Na'im Ƙasim
| Daga cikin jagororin Hizbullahi Lubnan | |
|---|---|
| Tarihin Haihuwa | 1953m |
| Wurin Haihuwa | Kafarfila |
| Mazhaba | Shi'a |
| Aiki | Malamin addini/Ɗan siyasa |
| Muƙamai | Babban Sakataren Hizbullahi Lubnan |
| Rubuce-rubuce | Hizbullahi Lubnan Khaɗɗi Mashyi, Guazashte Wa Ayaende An, Al-Imam Al-Khomaini Bainal Asalai Wat Tajdid, Alwailyul Al-Mujaddid da sauransu.... |
| Adireshin Mai Lasisi | https://naimkassem.com.lb/index.php |
Na'im Ƙasim wanda ka fi sani da Shaik Na'im Ƙasim, (Larabci: نعیم قاسم ) an haife shi 1953m, na huɗu cikin jerin manyan sakatarorin Hizbullahi Lubnan.
A lokacin shugabancin Sayyid Abbas Musawi da Sayyid Hassan Nasrullah ya kasance mataimakin babban sakatare, bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrullah sai aka zaɓe shi matsayin babban sakataren ƙungiyar Hizbullahi Lubnan. A baya can ya kasance memba a Harkatu Amal, kuma ya taka muhimmiyar rawa shi da Imam Musa Sadar cikin kafa Harkatu Mahrumin (Ƙungiyar taimakon marasa galihu). Har ila yau, ya kasance cikin mutanen da suka kafa ƙungiyar Hizbullahi Lubnan, a shekarar 1991m ya kasance mataimakin shugaban wannan ƙungiya.
Na'im Ƙasim ya kasance shugaban majalisar shura ta ƴan majalisar Hizbullah kuma shugaban haɗin kan ministoci makusanta da Hizbullah a daular Labanun. Ya kasance mutum da ya yi imani da nazariyyar wilayatul faƙihi, ya wallafa litattafai guda biyu game da Imam Khomaini da Sayyid Ali Khamna'i, jagororin jamhuriyar Muslunci ta Iran.
Tarihin Rayuwa
An haifi Na'im Ƙasim a shekarar 1953m, a wani ƙauye da ake kira da sunan Kafrufila a jihar Nabɗiyya da yake kudancin Labanun..[1] Ya kware cikin harshen Faransanci. A shekarar 1970 ya samu shaidar digiri na ɗaya cikin fannin sanin sinadarai da azalai (Chemistry), a fannin ilimin addini kuma ya kasance ɗalibin Sayyid Muhammad Husaini Fadlullah..[2]
Babban Sakataren Hizbullahi Lubnan
Ƙungiyar Hizbullah Lubnan a ranar 29 Oktoba 2024m, kusan wata guda bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrullah, ta naɗa Na'im Ƙasim matsayin babban sakatare, da wannan ne ya zama mutum na uku a wannan maƙami.[3] Na'im Ƙasim kafin wannan muƙami ya kasance shugaban majalisar shura ta ƴan majalisar Labanun daga ƙungiyar Hizbullah, kuma shi ne mai kula da alaƙoƙi tsakanin ministoci masu kusanci da Hizbullah a cikin daular Labanun.[4]
A shekarar 1982m, tare da Sayyid Abbas Musawi, Subhi Ɗufaili, Muhammad Yazbek, Ibrahim Amin Sayyid da Sayyid Hassan Nasrullah sun taka muhimmiyar rawa cikin kafa ƙungiyar Hizbullah, sannan a shekarar 1991m, ya kasance mataimakin shugaban wannan ƙuniya.[5]
Muhimmiyar Rawa Cikin Kafa Ƙungiyar Marasa Galihu
Na'im ƙasim ya fara hakar siyasa daga shekarar 1970m, cikin Harkatu Amal ƙarƙashin jagorancin Imam Musa Sadar, kamar dai yadda ya yi bayanin hakan da bakinsa, haka nan cikin kafa Harkatul Mahrumin (Ƙungiyar taimakon marasa galihu) ya taka muhimmiyar rawa..[6] Har ila yau, ya kasance shugaban saƙafa a cikin ƙungiyar Harkatu Amal, sannan bayan ɓatan Sayyid Musa Sadar sai ya fice daga ƙungiyar Harkatu Amal..[7]
Imani Da Wilayatul Faƙihi Da Kuma Alaƙa Da Iran

Kamar dai yadda Shafin yanar gizo na Na'im ƙasim ya bayyana, haƙiƙa ya yi imani da nazariyyar wilayatul faƙihi, ma'ana ya yi imani da wilayar Sayyid Ali Khamna'i bayan Imam Khomaini, ya kuma wallafa littafi kan ko wane ɗaya daga cikin mutane biyun.ref>«السیرة الذاتیة»، Shafin yanar gizo na Shaik Na'im Qaseem.</ref>
A lokacin da Sayyid Ali Khamna'i ya yi rashin lafiya har ta kai ga kwanciyar a asibiti, Shaik Na'im ƙasim wanda a daidai wannan lokaci ya je ƙasar Iran domin babban taron malaman Muslunci domin goyan bayan Falasɗinu, ya yi amfani da wannan dama inda shi da rakiyar malaman Muslunci suka je dubiyar Sayyid Ali Khamna'i a asibin da aka kwantar da shi.[8]
Na'im ƙasim, daɗi kan haka, ya yi tarayya a cikin mafi yawancin manyan tarurruka da aka yi a Iran, daga jumlarsu tarurrukan Majma Jahani Ahlul-Baiti (Majalisar Ahlul-Baiti Ta Duniya), Majma Taƙrib Mazahib, tarurrukan haɗin kai na Muslunci, da babban taron ranar ƙudus ta duniya.[9]
Wakilin Ayatullahi Khamna'i
Bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrullah, Ayatullahi Khamna'i cikin wani hukunci da ya fitar, ya naɗa Shaik Na'im ƙasim matsayin wakilinsa a ƙasar Labanun.[10]
Wallafe-wallafe
Shaik Na'im Ƙasim ya kasance marubuci, a fagen haƙƙoƙin fararen hula, yanayin mata, yanayin malamai, yanayin ɗaliban firamare da sakandire, haƙƙoƙin maza da mata, nauyin da yake wuyan iyaye dangane da ƴaƴansu da…[11] Ya rubuta littafin “Al-Imam Khomaini Bainal Asalati Wat Tajdid” game da Imam Khomaini da kuma littafin “Al-waliyyul Al-Mujaddid” game da Sayyid Ali Khamna'i.[12] Har Ila yau, ɗaya daga cikin wallafe-wallafensa akwai wani litttafi wanda da harshen Farsi ake masa suna (Hizbullahi Lubnan; Khaɗɗi Mashyi, Guzashte Wa Ayande An) wanda a shekarar 2002m ya rubuta shi, zuwa yanzu an tarjama wannan littafi da harshen Farsi, Ingilishi, Faransanci, Turkanci, Urdu da Indunusiya.[13] Sauran rubuce-rubucensa sun kasance kamar haka:

- Sabilullahi
- Al-ƙur'an Wa Minhajul Hidaya
- Mujtama'ul Muƙawama
- Almahdi Almukhallis
- Al-Shab Shu'ulatu Tahraƙu Au Tuzi'u
- Ƙissati Ma'al Hijab
- Sabiluka Ila Makarimil Akhlaƙ
- Hizbullahi… Al-minhaj.. Attajriba.. Al-Mustaƙbal
- Fi Rihab Risalatil Huƙuƙ
- Sharhu Risalatul Huƙuƙ Imam Zainul Abidin Alaihis Salam
- Huƙuƙun Nasi
- Al-Huƙuƙus Salasa
- Huƙuƙul Al-Mu'allim Wal Muta'allim
- Huƙuƙuz Zauji Waz Zauja
- Huƙuƙul Af'al
- Huƙuƙul Walidaini Wal Walad
- Huƙuƙul Jawarihi
- Ashura Madad Wa Hayat
- Ma'alim Lil Hayat Min Nahji Amiril Muminin Alaihis Salam.[14]
Bayanin kula
- ↑ «Naim Qassem»Shafin yanar gizo na Hizbullahi Lubnan
- ↑ «Naim Qassem»، Shafin yanar gizo na Hizbullahi Lubnan
- ↑ «إنتخاب سماحة الشيخ نعيم قاسم أمينًا عامًّا لحزب الله»،Al-Manar
- ↑ «السیرة الذاتیة»،Shafin yanar gizo na Sheikh Na’im Qasse.
- ↑ «Naim Qassem»، Shafin yanar gizo na Hizbullahi.
- ↑ «Naim Qassem»، Shafin yanar gizo na Hizbullahi.
- ↑ «السیرة الذاتیة»، Shafin yanar gizo na Shaik Na'im Qaseem.
- ↑ «روایت جانشین سیدحسن نصرالله از عیادت رهبر انقلاب»،Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Bayt (ABNA).
- ↑ «السیرة الذاتیة»،Shafin yanar gizo na Shaik Na'im Qaseem.
- ↑ شیخ نعیم قاسم نمایندهٔ رهبر انقلاب در لبنان شد، Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr.
- ↑ «السیرة الذاتیة»،Shafin yanar gizo na Shaik Na'im Qaseem.
- ↑ «السیرة الذاتیة»،،Shafin yanar gizo na Shaik Na'im Qaseem..
- ↑ «حزبالله لبنان؛ خطمشی، گذشته و آیندۀ آنShafin yanar gizo na Adinebook.
- ↑ «السیرة الذاتیة»،،Shafin yanar gizo na Shaik Na'im Qaseem..
Nassoshi
- «إنتخاب سماحة الشيخ نعيم قاسم أمينًا عامًّا لحزب الله»، Tashar Al-Manar, ranar da aka wallafa labari: 29 Oktoba 2024 Miladiyya
- «Naim Qassem»،Shafin yanar gizo na Hizbullah, ranar ziyara: 12 ga watan Mehr na shekarar 1403 Hijira Shamsiyya.
- «السیرة الذاتیة»، Shafin yanar gizo na Na'im Qassem, ranar ziyara: 12 ga watan Mehr shekarar 1403 Hijira Shamsiyya
- «روایت جانشین سیدحسن نصرالله از عیادت رهبر انقلاب»، Kamfanin labarai na ABNA, ranar wallafa: 21 Shahrivar 1393 Hijira Shamsiyya, ranar ziyara: 12 Mehr 1403 Hijira Shamsiyy
- «حزبالله لبنان؛ خطمشی، گذشته و آیندۀ آن»،Shafin AdineBook, ranar ziyara: 12 Mehr 1403 H-Sh."
- شیخ نعیم قاسم نمایندهٔ رهبر انقلاب در لبنان شد،Kamfanin labarai na Mehr, ranar da aka wallafa labarin: 17 Bahman 1403 shamsi/2024 miladiyya