Labbaika ya Husain

Daga wikishia

Labbaika ya Husain (Larabci: لَبَّيكَ يا حسين), amsa kiran Imam Husaini ne, kuma wani shi'ari ne na ƴan shi'a domin nuna amsa kiran Imam Husaini (A.S), a lokacin yaƙi a karbala a ranar ashura ya yi kira domin neman taimako,.

wannan kira da ya yi ya zo cikin lafuzza daban-daban mafi shahara daga cikinsu su kasance kamar haka: هَلْ مِنْ ناصرٍ یَنْصُرُني؟

Tutar Labbaika Ya Husain a wani taro na zaman makoki

manufar wannan fadin shi'ari da slogan (Take) shi ne shelanta kasancewar tare da Imam Husaini (A.S) da cika alkawari da amsa kiransa na neman taimaka masa, ya zo a tarihi cewa wannan take ya gabatar da waƙi'ar karbala matsayin wata tafiya ta wasu jama'a masu da suke kan wata manufa a tsawon tarihi, kuma sababi na wanzuwar batun da munakashar ashura, wannan take ya kasance wani ramzi da alama ta kwankwasar girmar kai da yakar zalunci da kin miƙa wuya ga ƙasƙanci da wulaƙanta

Ana amfani da wannan shi'ari yayin zaman makoki da ake yi a watan Muharram a ƙasashe da garuruwa daban-daban domin nuna biyayya ga Imam Husaini (A.S), kuma an samar da ayyukan fasaha masu yawa kan wannan shi'ari, shi'a su na maimaita shi a lokacin yaƙi, da lokacin jana'izar shahidai, kuma sakamakon koyi da wannan shi'ari an samar da wasu misalai masu kama da shi waɗanda ake maimaitawa a wajan taruka da zanga-zanga da kuma tarurrukan addini, kamar Labbaika ya Haidar, da Labbaika ya Mahadi.

Gabatarwa

Labbaika ya Husaini sananniya jumla ce wanda take da alaƙa da abin da ya faru a waƙi'ar ashura[1] hakan yana nufin amsa kiran Imam Husaini (A.S),[2] saboda Imam Husaini (A.S) yayin da yake kan hanyarsa daga Makka zuwa Iraƙi ya yi kira musulmi da su taimake shi,[3] daga cikin gurin da ya faɗi haka akwai huɗubarsa da ya yi a Makka, wannan jumla Labbaika ya Husain ta zo a ciki wani yanki na huɗubar

وخُيّر لي مَصرَع أنا لاقيه، كَأَنِّي بَأَوْصَالِي تُقطَّعُهَا عُسْلاَنُ الْفَلَوَاتِ بَيْنَ النَّوَاوِيسِ وَكَرْبَلاَءَ؛ فَيَمْلاَنَ مِنِّي أَكْرَاشاً جُوفاً، وَأَجْرِبَةً سُغْباً ... مَنْ كَانَ فِينَا بَاذِلاً مُهْجَتَهُ، وَمُوَطِّناً عَلَي لِقَاءِ اللَهِ نَفْسَهُ، فَلْيَرْحَلْ مَعَنَا

ma'ana Imam Husaini (A.S) yana cewa an zaɓa min gurin da zan mutu da kuma yadda zan mutu kuma babu yadda zan yi sai hakan ta faru, zan je wani waje a tsakanin Nawawis da Karbala mayunwatan Kuraye za su farmi ni su yi gunduwa-gunduwa da ni, za su yayyaga ni su cika cikinsu da nama na, to ya ku waɗanda kuke tare da ni kusani duk wanda yake so ya sadaukar da jininshi domin mu kuma ya shirya haɗuwa da Allah, to ya zo mu tafi tare da shi.[4]

a wata wasiƙa da ya tura zuwa ga dattawan basra ya kirasu da su taimake shi,[5] ana lissafa wannan wasiƙa cikin mafi shaharar wasiƙa goran gayyatar kawo agaji a da Imam Husaini (A.S) ya rubuta a ranar Ashura,[6]] ita ce dai sananniyar jumlar nan ta هَلْ مِنْ ناصرٍ یَنْصُرُ(Akwai wani mai taimako da zai taimaka min?)[7]

Muhimmacin Da Matsayi

Bayan waƙi'ar Ashura ƴan shi'a suka fara faɗar wannan jumla ta Labbaika ya Husain domin shelanta kasancewa tare da Imam Husaini.[8]kuma da shelanta shirin sadaukarwa da rayuka da dukiya da ƴa'ya domin Imam Husaini (A.S) da kuma ko yi da sahabbanshi kan abin da ya faru a waƙi'ar Karbala.[9] kuma ana cewa wannan shi'ari ya zama shi'ari na duk faɗin duniya,[10] ba ya keɓanta da wani lokaci ba ne kaɗai, a a ana amfani da shi a kowana lokaci,[11] kuma wannan shi'ari yana tallata waƙi'ar Ashura kamar wani abu da ya faru a tarihi kuma zai ci gaba da wanzuwa tsawon tarihi,[12] ƙari kan kasancewar wannan shi'ari yana kiyaye ashura,[13] kuma yana dawamar da huɗubobi na ashura.[14]

Labik ko Hussain a bangon gida a Iraki a lokacin ziyarar al-Arbaeen

Kuma ana lissafa shi matsayin izza da karama da nesantar ƙasƙanci,[15] da ƙin yarda da zalinci da sadaukarwa bisa hanyar gaskiya,[16] da ƴantuwa daga dukkanin maƙiya, [17] da lallata duk maƙarƙashiyar maƙiya,[18] da kawar da danniyar ƴan mulkin mallaka,[19] duk waɗannan su na cikin tasirin da wannan shi'ari yake haifarwa, saboda haka wannan shi'ari ya zama alama ta yaƙar ƴan mulkin mallaka da bijire musu da ƙin bada kai buri ya hau da ƙin yarda da ƙasƙanci da taɓewa,[20] wasu masu tinani su na ganin cewa cin nasarar juyin juya hali ya yi a ƙasar Iran da assasa shi da yaɗa shi a duniya ya kasance albarkacin wannan shi'ari ne na labbaika ya Husaini ne.[21]

Labbaika Ya Husani A Cikin Nassoshin Addini

An yi amfani da kalmar Labbaika tsawon tarihi da ma'anar amsa kira da biyan buƙatun wasu.[22] a wurare da dama, sahabbai sun yi amfani da wannan kalma, [23] suma masu amsa buƙatar Annabi (S.A.W), kamar yaƙin Hunaini, inda suka amsa masa da kalmar Labbaika.[24] saboda haka iƙirarin wahabiyawa cewa yin amfani da wannan kalmar kan wanin Allah ana ganin ba abin karɓa ba ne kuma ba daidai ba ne.[25] A daya daga cikin ziyarori da aka ruwaito daga Imam Sadik (A.S) dangane da kakansa Husaini, yana daga cikin ladubban wannan ziyara mai ziyara ya maimaita sau bakwai yana cewa: "لَبَّيْكَ داعِي اللهِ (Labbaika ya mai kira zuwa ga Allah).[26] a cikin ziyarar Rajab an yi magana da Imam Husaini (A.S) an yi amfani da jumlar "لَبَّيْكَ داعِي اللهِ". [27] Har ila yau cikin Du'a'u Ahad an yi ishara da talbiyar kiran Imam Mahadi (A.S). [28]

Masana ilimin harshe sun yi la'akari da cewa tushen Labaika yana komawa ga biyayya [29] da amsa kira, [30] Su na cewa asalin kalmar "لبيك " لَبَّا لَكَ" Ma'ana: “Na kuduri aniyar yin biyayya gare ku da kuma amsa muku. [31] [32]

Ana amfani da wannan kalma wajen cika aikin Hajji Tamattu da Umra da wannan magana: "لَبَّیك الّلهُمَّ لَبَّیك، لَبَّیك لاشَریك لَك لَبَّیك" "Mun amsa kiranka ya Allah, mun amsa kiranka babu abokin tarayya gare ka. [33]


Amfani Da Wannan Shi'ari

Taken Labik ko Hossein, wanda aka rubuta a cikin Al-Thult, Al-Mukhtar ne ya rubuta shi a cikin littafin zanen Labik ko Hossein.

Ana yin amfani da taken "Labbaika Ya Hussain" a wajen jana'izar da kuma nuna biyayya ga Imam Husaini (A.S), da kuma a fagagen al'adu da fasaha da abubuwan da suka shafi juyin juya hali a tarihi.

A Tarurrukan Addini Da Zaman Makoki

Ana rera taken "Labbaika Ya Husaini"،[34] Turkiya, [35] Labanun[36] Iran,[37] Iraƙ da wasu ƙasashan yammacin duniya, kamar Holand.[38] kamar yadda mutanan Iraƙi masamman mutanan yankin ɗuwairij[39] da ƙabilar Banu Asad[40] a ranar Ashura a lokacin da suke tattaki zuwa haramin Imam Husaini (A.S) su na rera wannan shi'ari, kai a Iran ma wasu manya taruka ana kiransu da Labbaika ya Husaini,[41]kuma a lokacin da ake canza tuta baƙa ta zaman makoki a wata Muharrama ana rera wannan shi'ari na Labbaika ya Husain,[42] a shekara ta 2018 an baza tuta ta labbaika ya husain wadda take da tsayi na tsakanin haramin Imam Husaini dana Sayyidina Abbas (A.S) a wajan jerin gwanon makoki da akeyi na Arba'in.[43]

Sayyid Hassan Nasrullah
labbaika ya husaini tana nufin ka kasance a filin gwagwarmaya ko da kuwa kai ɗaya ne ko da mutane sun barka kuma suka tuhume ka, kuma kai da kuɗinka da iyalanka ka kasance a wannan gwagwarmaya.



(Jawabin Sayyid Hassan Nasrullahi Lokacin Jerin gwanon likkafani: 21-5-2004 )


Labbaika Ya Husaini Cikin Al'adu Da Cikin Fanni

Shi'arin labbaika ya Husain ya zo a cikin waƙar mawaƙa, [44] kuma yana da tasiri a abubuwa daban-daban na al'ada kamar yadda aka samar da abubuwa da yawa a ƙarƙashin wannan shi'ari, kamar yadda aka samar da wannan shi'ari ta hanyar rera shi da muryar Sadiƙ Ahangaran a lokacin taron Arba'in,[45] a fannin rubutun hannu ma akwai fasashohi da aka baje kolinsu cikin wannan shi'ari na labbaika Ya Husain, har ila yau akwai rubuce-rubuce na musamman da wannan jumla ta labbaika ya Husain.[46]

Amfani Da Shi'arin Labbaika Ya Husain Kan Abubuwa Daban-daban Waɗanda Suka Faru

An yi amfani da wannan taken ko shi'ari a cikin abubuwan da suka faru a ƙasashe daban-daban, ciki har da lokacin da Ayatullah Sayyid Ali al-Sistani ya ba da fatawar jihadi a kan kungiyar ISIS, inda wasu bangarori na al'ummar Iraki suka yi maraba da wannan fatawar, su na rera taken Labbaika ya Hussein [47] Su na rera wannan taken ne a cikin hare-haren da suke kai wa kan kungiyar ISIS,[48] kuma an yi amfani da wannan taken wajen jana'izar shahidan gwagwarmaya a Iran,[49] Iraki,[50] da Lebanon.[51]

Bisa Irin wannan shi'ari ko take, labbaika ya Hussain, an ƙirƙiri wasu kamar su a taruka, da jerin gwano ko zanga-zanga, tarukan na addini, misalin waɗanda aka ƙirƙira kamar, labbaika ya Manzon Allah”[52]] da labbaika ya Haiderul Karrar, da labbaiki ya Zainab, da labbaika ya Abbas, da labbaika ya kur'ani, da labbaika ya Mahdi, [53] da labbaika ya Khumaini. da labbaika ya Khamnna'i.[54]

Bayanin kula

  1. «شرح لبیک یا حسین بخش اول: نوشتاری از استاد هادی سروش»، شفقنا.
  2. «شعار «لبیک یا حسین» به معنای اجابت دعوت سیدالشهدا(ع) است»، وكالة مهر.
  3. «شعار «لبیک یا حسین» به معنای اجابت دعوت سیدالشهدا(ع) است»، وكالة مهر.
  4. Al-Halwani, Nozha al-Nazir, 1408 AH, shafi 86; Ibn Tavus, Allahouf, 1348, shafi na 60.
  5. Ibn Tavus, Allahouf, 1348, shafi na 38.
  6. Ibn Tavus, Allahouf, 1348, shafi na 116; Ibn Nama al-Hali, Sa'i'i al-Ahzan, 1406H, shafi na 70.
  7. Muhaddith, Farhang Ashura, 1376, shafi na 471.
  8. «لبیک یا حسین موجب ماندگاری گفتمان عاشورایی است»، وكالة رضوی.
  9. «شعار «لبیک یا حسین» به معنای اجابت دعوت سیدالشهدا(ع) است»، وكالة مهر.
  10. «شعار لبیک یا حسین جهانی شده است»، ایسنا.
  11. «لبیک یا حسین موجب ماندگاری گفتمان عاشورایی است»، وكالة رضوی.
  12. «فراخوان رقابتی حروف نگاری لبیک یا حسین»، کانون هنری شیعی.
  13. «شعار «لبیک یا حسین» به معنای اجابت دعوت سیدالشهدا(ع) است»، وكالة مهر.
  14. «لبیک یا حسین موجب ماندگاری گفتمان عاشورایی است»، وكالة رضوی.
  15. «شعار لبیک یا حسین مبارزه با استکبار ستیزی است»، وكالة رسا.
  16. «شعار لبیک یا حسین مبارزه با استکبار ستیزی است»، وكالة رسا.
  17. ««لبیک یا حسین یعنی رهایی از همه قدرت ها: نوشتاری از استاد هادی سروش – بخش هفتم»، شفقنا.
  18. «لبیک یا حسین خنثی کننده توطئه دشمنان است»، حوزه نمایندگی ولی فقیه در امور حج و زیارت.
  19. «شعار ” لبیک یا حسین” هیمنه استکبار را درهم‌شکسته است»، زرین خبر.
  20. «شعار لبیک یا حسین مبارزه با استکبار ستیزی است»، وكالة رسا.
  21. «شعار لبیک یا حسین مبارزه با استکبار ستیزی است»، وكالة رسا.
  22. Misali, duba: Al-Tabari, Tarikh al-Umam Wal-Muluk, 1387 AH, juzu'i na 8, shafi:84; Ibn Saad, Tabaqat al-Kubara, 1410 AH, juzu'i na 3, shafi na 92; Dinouri, Al-Akhbar al-Tawwal, 1368, shafi na 365.
  23. Misali, duba:: Al-Maqrizi, Imtaa al-Isma, 1420 AH, juzu'i na 6, shafi na 369; Juzu'i na 12, shafi na 376; Juzu'i na 13, shafi na 379; Al-Bayhaqi, Dala'ilul Annubuwati, 1405 AH, Mujalladi na 5, shafi na 174; Al-Balazari, Fatuh al-Buldan, 1988, shafi na 48.
  24. Waqidi, Al-Maghazi, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 900-901; Al-Tabari, Tarikh Al-umam wa Al-muluk 1387 Hijira, Juzu’i na 3, shafi na 75-76.
  25. «شرح لبیک یا حسین بخش اول: نوشتاری از استاد هادی سروش»، شفقنا.
  26. Ibn Qolwayh, Kamel al-Ziyarat, 1356, shafi na 230.
  27. Ibn Tawoos, Iqbal al-Amal, 1409 AH, Juzu'i na 2, shafi na 713-714; Al-Shaheed al-Awl, al-Mazar, 1410 AH, shafi na 142.
  28. Ibn Mashhadi, Al-Mazar al-Kabir, 1419 AH, shafi na 666-663; Kafami, al-Misbah, 1405 AH, shafi na 552-550.
  29. Al-Farahidi, Kitab al-Ain, 1410 AH, juzu'i na 8, shafi na 341.
  30. Al-Azhari, Tahdeeb al-Legha, Beirut, juzu'i na 15, shafi na 242.
  31. Al-Azhari, Tahdeeb al-Legha, Beirut, juzu'i na 15, shafi na 242.
  32. Al-Johari, Al-Sahah, Beirut, Juzu'i na 1, shafi na 216; Sahib bin Abbad, Al-Asha'at fi al-Lagha, 1414 AH, juzu'i na 10, shafi na 312.
  33. Al-Shaheed al-Thani, Masalak al-Afham, 1416 AH, juzu'i na 2, shafi na 226; Al-Fadel al-Hindi, Kasf al-Latham, 1416 AH, juzu'i na 5, shafi na 20; Al-Najafi Javaher Kalam, 1362, juzu'i na 18, shafi na 3-4.
  34. «بی‎‌توجهی جامعه بین‌‎المللی به نقض حقوق‎ بشری شیعیان نیجریه»، وكالة میزان.
  35. Badel, "Sharayiɗ dini wa mazhabi kishware Turkiyye", shafi na 298.
  36. «دسته‌های عزای عاشورایی در سراسر لبنان»، الکوثر.
  37. «اجتماع عظیم اردبیلی‌ها در روز تاسوعا با شعار لبیک یا حسین»، خبرآنلاین.
  38. «شعار لبیک یا حسین(ع) و لبیک یا خامنه‌ای در لاهه هلند»، خبرنامه دانشجویان ایران.
  39. «دسته طویریج دسته‌ای به بلندای چهارده قرن»، خبرآنلاین.
  40. «فریاد "لبیک یا حسین" زنان قبیله بنی‌اسد در حرم سیدالشهدا طنین‌انداز شد»، وكالة مهر.
  41. «لبیک یا حسین موجب ماندگاری گفتمان عاشورایی است»، وكالة رضوی.
  42. تعویض پرچم گنبدحرمهای کربلا. وكالة مهر.
  43. پرچم لبیک یا حسین در بین الحرمین. وكالة مهر.
  44. Shabar, Adab al-Taf, juzu'i na 1, shafi na 130
  45. «لبیک یا حسین جدیدترین اثر حاج صادق آهنگران»، رجانیوز.
  46. «فراخوان رقابتی حروف نگاری لبیک یا حسین»، کانون هنری شیعی.
  47. "لبيك يا حسين" بعد فتاوى الجهاد الكفائي في حرم ابي الفضل العباس عليه السلام، موقع يويتوب.
  48. «نام عملیات از "لبیک یا حسین" به "لبیک یا عراق" تغییر کرد»، وكالة جمهور.
  49. «تشییع پیکر شهید حاج قاسم سلیمانی در مشهد»، افکار نیوز.
  50. «صحن اباعبدالله؛ لبیک یا حسین در هنگام ورود پیکر شهدا»، راسخون.
  51. «طنین شعار لبیک یا حسین(ع) در مراسم تشییع شهید «علی یوسف علاء الدین» از رزمندگان حزب‌الله» وكالة دانشجو.
  52. تحرير اكثر من ألف كم مربع بعمليات لبيك يا رسول الله 2، موقع قناة العالم.
  53. هنا النجف؛ صوت يتعالى إلى عنان العرش " لبيك يا حيدر الكرار "، وكالة تسنيم.
  54. أصداء ثورة الامام الخميني تصدح في أرض المقاومة، وكالة ارنا

Nassoshi

  • Ibn Mashhadi, Muhammad bin Jaafar, Al-Mazar Al-Kabir, Kum, Jami'ar Modarresin, 1419H.
  • Ibn Nama al-Hilli, Musirul Ahzan, Qum, Makarantar Imamul Mahdi, 1406H.
  • Ibn Saad, Muhammad, Tabakatul kubra, wanda: Muhammad Abd al-Qadir Atta, Beirut, Darul Kutub al-Ilmiyya ya buga, 1410H.