Jump to content

Samir Ƙanɗar

Daga wikishia
Samir Ƙanɗar
Memba a ƙungiyar ƙwaton ƴancin Falasɗinu
MazhabaYa Fahimci Shi'a daga Duruz
Ranar haihuwa1962 miladiyya
Wurin haihuwaLabanun
Wurin rayuwaLabanun, shekaru 30 a kurkukun Isra'ila
Shahada20 Disamba 2015m, sakamakon harin makami mai linzami da Isra'ila ta kai masa a garin Jarmana kusa da Dimashƙi
KabariDahiyatu Bairut
AyyukaYaƙar Isra'ila


Samir Ƙanɗar, (Larabci: سمير قنطار) wanda ya rayu tsakanin shekaru 1962-2015m, ɗan gwagwarmaya mabiyin mazhabar Duruz kuma memba a ƙungiyar neman ƴancin Falasɗinu wanda daga ƙarshe ya zama ɗanshi'a.

Isra'ila ta kama shi a wani ofireshi na soja wanda daga ƙarshe ta jefa shi a kurkuku. A cikin wani musayen fursunoni da ya kasance a shekarar 2008m tsakanin Isra'ila da Hizbullahi Lubnan aka saki Samir Ƙanɗar ya shaƙi iskar ƴanci. a ranar 20 Disamba shekarar 2015m a wani hari da jiragen yaƙin Isr'aila suka kai a Siriya ne suka shahadantar da Samir Ƙanɗar. Hizbullahi Lubnan tana ɗaukarSa matsayin gwarzo kuma wata alama ta gwagwarmaya.

Tarihin Rayuwa

An haifi Samir Ƙanɗar a shekarar 1962m, a ƙasar Labanun cikin dangi mabiya mazhabar Duruz. Danginsa suna cikin dangi ƴangwagwarmaya a Labanun, ya shiga ƙungiyar nemo ƴancin Falasɗinu tun yana da shekaru 14 a rayuwa.[1]


Yaƙi

A ofireshin ɗinsa na farko da aka aika shi kutsawa Falasɗinu ta wata ɓoyayyar hanya ya faɗa hannun sojojin ƙasar Jodan, sakamakon haka ya zauna a kurkuku kusan shekara guda, bayan sakinsa ne aka haramta masa shiga wannan ƙasa.[2]

Ofireshin A Cikin Mamayayyar Ƙasa

A tsakiyar daren 21 Afrilu 1979m, a lokacin Samir Ƙanɗar yana shekara 16, tare da wasu matasa daban suka kutsa garin Nahari mai nisan kilomita 10 da iyakar ƙasar Labanun, ana cewa ɗaya daga cikin manufofinsu shi ne sace masanan Isra'ila domin yin musayen fursunoni da su da fursunonin Labanun, ƙata ƙungiya ƙarƙashin jagorancinsa sun yi gwabza rikici tare da sojojin Isra'ila, lamarin da ya kai ga kashe waɗanda suke tare da shi da kuma kama shi.[3]

Zaman Kurkuku Na Tsawon Shekaru 30

Bayan yankewa Ƙanɗar hukunci, a shekarar 1980m ne bisa tuhumarsa da kashe mutane biyar, kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai har karo biyar da kuma ƙarin ɗaurin shekaru 47 a kurkuku. Samir Ƙanɗar ya zauna a kurkuku na kusan tsawon shekaru 30. A shekarar 2004m, a wani musayen fursunoni da ya gudana tsakanin Hizbullahi Lubnan da Isra'ila a kan iyakar ƙasar Labanun saura ɗan kaɗan Samir Ƙanɗar ya shaƙi iskar ƴanci, sai dai cewa Isra'ila ba ta amince da sakinsa ba.[4][5]

Shaƙar Iskar Ƴanci

A ranar 16 Yuli 2008m, shekaru biyu bayan yaƙin kwanaki 33, Samir Ƙanɗar tare da membobi huɗu na Hizbullahi Lubnan aka yi musayensu da gawarwaki guda biyu na sojojin Isra'ila. sakinsa bayan shekaru 28 a kurkuku, ya jawo cece-cece kuce da suka mai yawa a Isra'ila, sai dai kuma cewa filin tashi da saukar jiragen saman a Bairut shugaban ƙasar Labanun na lokacin da firaminista da shugaban majalisa sun tarbi Samir Ƙanɗar irin tarbar da ake yi wa (Gwarzon ƙasa).[6]

Zuwa Iran Da Siriya

A shekarar 2009m, Samir Ƙanɗar ya yi tafiya zuwa Iran, ya kuma gana da ƙusoshin gwamnatin ƙasar, daga jumlarsu Ayatullahi Khamna'i jagoran juyin juya halin Muslunci na Iran.[7] Daga lokacin fara yaƙin cikin na Siriya, Samir Ƙanɗar ya kasance yana aiki tare da Hizbullahi a tsaunuka Jolan na Siriya.[8]

Shi'ancewa

Da farko Samir Ƙanɗar ya kasance kan mazhabar Duruz, amma a lokacin zamansa a kurkukun Isra'ila sai ya rungumi mazhbar Shi'a, cikin wata tattaunawa da aka yi da shi ya bayyanawa duniya cewa a lokacin zamansa da kurkuku ne ya fara sanin Shi'anci da littafin Nahjul Balaga ya kuma zaɓi mazhabar Shi'a.[Akwai buƙatar kawo madogara] Sai dai cewa a lokacin da yake kurkukun bai bayyanar da wannan lamari ba, a cewar shuwagabannin Hizbullahi Lubnan ya yi hakan don gudun ka da ace ya canja mazhaba domin a sako shi daga kurkuku.[Akwai buƙatar kawo madogara]

Shahada

A ranar 20 Satumba 2015m, a lokacin da Samir Ƙanɗar yake da shekaru 53 a duniya ya yi shahada sakamakon wani hari na makami mai linzami da Isra'ila ta kai kansa a garin Jarmana kusa da Dimashƙi babban birnin Siriya, an binne Samir Ƙanɗar a maƙabartar raudatu haura Zainab da take Dahiyatu Bairut.[9]


Faɗaɗa Nazari

Littafin Haƙiƙat Samir: Tarihi ne na rayuwar Samir Ƙanɗar, wanda aka buga shi a shekarar 2015 ta hannun kamfanin Intisharat Mehri.[10]

Bayanin kula

  1. Tawakkuli Haqiqat Samir az Naqle، خبرگزاری مهر.
  2. Tawakkuli Haqiqat Samir az Naqle، خبرگزاری مهر.
  3. Tawakkuli Haqiqat Samir az Naqle، خبرگزاری مهر.
  4. Tawakkuli Haqiqat Samir az Naqle، خبرگزاری مهر.
  5. Samir Qantar daga kamu zuwa shahada, jaridar Etelat, Lahadi, 26 ga Janairu, 2015.
  6. Samir Qantar daga kamu zuwa shahada, jaridar Etelat, Lahadi, 26 ga Janairu, 2015.
  7. شهید قنطار:هرگز ایران را تنها نخواهیم گذاشت/ صهیونیست‌ها از نام نصرالله وحشت دارند،Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
  8. Samir Qantar daga kamu zuwa shahada, jaridar Etelat, Lahadi, 26 ga Janairu, 2015.
  9. واکنش مقامات صهیونیستی به خبر شهادت «سمیر قنطار»، خبرگزاری فارس؛ مزار شهید سمیر قنطار، Serat News.
  10. حقیقت سمیر، Soure Mehr Publications.

Nassoshi

  • Samir Qantar Az Isarat Ta shahadat, Jaridar Etelaat, Lahadi, 26 ga Janairu, 2015.
  • Tavakoli, Yaqoob, Haqiqat Samir, Sooreh Mehr Publications, bugu na biyu, Tehran, 2015.
  • Shahidi Qantar: Hargez Iran Ra Tanha Nakhohim Guzashte/Sahayunistha Az Name Nasrullah Wahashat Daran, Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, ranar buga: 19 ga Disamba, 2015.
  • Wakanesh Maqamat Sahayunisti Beh Khabar Shahadat "Samir Qantar", Kamfanin Dillancin Labarai na Fars, ranar buga: 19 ga Disamba, 2015.
  • Mazare Shahid Samir Qantar, Sirat News, Ranar bugawa: Janairu 25, 2015.
  • Haqiqat Samir, Sooreh Mehr Publications.