa Wuta kan Ofishin Jakadancin Isra’ila [31] a wasu Kasashen Musulmi kamar misalin Iran da Irak sun sanar hutun kwana daya don Zaman Makoki da Alhini a baki dayan Kasa [32] haka kuma a kasar Iran an canja Kalar Tutar Haramin Imam Rida (A.S) da Bakar Kala don nuna Alhini da Jimami kan abinda ya samu Al’ummar Musulmai a zirin Gaza [33]

Sakonnin Tattalin Arziki Siyasa da Tsaro

An samu mummunar Faduwar Kasuwar Hannun Jari na Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Bayan Tufanul Al-Aksa da cigabanta zuwa kwana biyar `Yan Kasashen waje Mazauna Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun tattara inasu-inasu sun fice sun gudu [34] Al’amarin da ya haifar da mummunar Faduwar Kasuwar Hannun Jari, da raguwar darajar Takardar Kudaensu a Kasashen Duniya duka haka yana daga

Sakon da Tufanul Al-Aksa ya isar

daga cikin Sakkoni masu dogon Zango da Harin ya isar shine za a samu raguwar saka hannun Jari a Haramtacciyar Kasar Isra’ila [35]

Jingine Daidaita Alaka tsakanin Kasar Saudi Arabiya da Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kan Asasin rahotanni da suka zo bayan Harin neman `yanci na Tufanul Al’aksa, Kasar Saudi Arabiya ta dagatar da shirinta na Daidaita Alaka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila [36]

Dauki ba dadin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tare da Kungiyar Hizbullahi Lubnan

rana tga biyu da kai Harin neman Yanci da Hamas ta yi, Kungiyar Hizbullahi Lubnan ta goyi baya, kuma ta yi da’awar cewa kai Hare-hare kan Matsugunan Sojojin haramtacciyar Kasar Isra’ila har guda uku [37] haka kuma a rana ta uku Hizbullahi Lubnan cikin Martanin da ta yi kan kashe mata wasu adadi Dakaru, ka Harba Makamai Masu Linzami kan cibiyoyin Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila [38]

Bayanin kula

1. "Ranar 10 na aiki" guguwar Al-Aqsa", cibiyar sadarwa ta Al-Alam.
2. "Wane ne babban wanda ya yi hasarar aikin " guguwar Al-Aqsa "?
3. "Guguwar Al-Aqsa ita ce madaidaicin koma bayan gwamnatin sahyoniyawan", Cibiyar Bincike ta Majalisar Musulunci.
4. "Ranar 10 na aiki" guguwar Al-Aqsa", cibiyar sadarwa ta Al-Alam.
5. "Lokaci zuwa yanzu tare da kwana na uku na guguwar Al-Aqsa", kamfanin dillancin labarai na Al-Alam.
6. مراسم مشترک دانش‌آموختگی دانشجویان دانشگاه‌های افسری نیروهای مسلح»، دفتر و حفظ و نشر آثار آیت‌الله خامنه‌ای
7. دهمین روز از عملیات طوفان الاقصی
8. "Lokaci zuwa lokaci tare da aikin Tofan al-Aqsa", cibiyar sadarwar Al-Alam.
9. "Wane ne babban wanda ya yi hasarar aikin " guguwar Al-Aqsa "?
10. دوازدهمین روز از عملیات طوفان الاقصی.https://www.nbcnews.com/news/world/live-blog/israel-hamas-war-live-updates-rcna120978
11. "Guterres: War also has rules", Anadolu Agency.
12. Misali, duba: "Farin cikin mutanen Tehran bayan nasarar da Falastinawa suka samu a farmakin guguwar Al-Aqsa", kamfanin dillancin labaran IRNA.
13. Farin cikin al'ummar Afganistan bayan harin guguwar Al-Aqsa", kamfanin dillancin labarai na Mehr.
14. "Hoton bikin farko na aikin guguwar Al-Aqsa". An fara bukukuwan murna da farin ciki", 'yan uwanta
15. "Tehran na ci gaba da bayar da goyon baya ga dukkanin gwagwarmayar Palasdinawa, goyon bayan Iran ga " guguwar Al-Aqsa ", shafin yanar gizon jaridar Dunyai Ekhtaz.
16. "Lokaci zuwa lokaci tare da rana ta biyu na aikin guguwar Al-Aqsa]", Al-Alam Network.
17. "Taron yaye daliban jami'o'in sojoji na hadin gwiwa", ofishin kiyayewa da buga ayyukan Sayyidina Ayatullah Azmi Khamene'i.
18. "Aikin guguwar Al-Aqsa mafarin babban sauye-sauye ne a duniyar Musulunci da kuma yankin", Majalisar Tsaro.
19. "Lokaci zuwa lokaci tare da kwana na biyar na aikin " guguwar Al-Aqsa ", kamfanin dillancin labarai na Al-Alam.
20. "Ranar 10 na aiki" guguwar Al-Aqsa", cibiyar sadarwa ta Al-Alam.
21. "Ranar 8 na aikin " guguwar Al-Aqsa ", kamfanin dillancin labarai na Al-Alam.
22. دوازدهمین روز از عملیات طوفان الاقصی
23. https://www.nbcnews.com/news/world/live-blog/israel-hamas-war-live-updates-rcna120978
24. غزة تحت النار و الحصار
25. «تصاویر ویرانه‌های مسجد الحبیب محمد در حملات هوایی اسرائیل به غزه»
26. "Ranar 9 na aikin " guguwar Al-Aqsa ", cibiyar sadarwa ta Al-Alam.
27. Kamfanin dillancin labaran Mashreq ya ce " martanin da mahukuntan Taqlid suka yi kan laifukan gwamnatin Sahayoniya.
28. "Haduwar fitattun malamai da kwararrun masana kimiyya tare da jagoran juyin juya halin Musulunci", ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatollah Khamenei.
29. "An kai harin bam ne a Asibitin Mohamedani", kamfanin dillancin labarai
30. دوازدهمین روز از عملیات طوفان الاقصی
31. "Kana wuta ga ofishin jakadancin yahudawan sahyoniya a Jordan", Khabaronline.
32. «العراق وإيران ودول عربية تدخل حدادا عاماً على أرواح ضحايا غزة»
33. «اعلان عزا در حرم مطهر رضوی به دنبال جنایات صهیونیست‌ها در نوار غزه»
34. "Lokaci zuwa lokaci tare da rana ta biyar na " guguwar Al-Aqsa ", Al-Alam Network.
35. "Wane ne babban wanda ya yi hasarar aikin " guguwar Al-Aqsa "?
36. "Majiyar da ke kusa da gwamnatin Saudiyya: Riyadh ta dakatar da tattaunawar daidaitawa da Isra'ila", kamfanin dillancin labarai na Tasnim.
37. "Lokaci zuwa lokaci tare da rana ta biyu na aikin guguwar Al-Aqsa]", Al-Alam Network.
38. "Lokaci zuwa lokaci tare da rana ta biyu na aikin guguwar Al-Aqsa]", Al-Alam Network.

Nassoshi

Template:چپ‌چین

Template:پایان چپ‌چین