Isma'il Haniyye

Daga wikishia
Wannan ƙasida ko kuma wani ɓangare daga cikinta ƙasida da ce da ta ƙunshi wani abu da ya faru a wata rana.

Isma'il haniyye (Larabci: إسماعيل عبد السلام أحمد هنية) (Haihuwa: 1963, Rasuwa:2024) ya kasance shugaban ɓangaren siyasa a ƙungiyar gwagwarmayar kwaton yanci ta hamas wanda haramtacciyar ƙasar Isra'ila ta kashe shi a birnin Tehrean na ƙasar Iran.

Haniyye ya kasance ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar gwagwarmayar muslunci gaban mamayar garuruwan palasɗinu, ya yi tsaya kyam yana mai fafutika da gwagwarmaya har numfashinsa na ƙarshe yana mai ƙalubalantar sahayoniyanci, Haniyye ya zauna a fursun na ƴan mamaya a lokuta da dama, a shekarar 1992 miladi an kore shi zuwa kudancin ƙasar labanun.

Kisan gilla da Isra'ila ta yi kansa a Tehran ya haifar da martani daban-daban daga sassan duniya, ɗaiɗaikun fitattun mutane da ƙungiyoyin siyasa da na addini sun yi Allah wadai da wannan ta'addanci da Isra'ila ta aikata. Musulmai daga ƙasashe daban-daban daga sassan duniya sun shirya jerin gwano don nuna rashin amincewa kan wannan ta'addanci na kashe Haniyye, a ranar 31 ga watan August ne akayi jana'izarsa a birnin Tehran, washegari kuma aka kaishi ƙasar ƙatar inda suka sake masa sallar gawa tare da binne shi a can.

Shugaban ofishin siyasa na ƙungiyar hamas, tun daga shekarar 2017 zuwa 2024 shi ne ya kasance Firaminstan hukumomin ƴan sakai na ƙasar palasɗinu, shugabantar jami'ar muslunci ta gaza da shugabancin ofishin Shaik Ahmad Yasin suna daga cikin ofishoshi da suka kasance ƙarƙashin jagorancinsa, haƙiƙa ya samu matsayin na girmamawa daga kasancewa wata alama a fagen gwagwarmayar kwato ƴanci da kuma laƙabin shahidin ƙudus.

Ɗauki Ba Daɗi Tare da ƴan Mamayar Isra'ila

Isma'il Haniyye ya kasance daga cikin jagororin gwagwarmayar muslunci ta palasɗinu, ana masa laƙabi da alamin gwagwarmayar palasɗinu[1] da kuma shahidin ƙudus,[2] Isma'il Haniyye ya a lokuta da dama ya zauna a fursun ɗin Isra'ila, daga jumlarsu a shekarar 1989 inda aka ɗaure shi tsawon shekaru uku.[3]a shekarar 1992 nan ma tare da wasu adadi membobin ƙungiyar hamas da jihadul islami an kore shi tsawon shekara ɗaya zuwa garin marju zuhur da yake a kudancin ƙasar Labanun.[4] ƴaƴan Haniyye guda uku da jikokinsa guda uku duk Isra'ila ta kashe su lokacin hare-harenta a zirin gaza a ranar 10 ga watan April 2024 miladi.[5]

Isma'il Haniyye
Har abada ba za mu taɓa yarda da halascin hukuma Isra'ila ba

[6]

Jagorancin Ofishin Siyasa Na ƙungiyar Hamas

Isma'ail Haniyye tun daga ranar 6 ga watan May shekarar 2017 bayan Khalid Mash'al ya fara jagorantar Ofsihin harkokin siyasa na hamas.[7] gabanin haka bayan samun nasara a zaɓen da ya gudana a palasɗinu a shekarar 2006 miladi, ya samu muƙamin firaministan ƙungiyoyi masu zaman kansu na palasɗinu; sai dai kuma a watan June shekarar 2007 miladi, Mahmud Abbas ya cire shi daga wannan muƙami na firaministan ƙungiyoyin palasɗinu masu zaman kansu.[8] haka nan tsawon lokaci ya kasance shugaban ofishin siyasa na Shaik Ahmad Yasin.[9] A shekarar 2018 miladi ƙasar Amurka ta sanya sunan Isma'il cikin jerin ƴan ta'adda.[10] a cikin shekarun ƙarshen rayuwarsa ya zaune a ƙasar ƙatar.[11]

Alaƙarsa Tare Da Mihwarin Gwagwarnmaya

Isma'il Haniyye tsawon tarihin gwagwarmayarsa da ayyukansa na siyasa tare da jagororin gwagwarmaya ya kasance yana bada haɗin kai ga mihwarin muƙawama. Lokuta da daman gaske ya je ƙasar Iran tare da ganawa da manya-manyan jagororin ƙasar daga cikinsu har da Ayatullahi Khamna'i..[12] ya je Iran lokutan jana'izar Ƙasim Sulaimani babban kwamandan dakarun ƙudus sipa pasidaran,[13]da lokacin jana'izar Sayyid Ibrahim Ra'isi, shugaban ƙasar Iran na takwas.[14] haka nan ya gana da Sayyid Hassan Nasrullahi babban sakataren ƙungiyar Hizbullahi,[14] sannan kuma suna aiki tare.[15]

Isma'il Haniyye Tare da wasu Adadin `Yan gwagwarmaya zaku iya ganin Hassan Nasrullahi

Kisan gilla da Isra'ila ta yi kan Haniyye a ƙasar Iran, ya haifar da saƙonni daban-daban, ba'arin masu nazari da kuma fashin baƙi suna ganin cewa Isra'ila ta yanke shawarar kashe shi ne sakamakon ci gaban da taka ƙungiyoyin gwagwarmaya suna samu ta hanyar haɗa kawukansu da ɗinke ɓarakar da take tsakaninsu, wanda hakan babbar baraza ne ga samuwar Isra'ila.[16]

Ta'addancin Kisan Gilla

Jana'izar Isma'il Haniyye A Babban Birnin Tehran Ranar 1 Ga Watan August

Isma'il Haniyye a ranar 31 ga watan August 2024 miladiya aka masa kisan gilla a masaukinsa da yake babban birnin Tehran a ƙasar Iran.[17] ya je ƙasar Iran domin taron bikinn rantsar da sabon shugaban zaɓaɓɓen ƙasa..[18] ƙungiyar hamas[19] da ma'aikatar harkokin ƙasar waje ta Iran[20] sun danganta ta'addanci kisan Haniyye kan gwamnatin sahayoniyawa ta Isra'ila. Gwamnatin sahayoniya cikin bayanin da suka fitar sun ɗauki alhakin aikata wannan ta'addanci.[21] Isra'ila a shekarar 2003 miladi da shekarar 2006 miladi sun yi yunƙurin hallaka Isma'il Haniyye ta hanyar kai hare-haren bama-bamai daga jirgin sama a kansa. Sai dai cewa ya tsallake rijiya da baya Allah ya kuɓutar da shi.[22]

Jan'aizar Haniyye A Tehran Da ƙasar Ƙatar

Sallar Jan'izar Isma'il Haniyye Da Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i Ya Jagoranta

Ayatullahi Khamna'i jagoran juyin juya halin muslunci na Iran, a ranar 1 ga watan ugusta a babban birnin tehran ya jagoranci sallar jana'iza kan Isma'il Haniyye..[23] washegari a ranar 2 ga watanb ugusta ne aaka kai jana'izarsa babban birnin doha na ƙasar ƙatar, cikin halartar gayyar jama'a daga fitattun ƴan siyasa da addini misalin sarkin ƙatar an yi jana'izarsa da binne a garin lusaili da yake kusa da babban birnin doha.[24]jagorancin sallar jana'izar Isma'il haniyye ahlus-sunna ɗan gwagwarmaya da Ayatullahi Sayyid Ali Khamna'i ya yi matsayinsa jagoran jamhuriyar muslunci ta Iran, kuma marja'in taƙlidi a duniyar ƴan shi'a ya jawo hankalin kafafe watsa labarai na duniya,[25] dandalin sada zumunta.[26]

Sayyid Ali Khamna'i, Jagoran Jamhuriyar Muslunci ta Iran
Jarumi kuma fitaccen mujahidi Falastin Isma'il haniyye a asubahin yau ya amsa kiran Allah, babbar kungiyar gwagwarmaya ta shiga zaman makoki, shahid haniyye tsawon shekaru ya sadaukar da rayuwarsa a fagen dauki ba dadi da kuma gwagwarmaya, ya shiryawa shahada, ya sadaukar iyalansa kan wannan hanya, hakika ya kasance bashi da kowanne irin tsoro cikin hanyar shahada a tafarkin Allah domin ceton bayin Allah daga zalunci yan mamaya.

[27]

Martani

Kisan ta'addanci kan Haniyye ya haifar da martani daban-daban masu tarin yawa daga ɓangaren jagororin siyasa da addini, Sayyid Ali Khamna'i jagoran jamhuriyar muslunci ta Iran.[28] Nuri Hamadani,[29] Nasir Makarim shirazi,[30] da Abdullahi Jawadi Amoli[31] daga maraji'an taƙlidi na shi'a sun aiko da saƙon ta'aziyya kan Isma'il hanbiyye . shugaban ƙasar turkiyya,[32] ƙungiyoyin gwagwarmayar muslunci misalin Hizbullahi lubnan, ƙungiyar Asarullahi Yaman, ƙungiyar jihadul islami ta palasɗinu, firaministan ƙasar lubnan, ministocin harkokin waje na ƙasashen misalin Sin, Turkiya, Rasha, Siriya, ƙatar, Jodan, Misra, Iraƙi, Pakistan da Oman, ƙungiyoyi masu zaman kansu na palasɗinu, ƙungiyar fatahu, hikmat milli iraƙi, ikhwanul muslimin a ƙasar jodan dukkaninsu sun Allah wadai da kisan ta'addanci kan Isma'il Haniyye da Sahayoniya suka aikata.[33] ministocin harkokin waje na ba'arin ƙasashe misalin Iraƙi,[34] Oman da Jodan sun bayyana kisan Haniyye matsayin take dokokin majalisar ɗinkin duniya kuma wata barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin gabas ta tsakiya.[35]

Al'ummar ƙasashe daban-daban misalin Yaman,[36] Jodan,[37] Turkiyya, Maroko, Tunisiya da labanun,[38] sun jerin gwano domin nuna Allah wadai da kisan Isma'il Haniyye, a ƙasar Iran da Yaman an shelanta zaman makokin bakiɗayan ƙasa na kwanaki uku[39] a Palasɗinu kuma kwana ɗaya.[40] haka kuma a masallacin jamkaran da yake birnin ƙum mai tsarki ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin addini, a saman ƙubbar wannan masallaci an ɗaura jar tutar ɗauke da rubutun ya lasarat husaini, wanda wata alama ce ta ɗaukar fansa.[41] Bayan samun labarin kisan ta'addanci Isma'il Haniyye, majalisar tsaro ta majalisar ɗinkin duniya ta kira taron gaggawa, ba'arin membobin wannan majalisi sun yi Allah wadai da kisan Haniyye.[42]

Zanga-zangar Allah wadai da kisan Isma'il Haniyya a kasar Turkiyya

Alƙawarin ɗaukar Fansar Jininsa

Ayatullahi Khamna'i cikin saƙon ta'aziyya da ya fitar tare da ishara kan kasancewa yin wannan ta'addanci a ƙasar Iran, ya bayyana cewa ɗaukar fansar jinin Haniyye wata wazifa ce da take wuyan ƙasare Iran, ya kuma bayyana cewa hukunci mai tsanani yana nan yana jiran ƴan ta'addan da suka aikata ta'addancin kashe Haniyye.[43] Sayyid Hassan Nasrullahi[44]da Dakarun ƙudus[45] su ma tare da Allah wadai kan kisan Haniyya da Isra'ila ta yi, sun shelanta cewa tabbas z asu bada amsa mafi tsanini kan wannan ta'addanci. Haka kuma ƙungiyar Hamas tare da bayyana cewa wannan ta'addanci aiki ne na matsorata, sun shelanta cewa tabbas za su bada amsa.[46]

Karatu Da Jagoranci

An haifi Isma'il Abdus-salam Ahmad wanda aka fi sani da Haniyye wanda ake yiwa laƙabi da Abul-Abdi a ranar 23[47] ko 29[48] ga watan June 1962[49] ko 1963 miladi[50] a sansanin ƴan gudun hijira na Alshaɗi da yake zirin gaza. A wannan sansani ne ya kammala karatun firamare da sakandire, bayan nan ya shiga jami'ar gaza.[51] a shekarar 1987 miladi ya kammala karatun digirinsa na farko a fannin adabin harshen larabci.ref>«اسماعیل هنیه که بود؟»، خبرگزاری ایسنا.</ref> bayan nan ya jagoranci muƙamai daban-daban daga misalin: babban sakataren kwamitin amintattu na jami'ar muslunci ta gaza, daraktan ilimi na jami'ar muslunci a gaza, memba a kwamitin jam'iyyar muslunci a gaza, shugaban ƙungiyar jamai'ar muslunci a gaza har tsawon shekara goma.[52] shugabancin jami'ar muslunci a gaza.[53]

Bayanin kula

  1. برای نمونه نگاه کنید به: «فیدان: هنیه نماد مقاومت فلسطین بود»، خبرگزاری آناتولی؛ «اسماعیل هنیه؛ رهبری که نماد مقاومت سیاسی و نظامی فلسطین بود»، خبرگزاری مهر.
  2. برای نمونه نگاه کنید به: «مراسم گرامیداشت شهید القدس اسماعیل هنیه»، خبرگزاری جمهوری اسلامی؛ «پیمان جبهه مقاومت از تهران تا غزه: انتقام خون شهید القدس قطعی است»، خبرگزاری مهر؛ «پیکر شهید القدس در خانه ابدی آرام گرفت»،‌ خبرگزاری مشرق نیوز.
  3. «گزارش‌ها از ترور اسماعیل هنیه رهبر سیاسی حماس در تهران»، سایت بی‌بی‌سی فارسی؛ «إسماعيل هنية.. لاجئ من مخيم الشاطئ قاد حركة حماس»، الجزیرة نت.
  4. «اسماعیل هنیه ملقب به ابوالعبد که بود؟»، خبرگزاری مهر؛ «اسماعیل هنیه که بود؟»، خبرگزاری ایسنا.
  5. «اسماعیل هنیه که بود؟»، خبرگزاری ایسنا.
  6. «اسماعیل هنیه که بود؟»، خبرگزاری العالم.
  7. «اسماعیل هنیه ملقب به ابوالعبد که بود؟»، خبرگزاری مهر؛ «گروه اسلامگرای حماس چیست؟»، بی‌بی‌سی فارسی؛ «إسماعيل هنية.. لاجئ من مخيم الشاطئ قاد حركة حماس»، الجزیرة نت.
  8. «إسماعيل هنية.. لاجئ من مخيم الشاطئ قاد حركة حماس»، الجزیرة نت؛ «نگاهی به زندگی و اقدامات شهید اسماعیل هنیه»، خبرگزاری تسنیم.
  9. «اسماعیل هنیه ملقب به ابوالعبد که بود؟»، خبرگزاری مهر.
  10. «گزارش‌ها از ترور اسماعیل هنیه رهبر سیاسی حماس در تهران»، سایت بی‌بی‌سی فارسی؛ «إسماعيل هنية.. لاجئ من مخيم الشاطئ قاد حركة حماس»، الجزیرة نت.
  11. «گزارش‌ها از ترور اسماعیل هنیه رهبر سیاسی حماس در تهران»، سایت بی‌بی‌سی فارسی.
  12. برای نمونه نگاه کنید به: «دیدار اسماعیل هنیه رئیس دفتر سیاسی حماس با رهبر انقلاب»، دفتر حفظ و نشر آثار آیت‌الله خامنه‌ای؛ «دیدار نخست وزیر فلسطین و هیأت همراه با رهبر انقلاب»، دفتر حفظ و نشر آثار آیت‌الله خامنه‌ای.
  13. «إسماعيل هنية: قاسم سليماني “شهيد القدس»، الجزیره مباشر.
  14. «حضور اسماعیل هنیه در مراسم تشییع پیکر رئیس جمهور»، خبرگزاری تسنیم.
  15. برای نمونه نگاه کنید به: «سید حسن نصرالله با هنیه در بیروت دیدار کرد»، خبرگزاری مهر؛ «سید حسن نصرالله و اسماعیل هنیه دیدار کردند»، خبرگزاری تسنیم.
  16. «پس از ترور شهید «هنیه»، جبهه مقاومت وارد مرحله تعیین‌کننده‌ای شد»، خبرگزاری مهر.
  17. «اسماعیل هنیه در تهران کشته شد»، خبرگزاری آناتولی.
  18. name=":0">«اسماعیل هنیه در تهران کشته شد»، خبرگزاری آناتولی.
  19. «بیانیه حماس در پی شهادت اسماعیل هنیه»، خبرگزاری العالم.
  20. «بیانیه وزرات امور خارجه جمهوری اسلامی ایران در خصوص شهادت رییس دفتر سیاسی جنبش مقاوت اسلامی فلسطین»، سایت وزارت امور خارجه جمهوری اسلامی ایران.
  21. «در پی شهادت اسماعیل هنیه، ۳ روز عزای عمومی در کشور اعلام شد»، خبرگزاری مهر.
  22. «إسماعيل هنية.. لاجئ من مخيم الشاطئ قاد حركة حماس»، الجزیرة نت؛ «اسماعیل هنیه که بود؟»، خبرگزاری ایسنا.
  23. «مراسم تشییع جنازه اسماعیل هنیه رئیس دفتر سیاسی حماس در تهران برگزار شد»، خبرگزاری آناتولی؛ «گزارش ایسنا از تشییع پیکر اسماعیل شهید در تهران»، خبرگزاری ایسنا.
  24. «اسماعیل هنیه در قطر به خاک سپرده شد»، یورونیوز.
  25. برای نمونه نگاه کنید به «بدرقه ایرانی هنیه»، جوان آنلاین.
  26. «واکنش کاربران مجازی به تشییع پیکر شهید اسماعیل هنیه در ایران»، باشگاه خبرنگاران جوان.
  27. «پیام رهبر انقلاب اسلامی در پی شهادت مجاهد بزرگ آقای اسماعیل هنیه»، دفتر حفظ و نشر آثار آیت‌الله خامنه‌ای.
  28. «پیام رهبر انقلاب اسلامی در پی شهادت مجاهد بزرگ آقای اسماعیل هنیه»، دفتر حفظ و نشر آثار آیت‌الله خامنه‌ای.
  29. «آیت‌الله نوری همدانی: شهادت هنیه راه محو رژیم صهیونیستی را هموار خواهد کرد»، خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  30. «واکنش آیت‌الله مکارم شیرازی به ترور هنیه؛ دشمن کینه‌توز را به اشد مجازات برسانید»،‌ خبرگزاری جمهوری اسلامی.
  31. «پیام یک مرجع تقلید در واکنش به ترور شهید هنیه در تهران»، همشهری آنلاین.
  32. «اردوغان ترور اسماعیل هنیه در تهران را به شدت محکوم کرد»، خبرگزاری آناتولی.
  33. «واکنش‌ها به شهادت اسماعیل هنیه»، خبرگزاری ایسنا؛ «در پی شهادت اسماعیل هنیه، ۳ روز عزای عمومی در کشور اعلام شد»، خبرگزاری مهر.
  34. «العراق: اغتیال هنیة فی ایران عملیة عدوانیة و تهدید لاستقرار المنطقة»، الفرات نیوز.
  35. «واکنش‌های بین‌المللی به ترور شهید هنیه در تهران»، خبرگزاری فارس.
  36. «اجتماع مردم یمن در محکومیت ترور اسماعیل هنیه»، خبرگزاری العالم.
  37. «تظاهرات گسترده در اردن در محکومیت ترور هنیه»، خبرگزاری العالم.
  38. «اغتيال هنية.. غضب ومظاهرات بعدة دول ودعوة لطرد السفير الأميركي»، الجزیره نت.
  39. «در پی شهادت اسماعیل هنیه، ۳ روز عزای عمومی در کشور اعلام شد»، خبرگزاری مهر.
  40. «محمود عباس یک روز عزای عمومی اعلام کرد»، خبرگزاری تسنیم.
  41. «اهتزاز پرچم سرخ انتقام برفراز گنبد فیروزه ای جمکران»، خبرگزاری مهر.
  42. «برخی از اعضای شورای امنیت ترور هنیه را محکوم کردند»، خبرگزاری آناتولی.
  43. «پیام رهبر انقلاب اسلامی در پی شهادت مجاهد بزرگ آقای اسماعیل هنیه»، دفتر حفظ و نشر آثار آیت‌الله خامنه‌ای.
  44. «سید حسن نصرالله: ایران ترور هنیه را خدشه به امنیت و حاکمیت خود می‌داند»، خبرگزاری العالم.
  45. «اطلاعیه جدید سپاه: پاسخ سخت و دردناک مقاومت در راه است»، خبرگزاری فارس.
  46. «واکنش‌ها به شهادت اسماعیل هنیه»، خبرگزاری ایسنا.
  47. «إسماعيل هنية.. لاجئ من مخيم الشاطئ قاد حركة حماس»، الجزیرة نت.
  48. «اسماعیل هنیه ملقب به ابوالعبد که بود؟»، خبرگزاری مهر؛ «اسماعیل هنیه که بود؟»، خبرگزاری العالم.
  49. «اسماعیل هنیه که بود؟»، خبرگزاری ایسنا.
  50. «اسماعیل هنیه ملقب به ابوالعبد که بود؟»، خبرگزاری مهر؛ «اسماعیل هنیه که بود؟»، خبرگزاری العالم.
  51. «اسماعیل هنیه که بود؟»، خبرگزاری العالم.
  52. «اسماعیل هنیه ملقب به ابوالعبد که بود؟»، خبرگزاری مهر.
  53. «اسماعیل هنیه که بود؟»، خبرگزاری ایسنا.

Nassoshi