Jump to content

Abdul-Malik Al-Husi

Daga wikishia
Abdul-Malik Al-Husi
Cikakken SunaAbdul-Malik ‌Badrud-dini Al-Husi
LaƙabiAbu Jabra'il
NasabaSharifai jikokin Imam Hassan
Wurin HaihuwaYaman
Sanannun DangiBadru-Dini Al-Husi. Husaini Al-Husi
AddiniMuslunci
MazhabaZaidiyya
MuƙamaiShugaban Harkatu Ansarullahi Yaman
MalamaiBadrud-dini


Abdul-Malik Al-Husi, (Larabci: Samfuri:Arabice) na uku cikin jagororin harkatu Ansarullahi Yaman. Mutum ne da yake goyan bayan haɗin kan musulmi da kuma goyan bayan Falasɗinu. A lokacin shugabancinSa na harkatu Ansrullahi Yaman ya fuskanci zafafan hare-haren soja daga ɓangaren ƙungiyar haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa da ya ƙunshi wasu adadin ƙasashe cikin kuwa har da Saudi Arabiyya. Harkatu Ansarullahi Yaman ƙarƙashin jagorancin Abdul-Malik Al-Husi nasara kai hare-hare kan wasu cibiyoyi a ƙasar Saudi Arabiyya.

Daga jumlar matakai da aka ɗauka a lokacin shugabancin Abdul-Malik Al-Husi, akwai harba makamai masu linzami kan Isra'ila, kai hari kan jiragen ruwa da suka da alaƙa da gwamnatin Sahayoniyya a kogin Bahar Maliya da Babul Mandab, an ƙaddamar da wannan hare-hare don ƙara jaddada goyan baya ga Falasɗinu.

Hare-haren soja da Abdul-Malik ya kai kan muradun Amurka da Isra'ila ya haifar sanya takunkumi kansa daga ɓangaren majalisar ɗinkin duniya da Amurka.

Tarihin Rayuwa

Abdul-Malik Al-Husi, mutum na uku cikin jerin shugabannin ƙungiyar Ansarullahi Yaman, bayan ɗan uwanSa Husaini Al-Husi da babansa Badrud-Dini.[1] Daidai da rahotanni da aka bayar, mahaifinSa ne ya naɗa shi muƙamin shugabancin wannan ƙungiya.[2] Wasu suna ganin cewa ya fara jan ragamar shugabancin wannan ƙungiya ne a shekarar 2010 miladiyya (Shekarar da Badrud-Dini Al-Husi ya rasu).[3] Wasu kuma suna ganin cewa tun daga shekarar 2004 miladiyya (Shekarar da aka kashe Husaini Al-Husi). ne ya fara shugabantar ƙungiyar[4] Wasu daban kuma suka ce ya fara ne a shekarar 2006 miladiyya.[5]

Abdul-Mailk sakamakon kasacewarsa mutum Jarumi mai kaifin basira[6] ana ɗaukarsa daga cikin fitattun mutane ƴan siyasa na duniya.[7]Daga jumlar baiwarsa, akwai kwarewa cikin yin dogon jawabi ba tare da an rubuta masa ba, da yin bayani filla-filla kan batun Falasɗinu.[8]

An haifi Abdul-Malik a jihar Sa'ada. mahaifinSa Badrud-dini, ɗaya ne daga cikin maraji'an addini a mazhabar Zaidiyya, kakansa Amirud-dini yana daga sanannun malaman wannan gari.[9] An bayyana shekarar 1979 ko 1982 miladiyya matsayin shekarar da aka haife shi.[10] Ana masa alkunya da Abu Jabra'il .[11]] Sakamakon dangantakarsa da Annabi (S.A.W) ana masa laƙabi da Sayyid.[12] Abdul-Malik ya yi karatun addini[13]] da adabin Larabci a wurin mahaifinSa, bai samu wata shaida ta karatun zamani ba.[14]

Kan asasin fihirisar da "Cibiyar Masu Nazarin Tsare-tsaren Musulunci ta Masarautar" ta fitar babban birnin Jodan, Abdul-Malik Al-Husi a shekarar 2025 miladiyya ya kasance cikin jerin fitattun mutane hamsin masu matuƙar tasiri a duniyar muslunci.[15]

Halaye Da Mahanga

A ra'ayin masana, Abdul-Malik Al-Husi bayan kashe ɗan uwansa Husaini da gwamnatin Yaman ta yi, ya samu nasarar zama kwamanda da ya takawa sojojin gwamnatin Yaman burki daga ci gaba da shigowa yankunansu.[16] An bayyana shugabancin Abdul-Malik, matsayin babban dalili samun nasarar tsayuwa gaban kutse da tasirin Saudi Arabiyya a ƙasar Yaman.[17] an danganta ƙarfin da Abdul-Malik yake da shi, ya samu ne sakamakon goyan da ya samu daga al'ummarsa.[18] An ce tare da kwaikwayon salon Sayyid Hassan Nasrullah jagoran ƙungiyar Hizbullahi Lubnan ne Sayyid Abdul-Malik Al-Husi ya samu nasarar jawo dubunnan ɗaruruwan mutane zuwa gare shi.[19]

Bayan harin makamai masu linzami da Ansarullahi Yaman suka ƙaddamar a babban birnin Saudi Arabiyya cikin ba da amsa da martani kan hare-haren haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa ƙarƙashin jagorancin Saudi Arabiyya, a shekarar 2017 miladiyya ne ita ƙasar Saudiyya ta sanya ladan dalar Amurka miliyan 30 ga duk wanda ya tsegunta mata bayanan sirri da za su taimaka mata ta kai ga kama Abdul-Malik Al-Husi.[20]

Abdul-Malik Al-Husi ya kasance cikin masu goyan bayan haɗin kan musulmi yana kuma adawa da rikice-rikicen mazhaba.[21] Ya kasance mutum mai rajin kare haƙƙoƙin Falasɗinu da goyan bayan dakarun Falasɗinawa masu yaƙar Isra'ila. Yana la'akari da ofireshin ɗin Tufanul Al-aksa matsayin babbar nasara ta tarihin Falasɗinawa da ma al'ummar musulmi.[22]

  • Alaƙarsa da Iran

Farkon alaƙar Abdul-Malik Al-Husi da Iran ta fara ne tun farkon shekarun 1980 miladiyya, kuma ta kasance ta hannun mahaifinSa Badrud-dini Al-Husi[23] Wasu suna ganin cewa halaye da aƙidunsa sun samo asali da tushe ne daga Iran.[24] Masana, suna ganin cewa karfin iko da mallakar wani yanki daga gaɓar yamma na ta ƙasar Yaman a tekun Bahar Maliya da Ansarullahi suka yi, wata babbar nasara ce ga dabarun ƙasa ga Iran.[25]

Matakai Da Ayyuka

Abdul-Malik Al-Husi a lokacin hallarar ɗan uwansa Husaini a babban birnin San'a na Yaman matsayin wakili a majalisar ƙasar Yaman, shi ne ya ɗauki nauyi kare lafiyarsa.[26] Abdul-Malik mutum da ya yi matuƙar tasirantuwa da ɗan uwansa Husaini; ta kai ga yana ɗaukarsa matsayin uba na ruhaniya kuma abin kwaikwayo a gare shi.[27] Abdul-Malik mutum da ya yi matuƙar tasirantuwa da ɗan uwansa.</ref>] Ba'arin matakai da ya ɗauka a lokacin shugabancin ƙungiyar Ansarullahi Yaman, sun kasnace kamar haka:

  • Gabatar da mece ce ƙungiyar Ansarullahi ta hanyar samar da Shafin gidan yanar giza gizo mai suna Al-Minbar a shekarar 2007 miladiyya, da kuma samar da tashar talabijin ta tauraron ɗan Adam mai suna shabakatul Al-Masira a shekarar 2012 miladiyya, wanda hakan ya taimaka cikin ƙarin samun yawan Mabiya da masu goyan baya ga ƙungiyar Ansarullahi Yaman..[28]
  • Samar da motsi domin kifar da lalatacciyar gwamnati mai ci, gyaran tattalin arziƙi da gudanar da tattaunawar jin ra'ayin al'umma a shekarar 2014 miladiyya.[29]
  • Gwagwarmayar kishiyantar haɗin gwiwar Larabawa na Saudi Arabiyya kan Ansarullahi Yaman.[30]
  • Yaƙi da cin hanci da rashawa na tattalin arziƙi.[31]
  • Kai hare-hare kan Isra'ila da jiragen ruwa da suka ta'allaƙa da ita domin nuna goyan baya ga Falasɗinu cikin ofireshin Tufanul Al-Aksa a shekarun 2023-2024 miladiyya.[32]

Takunkumi

Kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya, a shekarar 2015 miladiyya, sun sanya takunkumi kan Abdul-Malik Al-Husi, ƙarƙashin taken bore kan halastacciyar gwamnati.[33] Daular Amurka a ƙarshe-ƙarshen shekarar 2020 miladiyya lokaci ɗaya da sanya Ansarullahi Yaman cikin jerin ƙungiyoyin ta'addanci, ta sanya takunkumi kan Abdul-Malik Al-Husi. Sai dai kuma sabuwar gwamnatin ƙasar a shekarar 2021 miladiyya ta soke wannan takunkumi..[34]

Abubuwan Da Suka Faru A Lokacin Shugabancin Abdul-Malik Ga Ansarullahi

A zamanin jagorancin Abdul-Malik Al-Husi ga ƙungiyar Ansarullahi, wasu muhimman abubuwa sun faru, za mu yi ishara zuwa ga ba'arinsu:

  • Faruwar wasu adadin yaƙoƙi tare da daular Yaman daga farkon shekarar 2010
  • Rikici da sojojin Saudi Arabiyya a cikin ƙasar a shekarar 2010 miladiyya
  • Fara bore da kifar da gwamnati mai ci ta Ali Abdullahi Salih a watan Fabrairu shekarar 2011 miladiyya
  • Shirya tattaunawar jin ra'ayin al'umma da Allah wadai da hare-haren gwamnatin ƙasar kan husawa a shekarar 2013 miladiyya[35]
  • Karɓe iko kan babban birnin San'a na ƙasar Yaman, da hanɓarar da gwamnatin Ali Abdullahi Salih a shekarar 2014 miladiyya[36]
  • Hare-haren haɗin gwiwar Larabawa kan Yaman ƙarƙashin jagorancin Saudi Arabiyya a shekarar 2015 miladiyya[37]
  • Kashe Ali Abdullahi Salih ta hannun dakarun ƙungiyar Ansarullahi Yaman a shekarar 2017 miladiyya[38]
  • Hare-haren ƙasashen Amurka da Ingila kan wasu cibiyoyin ƙungiyar Ansarullahi Yaman, cikin ba da amsa kan hare-haren harkatu Ansarullahi da ta ƙaddamar kan jiragen ruwan Isra'ila a shekarar 2024 miladiyya.[39]

Bayanin kula

  1. «عبدالملک الحوثی..من متمرد من الاقالیم الی زعیم وطنی»، Gidan yanar gizon kamfanin dillancin labarai na Reuters.
  2. «عبدالملک الحوثی»، Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network.
  3. «عبدالملک الحوثی»،Gidan yanar gizo na Annashra.
  4. «عبدالملک الحوثی.. المرشد الاعلی فی الیمن»، Shafin Harka Islamiyya.
  5. «حقائق لا تعرفها عن عبدالملک الحوثی»، Yanar Gizon Mujallar Wase Sadrak.
  6. Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullahi Yemen, shafi. 194
  7. «حقائق لا تعرفها عن عبدالملک الحوثی»،Yanar Gizon Mujallar Wase Sadrak
  8. «الیمن: من هو قائد انصارالله عبدالملک الحوثی»، Shafin yanar gizo na gidan labarai na France 24.
  9. «قائد انصارالله السید عبدالملک الحوثی»، Gidan yanar gizon Alkhanadiq.
  10. «عبدالملک الحوثی»، Gidan yanar gizon Al Jazeera News Network.
  11. «قائد انصارالله السید عبدالملک الحوثی»Gidan yanar gizon Alkhanadiq
  12. «عبدالملک الحوثی.. الامام الثالث»،Shafin jaridar Asharq Al-Awsat.
  13. «yanar gizon Alkhanadiqd=15 قائد انصارالله السید عبدالملک الحوثی»، Gidan yanar gizon Alkhanadiq.
  14. Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullahi Yemen, shafi. 194
  15. «Top 50-2025»، The Muslim 500.
  16. «عبدالملک الحوثی من زعیم المتمردین الی صانع الملوک»،Gidan yanar gizon labarai na Noon Post.
  17. «راز مقاومت و شکست‌ناپذیری رهبر انصارالله یمن چیست؟»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
  18. «من این یستمد عبدالملک الحوثی قوته»، Gidan yanar gizon kamfanin dillancin labarai na Deutsche Welle.
  19. «عبدالملک الحوثی.. المرشد الاعلی فی الیمن»،Shafin Harka Islamiyya.
  20. احمدی، «عبدالملک الحوثی.. زعیم خفی تلاحقه قائمة ارهاب ترامب»، Yanar Gizo na Anatolu Agency.
  21. «السید عبدالملک الحوثی یدعوا الی وحده الامه و نبذ الخلافات»، Kamfanin Dillancin Labarai na Taqreeb.
  22. «النص الکامل لکلمة عبدالملک الحوثی حول طوفان الاقصی و الرد الاسرائیلی»، Gidan yanar gizo na CNN News Network.
  23. «هذا عبدالملک الحوثی ذراع ایران فی الیمن»، Shafin yanar gizo na Al Arabiya News Network.
  24. Alal misali ku duba: «عبدالملک الحوثی.. الامام الثالث»،Shafin jaridar Al-Sharq Al-Awsat; «عبدالملک الحوثی.. المرشد الاعلی فی الیمن»، Shafin Harka Islamiyya
  25. «من هو زعیم الحوثیین عبدالملک الحوثی؟»،Gidan yanar gizon Masrawy.
  26. «قائد انصارالله السید عبدالملک الحوثی»، Shafin yanar gizo na Alhanadiq.
  27. «قائد انصارالله السید عبدالملک الحوثی»،Shafin yanar gizo na Alhanadiq.
  28. «حقائق لا تعرفها عن عبدالملک الحوثی»، Gidan yanar gizon Mujallar Wase Sadrak.
  29. Sheikh Husseini, Janbashe Ansarullah Yaman, shafi na 252-253
  30. «حقائق لا تعرفها عن عبدالملک الحوثی»، Gidan yanar gizon Mujallar Wase Sadrak
  31. «حقائق لا تعرفها عن عبدالملک الحوثی»، Gidan yanar gizon Mujallar Wase Sadrak.
  32. «السید الحوثی: نرصد السفن الاسرائیلیه فی البحر الاحمر.. سنظفربها و سنستهدفها»،Shafin yanar gizo na Al-Mayadeen News Network;«راز مقاومت و شکست‌ناپذیری رهبر انصارالله یمن چیست؟»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
  33. «جماعة الحوثیین.. حرکة یمنیه جمعت بین الزیدیه و النهج الایرانی و الحکم العائلی»Gidan yanar gizo na Aljazeera News Network.
  34. «جماعة الحوثیین.. حرکة یمنیه جمعت بین الزیدیه و النهج الایرانی و الحکم العائلی»، Gidan yanar gizo na Aljazeera News Network..
  35. «عبدالملک الحوثی.. المرشد الاعلی فی الیمن»،Shafin Harka Islamiyya.
  36. «عبدالملک الحوثی»،Gidan yanar gizo na gidan labarai na Al Jazeera.
  37. «الخروج من حرب الیمن یعزز امن السعودیه و رؤیتها الاستثماریه»، Shafin yanar gizo na jaridar Al Arab.
  38. «مقتل علی عبدالله صالح برصاص الحوثیین»،Gidan yanar gizo na gidan labarai na Al Jazeera.
  39. «ضربات امریکیه و بریطانیه علی اهداف فی صنعاء و الحدیده و الحوثی یتوعده بالرد»، Gidan yanar gizo na gidan labarai na Al Jazeera.

Nassoshi