Jump to content

Fihirisar Kashe-Kashen Isra'ila

Daga wikishia

Fihirisar Kashe-Kashen Isra'ila, (Larabci| قائمة المجازر الإسرائيلية) magana ce game da kashe-kashe da Isra'ila ta yi a Falasɗinu da garuruwan da suke cikinta a tsawon tarihin mamaye Falasɗinu da ta yi, kamfanin dillancin labarai na Mehr sun ba da rahoto kashe-kashe har guda 62 shi kamfanin dillancin labarai na Masheƙ ya kawo guda 125 daga kashe-kashe da hare-haren soja da gwamnatin Sahayoniyya ta Isra'ila ta aika a tsawon tarihin mamaye Falasɗinu da sauran yankuna, sun naƙalto ne daga cibiyar nazari ta Al'asra.[1] Bisa rahotan cibiyar sadar da bayanai ta Falasɗinu, daga shekarar 1948 zuwa 2024 miladiyya, Isra'ila ta kashe fiye Falasɗinawa dubu ɗari.[2] Jaridar harshen Ingilishi ta Irish Independent, cikin wani rahoto mai taken “Mafi hatsarin masu kisa” ta kira hukumar leƙen asiri ta Isra'ila mai suna (Mossad) da sunan inji kashe mutane mafi rashin imani da tausayi.[3]

An ce cikin adabin siyasa na Farsi, gwamnatin Sahayoniya ta shahara da sunan gwamnatin kashe ƙananan yara.[4] Bisa ƙididdigar alƙaluma hukumomin ƙasa da ƙasa, daga shekarar 2008 zuwa yau Isra'ila ta kashe ƙananan yara dubu talatin da takwas cikin hare-haren da take kai wa kan Falasɗinu.[5]

Manyan hare-haren Isra'ila kan mutanen Falasɗinu da kuma kashe-kashen fararen hula da ƙananan yara an yi la'akari da shi matsayin yunƙurin kisan ƙare dangi.[6] Daga jumlar kisan ƙare dangi, Bisa rahotan kamfanin dillancin labarai na Aljazira, akwai farmakin Isra'ila kan zirin Gaza a Oktoba 2023 wanda ya tattara dukkanin sharuɗɗan kisan ƙare dangi, cikin wannan hari, Isra'ila ta kai farmaki kan baki ɗayan Gaza, wurare na fararen hula misalin asibiti da makarantu da gine-ginen matsuganansu duka ta ƙaddamar da ruwan bama-bamai a kansu, tare da kashe dubunnan ƙananan yara da mata.[7]

Jerin Kashe-Kashen Isra'ila Zuwa Shekarar 1948 Miladiyya

Ba'arin kashe-kashe da gwamnatin Sahayoniyya ta aikata daga shekarar 1948 miladiyya (Zamanin da aka kafa Isra'ila)

Layi Suna Lokaci Wuri Abin da Ya Faru
1 Kashe-kashen kasuwar Haifa 6Maris 1938m Garin Haifa Wani bom ne ya fashe a kasuwar Haifa da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21 da raunata 38
2 Kashe-kashen kasuwar Haifa 6 Yuni 1938m Garin Haifa Sahayoniyyawa sun dasa bom cikin motoci guda biyu a kasuwar Haifa motocin suka tarwatse suka kashe mutane 21 tare da raunata 35
3 Kashe-kashen kasuwar Larabawa 26 Agusta 1938m Birnin Ƙudus An tarwatsa wata motar da aka saka bama-bamai a kasuwar Ƙudus, inda mutane 34 suka mutu, 35 kuma suka jikkata
4 Kashe-kashen kasuwar A-arabiyya 25 Yuki 1938m Garin Haifa An tarwatsa wata motar da aka saka bama-bamai a kasuwa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 35 da jikkatar wasu 70.
5 Kashe-kashen kasuwar Haifa 26 Yuli 1938m Garin Haifa An tarwatsa wani bam da ake ɗauka a hannu a kasuwa, inda mutane 47 suka mutu.
6 Kashe-kashen Haifa 2 Maris 1939m Garin Haifa A yayin fashewar wani bam a birnin Haifa, mutane 27 sun mutu kuma 39 sun jikkata.
7 Kashe-kashe a cikin kasuwar Haifa 20 Yuni 1940m Birnin Ƙudus Wani bam ta tashi a kasuwar Haifa inda ya haddasa mutuwar mutane 78 da jikkatar wasu 24.
8 Kashe-kashen babaul al-Amud 29 Disamba 1947m Garin Haifa Wa durom da ke ɗauke da abubuwan fashewa daga rundunar Argun ya fashe, mutane 14 sun mutu. Washegari kuma wannan runduna ta kashe wasu 11.
9 Kashe-kashen Shaik Barik 30 Disamba 1947m Ƙauyen Shaik Barik Harin da sojojin Sahiyoniyya suka kai kan wannan ƙauye, wanda ya sanadiyyar mutuwar mutane 40.
10 Kashe-kashen Balad Shaik 31 Disamba 1947m Ƙauyen Balad Shaik a filayen Haifa Harin da sojojin Palmach suka kai kan wannan ƙauye, wanda ya janyo mutuwar mutane 60, rushe gidaje da dama, da tserewar al'umma daga yankin.
11 Kashe-kashen Assaraya Al-arabiyya 8 Janairu 1948m Garin Yafa Rundunan Sahiyoniyya sun tayar da wata mota da aka dasa bama-bamai a ginin al-Saraya al-Arabiyya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 70 da jikkatar ɗaruruwan jama'a
12 Kashe-kashen Ammara garbu 18 Janairu 1948m Garin Haifa An fashe bam ɗin lokaci a titin Salah al-Din a birnin Haifa, wanda ya haddasa mutuwar mutane 31 da raunata wasu 60.
13 Kashe-kashen Shari'i Abbas 28 Janairu 1948m Garin Haifa Harin da sojojin Sahayoniyya suka kai kan titin Abbas, tare da tayar da duro mai ɗauke da bama-bamai wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 20 da jikkatar wasu 50.
14 Kashe-kashen ƙauyen Sa'asa'a 14 Faibrairu 1948m Ƙauyen Sa'asa'a kusa da Haifa Rundunar Palmach ta kai hari kan wannan ƙauye, inda ta kashe mutane 60 tare da lalata gidaje da dama
15 Kashe-kashen ƙauyukan Al-Husainiyya 1948m Ƙauyen Al-husaainiyya kudancin filayen Al-hula A farmakin farko da rundunar Palmach ta kai kan wannan ƙauye, mutane 15 sun mutu. A farmakin na biyu da aka kai a ranakun 16 da 17 ga Maris, an kashe fiye da mutane 30.
16 Kashe-kashen jirgin ƙasa na Haifa 31 Maris 1948m Jirgin ƙasa daga Haifa zuwa Yafa Wasu jama'a daga jam'ain tsaro na Hagana sun kai farmaki kann jirgin ƙasa tare da kashe mutane 40.
17 31 Maris 1948m 31 Maris 1948 Jirgin ƙasa na Haifa al-Ƙahira zuwa Haifa An dasa bam a cikin jirgin ƙasa daga birnin al-Ƙahira zuwa Haifa, wanda ya haddasa mutuwar mutane 40 da jikkatar wasu 60
18 Kashe-kashen Dir Yasin 9 Afrilu 1948m Ƙauyen Yasin (Yammacin garin Ƙudus) Rundunonin Irgun da Shateran sun kai hari kan wannan ƙauye, inda suka yi kisan kiyashi, suka lalata gidaje, kuma suka mamaye yankin. A harin, mutane 250 zuwa 360 sun mutu
19 Kashe-kashen ƙauyen Ƙaluniya 12 Afrilu 1948m Ƙauyen Ƙaluniya a hanyar Ƙudus zuwa Yafa Rundunar Palmach ta kai farmaki biyu a cikin kwanaki biyu kan wannan ƙauye, inda ta lalata ƙauyen gaba ɗaya kuma ta kashe mutane da dama
20 Kashe-kashen garin Haifa 22 Afrilu 1948m Garin Haifa Sahayoniyya sun lalata ƙauyen da makamin atilari goma sha biyu (12 artillery) kuma suka kashe mutane 70 daga cikin mazauna yankin
21 Kashe-kashen ƙauyen Ainul Zaitun 4 Mayu 1948m Ƙauyen Ainul Zaitun Sahayoniyya sun lalata ƙauyen ta amfani da makamin atilari 12 kuma suka kashe mutane 70 daga mazaunan yankin
22 Kashe-kashen garin Safad 13 Mayu 1948m Garin Safad Lokacin harin da ƙungiyar Haganah ta kai kan wannan birni, mutane 70 daga cikin mazauna yankin sun mutu.
23 Kashe-kashen Baitul Daris 21 Mayu 1948m Ƙauyen Baitul Daril arewa masu gabas na Gaza Cikin kai wannan hari da wasu jama'a daga Sahayoniyya suka yi kan wannan ƙauye, sun kashe mutane 260
24 Kashe-kashen ƙauyen Ɗanɗura 22 da 23 Mayu 1948m Ƙauyen Ɗanɗura An kai hari kan ƙauyen Ɗanɗura wanda ya haddasa mutuwar mutane 250
25 Kashe-kashen garin Alludi 11 Yuli 1948m Garin Alludi Dakarun kwanton bauna na Isra'ila ƙarƙashin jagorancin Moshe Dayan sun kai hari kan wannan birni, inda suka yi kisan kiyashi. Harin ya haddasa mutuwar mutane 426
26 Kashe-kashen Dawamiye 29 Oktoba 1948m Ƙauyen dawamiye yammacin tsaunukan Al-Khalil Sojojin Isra'ila sun kashe mutane 200 sakamakon hari da suka kai a wannan ƙauye.[8]

Jerin Kashe-Kashen Isra'ila Bayan Shekarar 1948 Miladiyya

Ba'arin kashe-kashen Isra'ila daga shekarar 1948m (Lokacin da aka shelanta kafa Isra'ila)

Kashe-Kashe Na Sirri
Layi Suna Lokaci Wuri Abin da Ya Faru
1 Kashe-kashen Ƙalƙiliyya 10 Oktoba 1953m Garin Ƙalƙiliyya a yammacin kogin Jodan Sojojin Isra'ila sun kai hari tare da kashe mutane 70 daga ahalin wannan gari
2 Kashe-kashen Ƙabiyya 10 da 15 Oktoba 1953m Ƙauyen Ƙabiyya A yayin wani hari da sojojin Isra'ila suka kai karkashin jagorancin Ariyal Sharon zuwa wani ƙauye, mutane 69 sun mutu, kuma gidaje da dama aka rushe.
3 Kashe-kashen Gaza 28 Fabrairu 1955m Zirin Gaza A lokacin wani hari da sojojin Isra'ila suka kai yankin Zirin Gaza, mutane 39 sun mutu sannan wasu 33 suka jikkata.
4 Kashe-kashen Kufru Ƙasim 29 Oktoba 1956m Ƙauyen Kufru Ƙasim A cikin harbin da dakarun Isra'ila suka yi wa mutanen wani ƙauye, mutane 49 sun mutu.
5 Kashe-kashen Khan Yunus 3 Nuwamba 1956m Garin Sansanin gudun hijira na Khan Yunus Sakamakon harbe-harben bindiga na sojojin Isra'ila mutane 275 suka mutu
6 Kashe-kashen Ma'aikatar Abu Za'abal 12 Fabrairu 1970m Jirgin sojan Isra'ila ya kai farmaki kan ma'aikata tare da da kashe ma'aikata guda 70 da kuma jikkata 69
7 Kashe-kashen Saida 16 Yuli 1982m Garin Saida a kudancin Labanun Cikin harin da Sahayoniyya suka kai kan wannan gari sun kashe mutane 80
8 Kashe-kashen Sabra Da Shatila 16-18 Satumba 1982m Sansanin ƴan gudun hijira na Sabra da Shatila a Labanun A lokacin yakin Isra'ila da Labanun a shekarar 1982, dakarun Isra'ila tare da tallafin dakarun Falanjis na Labanun sun kai hari kan ƙauyukan Sabra da Shatila — sansanonin 'yan gudun hijira da ke birnin Bairut.
9 Intifazal Falasɗinawa ta farko Disamba 1987-1991m A wannan ƙaddamar da bore (Intifada), sama da mutane 1,300 Falasɗinawa suka mutu.
10 Kashe-kashen haramin Ibrahim 25 Fabrairu 1994m Masallacin Al-Aksa (Baitul Muƙaddas) Baruch Goldstein tare da wasu 'yan ƙungiyar yahudawan ƙasar Isra'ila masu zaune a sansanin mamaya, sun shiga masallacin Al-aksa inda suka harbi masu sallah har suka kashe mutane 60.
11 Kashe-kashen Ƙana 18 Afrilu 1996m Ƙauyen Ƙana a kudancin Labanun A lokacin harin Isra'ila da Labanun da ake kira “Operation gungun fushi”, sojojin Isra'ila sun kai farmaki kan ƙauyen Ƙana (قانا) da ke kudancin Labanun. Wannan hari ya faru a ranar 18 ga Afrilu, 1996.
12 Kashe-kashen Hayyud Daraj 22 Yuli 2002m Yankin gidajen mutane da yake kusa da Filin wasa Yarmuk a Gaza A yayin wani hari da jirgin yaki na Isra'ila, an kashe mutane 174 kuma 140 sun jikkata.
13 Kashe-kashen Rafa 18-20 Mayu 2004m Rafa A lokacin wani hari da Isra'ila ta kai da tankoki da jiragen sama masu saukar ungulu, aka kashe mutane 56 'Falasɗinawa, sannan 150 suka jikkata.[9]
14 Kisan Kiyashi da ya Faru a Asibitin Alma'amadani 17 Oktoba 2023m Asibitin Al-ma'amadani A lokacin harin da jiragen yaki na Isra'ila suka kai kan Asibitin al-Maʿamadani (ko al-Ahli al-Arabi) a Gaza, fiye da ƴan gudun hijira 500 da ba su da makami sun mutu.[10]
15 Fashewar Na'urorin Pager Na Hizbullahi Lubnan 18 Satumba 2024 Labanun Da Siriya A cikin waɗannan fashewar, akalla mutane 12 sun mutu, kuma kimanin 2,800 sun jikkata.[11]
16 Kashe-kashen mutanen Iran a Yaƙin Isra'ila Da Iran 11-23 Yuni 2025m Iran A cikin waɗannan hare-hare, mutane kusan 1,100 sun mutu sannan sama da 5,800 suka jikkata.[12]

Kashe-kashen Shammace

An ce Sahayoniyyawan Isra'ila tun bayan shelanta kafa daularsu, sun aikata kashe-kashe na sirri fiye da mutum 2700.[13] Kisan gilla da wannan haramtacciyar gwamnati ta shahara da aikatawa bai taƙaitu cikin Falasɗinawa da jagororinsu da dakarun sojansu ba kaɗai, bari dai sun aikata wannan ta'addanci na su kan shugabannin siyasa da malamai masu tarin yawa a faɗin duniya.[14]] daga jumlatsu sun kashe Sayyid Hassan Nasrullah, na uku cikin jerin manyan sakatarorin Hizbullahi Lubnan, Muhammad Baƙiri, Babban kwamandan dukkanin rundunonin sojojin ƙasar Iran, Husaini Salami, kwamandan dakarun kare juyin juya halin muslunci, Isma'il Haniyye, sakataren harkatu Hamas Ba'arin mutanen da Isra'ila ta kashe su kisan shammace, su ne kamar haka:

Layi Suna Lokaci da wurin da aka aikata kisan Bayanin abin da ya faru
1. Sayyid Abbas Musawi 16 Fabrairu 1992m/ kusa da Bairut Na biyu cikin manyan sakatarorin Hizbullahi Lubnan
2. Imad Mugniyya 12 Fabrairu 2008m/Damishƙi Daga cikin fitattun kwamandojin Hizbullahi Lubnan na ƙasar Labanun wanda aka fi sani da Shehun shahidan gwagwarmaya[15]
3. Shaik Ragib Harbi 16 Fabrairu 1984m Malamin Shi'a
4. Ahmad Yasin 22 Maris 2004m/Zirin Gaza Daga cikin jagoririn Hamas
5. Samir Ƙanɗar 20 Disamba 2015m Daga cikin membobin mazhabar Shi'a a ƙungiyoyin ƴancin Falasɗinu wanda ya zauna a kurkuku na kusan tsawon shekaru 30 a Isra'ila
6. Abdul-Aziz Rantisi 17 Afrilu 2004m/Zirin Gaza Daga shugabannin Hamas
7. Fatahi Shaƙaƙi 26 Oktoba 1995/Tsibirin Malta Cikin mutanen da su ka kafa Ƙungiyar Jihadul-Islam
8. Baha'u Abul Aɗa 12 Nuwamba 2019m/Zirin Gaza Daga cikin manyan kwamandojin harkatu Jihadul Islami Falasɗinu
9. Mahmud Almabhu 19 Janairu 2010m/Dubai Daga cikin manyan kwamandojin Hamas
10. Khalil Al-Wazir (Abu Jihad) 16 Fabrairu 1988m/A garin Tunis Daya daga cikin mutanen da suka kafa ƙungiyar gwagwarmayar Fatah a Falasɗinu kuma mataimaki ga Yasir Arafat.
11. Nazar Abdul-ƙadir Rayyan 1 Janairu 2009m/Zirin Gaza Daga cikin manyan jagororin Hamas
12. Mas'ud Ayyaz 3 Fabrairu 2001m/Zirin Gaza Daga shuwagabannin Hizbullahi Lubnan
13. Salahu Musɗafa Muhammad Shahad 22 Janairu 2002m/Zirin Gaza Daga cikin shugabannin rundunar al-ƙassam, reshen soja na ƙungiyar Hamas.
14. Jamal Mansur 31 Yuli 2001m/Gaɓar kogin Jodan Dga cikin manyan ƙusoshin Hamas
15. Zuhairu Muhsin 26 Janairu 1979mm/ A kudancin Faransa Daga cikin shugabannin soja na ƙungiyar ƴancin Falasɗinu
16. Abu Ali Musɗafa 27 Oktoba 2001m/ Ramallah
17. Sa'id Siyam 15 Janairu 2009m/Jabaliyya Babban sakataren gwagwarmayar kwato ƴancin mutanen Falasɗinu
18. Muhammad Azzawari 15 Disamba 2016m/Garin Safaƙus Tunis Memba a rundunar al-ƙassam kuma ƙwararre a fasahar sarrafa jiragen sama daga ƙasar Tunisia.
19. Yahaya Ayyash 6 Janairu 1996m/Zirin Gaza Injiniyan makamai a harkatu Hamas
20. Yahaya Almashad 13 Yuni 1980m/A birnin Faris Masanin makamashin nukiliya
21. Awad Abu Nasir 11 Janairu 2010/Diru Balahi Daga cikin manyan kwamandojin Jihadul Islami
22. Isa Abdul-Hadi 30 Yuli 2010m/Zirin Gaza Daga cikin kwamandojin Izzud-dini Al-ƙassam
23. Adli Hamdan 24 Janairu 2002m Daga manyan ƙusoshin Hamas
24. Hassan Holu Allaƙis 4 Disamba 2013m/Kudancin Labanun Shugaban sashen fasaha, makamai da sadarwa na Hizbullahi Lubnan[16]
25. Salihu Aruri 2 Janairu 2024m/Bairut Daga cikin ƙusoshin Hamas[17]
26. Muhammad Rida Zahidi 1 Afrilu 2024m /Damishƙi Daya daga cikin manyan kwamandojin Dakarun Ƙudus Iran, wanda ya mutu cikin harin iska da Isra'ila ta kai ofishin jakadancin Iran, tare da wasu mutum shida.[18]
27. Isma'il Haniyye 31 Yuli 2024m/Tehran Daya daga cikin manyan jami'an ƙungiyar Hamas, tare da wani mai tsaronsa mai suna “Wasim Abu Shaaban”.[19]
28. Fu'ad Shukur 30 Yuli 2024m, cikin wani hari da Isra'ila ta kai kan bene a kudancin Labanun Yana cikin kwamandojin soja na Hizbullahi Lubnan[20]
29. Ibrahim Aƙil 20 Disamba 2024m, ya yi shahada sakamakon harin jirgin yaki na Isra'ila Daga cikin kwamandojin soja na Hizbullahi Lubnan[21]
30. Sayyid Hassan Nasrullah 27 Satumba 2024, ya yi shahada sakamakon harin Isra'ila kan wani dogon bene da yake ciki a Dahiyatu Bairut Na uku cikin manyan sakatarorin Hizbullahi Lubnan[22]
31. Sayyid Abbas Nilfuroshan 27 Satumba 2024m, sakamakon harin Isra'ila kan wani dogon bene da yake ciki a Dahiyatu Bairut. Daga cikin kwamandojin Dakarun Kare Juyin juya halin muslunci, kuma mai bada shawara a Labanun.[23]
32. Ali Karaki 27 Satumba 2024m, sakamakon harin Isra'ila kan wani dogon bene da yake ciki a Dahiyatu Bairut Daga cikin kwamandojin Hizbullahi Lubnan[24]
33. Nabil Faruƙ 28 Satumba/Bairut Malamin addini kuma memba a majalisar zartarwa ta Hizbullahi[25]
34. Sayyid Hashim Safiyud-dini 23 Oktoba 2024m/Aka tabbatar da ya yi shahada Shugaban majalisar zartarwa ta Hizbullahi Lubnan[26]
35. Muhammad Baƙiri 12 Yuni 2024m/Tehran Shugaban dukkanin rundunonin sojan Jamhuriyar muslunci ta Iran
36. Husaini Salami 12 Yuni 2024m/Tehran Kwamandan Dakarun Kare Juyin juya halin Muslunci
37. Gulam Ali Rashid 12 Yuni 2024m/Tehran Kwamandan sansanin "Khatam al-Anbiya" na rundunar Kare juyin juya halin Muslunci(IRGC)
38. Amir Ali Haji Zade 12 Yuni 2024m/Tehran Kwamandan Rundunar Sararin Samaniya da Makamai na Rundunar Pasdaran (IRGC Aerospace Force Commander)

Kan asasin takardun shaida da rahotanni, hukumar leƙen asiri ta Isra'ila (Mossad) tana da hannu dumu-dumu cikin kisan shammace da aka aikata kan masana makamashin nukiliya na Iran misalin Mas'ud Ali Muhammadi, Majid Shahriyari, Musɗafa Ahmadi Roshan, Dariyush Rizayi Nejad da Muhsin Fakhri Zade.[27] Jaridar Ingilishi da Irish Independent, cikin wani rahoto ta rubutu cewa hukumar leƙen asiri ta Isra'ila (Mossad) tana da hannu cikin kisan shammace da aka yi kan masana nukiliya na Iran.[28] A rahotan kamfanin dillancin labarai na (NBC) ƙusoshin gwamnatin Amurka suma suna da hannu, su ne suka ba da horo da makamai ga jami'an leƙen asiri na Isra'ila cikin ƙaddamar da kisan shammace kan masana nukiliyan Iran.[29]


Yaƙoƙin Isra'ila Kan Musulmi

Isra'ila tun daga shekarar da ta mamaye Falasɗinu. Lokuta da daman gaske ta dinga yaƙi da musulman Falasɗinu da kuma ƙasashe maƙotanta da suka haɗa da Misra, Siriya, Labanun da Jodan, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane masu yawa da rasa mahallansu da suke rayuwa a ciki, kana sasin rahotanni, a shekarar 1948 a lokacin yaƙin nakbat, mutane dubu goma sha biyar ne Isra'ila ta kashe,[30] a lokacin yaƙin kwanaki shida a shekarar 1967 m, fiye da mutum 17 ne suka aka kashe.[31] A cikin yaƙi na huɗu da Isra'ila ta yi da Larabawa a shekarar 1973m shi ma an kashe mutane dubu takwas.[32]Haka nan a lokacin ofireshin na Salamat Jalil a shekarar 1982m da Isra'ila ta ƙaddamar kan Labanun shi ma an kashe mutane dubu goma sha tara[33] Har ila yau, a cikin ofireshin ɗin Takubban ƙarfe, wanda Isra'ila ta ƙaddama cikin martaninta kan ofireshin ɗin Tufanunl Al-aksa da gwagwarmayar Falasɗinu ta fara ƙaddamarwa kan Isra'ila, a 7 Oktoba shekarar 2023m, Isra'ila ta kashe fiye da mutane dubu hamsin da bakwai.[34] Haka kuma cikin yaƙin kwanaki goma sha biyu da ta yi da Iran a shekarar 2025m, nan ma ta kashe mutane 1100[35]tare da raunata mutum 5700.[36]

Bayanin kula

  1. Ku duba «تجاوز به زنان پیش چشم همسران در ملاعام/ قتل عام شهروندان یک روستا و مثله کردن جنازه‌ها/کشتار کودکان با باتوم», Kamfanin Dillancin Labarai na Masreq;«دهه‌ها جنایت از بزرگ‌ترین جانی جهان»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
  2. «سال از فاجعه نکبت (اشغال فلسطین) گذشت»، Cibiyar Bayanin Falasdinu.
  3. «The world's deadliest assassins», Irish independent.
  4. «آیا خدای واقعی رژیم کودک‌کُش را می‌شناسید؟+فیلم و عکس»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
  5. «آیا خدای واقعی رژیم کودک‌کُش را می‌شناسید؟+فیلم و عکس»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars
  6. برای نمونه نگاه کنید به: «نمایندگان پارلمان اروپا حملات اسرائیل علیه غزه را نسل‌کشی دانستند»، Anatoly Agency؛ Ayyash, «A genocide is under way in Palestine», Al Jazeera Media Network.
  7. Adel and Gallagher, «Genocide in Gaza: A call to urgent global action», Al Jazeera Media Network.
  8. Alal misali ku duba:«قتل‌عام‌های اشغالگران تا سال ۱۹۴۸م»، Rasikhun؛ «پرونده سنگین جنایت‌های ارتش اسرائیل»، Kamfanin dillancin labarai na Mehr«تجاوز به زنان پیش چشم همسران در ملاعام/ قتل عام شهروندان یک روستا و مثله کردن جنازه‌ها/کشتار کودکان با باتوم»، Kamfanin Dillancin Labarai na Mashregh؛ «سیاهه جنایت‌های صهیونیست‌ها-۱|از بالفور تا ترامپ»Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
  9. Alal Misali Ku duba«پرونده سنگین جنایت‌های ارتش اسرائیل»، Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr;«تجاوز به زنان پیش چشم همسران در ملاعام/ قتل عام شهروندان یک روستا و مثله کردن جنازه‌ها/کشتار کودکان با باتوم»، Kamfanin Dillancin Labarai na Masreq;«دهه‌ها جنایت از بزرگ‌ترین جانی جهان»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars؛ «کارنامه سیاه صیهونیست‌ها علیه مردم فلسطین: ۷۵ سال جنایت»، Jaridar Kihan؛ «سیاهه جنایت‌های صهیونیست‌ها-۲|کشتار صبرا و شتیلا و فاجعه قانا», Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
  10. .What we know so far about the deadly strike on a Gaza hospital", AlJAZEERA"
  11. «حزب الله: انفجار أجهزة “بايجر” كانت لدى عدد من العاملين في الحزب والأجهزة المختصة تقوم بالتحقيقات»، Gidan yanar gizo na Al-Manar.
  12. «یک هزار و ۶۸ شهید در جنگ ۱۲ روزه/ ۴۷ شهیدِ کودک و نوجوان»، Tabnak.
  13. «نگاهی بر جنایات رژیم صهیونیستی در ۸۶ سال گذشته»،Kamfanin Dillancin Labarai na Fars«مهمترین ترورهای انجام شده توسط اسرائیل در سراسر جهان»، Jamaran News «بیش از ۲۷۰۰ ترور هدفمند میراث شوم اسرائیل»،kamfanin dillancin labarai na hukuma a Iran
  14. «نگاهی بر جنایات رژیم صهیونیستی در ۸۶ سال گذشته»،Kamfanin dillancin labarai na Fars.
  15. ««من شیخ راغب حرب هستم»»،Kamfanin dillancin labarai na Far
  16. Alal misali ku duba «بیش از ۲۷۰۰ ترور هدفمند میراث شوم اسرائیل»، خبرگزاری جمهوری اسلامی؛ «نگاهی بر جنایات رژیم صهیونیستی در ۸۶ سال گذشته»، Kamfanin Dillancin Labarai na Fars (Fars News Agency؛ «مهمترین ترورهای انجام شده توسط اسرائیل در سراسر جهان»،Jamaran News Platform
  17. «شیخ صالح العاروری به شهادت رسید»،Palestine Information Center.
  18. «خبرگزاری فرانسه: سردار سپاه که در حمله به کنسولگری ایران کشته شد از مشاوران عالی حزب الله بود»،‌ Euro News.
  19. «اسماعیل هنیه در تهران کشته شد»، Kamfanin Dillancin Labarai na Anatoly (Anatoly Agency.
  20. «قاد جبهة الإسناد اللبنانية وناصر المسلمين في البوسنة والهرسك.. من هو الشهيد “السيد محسن شكر”؟»، Al-manar.
  21. حزب الله ینعی قائدین و14 مقاتلا وإسرائیل اتخذت قرار الاغتیال بوقت قصیر»، Aljazira.
  22. «شهادة الأمين العام لحزب الله سماحة السيد حسن نصرالله»، Shafin Al-manar.
  23. «سردار نیلفروشان در بیروت به شهادت رسید+بیوگرافی»، Kamfanin dillancin labarai na Al-alam.
  24. «تصویری از دیدار شهید شیخ نبیل قاووق با رهبر انقلاب»، Shafin Tashar Al-Alam.
  25. «تصویری از دیدار شهید شیخ نبیل قاووق با رهبر انقلاب»،Shafin Tashar Al-Alam.
  26. «حزب الله يزف السيد هاشم صفي الدين شهيداً على طريق القدس»، Shafin Yanar Gizo na Al-Manar.
  27. بAlal misali: «نقش آمریکا در عملیات تروریستی در ایران بعد از پیروزی انقلاب اسلامی»، Cibiyar Takardu da Tarihin Juyin Juya Halin Musulunci na Iran
  28. «The world's deadliest assassins", Irish independent.
  29. «Israel teams with terror group to kill Iran's nuclear scientists, U.S. officials tell NBC News", NBC news.
  30. «تظاهرات مردم فلسطین به مناسبت روز نکبت»، Kamfanin Dillancin Labarai na Anatoly.
  31. Kaffash da sauransu, Dayiratul Almarif Musawwar Tarikh Falasdin , 2013,shafi. 222.
  32. تارخ، «جنگ سال ۱۹۷۳م یوم کیپور», Jangavaran site.
  33. از عملیات سلامت الجلیل و شکل‌گیری حزب‌الله تا خوشه‌های خشم»،Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
  34. «آمار شهدای حملات رژیم صهیونیستی به غزه به ۵۷ هزار و ۵۷۵ نفر رسید»، Kamfanin dillancin labarai na dalibai.
  35. «آمار شهدای تجاوز رژیم صهیونیستی به مرز ۱۱۰۰ نفر رسید»،‌ خبرگزاری مشرق؛ «آسیب ۷ بیمارستان و جراحت ۵۷۵۰ نفر در حمله رژیم صهیونی»،‌ Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr;.
  36. «آسیب ۷ بیمارستان و جراحت ۵۷۵۰ نفر در حمله رژیم صهیونی»،‌ Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr.

Nassoshi